Showing 24001 words to 27000 words out of 108894 words
cikin Dan takaicin yanda idanuwansu umma Jamila ke rufewa Akan komai,
Koda zata tafi da ita amatsyinta na wadda zata aura Mai Hali yakamata ace andinka Mata ko kala biyu ne na tufafi Amma shine za'a Bata tsofin Kayan da ita takashe taje dasu.
Wani murmushin takaici da baqin cikine ya kufce Mata,
Ita yanzu sun kore Mai aurenta da qarfi da yaji sbd zasuyi auren yaudara da ita
Gashi yanzu zata tashi a Babu tunda biyu Babu takamata.
Kallon Laylah tayi tace"
Aje kayan bazaki dasuba za'a Baki wainda Zaki ringa sakawa idan munje.
Ba musu ta ajiye kayan tareda dagowa ta zubawa Anty Sa'adah din idanuwa tana kallon sauyawar datai tareda tayata farin cikin auren dazatai din Babu babban farin cikinta irin tafiya da ita dazatayi Dan kuwa ita kanta da kanta tasan kanta yakusa qarasa juyewa sbd wasu abubuwan datakeyi wani lokacin.
Akwai gyaran yamma da ake Mata Dan Haka Koda masu gyaran sukazo Laylah tasaka suyiwa tace"
Kuyiwa qanwata gatanan itama da Dan sauya tunda da ita zani.
Momy dai batace komaiba ta qyale akaiwa laylahn sbd lallaba Sa'adah dasukeyi asamu ayi auren tukuna.
Fes Akaiwa Laylah wata irin dilka da wankan lalle tareda wasu gyaran da fatarta ta amsa atake sbd tanada Hasken fata sosai hakama tafi Sa'adah fata Mai taushi sosai shiyasa gyaran atake yaringa shiga jikinta tayi Dan Shar da ita
Abdullahi daya shigo yayi Ido hudu da Laylan tsinkewa yawunsa yayi Yana dauke Kai zuciyarsa na basa qwarin gwiwa da tabbacin Ana Gama bikin Sa'adah zai bayyanarda kansa a manemin auren Laylah din yasan Kuma zasu basa tunda neman Kai su umma Jamila keyi da ita kokuma ya lallaba Kawu saidu kafin yakoma yabasa aurenta basaima Sa'adah ta tafi da ita dinba Dan zata iya fin qarfinsa idan taje daular gidan Turaki ta samu sauyin rayuwa.
Da daddare duk maganin da aketa faman dirkawa Sa'adah Haka ta tattarosu ta bawa Laylah tasata ta shanye a sunan maganin rashin lafiyartane ba musu laylan ta shanye.
Washe gari da safe bayan angama gyaransu masu gyaran sun tafi umma Jamila tareda Haj Karima suka iso gidan da wasu irin Kaya na Alfarma da aka dinkowa Sa'adah din wasu manyan lace ne dasuka Sha maqudan kudi tareda gyalensa da takarmi aka Bata ta shirya tafito fes a Amarya sai qamshi take zubawa.
Kallon Laylah dake zaune gefe tana kallonta tayi tasaki murmushi jikinta amace tanajin inama aurentane na gaskia da Amana za'ai
Datayi farin ciki sbd ita kanta tanason tayi auren Dan ta tallafa rayuwar Laylah din Amma wannan aurene da ake Shirin ginawa Kan yaudara.
Fitowa tayi riqeda hannun Laylah Dake sanyeda doguwar rigar jallabiya sabuwa Navy blue da Sa'adah din tabata tasaka
Kanta nade cikin gyalen Abayar
Idanuwanta ki kwalli babu
Babu komai akan fuskarta sai asalin zallan kyawunta da Allah yabata duk da Babu wata walwala ko sakewa a fuskar tata Wanda Kuma hakan dabiarta ne tunda ahaka ta taso ba walwalar.
Kallonsu Haj Karima tayi kafin ta tsayarda kallonta Kan Laylah Dake rabe bayan Sa'adah din
Ta bude Baki zatai magana
Umma Jamila ta tareta da cewa"
Karma kiyi wahalar magana barta taje da ita din dan taurin Kan Sa'adah Ni har tsoro yakeban yanda kikasan kafiran farko Haka take da taurin tsiya akan wannan Mai Kama da 'yar tsanar.
Shiru Haj Karima tayi tareda dauke Kai daga kallon inda suke din ta kalli Momy dake zaune tana kallon su Sa'adah din itama tace"
Gatanan gurin gaida uwar mijinta dasuka iso yau za'a kaita.
Umma Jamila ce ta karba zancen da cewa"
Ga abinci dasu komai can a mota duk ansaka.
Miqewa Haj Karima tayi dayake ita zata kaita suka fito bayan umma Jamila tasake bin jikin Sa'adah din da turarukan (AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902) masu qamshi.
Suna fitowa suka shiga babbar CR-V din Haj Karima driver yajasu zuwa masaukin Anne wadda ta iso aranar tareda jamaarta su biyu.
Wani babban makeken guest house din Turaki dake garin suka dosa
Tun a gate Sa'adah ke kallon koina zuciyarta a sanyaye har aka abarsu suka qarasa harabar gidan sukai parking suka fito.
Kallon Laylah da kanta ke sunkeye cikin sanyi Haj Karima tayi Kai tsaye tana cewa"
Kwaso kayan abincin,
Ki dauko da kyau karki barar kosu hargitse.
To" tace anatse tareda daukan kayan abincin tanabinsu abaya.
Wani babban palon dayake a tsare da komai na irin Rayuwar turawa akai musu iso suka zauna Kan milk and golden Royal set dake palon
Banda Laylah data tsaya da kayan abincin tana jiran afada Mata inda zata aje
Kafin suyi wata magana qamshin turaren Haj Anne yafara iso musu kafin ta fito cikin doguwar jallabiyar kuwait baqa Mai Fadi sosai kanta yane da mayafi Mai Dan girma sosai Wanda yasaka Hasken fatar datake dashi fitowa sosai duk da tsufa da manyanci Amma komai nata a natse yake,
Fuska dauke da Dan murmushi take qarasowa tana kallonsu ta iso ta zauna Kan 2 seater tana amsa gaisuwarsu a mutunce musamman Sa'adah wadda ke zaune gefn Haj Karima din.... Sauka Idanuwanta sukai Kan Laylah Dake tsaye har lokacin daukeda kayan abincin...
Dukkanin hankalinta da idanuwanta zubawa Laylah su tayi sbd ba shakka fuskar Zainab take gani akan fuskar yarinyar,
Babu abinda tabaro na zainab face yanayin jikinsu daya banbanta ita sirirya zainab Kuma ba siririya bace Amma kamanninta da mahaifiyar sunyi nauyi sosai take taji qaunar datakewa Zainab din kafin rasuwarta tadawo Mata sabuwa fil akan Laylah
da mamaki Kan fuskarta Tace"
wannan 'yar Zainab ce basai nayi tambayaba.
Haj Karima wani juyi tayi tareda Yi kamar batajiba tasake dasa sabuwar gaisuwa da barka da hanya kafin tacewa masu aiki dasuke kawo musu kayan tarba su karba abincin.
Suna karba ta kalli Laylah zatai mgn Anty Sa'adah tariga cikin nutsuwa da cewa"
Laylah kixo ki gaida Mutane.
Sabone data taso cikinsa na idan ba umartarta akai da Abu ba Bata Yi sbd kaucewa laifi da matsala shiyasa Bata qaraso ta gaida Anne ba Saida Sa'adah din tayi magana
Ta qaraso ahankali cikin natsuwa batareda ta kalli Annen ba ta gaidata da muryarta Dake yankewa.
Kasa rike mamakinta Anne Tayi takai tattausan hannuwanta ta kamo hannuwan Laylah cikin tsananin kulawa tace"
Wannan 'yar Zainab ce ko?
Eh itace" Sa'adah tafada kanta a qasa
Haj Karima kuwa kasa hakuri tayi ta miqe tana cewa"
Bari muje mukai wani sakon sainmu dawo mu dauki Sa'adah din daga baya Idan tagama gaidaki.
Cikin kulawa Anne tace"
Ba damuwa kuje tunda zaku dawo saina sake gaisawa da Laylah ko? Tafada tana kallon Laylan Wanda har lokacin itadai bayan gaisuwa batace komaiba kanta na qasa Wanda yasa Anne fahimtar Kamar Laylan nada matsala ko damuwa sbd sanyinta da rashin kuzarin yayi yawa.
Sa'adah datafi kowa farin cikin tafiyar Haj Karima da Laylah
Tana ganin Haj Karima taja Laylah suntafi sbd karsu bada damar da Anne zata qaunaci Laylah
Shi Turaki basama maganarsa Dan sunsan bazai taba ganin laylan ba saidai idan yaganta wata Rana a gidansa acikin Yan aiki.
Ajiyar zuciya Mai sanyi anty Sa'adah ta sauke tareda Dan dagowa kadan tanason magana Amma tanajin nauyi da fargaba saiga sakon zuwan Kawu saidu ya isowa Anne Ana neman ison shigowa dashi.
Wata irin Ajiyar zuciya anty Sa'adah ta sauke sbd tabbas wannan zuwan nasa wani aike ne daga ubangiji.
##MAMUH#
👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇
Mamuhgee @Arewabooks
🔥🔥🔥🔥🔥
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
[6/3, 11:56 AM] MG💋: *_Mamuhgee 14_*
Washe gari gidan da wata irin hidima aka tashi Duk da kusan fiyeda Rabin hidimar a gidan umma Jamila ake yinta Dan ba qaramin Jin auren Nan takeyiba cikin tsakiyar ranta sbd dukkanin burikanta da mafarkantane zasu cika
Duk arzikin dasuke dashi batajin kammaluwar zuciya Kamar yanda take Shirin jinta daga lokacinda ta zama sirika ga AB TURAKI Dan Kamar itace uwa ga momyn kanta bare Sa'adah Dan Haka Bata dauki wannan auren da wasaba ko kadan
Danma anrage musu armashin komai dasu Anne suka nema aure a sirrance kawai batareda anyi hayaniyaba da Allah kadai yasan irin shiri da dukiyar dasuka so bajewa su zubar dan sunsan wannan yanzu ba matsala bane tunda sunsan inda 'yarsu zataje.
Tunda safe Aka fito da Sa'adah tsakar gidan aka Kuma darje koina jikinta da lalle tareda wasu ruwan qamshi kafin aka Bata ruwa tashiga wanka a toilet din dakinta tana fitowa tasaka Laylah tashiga tayo wanka da sauran ruwan lallen.
Koda qarfe goma ta safiya tayi angama shirya Sa'adah din cikin Alfarma ta manyan kayan mutunci dasukaji asalin dukiya Wanda Anne ce ta Aiko dasu da safiyar tace abawa Sa'adah din tasaka
Dan haka taci adonta tana daukan ido tamkar a ace aurentane za'a daura
Ga mamakinsu Umma Jamila da farin cikinsu ba kamar yanda sukaga tana walwala da farin ciki dauke a fuskarta hakan na musu nunin auren dai ta karba hannu bibbiyu itama Dan Haka suka sake sakin jiki Ana hidima.
Momy kuwa sai bin "yarta take da kallo cikin farin ciki tana qarawa
Fuskarta daukeda murmushi Dan tama kasa gane irin kewar 'yarta da zatai idan ta tafi itama gashi gobe da ita din za'a tafi da Abban qasar Germany.
Kamar yanda ake cewa _Rabo sai mai shi_ hakama Matar mutum kabarinsa
Andaura Auren *_MUHAMMAD ABUTURAB TURAKI_* da *_ZAINAB MAHMOUD LAYLAH_* Akan sadaki naira dubu dari cif Wanda Kawu ne ya karba laqadan ba ajalan ba
Hakama babbar Sa'ar da Kawun yasamu akan qudiri da niyarsa na hanawa dangin Zainab sanin komai kamar yanda suka so cin Amana
Kafin su Alhaji Atikun su qaraso yasa aka daura auren batareda anjirasuba Dan dama a masallaci ne Kuma ba wani babban masallaci bane daga shi sai Abdullahi sune dangin Laylah sai Turakin da amintaccen yaronsa A Abdoul sai jamaar Dake masallacin wainda basusan waye angonba bare Amaryar Dan kuwa ko labarin duniya basabi bare su shaida Turakin Dan Haka aure dai andaura yakuma samu jama'a daidai gwargwado dasuka ringa bi da adduar Allah ya sanyawa aure Albarka
Dan Haka Koda su Alhaji Atiku dasu Alhaji Qarami suka iso da manyan motocinsu
Suna fakin Ana Gama shafa addu'ar daurin auren saidai Suka ringa bi da Amin na adduoin da jama'a keyi suna ficewa,
Ransu yayi mummunan baci da hukuncin Kawun na daurin batareda anjirasu ba Amma Turaki agurin sai Basu bayyanarba harda qarin sanin Kar abar Turakin da zaman jira yasa aka daura auren ba Kira badan hakan ba da Kawun sai sun nuna Masa rashin mutunta su day yayi
Dan hakan Kamar tazartawane agaresu.
Washe bakuna Suka hau Yi suna gaggaisawa da Turaki Ana Masa adduar Allah ya sanyawa aure Albarka manyan shaddodinsu sai daukan ido sukeyi Dan kuwa ba laifi kowannensu yanada nasa abun duniyar Amma dogon buri da kwadayi yasa Babu abinda suke gani da hange sai Tarin girma da matsayin Turakin Wanda su connection suke dubawa kafin dukiyar tasa.
Daga gurin daurin auren Kai tsaye gida ya wuce batareda jiran Anne ba wadda zata taho dasu Laylan ya wuce airport ya komawarsa Dan yanada baqin Dake jiransa a Abujan.
Fes Laylah take zaune daki cikin adon Dan lace dinta da aka Bata jiyan saidai batai gangancin fitowaba sbd biki sukeyi gidan sosai har dare tukuna aka Kira Sa'adah din akaita mata nasihu da waazin da sirrikan Kama miji musamman Miji irin nata Wanda aqalla kafin yafara Mata kallon mace ma kila saita kusa hade shekaru nawa a gidan kafin yafara Mata kallon Mata Amma dai sun Yarda da sirrinkansu na kayan gyara dasukai Mata Dan Haka suna jiran kyakkwan labari.
Shiru tayi ta a sauraronsu jikinta duk a mace kukanma takasayi sbd batasan ta Yaya zasuji zancen waye auren yake kansaba
Saidai tasan ko tana hauka bazatai gigin fadar komaiba sbd a yanda tsanar Laylah take cikin jininsu komai zasu iya aikatawa akanta
Shiyasa ta sake roqar Anne da Kawu akan Kar afadawa ko Momy sai lokacinda aka tabbatarda zasu wuce da Abba Germany yanda batada lokaci ko damar sanarwa dangi bare wani mummanan al'amarin ya biyo baya tunda Suma a goben zasu wuce.
Daki Takoma inda ta tararda Laylah tayi sallah tana daga zaune gurin datai sallar
Ta dago ta kalla Sa'adah cikin yanayi na Dan bayyanarda tayata murna tace"
Anty Sa'adah duk ranarda Abba yatashi zaiyi farin cikin ganinki da aure,
Allah ya Sanya alkhairi Anty Sa'adah.
Wani irin murmushi Mai Dan ciwo Sa'adah tasaki tana cewa"
Amin ya Allah qanwata.,
Kuma kinsan kece Zaki ringa yimun dawainiyar kulawa dashi tunda Kinga kin fini iya aikin musamman abinci.
Fararen idanuwanta ta zubawa Anty Sa'adah din cikin jinjina Kai tace"
Eh Zan Miki komaima na aikin gidan Anty Sa'adah Inshallah.
Dafa kanta Sa'adah tayi kawai tana sake murmusawa
Aranta tace"
Tabbas wannan shine bahaguwar sauyin qaddara,
Anmiki aure batareda kinsan kece matarba,
Zakije gidanki da sunan 'yar riqon 'yayarki da kikewa kallon nice Matar,
Nikuma daga aure naqare a zuman riqo gidan Auren qanwa
Wannan badan akwai zumunci ba da dawane suna zasu Kira wannan sauyin lamarin.?.
Gidan umma Jamila ta kwana sbd goben da safe su Momy zasu fara wucewa kafin suma su wuce
Dan Haka duk wani saura ragamar rayuwar Sa'adah umma Jamilan tagama karbarsa daga yau din tunda momyn dai zatabi Abban bayan irin hanatan dasu umma Jamilan da Haj Karima basuyiba har fushi sukaso Yi da ita akan zata kassara sauran rayuwarta gurin jinyar Wanda gurin Cin Amanarta da son zuciyarsa ya hadu da hukuncin dasuke ganin Allah yayimasa akan abinda yayiwa momyn
Amma sbd zamtowarta sirikar Turaki yasa Suka danne fushinsu Dan yanzu Kam zata wuce rainin kowa duk da sunsan har abada sune masu juya momyn sai abinda sukace Mata takeyi.
A Daren Momy tasake jaddadawa Sa'adah komai nata yanzu su umma Jamila ne
Tunda batanan yanzu sune iyaye Kuma gatanta Dan Haka karta ringa komai batareda shawararsu ba
Itadai Sa'adah to kawai take cewa sai alokacin nema tasamu ta rungeme Momy tasaki kukan data keta dannewa aranta tun jiyan ga Kuma kewar mahaifiyarta dazatai dama mahaifin nasu da Babu tabbacin zasu sake haduwa dashi tunda ciwone Babu Wanda yasan yanda Allah zaiyi dashi,
Wani irin nauyi takeji aranta shiyasa ta qanqame momyn tana sake kuka siriri Mai tsananin tsima zuciya Amma su umma Jamila Kam Babu wani Abu dasukaji a zuciyarsu saima rarrashin dasuke Mata akan ai aure bautar Mata ne taje ta Kama uwar mijinta da kyau Dan kuwa mace ce Mai tsananin iko da kaida,
Sam Bata daukan Wasa ko shirme
Komai nata Kai tsaye take yinsa.
Sai datai kuka sosai har idanuwanta sukai nauyi ajikin momyn kafin ta saketa tanajin wasai a zuciyarta
Duk nauyi da radadin datake ji ya sauka gabaki daya tasauke Ajiyar zuciya tareda miqewa ta nufi dakinta tana Jin komai ya Kau akanta sai Kuma fuskantar sabuwar rayuwar Dake jiransu a Gidan riqonsu
Dan kuwa tasan Laylah ma dai kamar riqo ne za'ai Mata Dan maganar auren Anne tace ba yanzu zaaita ba lafiya da ilimi zasu kutsar da ita ciki.
Da wannan tayi adduarta ta kwanta ranta ba wata doguwar damuwa Dan kuwa tasan kyakkyawar rayuwarda mahaifinsu ke musu buri da fata zasuyi ta samun ilimi Mai inganci da zurfi.
Qarfe goma na safe su Momy jirginsu zai tashi Dan Haka tun qarfe Takwas na safe akazo da lafiyayyar mota motar Lexus aka dauki Amarya Laylah da 'yar uwarta kokuma dai ace Amarya Sa'adah da qanwarta zuwa gidan Turakin Dake Nan,
Sosai Anne ta nuna yabawarta tareda karban Amanar yaran da zuciya Mai kyau
Nan akaiwa su umma Jamila yanda suke so wato kyautar girma data kusan sakata zubewa gaban Anne din Haka suka ringa zuba godiya suna qarawa da iyayi kala kala har suka tafi
Dan take daga umma Jamilan har Haj Karima da Matar Alhaji Qarami sukaji buqatar fita gidan Dan sanin yanda wannan kyautar tasu zata jujjuya a hannuwansu Dan kuwa dalolin Amurka ne Anne ta Basu wainda idan suka canjasu ba qananun kudade bane shiyasa ba kunya kowaccensu ta gifta uzurin rashin damar rakiyar Sa'adah din yanzu zadai suzo daga baya Idan sungama sallamar baqin nesa dasukazo biki
Illa kuwa canjin dalilinsu sukeson tsayawa suyi su kammala Kan dukiyar kowa yasan abinda yayi da tasa daga baya sunbi sahun su Sa'adah din Dan dama zuwa gidan Turaki yanzu Dole ne.
Bayan tafiyarsu motar daukar Momy zuwa airport tazo bakowane acikiba sai driver da Kawu a gaba.
Shigowa Kawun yayi Suka zauna Palo daga momyn sai shi sai Anne wadda kai tsaye tafara magana da cewa"
ZAINAB kamar dai yanda Kika sani Allah Yana jarabtan bawansa ne Dan gwada qarfin imaninsa Dan Haka ki dauka komai na rayuwa na samu da rashi dakuma wasu sauyin duk cikin jarabawa da qudirar ubangiji ne,
Kamar yanda kikafi kowa Sani da shaidawa idan rabo ya rantsa tunda ga Laylah Nan Kin gani ishara
Hakane yakuma faruwa auren da aka daura jiya da Laylah aka daurashi sbd itace da haqqin hakan kin sani
Dan Haka idan da ansaka son Rai an daura da Sa'adah to wlh matuqar akwai rabo tsakanin Turaki da Laylah wannan Rabon saiya kashe Sa'adah ta rasu Dan kawai ayi auren a haifosa yazo duniya Dan Haka mudai munyi adalci kamar yanda Sa'adah da kanta tazo tafada Kuma ta roqemu akan hakan sbd hakan dai shine daidai,
Zainab ki godewa Allah daya Baki 'ya kamar Sa'adah wadda wlh samun 'ya kamarta ayanzu Abu ne Mai wuya,
Tayi hankali sosai nakuma yaba Mata iya yabawa shiyasama Zan tafi da ita a hannuna na dauka riqonta da yardar Allah harsai Mahmoud yasamu lafiya Inshallah.
Wani irin kuka Mai sauti da shiga Rai Momy tasaki tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta dake wata irin rawa.
Shiru sukai dukkaninsu sbd Bata damar kokawa Dan sunsan hakan akwai tsananin ciwo
Tana ganin ta aurar da 'ya yanzu Ana fada mata ba wani aure.
Kuka takeyi sosai wanda yasakawa Anne tausayinta tafara Mata nasiha da rarrashi har zuciyar momyn ta Dan Yi sanyi Amma Kam wani nauyi da 'daci sun Riga sun dasa Mata shi Dan Haka share hawayenta kawai tayi batareda ta dago ta kalli Annen ba murya a cikin yanayi na sanyi da 'dacin zuciya tace"
Nagode nakuma bar Sa'adah a hannunku.
Jinjina Kai Anne Tayi tana sake Jin tausayin momyn sbd bayan qunci da baqin ciki Babu abinda yake zagaye da rayuwar momyn tsayin shekaru
Dan Haka tana Mata fatar samun budaddiyar zuciya Nan gaba.
Kasa ganin Sa'adah Momy tayi Dan bazata iya hada idanuwa da Sa'adahn ba Dan Haka Kai tsaye fice ta shige mota suka wuce airport
Suna Isa jirginsu ya daga.
Bayan tafiyar Momy da awa biyu Suma masu jirgin ya daga Wanda yasaka daga Sa'adah har Laylah cikin wani mugun yanayi Dan kuwa Babu Wanda yataba ko barin gari acikinsu bare Hawa jirgi