Showing 102001 words to 105000 words out of 108894 words

Chapter 35 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

35

Middle Ads

da wannan Cin Amanar da yaudarar da akai Mana....

Jikin Na'iman har wani irin rawa yakeyi idonta yayi jajir tafara bubbuga kanta tana maimaita kalmar"

Bazan yardaba,
Cin Amanata sukayi,
Yaudarata sukayi,
Saina kashe Laylah da cikinta sunbar duniya...
Sai sun bar duniya..

Miqewa tayi tana tareda ture duka kayan abincin Dake Kan dining din tana bin hanya ko gani Sosai batayi sbd masifar Dake ci acikin jikinta.

Wani murmushin cika aiki Zinat tasaki tana kamota ta riqe da qarfi tana cewa"

Ki nutsu Zinat zamu ladabtar da Laylah Amma ba yanzuba sbd Bata gari tana gidansu Turakin ya aikata Dan Haka gobe tunda safe zamu tafi da hannuwanmu zamu dasa Mata tarihi kaman yanda ta dasa Mana.

Qwacewa Na'iman tayi tana cewa"

Bazan iya Bari sai gobe ba wlh ayau saina tafadamin da bakinta yanda ta auri mijina taje tazauna a gidana harta damu wannan cikin.....

Ubantama yau saiya amsamin tambayoyina kafin na qarasa gurgunta rayuwarsa...

Yanda taringa fizgewa tana hauka tuburan sbd qarfin qwayar data Bata yasa Dole tayi Mata allurar wadda zata saukar da ita kafin gobe da safe ta saketa tayi Mata abinda takeso din.

Anan palon tabarta yashe takira siddika tace ta shigar da ita daki.

Cikin kayan Na'iman da aka kawo ta qarasa ta bude ta kwashe duk wasu dukiyar manyan sarkokin gold dinta dasu diamond ta zuba Jakarta ta fice dasu daga Gidan.

Daqyar siddika ta iya Jan Ms Na'ima tana hawayen azaba da baqin cikin halinda suke ciki sbd tabbas tasan tana gamawa da Ms Na'ima Dole zata kawar da ita tunda tasan sirrin komai,

Ita bazata iya gudu ba tunda Haj Zinat din taje har garinsu ta daukota Dan tayiwa Na'ima aiki takuma ringa daukan Mata rahoton komai dakomai na rayuwar Ms Na'iman musamman akan yanda take Bata qwayoyin dasuka juyar Mata da qwaqwalwa tsawon shekarun tana juyata sai abinda tace tayi,

Dan Haka tasan Kota gudu Bata tsiraba saima sake bawa Haj Zinat din damar kawar da ita Dan Haka bazata gudu ba zata ceto kanta da Ms Na'ima ko zasu samu rayuwar kwanciyar hankali da 'yanci agaba.

Tana Kai Ms Na'ima daki ta fito ta nufi dakin Haj Zinat dayake tasan inda take aje takardun shaidar haukar Na'ima dakuma takardun maganin datake Bata harma Dana allurar da wani likita yake batasu
Tun farko shinema yake yiwa Zinat aikin komai na juyar da qwaqwalwan Ms Na'ima.

Dauke takardun tayi duka ta fita da sauri..

Harta Kai kofar dakinta ta tuna da Babu ranarda Zinat Bata duba takardun Kuma ta tabbarda dasu zata tafi duk inda zasu goben
Dan Haka da sauri taje ta debo wasu takardun makarantar 'dan Haj Zinat din data gani a Palo taje ta Sanya Mata ta fito da sauri.

Daukan takardun tayi ta daure cikin leda kafin takaisu can baya cikin sharar kitchen ta Sanya tadawo ciki jikinta na zuciyarta suna rawa tana fatan kada wannan abun datai ya kashesu gabaki daya itada Ms Na'iman agurin zinat,
Dan Haka har dare yayi Haj Zinat tadawo hankalinta ba'a kwance yakeba zuciyarta bugawa takeyi da qarfi matse take da goben tayi su tafi itama ta tafi gidan AB TURAKI RES takaiwa Anne takardun sbd tasan bazata iya samun ganin Turakin Kai tsayeba ta isar Masa takardun.

Har akai sallar asuba siddika na zaune tana yawon bandaki sbd tsoro da jiran wani tashin hankali daga Zinat Amma shiru
Dan haka tana Gama sallah ko wanka batayiba ta fito tana aikin kaida kawo na aiki a kitchen ko zataji wani zancen Amma shiru duk da hakan hankalinta har lokacin a matuqar tashe yake.

Qarfe goma Suka fito Haj Zinat shiye tsaf cikin wani arnen tsadadden lace brown sai handbag dinta da takarman Dior sai qamshi take zubawa.

Ms Na'ima kuwa doguwar Rigar Dubai ce ajikinta ta wani tsaddaden material blue fuskarta ta fada sosai a dare daya sbd qwar da aka Bata Mai tsananin karfice wadda har lokacin ajikinta Bai saketaba saima tsananin juyar Mata da qwaqwalwa datake qara Yi Amma allurar da akai Mata yasa Bata iya komai sai jikinta a sake sake take ba qwari sai sun Isa zata banka Mata wata qwayar abun ya tashi.

Dan Haka ko breakfast Basu tsaya sunyiba Suka fice zuwa airport.

Suna fita da awa daya siddika ta Isa dakin Haj Zinat ta hau bincike jikinta na wata irin rawar tsoro da tashin hankali ta ringa watsi da Kaya tana bincike dakin.

Daqyar tagano jakar data fita da ita jiyan da gwalagwalan Ms Na'ima tadawo da ita Kila ba'a siya yanda takeso ba Dan Haka Bata tsaya Bata lokaciba ta dauke jakar ta fito ta nufi kitchen ta zazzage kwandon sharar ta dauki ledar takardun ta fito sanyeda doguwar Riga da qaramar hijabi ko ganin gabanta batayi Sosai
Har saidata ga anason Gane Bata hayyacinta tukuna tayi kokarin saita kanta ta dauka drp din mota zuwa Gidan TURAKI.




*******Cikin kwanakin datayi a gidan tasamu kwanciyar hankali da nutsuwa
Hakama anty Sa'adah zuwan laylan yasa tasamu kanta cikin wata sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa sbd zuwanta yasa shaquwa da sabuwar kauna ta qaru tsakaninta da Abbansu sbd dama ba wani shaquwa tsakaninsu Sosai.

Momy gabaki daya tun zuwan Laylah ta Rasa walwalarta ta zaman gidan
Koyaushe Bata zama gida,
Abba baida magana saita Laylah da cikinta,
Ga yarta da abban sun koma tamkar wasu bayin Laylan hidimarta kawai suka sani,

Ta bangare daya ma Sa'adahn batada lfya tana fama da yawan habon jini koyaushe Amma taqi tsayawa suje asibiti sbd idan adacan zafi ne yanzu suna rayuwar AC koina tayaya za'ace zafi ne tafi kyautata zaton Dan kanoma ne sbd idan yayiwa mutum tsanani yakan saka hakan wani lokaci...

Ita babbar damuwarta kada ya taba lafiyar Mara Kota mahaifar Sa'adah
Ganin yanda takewa Laylah ta tabbatarda tanajin tsananin kewar inama zatai auren ta Haifa nata 'yayan.

Yau tunda safe ta shirya itada Sa'adah Suka nufi asibiti sbd Abba da kansa yace Sa'adahn taje asibiti.

Daga Laylah sai Ruky da hadiza Dake aiki ne a gidan ko Abban bayanan ya fita tareda Abdullahi zuwa tsohon gidansa da ake gini.

Zaune take Palo sanyeda doguwar Riga Mai qaramin hannu sai farar hula akanta
Fuskarta tayi fresh sbd hutu.

Furar dataji Madara d fresh nono takesha cikin cup tana duba wayarta dataketa Kiran Abbahh Bata shiga,

Yau tun safe take kiransa takasa samu..

Hankalinta baya Kan tv Dake aiki Yana Kan wayar hannunta Dan Haka ko dataji sallama bata dagoba sai data aje wayarta Dake hannunta gefe tareda kallon kofar tunaninta su Anty Sa'adah ne suka dawo.

Cup din hannunta ne ya subuce Mata lokaci daya tana sauke kafarta data miqe daga Kan table dake gabanta gabanta yayi mummunan faduwa ta miqe tsaye tana kallon umma Jamila dake gaba Haj Karima na biyo bayanta sai Anty fatima.

Cak umma Jamila ta tsaya tana kallon fuskarta da kyau sbd kwanakin tana fama da Ido ta waiwayo ta kalli Haj Karima Dake qarasowa ciki idonta akan cikin Laylan itakuma tace"

Haj karima wannan Kuma dai gata Kamar 'yar Mahmoud da kishiyar zainab kokuwa idon ne?

Anty Fatima datake qanwarsu tace"

LAYLAH?????

Qarasowa suka fara Yi umma Jamila na sake qure kallonta akan Laylan da mugun mamaki tace"

Harda tsarabar cikinta tadawowa Mahmoud gashinan ajikinta.

Wata muguwar dariya Haj Karima tasaki tana nufar kujera ta zauna tace"

Allah sarki,
Shikuwa Mahmoud ahaka zai qare daga haihuwar 'yar da ba'a tabbatarda aurensa da uwartaba sai samun jikan wata hanyar.

Hannu umma Jamila takai ta janyeta da qarfi ta watsar gefe tareda zaunawa tana cewa"

Can ya matse musu idan shege dari zata Haifa su Suka sani,
Fata dai wlh baza'a haifawa zainab shege acikin gidaba,
tunda bin baza ta zaba taj ta bisu can kowama ya huta.

Tashi tayi daga jefar da ita da umma Jamilan tayi tareda Dan sauke Kai cikin girmamawa ta gaidasu Amma Babu Wanda ya kalleta bare ya tanka
Ta juya tabar gurin jiki Amace ta shige daki.

Tana shiga su Momy na shigowa
Tun a haraba da Momy taga motar umma Jamila tasan suna gidan hankalinta yaso tashi Amma Kuma ta Dake tunda ba ruwanta da shaanin Laylahn ita yanzu ta yarta da aka dinga diban jinin Dan gwaje gwaje take.
##MAMUH#
[7/4, 10:57 PM] MG💋: *_Mamuhgee 55_*
Momy na shigowa palon ta kallo daya tayiwa fuskokinsu ta dauke Kai tana qarasowa ta zauna tareda bude Baki a sanyaye ta gaidasu sbd ganin yanda umma Jamila ke Mata kallon datasan maganar da za'a fada Mata bamai Dadi bace.

Ita kanta Sa'adah jikinta mutuwa ya sakeyi akan na zazzabin data dawo dashi na dibar jininta da aka ringa Yi dakuma kaida kawo,
Daqyar ta iya driving dinsu Suka dawo gidan.

Cikin sanyin murya ta gaidasu ta juya ta nufi dakinta ta shige.
Gabaki daya jikinta a mace yayi yayi Sanyi sosai hakanan yau zuciyarta take sakayau Bata Jin nauyin komai Kamar wadda ba zuciyar a kirjinta.

Laylah na zaune tashigo Bata iya cewa komaiba ta wuce toilet tayo wanka da alwala tafito daureda qaton towel ta shirya cikin Riga da skirt na atamap ta Sanya qatuwar hijab ta tada sallah.

Tana idarwa hadiza ta shigo ta kawo Mata abinci Amma Sam batajin cin abincin
Ruwa kawai Tasha ta Haye gado ta kwanta tareda rufe ido koina na gabobin jikinta suna Mata ciwo.

Cikin kulawa Laylah tayi Mata sannu tareda gyara Mata rufarta Jikinta na sanyi tace"

Anty Sa'adah ko dai zaki koma Abuja ne saikiga likata acan?

Girgiza Kai tayi tana cewa"

Bafa komai bane Momy ce itama duk tabi ta daga hankalinta.

Wani sanyayyan murmushi Laylan tasake ahankali Jin abinda anty Sa'adahn tafada,
Ahankali tace"

Momy Dole zata damu tunda bakida lafiya Kuma jikinki ya nuna hakan.

Yanda Laylah tayi mganar cikeda sanyin jiki Dana murya yasa anty Sa'adahn bude idonta ta zubawa Laylahn sbd tajiyo 'dacin rashin mahaifiya acikin sautin maganarta.

Ahankali ta bude Baki tace"

Laylah kinsan cewa kinfimu gata dagani har Momy?

Rashin mahaifiya bashine rashin uwa ba,
Kina tareda soyayyar mahaifinki tun lokacinda kike qaramarki cikin Hali na maraicin uwa,

Kin taso cikin Rashi na makusanta Amma Kuma nida Momy mun rayuwa cikin Yan uwan da makusantan Amma Kuma a qasqance sbd ganin Ana tallafe damu,

Ki godewa Allah da wani kadaicin da wani rashin makusantan alkhairi ne tunda gashi yanzu daga mu din har makusantan mu muna qarqashin inuwarki,

Wani gatan da Jin dadin da Turaki ya sakar Mana bana kusancinsa da Abba bane kawai na girman dakike dashi ne a zuciyarsa..
Dan Haka Laylah ki daina Jin daci arayuwarki Dan bakida maraici yanzu.

Murmushi Mai ciwo Laylah tasaki tareda maida hawayen dasuka ciko idanuwanta ta bude Baki akaro na farko datai maganar maraicinta na rashin uwa tace"

Anty Sa'adah duk gatan dazan samu a duniya zanso inada mahaifiyar da zata kalleni tasan ciwona da damuwata saidai Allah Bai kaddareni da samun wannan gatanba saiya bani wani gatan na daban...

Tashi zaune anty Sa'adah tayi tana kallon fuskarta tace"

Laylah maraicin mahaifiyar data haifeki kawai Zakiyi sbd Babu Wanda zai taba maye gurbinta Amma na tabbata Anne da abbah turaki bazasu taba Bari kiyi wani maraicinba har lokacinda Momy zata bude Miki zuciyarta ki Shiga ta karbeki amatsayi na 'ya..

Wani sanyayyan murmushi takuma saki hawayen datake riqewa Suka ga gangaro Mata sbd tasan qaddararta da Momy Allah Bai rubuto musu zama makusantaba.

Murmushi Sa'adah tayi tana cewa"

Kina mamaki ne?
Inshallah wata Rana zaki samu gurbi Mai girma a azuciyarta.

Shiru kawai Laylah tayi Bata sake cewa komaiba har bacci ya dauke Anty Sa'adahn
Ta zuba Mata idanuwanta dasukai ja sbd hawayen datayi.,

Anty Sa'adah zuciyarta Mai tsafta ce shiyasa take ganin Momy zata kaunace kamar 'ya wataran,

Ita basai momyn ta karbetaba ahakama tana kaunarta sbd itace mahaifiyar Anty Sa'adah.

Wayarta Dake gefenta takuma dauka ta saka Kiran Abbahh Amma still Bata shiga,

Hakanan takejin kadaici da maraici na shigarta Dan Haka ta koma Kan kujera ta zauna rakube tana kallon fuskar Anty Sa'adah Dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hayaniya ce ta kaure a Palo ba zata ba tsammani sai ganin umma Jamila tayi akanta tana dago fuskarta kuwa ta kifa Mata wasu fararen Marika a jere tareda finciko ta tayo Palo da ita jikin har wani irin rawa yake tana cewa"

Nafada nakuma fada wannan itace muguwar qaddarar rayuwarki Zainab Dake da 'yarki Kika qi Jina ga irin kyakkwan sakamakon data nuna na cewan ita jinin Mahmoud da uwarta ne,

Mahmoud ne da matsiyacin Kawun can suka daure gindi akai wannan gagarumar cin amanar ta sauyawa Sa'adah Miji a daurawa wannan maciyar Amanar butulu wadda Bata gade alkhairi,

Tsawon shekaru Muna dakon aure Sa'adah keyi shine sai yanzu kike sanar damu riqonta akeyi a gidan turaki¿
Kutumar uban riko duk inda yake
Wlh yau Mahmoud saina wanke Masa allon rashin mutinci.

Haj Karima dataga mutuwa tsaye da baqin cikin zamtowar Momy Yar uwarta murya cikeda baqin ciki tace"

Allah ya Isana tsakanina Dake zainab,
Wlh ban dauka lalacewar da mutuwar zuciyarki yakai wannan zarafinba Dan kuwa ke ko ajikin danginmu kinfi kowa zama asararrar,

Miji ya cuceki ya aura watacan daban bada saninkiba harda haihuwar asara Amma Kika kasa rabuwa dashi saima zaman jinyar nakasasshe,
Keda yarki kuka Gama zama 'yan maula shine yanzu anyi wannan Cin Amanar an rufemu kema Kika biye aka ringa binmu da kallon shashashu gamu Yan iskan iska wato,

To wlh kuwa Zainab daga yau babuni Babu ke,
Dan kin Haifa mace mun nuna munasonta muna fatar tayi aure gidan hutu taj dadi shine muka zama makiyanki kika biye musu aka rufe mu wato mu makwadaita..

Tsabar baqin ciki daya Gama rufe idon umma Jamila sake fizgar Laylahn tayi batareda la'akari da cikin dake jikinta tayo palon waje da ita inda ta tabbatarda Mahmoud na Nan

Ido rufe ta saki Laylahn agabansa tareda kallonsa cikin tsananin baqin ciki da bacin rai tace"

Mahmoud kaji kunyar duniya saura ta lahira wlh,

Duk cin Amana da quncin daka saka zainab akan uwar yarinyar Nan Bai issaba ta kashe rayuwarta gurin jinyar Maci Amana irinka duk da hakan Bai isaba shine yanzu aka tozartata ta hanyar aurar da 'yarka ga Wanda kakeso bayan Sa'adahn ce babba qarshen wulaqantawa kowa na Mata kallon Matar aure sai yanzu ace wannan ce Matar ita riqonta akeyi...
Shin Mahmoud kana ganin Sa'adahn ta cancanta hakan daga gareka?
Kokuwa ita 'yarka bace musani wannan ce kawai yarka???

Abba shiru kawai yayi Mata baice komaiba sbd jikinsa da yayi Sanyi da abinda tayi din gaban Wanda yakeda matuqar mutunci da girma a idonsa Kuma uban 'dan cikin datake kokarin aibantawa.

TURAKI kuwa Dake zaune tareda Abban shigowarsa kenan
LAYLAH daya riqe jikinsa Lokacinda ta sakota zata Fadi yake kalla idanuwansa sun sauya take saidai yanayin Shirun da Abba yayi dakuma Laylan da idanuwanta suke rufe tana tsiyayar hawaye batareda ta iya dagowab ya sanyashi dakewa kamar baya gurin ya miqe tsaye da kyau sai alokacin ta waiwayo ta kalli Wanda ke zaune Tareda Abban batace komaiba ta juya ta fice tana Jin zuciyarta Kamar zata tafashe tsabar baqin cikin dasuke ciki yau.

Mahmoud ya haifar musu masifa
Ya haifar musu bala'i.

Acan cikin Koda ta iso Momy kuka takeyi sosai na irin cin zarafi da maganganu masu dacin gaske da Haj Karima ke fada Mata,
Umma Jamila Jin tayi ta tsani momyn da Sa'adahn gabaki daya Dan Haka komai bazata iya cewaba ta fizgi Jakarta tayi gaba tana cewa"

Har ababa bazaki sake ganinaba a gidanki zainab,
Kin zabi namiji kinbar Yan uwanki Zaki Kuma ganin sakamon da Zaki samu daga garesa.

Fita sukayi Haj Karima kuwa duk wata alaqarta ta yanke da momyn daga ranar taje sunbarwa Mahmoud ita.

Bayan fitarsu sakinta Turaki yayi Ahankali tareda kallon fuskarta a shaqe ya iya cewa"

Je ki shirya kifito zamuje ganin likita.

Batada karfi ko tunanin tsayawa musu Dan Haka ta juya Takoma ciki mararta har murdawa takeyi sbd tsabar dacin zuciya da damuwa Mai qarfin gaske data shigeta.

Kusan koina batada farin jini qinta suke kamar tabar duniyar su daina ganinta.

A Palo Momy kuka takeyi sosai Mara sauti Wanda yasa jikin Laylah qarasa yin sanyi hawayen dake idonta Suka fara saukowa suna gangara,

Tasan radadi da 'dacin kalaman dasuke fadawa Momy tun ba yanzuba basa fadar kalma Mai Dadi akanta sbd batada abun duniya,
Sun kasa barinta taji ta runguma kaddarar rayuwar aurenta koyaushe cikin sakata qunci suke fa kalamansu.

Batada iko ko damar bin gaban momyn sbd kada ta qara Mata quncin zuciya ta sanadin ganinta tunda ko yanzu itace silar da hakan tafaru.

Daki tashige cikinta na juyawa tareda Mararta sake ciwo kadan kadan.

Zama tayi bakin gadon da anty Sa'adah ke kwance har lokacin tana bacci cikin nutsuwa
duk hayaniyar da akai Bata tayar da itaba bayan Kuma batada wani nauyin bacci.

Bata iya sauya kaya ba sbd juyawar dataji cikinta yakuma Yi Dan
Abaya kawai ta dauro akan doguwar rigar Dake jikinta Mai qaramar hannu.

Tareda Ruky ta fito suna Isa jikin motar Abba yace Ruky tayi zamanta sbd Turakin nema da kansa ya karba tukin A Abdoul zamansa zaiyi gida su sake gaisawa da Abbansu Sa'adahn.

Kallonta abbanta yayi cikin kulawa da qauna Mai tsanani yace"

Zainab¿

Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa da Idanuwanta dasukai jajir saidai takasa amsawa,
Zuciyarta nauyi take Mata sai kawai hawaye Suka gangaro Mata ta kallesa cikin kauna ta mahaifi.

Laylah ki kula kinji,
Allah yasa muji alkhairi,
Karki damu da maganganunsu komai lokakacine dashi idan Kika tafi Babu Mai sake ganinki acikinsu.
Karki damu kinji?

Ahankali jiki amace ta gyada masa Kai tareda shigewa motar suka fice daga gidan yana kallonsu.

Hannunsa daya yakai ya riqe hannunta Dake aje Kan cinyarta zuciyarta wani irin nauyi da harbawa take mata dayasa takejin rashin nutsuwa Sosai.

Kasa dagowa ta kallesa tayi saima mutuwa da jikinta yayi har suka Isa lafiyayyar 5star hotel din daya sauka suka Isa qaton dakinsa dake floor din sama karshe.

Zaunar da ita yayi kafin ya zauna gefenta sai alokacin ta dago ta kallesa ya Dan rintse manyan idanuwansa dasuka sauya haryanxu Basu koma yanda sukeba sbd har lokacin zuciyarsa radadi da zafin abinda akai Mata sukeyi.
Kasancewarsu Mata Kuma harkan family yasa Bai tunanin daukan matakiba ko kadan saidai Kuma tabbas bazata sake zuwa duk inda dangin momyn sukeba,
A qataice za'a Samar Mata da nata gidan daban ta yanda idan tazo zata ringa zama acan kafin tagama kwanakinta ta tafi duk da ko zuwanma bayajin akwai ranarsa kusa matuqar ta koma.,

Shi gabaki daya wannan yawon ya ishesa tattara matansa zaiyi yakoma US hankalin kowa ya kwanta.

Dr Amatullah ce tazo har hotel din taduba Laylah Babu wani matsalar komai sai damuwa data sakawa kanta Wanda ya hawar da bp dinta shine yasakar Mata cin Dan ciwon Mara gashi Daman cikin yashiga wata bakwai yanzu.

Bayan tafiyar Dr Amatullah magani kawai ta iya Sha taso zuwa gida Amma ya hanata saita cire Mata kayanta da yayi sukai sallar magriba,
Daqyar ta iya Shan tea kawai sbd hakanan komai batajin dadinsa zuciyarta takasa samun nutsuwa
Suna Gama

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login