Showing 18001 words to 21000 words out of 108894 words

Chapter 7 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

14

Middle Ads

office room dinsa na cikin gidan inda A Abdoul ke jiransa da tarin bayanansa
Yana shigowa kuwa A Abdoul din ya miqe Yana Masa barka da fitowa kafin ya zauna Kan kujerar 1 seater dake facing din A Abdoul ya miqa hannu ya karba iPad din Dake hannun Abdoul din Yana duba bayanan.

Sai dare sosai ya fito ya ta kofar Dake palon qasan ya nufi sama ya Haye
Kai tsaye ya nufi bedroom dinsa.

Washe gari qarfe Tara an kammala komai na breakfast din gidan an jere sai qarfe goma yasauko sanye cikin Ash Kaftan na babban yadin Ambassador sai hular qube
Hannunsa sanye da agogon _Chanel_
Take qamshinsa ya gauraya palon kallo daya A Abdoul da M Sarat sukai Masa Suka sauke Kai ganin Mrs dinsa a gefensa sai wani Jan girma takeyi cikin nata adon.

Breakfast yayi tareda Ms Na'imah da A Abdoul kafin ya fito zuwa Inda zai gana da baqinsa.

Qarfe biyu yagama da baqinsa yadawo gida yayi lunch tareda Ms Na'imah kafin ya haye Bai fitoba sai qarfe hudu da rabi Ya sauko Kai tsaye suka shige mota zuwa airport dukkaninsu.

A jirgi ma hankalin Na'imah gabaki daya yakasa kwanciya Dan ita harga Allah ma rashin zuwan Turakin yafi Mata kwanciyar hankali akan zuwansa
Dan zuwansa kullum cikin sakata fargaba yake,
Kishinsa take sosai sbd bazaso akaro wadda zata tayata cin wannan dukiyarba.
#MAMUH#


👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇

Mamuhgee @Arewabooks

🔥🔥🔥🔥🔥
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261
[6/2, 11:20 PM] MG💋: *_Mamuhgee 11_*
Umma Jamila kasa nutsuwa tayi ta ringa addabar Haj Karima Saida suka sako Kawu saidu da Kira Kan Kira ya shiryo ya taho sbd matuqar ba yana garinba Turaki yazo yatafi to fa Babu wata maganar aure bayan sukam tuni suka hau Shirin aure gadan gadan batareda lissafin komaiba ko tunani irin na masu shekaru,

Koda Kawu saidun ya iso daga nijar ya sauka a dakin Abba sosai yashiga mamaki da takaicin ganin halinda Laylah ke ciki sbd shikam kallo daya yayi Mata bayan Sa'adah takawota sun gashesa ya fahimci batada isashiyar lafiya Dan kuwa ko dagowa ta kallesa bataiba kanta a qasa ta gaidasa.

Abinci kawai yaci yayi salloli ya wuce asibiti gurin Dan uwansa yabar gidan
Yana fita kuwa saiga Alhaji Atiku da Umma Jamila sunzo gurinsa Basu tarar dashiba Dole suka koma da niyar dawowa gobe Dan subarsa yau din ya huta.
A asibiti kuwa tunda yayi ido biyu da Dan uwansa take jikinsa yayi Sanyi Dan baiyi zaton Jikin yayi Munin hakanba take qwallar tausayi Dan uwa taciko idanuwansa ya hadiye Yana jinjina Kai Yana sauraron bayanin yanda Abban yaketa fama da jikin duk tsawon lokacin Nan daga Abdullahi...

Shiru Abdullahin yayi yanason sanarda kawun wasiyar Abban na bawa AB TURAKI auren Laylah ko bayan ransa Yana shakkar Shiga zancen sbd sanin maganace Mai girman gaske tunda aure ake magana
Auren Kuma da mutum kamar Turaki,
Shi daza'a basa auren Laylah dinma da wlh Yanaso ya karba.

A asibiti Kawu ya tarewarsa Bai sake komawa gidanba ya zauna jinyar Abban Abdullahi yasamu hutu duk da kullum da daddare saiya leqo asibitin kawowa Kawun abinci duk da Babu wata wata daga gidan umma Jamila ake kawo Masa abincin safe Rana dare Kuma abincin Alfarma lafiyayye Wanda tun Kawun Bai kawo tunanin komai aransaba yafara tunanin akwai dalilin hakan Dan Haka ya zuba musu ido yaringa cin abinda Dan yasan Umma Jamila batada Tausayin bawa Dan uwan Mahmoud ko abunda bataso matuqar ba babban daliline garesuba Mai matuqar mahimmanci.

Ganin dai Kawun baida niyar dawowa gida bare suzo ayi magana dashi yasa Suka yanke shawaran haduwa dashi a asibiti Dan Haka yau da daddare Yana zaune bayan yadawo daga masallacin asibitin sallar ishai yaci tuwon semo da miyar kubewa da gandar da aka kawo Masa tareda fruits
Gamawarsa kenan Yana kokarin amsa Kiran Mai dakinsa daya shigo wayarsa saiga Alhaji Qarami tareda Alhaji Atiku da umma Jamila sai Haj Karima data iso a jiya sunshigo sanye cikin shigar Alfarma,

Miqewa yayi cikin sakewar fuska Yana cewa"

Marabanku da zuwa,
Alhaji Qarami bismillah ku qaraso daga ciki,
Alhaji Atiku barka da zuwa
Sannunku sannunku
Yanzu da Daren Nan kuke shigowa.
Haj barkanku da zuwa Bismillah ku shigo,
Hannu ya miqa musu sukai msabaha Yana sake gaidasu cikin mutuntawa duk dai ya girmesu saidai kasancewarsu manyan mutane yasa shine yafara gaidasu din Suma cikin mutuntawa fuska asake suke gaidasa tareda maida kallonsu Kan Abba cikin alhini suke tambayar jikinsa,..

Allah yakawo sauki da afuwa yasa kaffarane.

Amin Amin ya Allah,

Alhaji Atiku Naga hidima anatayi damu
Allah ya Sanya alkhairi yabada Lada
Ana kokari sosai wlh
Ngd Sosai Haj Jamila.

Bakomai Kawu saidu ai duk yiwa Kaine musamman kaida kabaro iyali kazo nesa gashima bamu samu lokaci anyi maganar datai dalilin zuwan naka.

Gyara Basu gurin zama Kawun yayi Yana zama shima kafin ya nutsu Yana kallon Alhaji Atikun yace"

Eh wlh to nazo na tararda jikin na Mahmoud ba sauki ba sauyi shine hankalina duk ya koma kansa Amma ai tunda maganar aurece ba wata damuwa duk lokacinda magabatan yaron suka tsaida ranar zuwa sai a sanar Dani naje saimu taru a tattauna din....

Kallon Alhaji Qarami sukayi sbd shi Basu fada Masa ainihin gskiyar zancenba Dan bazai taba yarda da hakan ba
Haj Karima ta karbe zancen da cewa"

Aure Kam ai magana na hannunka Dan kaine Wanda zai tunkari Wanda aka bawa auren da maganar auren kasancewar Kaine tamkar uba agareta tunda Kaine tamkar uba ga mahaifin nata Dan Haka komai a hannunka yake.

Murmushi Kawu yayi Yana jinjina Kai yace"

Hakane,
Inshallah Allah wannan aiba wani matsala bane,
Auren ne manemin Bai tashiba kokuwa?sai anemesu muyi mgn dasu....

Alhaji Qarami ne ya gyara zama Kai tsaye cikin nutsuwa yace"

Alhaji Mahmoud ne kafin Allah ya sako Masa wannan jarabawa a kwanakin baya yabar wasiyar bada auren Sa'adah ga Aminsa AB TURAKI Wanda kasani,
To ita yarinyar yanzu akwai masu neman aurenta da har mun amince anbasu saigashi Kuma Haj Karima takirani akan a dakatar da waincan din sbd yarinya mahaifinta yariga yabada ita ga Amininsa shinefa Muka dakatar da waincan sbd Afaraji ga Turakin idan ya amsa shikenan sai adaura aure abawa waincan hakuri
Idanma akasin hakan aka samu kaga dai anfita haqqin wasiya sai abawa waincan dama sukuma fitowa sai ayi dasu wannan shine taqamaimai dalilin kiranka Alan kazo Dan kuwa Babu Wanda yafi cancanta yabada aurenta Kamar Kai
Hakama Kaine kafi cancantar neman AB TURAKI da maganar sbd ba huruminmu bane mu dangin uwa.

Shiru Kawu saidu yayi Yana jinjina Kai cikin Dan mamakin zancen Yana juya zallar tazara dakuma banbancin rayuwar Dake tsakanin AB TURAKI da Sa'adah din
Saidai tunda Allah Bai haramtaba ba illa bane face qarfafa tare dakuma bawa yarinyar rayuwa Mai kyau a gaba duk da Laylah ce tafi cancanta da hakan ko Dan maraicinta dakuma shaquwar Turakin da mahaifiyarta zaifi Mata riqo na gaske sbd uwarta.

Numfashi ya sauke ahankali Yana sake jinjina Kai ya dago yace"

Babu illa Inshallah zanyi magana dashi saikuyi hanyar da zata hadani dashi din sbd Baya daukan waya sai dace.

Wannan ba matsala bane Inshallah zamu saka lokaci saimuje gabaki daya can Abuja har gidansa sai ayi maganar sbd Inshallah Ana saka ran shigowarsa gobe.

Kawu dai zancen yazo Masa wani iri Amma tunda maganar aurece zaije din bakomai bane dama shine Kamar waliyin su Sa'adah din yanzu tunda mahaifinsu ga yanda Allah yayi dashi.

Da zasu tafi kudi sosai suka bawa Kawun Amma yaqi karba yace bazai karba ba hidimar abinci kawaima da akeyi dashi ya isa.

Haj Karima da umma Jamila sai Alhaji Atiku dasukasan gskiyar lamarin zukatansu cike suke da farin ciki da qaguwa har suka Isa gidajensu
Kawu kuwa dayake mutum ne Mai maimaicin zancen bayan tafiyarsa zaunawa yayi yanata sake juya lamarin har Abdullahi yazo Nan yasake bayyanarda zancen ya Dora da cewa"

Ina shakkar son abun duniya irin na zuriar Zainab idan basune sukeson ingizani Kai zancen wasiyar da babu ba mutuncina da Turaki yake gani ya zube
Dan kuwa Ina mamakin Ta yanda Mahmoud zai bawa Amininsa daya Isa haihuwar yarsa so dubu aurenta batareda laakari da komaiba
Hakama tayaya yake tunanin Turakin zai karba auren Shi Dana mazauniba,hakama baya haihuwa.......

Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun yanason magana Yana Hana kansa
Jin dai Kawun nata nanacin zancen yasashi bude Baki a natse yace"

Dan bada Aure kam Abba yabada aure ga Turaki Kuma yace wasiyace acikamasa ita Amma dai Kam ba Sa'adah ba......

Kawun Bai gama gane qarshen zancen Abdullahin ba yace"

To Allah yasa Turakin yasan da zancen Dan zaifi sauki da mutunci akan nine zanfara tunkararsa da zancen,
Tabbas nasan Akwai alqawarin hada zuria a tsakaninsu saidai ta 'yaya waya sani Ashe ba yayansu zasu hadaba Matar Turakin ce zata fito ta tsatson Aminin nasa,
Wannan da Laylah ce amaimakon Sa'adah da sainace Rabon aurensa da itane yasa ya tsaya tsayin dakan auren uwarta da ubanta harma shine ya biya sadakin.

Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun kawai sbd fahimtar ba sauraronsa zaiyiba bare ya fahimci zancensa sbd ya tsinke da zance.



******
Kwana biyu da zancen suka kwasa zuwa Abuja
Suka fara sauka gidan Haj Karima sukaci abinci suka huta tareda salloli sai dare sukai Shirin zuwa gidan Turaki,
Da Alhaji Atiku da alhajin qarami sai Haj Karima umma Jamila dai bata biyosuba sai Kawun.

Da farko ko babban gate din farko da qaton gidan ba'a Bari sun qarasa ba bare shiga ciki su Isa gate na biyu Wanda dagashi sai harabar gidan.

Daqyar Suka samu ganin A Abdoul wanda tashin farko ya sanar dasu cewar Turaki yariga yashige Yana sashen Mahaifiyarsa wadda idan Yana can bamai Kuma ganinsa Dan Yana jimawa sosai daga can Yana fitowa yake shigewa.

Neman appointment din ganinsa gobe sukai ya sanar dasu cewar goben akwai tafiya Mai mahimmanci a gabansa Wanda zaiyi tareda Mahaifiyarsa.

Sunajin hakan Alhaji Qarami yace"

Idan harda Haj Anne zaiyi tafiya Inshallah ba tantama gurin duba Mahmoud zasu tafi sbd Babu zuwan dayake batareda itaba itama ta dauka Mahmoud tamkar 'da.

Duk da hakan Dan karsuyi tsammanin daba shiba
Kawu ya kalli A Abdoul cikin nutsuwa yace"

Kayi hkr ka kirasa a waya kokuma kakira Haj Anne a waya kace Kawu saidu ne na Mahmoud.

Shiru Abdoul yayi Yana ganin girman Kawun sbd Kiran kansa da yayi a Dan uwan Alhaji Mahmoud Wanda yariga yasan irin Aminci Mai girma dake tsakanin Alhaji Mahmoud da Turakin duk da daga baya yasan labarinsu shida Turakin
Ta wani bangaren Kuma Yana jinjina tsari da kaidar Turaki Dan Haka ya kalli Kawun cikin Yar mutuntawa yace"

Kayi hkr Kawu gskia bazaku samu ganinsaba daga yau din har goben,
Amma idan har Yan uwan Alhaji Mahmoud ne ku taimako daya dazan bada shine ku koma gida ku jirasa sbd zuwansa duba Alhaji Mahmoud kamar kaidace da baya takewa.

Shiru sukayi dukkaninsu suna kallon makeken gate din gidan Da securities ke gadi Babu alamar zasu iya barinsu Shiga Koda kuwa da sakon mutuwar Mahmoud din sukazo bare,
Dan Haka sukaiwa A Abdoul din godiya suka juya
Tsabar Babu Jin dadin rashin damar ganinsa Tun a Daren sukai booking tickets washe gari qarfe Tara na safe suka biyo jirgi Suka dawo gida.


Tunda suka dawo shi kansa Kawun yakasa nutsuwa gida yakeson komawa Amma sun hanasa
Dan Haka a matse yake Kuma takure dason komawa.
Ganin wannan bazata fishesaba yasa abdullahi ya dauko Masa wayar Mahmoud din aka saka caji yace a Nemo Masa numbern Turakin Akira masa.

Kira Kan Kira Amma Bata Shiga Dan Haka Kai tsaye yace anemo Masa numbern Haj Anne Akira masa.

Cikin sa'a kuwa tata wayar tashiga Dan haka ya karba tareda nutsuwa yana jiran ta dauka.

Harta tsinke ba'a dagaba Yana Shirin sake Kira saiga kiranta yashigo wayar Kai tsaye ya dauka cikin tattaro nutsuwa da mutuntuwa yace"

Assalamualaikum
Haj Anne muna lafiya?
Ya gida?da iyali da Turaki?
Duk kowa na lafiya?

Cikin wata irin murya Mai tarin nutsuwa da Kamala tareda zallan ilimin bokonta Dana addini dasuke bayyane ciki lafuzanta tace"

Amin w slm,
Malam saidu ya gida ya iyali?

Lafiya kalau Alhmdlh Alhmdlh,
Ya Turaki? Ance Yana qasar nazo shekaran jiya bansamu damar ganinsaba Jamian kofar gidan sukace yariga yashige Kuma washe gari tafiya zaiyi
Sai kawai muka juyo Muka dawo..

Da mamaki a sautinta tace"

Subhanallh
Lallai ansamu kuskuren rashin sanine da tabbas Turaki bazaiqi ganinkaba kuwa duk uzurin Dake gabansa.

Hakane,shiyasa ban takura akan saina gansa din ba nabari idan yasamu zuwa duba Mahmoud ne sbd maganace Mai mahimmanci yasa naso ganin nasa.

Cikin bada hankali Haj Anne tace"

Allah yasa lafiya dai?
Ko jikin Mahmoud dinne?
Akwai wata matsala ne?
Zaka iya fadamun.

Numfashi ya sauke cikin sake nutsuwa da abinda zai fada yace"

Wata babbar maganace anan da Mahmoud yabar wasiyarta wadda na takeda Dan tsauri.

Uhmm Ina jinka..

Mahmoud yabar wasiyar cewa yabada auren 'yarsa Sa'adah ga Turaki Wanda daga hakan Allah ya tsananta yanayinsa yake cikin halin Rai da mutuwa dayake ciki ayanzu,
Babban dalilin dayasa nazo neman Turakin nayi maganar dashi shine ita Sa'adah din ta Isa aure manema Bata zuwar Mata Amma anqi Basu dama sbd wasiyar Mahmoud din,
Da nazone naji daga bakinsa idan zai karba auren kokuma abawa wasu damar aiko nasu magabatan.

Shiru Anne Tayi tana juya zancen cikin ranta,
Duk da zancen yazo wani iri sbd banbancin shekaru masu yawa dakuma yanayin rayuwar Turakin da baya son mace cikin rayuwarsa shiyasa yakeda mace daya ita dinma daqyar yayi auren bayan ta nuna bacin ranta to tayaya zai iya qara wani auren da qanqanuwar yarinya ma?
Ta wani bangaren Kuma tunanin Mahmoud din tayi tasan bazai taba barin wannan wasiya Mai nauyi hakaba Babu dalili Mai kyau
Hakama batajin akwai wata buqata ko Alfarma da Mahmoud zai nema agurinta ko Turaki su kasa cika Masa ita ko wace irice matuqar Bata Saba addini ba Dan Haka Kai tsaye tace"

Allah yabasa lafiya yasa Munada rabon shaida wannan Alkhairi daya qulla ko acikin ciwo,
Inshallah Aure Kam an karba Allah yazaba Mana abinda yafi alkhairi
Zan sanarwa da Turakin da kaina saidai shi din ba mazauni bane kamar yanda kuka sani Dan Haka idan har aure za'ayi saidai ayisa kafin yakoma cikin satin nan
Saiku shirya Inshallah idan zamuzo duba Mahmoud din zamuzo da komai sai ayi agama ba Abu bane daza'a Tara duniyaba inaga ayi al'amarin a saukake kawai abada Matar.

Godiya kawu yashiga zubawa Yana kori mata addu'a sbd dama can yasan Haj Anne macace Mai kaifi daya kamar namiji Bata Wasa kai tsaye take komai na rayuwarta shiyasa takeda matuqar girma da daraja agurin manyan mutane da dama.

Labari na isarwa su Alhaji Atiku da umma Jamila take dangi kowa yaji Wanda Sa'adah zata aura hayaniya ta kaure ko Ina ya dauka a dangi masu murna nayi masu baqin ciki nayi,
Su kam masu abun tuni aka hau fara shirye shiyen auren duk da dai auren kawai za'a daura Haj Anne tace basa buqatan hayaniyar biki
Gashi idan sukazo za'a daura auren su tafi da ita sai Yan rakiyarta su umma Jamila.

Hankalin Sa'adah yaso tashi Sosai Jin Wanda zata aura saidai hankalinta Bai qarasa mugun tashiba Saida taji umma Jamila suna maganar da Momy a daki cewan Laylah Abban yabada ba itaba sauyi sukeson Yi da ita take jikinta yayi Sanyi Takoma daki ta zauna bakin gado gefen Laylah Dake zaune tayi zuru.

Kallonta Sa'adah tayi take Idanuwanta suka ciko da hawaye ta riqo hannun Laylan Ahankali ta furta"

Bazan taba karban abinda yake naki ba nawaba har abada Laylah.,
Duk da bakida lafiya Zan tsaya tsayin dakan kin zama Matar mijinda Abba ya zaba Miki Amma ta Yaya zakije wani guri rayuwar aure a Haka bakida lafiya,
Bakida sabo,
Baki tana zuwa koinaba arayuwarki.

Washe gari ba kunya aka dauko masu gyaran Amarya takanas Dan fara gyaran Sa'adah
Ta rufe idanuwanta ta tsaya akan bazata yarda da gyaraba bare auren matuqar baza'a yarda da buqatarta tason zuwa da Laylah ba.

Umma Jamila da Haj Karima sakin Baki sukai suna kallon tsabar taurin Kan Sa'adah din,

Umma Jamila ta hauta da fada tako Ina Rai abace
Sa'adah kuwa ta kafe harda saka kuka
Haj Karima dataga suna Shirin rasa hamsin Kan biyar tace sun amince taje da ita Amma idan tayi kwana biyu zata dawo da ita gida.

Kai tsaye tace ta amince da hakan aka rufe zancen aka fara shirye shiyen biki Wanda Amaryar take matseda ganin Kawu Wanda Kiri Kiri Umma Jamila ta hanata ganinsa qarshema dauketa tayi daga gidan tamaidata gidanta aka bar Laylah da kadaici.
##MAMUH#



👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇

Mamuhgee @Arewabooks

🔥🔥🔥🔥🔥
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261
[6/2, 11:21 PM] MG💋: *_Mamuhgee 13_*


*_SAKINA VENDABLES_*
*_Ina ma'abota son qamshi da gyara? Ina masoya qamshi dasuka San darajar qamshi da gyara irin na qamshi?_*
*_To kuzo ga SAKINA VENDABLES Tasake zuwar muku da ingantattu Kuma tsararrin kayan qamshi masu kyau da qarko,_*
*_Ga wainda suke buqatan turarukan gaske masu kyau na asalin qamshi da Kama jiki da Kaya suzo ga inda aka tabbatarda kyau da qarfinsu a gurin SAKINA VENDABLES_*

*Turaren wuta list* 
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous
Khumra White & Black
*Kulaccam* Black(for hair) white (for body)

Handles *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibkes
08106974073


***********
Kallon Fattu Anne Tayi Kai tsaye tace"

A qarasa dashi daga ciki gama su Sa'adah anan,a shigo dashi.

Juyawa Fattu tayi ta koma can harabar gidan tayi Masa iso yabiyota daga baya har zuwa cikin palon
Ya Dan durqusa Yana gaidata cikin mutuntawa sbd ta girmesa sosai gata Kuma tamkar uwa.

A mutunce cikin kulawa tace"

Malam saidu Kaine da kanka kazo baka Bari Turakin yaje gurinka da kansa ba.

Murmushi yayi Yana zaunawa Kan kujerar one seater dake nesa da Annen Yana cewa"

Aa bakomai ai
Nima ai bama maganar komaiceba takawoni ke nazo yiwa barka da zuwa tunda Anjima sosai ba'a haduba,
Allah dai yaqara nisan kwana da lafiya da kwanciyar hankali,
Anata dawainiya sosai da kashe dukiya, ubangiji Allah yasaka muku da mafificin alkhairinsa yabar zumuncin da akaiwa,
Dan kuwa duk ranarda Allah ya tashi kafadun Mahmoud saiyayi qwallar farin ciki da wannan al'amari sbd kun rufa asiri tako Ina tareda dawainiya da iyalinsa.

Katsesa Anne Tayi da cewa"

Wannan duk yiwa Kaine bakomai bane,Allah dai yabasa lafiya
Yakuma Sanya alkhairi acikin wannan lamarin.

Amin Amin ya Allah" Kawu Yafada da hanzari Yana Dan kallon Sa'adah data gaishesa cikin girmamawa
Ya kalleta dakyau cikin Dan mamaki yace"

Wannan Sa'adah ce kokuwa?

A sanyaye tace"

Nice Kawu.

Kasa shiru yayi da mamaki da 'dan takaici duk da yana kokarin boyewa agaban Anne yace"

Ke dawa Kika zo?
Me kikazo Yi keda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login