Showing 6001 words to 9000 words out of 108894 words

Chapter 3 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

11

Middle Ads

ta dauko maganin data dafawa Momy Kai tsaye ta juyo tadawo palon cikin tsananin girmamawa ta qaraso gabansu ta aje kofin maganin gefen Momy anatse da biyayyarta tace"

Barka da fitowa Momy.
Ga magani andafa na ulcer dinki naga
Kamar zafin jiya ya tada Miki ita.

Batareda ta kalli gefenba ta dago ta kalli Sa'adah dake kallon Laylan cikin tsananin qaunarta kafin ta kalli Momy tasaki murmushi tana sake maida kallonta ga Laylah cikin sakewarta tace"

Laylah kinfi kowa sanin Momy da iya kulawa da ita.

Miqewa laylan tayi tabar gurin ta nufi kofa ta fice tsakar gida tana Kama hanyar kicin Dan Dora abincin Rana Dan kuwa tasani ko shekarun duniya zatai agurin ba tankawa Momy zataiba hakama ire iren wannan son cusata agurin momyn da anty Sa'adah keyi tana iya gani akan fuskar momyn tado Mata da tsananin dacin Dake zuciyarta na shekarune kawai takeyi shiyasa anty Sa'adah na farawa take ficewa Dan dama idan ba aikin doleba Bata tsayuwar data wuce minti biyu agurinda momyn take tunda momyn ta bayyanarda rashin son hakan qarara tuntuni.

Sbd ulcern momyn yau tuwan shinkafa tayi da miyar zogala da Babu Mai sosai,
Da kanta take zuwa bakin titin anguwar karbo kayan cefane gurin malam rabiu Wanda sai anhada kudi Kamar 4 zuwa biyar sai momyn tabiyasa sbd ita kanta duk qarfin haline,
Iyayenta da Yan uwanta nada arziki Mai yawa sbd kusan gidansu duk manyan Yan shiyasa ne,
Hakama yannanta da qannenta Mata duk masu hannu da shuni suke aure saidai kaf kusan danginta Babu Mai iya Taimaka Mata sbd aurenta da Abban da Babu Wanda yaso Dan Yana talaka Mara qarfi,
Ta tsaya tsayin daka ta auresa sbd tana sonsa,
Yanada iliminsa da hankalinsa Dan Haka bataga illar aurensaba Dan bayada kudi,
Mahaifinsu baya Raye sai mahaifiyarsu wadda Sam batawa momyn auren Wanda baida aikin Yi sai takardun karatu,
Yayyunta sunso inganta rayuwarta ta hanyar Bata karatu Mai zurfi tareda auren Hadi na tsakanin masu kudi Amma ta ture komai tace bataso sai Abba Wanda hakan yakawo rarrabewar Kai aka samu hargitsinda kowa yabarta ta aura Wanda takeso Wanda ba jimawa da auren yasamu aiki yafara ta samu kwanciyar hankali da nutsuwarda take tunanin tabbatuwarta har abada,

Mahaifiyarsu ta rasu alokacinda Abba baya gari ga laulayin ciki Haka tashiga damuwa da gagari Mai tsanani Dan kuwa acikin Yan uwanta kasa sakewa tayi ga ciwo,
Qarshe dasuka Bai dawoba Haka Kuma tana buqatar taimako suka kaita asibit saidata share sati uku a kwance kafin aka sallameta ahakan Takoma gidanta taci gaba da rayuwar kadaici da tawakkali sbd zuciyarta idan tanason Abu tana Masa sone mai tsananin gaske.

Saida cikinta ya Isa haihuwa Allah yabawa Abba ikon dawowa daga doguwar tafiyar da yayi ta haifi Sa'adah wadda taci sunan mahaifiyarsu,

Darajar sunan yasa Yan uwanta ke qaunar Sa'adah har suke iya Mata komai Ahankali ahankali harta shirya da Yan uwanta suka ringa Bata kulawa da gata kamar yanda mahaifiyarsu tabar musu wasiyyar kulawa da momyn kamar tasan wani abun zai faru,

Bayan haihuwar Sa'adah Abban tafiye tafiyensa suka tsananta ahaka Sa'adah ta taso ba shaquwa sosai da mahaifinta sbd baya zama,
Duk wani dawainiyar gidan momynce keyi sbd Abban kullum ciki yawon kamfani yake Wanda yake aiki sbd aikin gwamnatin Bai samuba har lokacin.

Momy nasonsa Bata taba Jin damuwa takaici ko gazawa da zamanta ahakan ba saima tausayi da qaunarsa datake qarawa ahakan.

Babban budin daya fara shigowa rayuwarsu shine dawowar babban Amininsa *_MUHAMMAD ABU TURAB TURAKI_* Wanda duniya tafi sani da *_AB TURAKI_*
Turaki shine ya bawa abba manyan kudin daya bude kamfanin kansa da kansa bayan ya siya Masa babban gida da babbar mota,

Da farko rayuwarsu Momy da yarta da abban Takoma ta kwanciyar hankali da Jin Dadi saigashi kwatsam Abban yaga ZAINAB yaji Yana qaunarta,qauna Mai tsanani batareda jawakai lokaciba ya aureta ya ajeta anata gidan daban tsawon shekara da shekaru har Allah yabata ciki momyn Bata saniba saidai yanada niyar bayan haihuwar ZAINAB din zai hadesu yafadawa momyn gaskia wadda halaccinta da kunyartane tun farko yasakashi boye Mata
Ashe qaddara bazata bar hakan ba Dan kuwa mummunan hadarin motar yafarune ranar da Turaki ya sauka Nigeria akan wata babbar nasarar rayuwa daya qara samu a qasar US
abban ya dauki zainab suka Isa gidan Dan tayasa murna da yiwa hajiyarsa wato Anne Allah ya Sanya alkhairi saigashi suna shiga gidan tsautsayi ya Tarawa zainab din ta zame tayi mummanar faduwa nakudar Dole ta taso mata,
Hankali tashe suka juya zuwa asibiti ganin halinda Abban yake ciki na rudu da rashin hankali yasa Turaki bin bayansu da mota wadda shine da kansa yake tuqawa gashi dare ne Dan Saida sukai ishai sukazo gidan.

Motar abbance tafara shigewa qarqashin babbar motar data Rasa burki tayo cikinsu kafin motar Turaki wanda Bai ankareba Saida yakawo gaf dasu shima tasa motar tayi cikinsu anan wannan mummunan hadarin ya afku Wanda yayi sanadiyar rayuwar zainab duk da ansamu ta haife cikin,
Shikuma Abban ya Rasa nasa qafafun da wasu raunika
Turaki kuwa Babu wani babban raunika ajikinsa saidai buguwa da yayi sosai wadda tayi sanadin tasa qaddarar ta rashin haihuwa da ake fada duk da Babu tabbacin rashin haihuwarne kokuma asalin inda ake samun haihuwarne yasamu matsala Dan kuwa tunda yabar qasar baikuma dawowa ba Saida lokaci Mai tsayi yaja
Zuwansa Nigeria saiya koma sai dace ne kawai duk da Suna da tarin dukiya da matsayinsa Babu inda Bai zagaba a jaridu da gidajen talabijin da media Amma Kam ganinsa sai dace Dan kuwa babban mutum ne da ko acikin masu kudin ba kowa ke samun damar ganinsa ko ganawa dashiba,saidai Amininsa Abba da koyaushe yakan ziyarcesa ya duba lafiyarsa duk yazo Nigeria saidai wannan karon ya Debi shekaru masu Dan dama Bai dawoba.

Bayan abunda ya faru dukkanin arzikin Abba Saida yashige gurin neman lafiyarsa Wanda daga qarshe wannan gidan dasuke ciki shine kawai ya rage musu Wanda aka siya da sauran kudaden kamfaninsa da kadarorinsa da aka siyar,

Dangin momy sunyi fushi da Allah wadai da ita akan zaman datakeyi da Abban har bayan irin abinda yamata gashi yanzu Takoma jinya da dawainiya dashi,
Ta ciyar da kanta,ta ciyar da yarta,ta ciyar dashi da tasa 'yar hakama itace dawainiyar komai da sutura duk da dai Bata yiwa yarsa sai abinda Sa'adah ta kashe ta bata Haka shima kayansa duk rufin asiri ne Dan Haka kowa danginta ya saka Mata ido suna muamala da ita Amma basa iya taimaka Mata,itama dama ayanda cin amanarsa ta kangarar Mata da zuciya sai Bata buqatar taimako ko tausayi daga kowa,
Zata Gina rayuwar yarta suyi rayuwa Mai kyau da Jin Dadi wannan shine babban burinta sbd a duniya tariga tasan bayan 'yarta data Haifa da cikinta babu wata qauna ta gaskia da Amana.
#MAMUH#


👇👇👇Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete 👇👇

Mamuhgee @Arewabooks

*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin?_*
*_Qaddararsu wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
*_NOOR ALBI Hasken rayuwata_*
_Littafina dayazo muku da wani salon na dabam Wanda soyayyarsa ta kere sauran labaraina,salonsa ya bambanta da sauran,nishadinsa da shauqinsa na musamman ne_
_Fata dai ku kasance taredamu kuji zafi zafin damuka dawo muku dashi_
*_NoorAlbi#MAMUH_*

Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261
[6/2, 11:20 PM] MG💋: *_NOOR ALBI_*
*_Mamuhgee_*


https://arewabooks.com/book?id=628264fab77ff582983da456

5
_Last Free Page_
Guraren la'asar Rana ta Dan bude kadan daga hadari da ruwan da aka tashi dasu
Tana ganin ranar ta Dan bullo ta kwaso kayan wankin jiyan datai Wanda iska ya lalata tasake wankewa sama sama ta shanya
Tana gamawa ta sakarwa abbanta labulan palonsa sbd magriba datai danma yau Bata fito dashiba Shan iska tsakar gida kamar yanda tasaba kullum take fitowa dashi yasha iskan yamma sai magriba ta turasa ciki
To yau sanyi sanyin ruwan da akai yahanata fitowa dashi Dan ita kanta dannewa tayi Amma zazzabin dukan ruwan datashane yake cinta sosai Amma ba amfanin kwantawar Dan haka ta danne sai idanuwanta ne dasuka ja
Sai Wanda yakeda zurfin ganewane zai gane zazzabi ne ajikinta.

Alwala tayi bayan tasake share tsakar gidan tas ta shigarda komai kicin tarufe kicin din Dan dama abinci daya sukeyi har dare basa abinci biyu matuqar ba baqi Momy tayiba aka cinye abincin Amma abinci daya akeyi har dare sbd lallabawa da neman da take.

Dakinta ta Isa ta tayarda sallah cikin dauriya tayi sallar tazauna tana adhkar har tsawon lokaci saidataji zazzabin na neman fin qarfinta ta miqe batareda ta cire hijabin sallartaba ta nufa kofa tafice zuwa gurin Abba Dan bashi abincinsa da magani kafin ta kwanta jikin ya hanata tashi.

Cikin qarfin hali tagama bawa Abban abinci tabasa magani ta maida kayan kafin tadawo ta zauna tana goge Masa fuska sai alokacin Abban yaji tsananin zafin hannuwanta da har wani siracin zafi sukeyi
Ya zuba Mata idanuwansa kafin ya Dan motsa hannunsa alamar mgn
Ta kallesa tana kawarda abunda ta fahimci yaji Wato zafin jikinta.

Cigaba da gage Masa fuska tayi tana qin Bari ya kalla idanuwanta dasukai laushi
Tana gamawa ta miqe tana Masa addua Tai Masa Saida safe ta fito takoma daki Kai tsaye Tai sallar ishai ta kwanata take baccin wahala ya dauketa a gefen katifarta ko rufar arzki bataiba.

Washe gari sbd zazzabin data dauka zai sauka kafin safiyar yasa tayi lattin tashi jikinta a matuqar zafafe da zafi Amma hakanan ta tashi taje tayo alwala tazo tayi sallah
Tana gamawa ta miqe ta fice Dan ayyukanta data Saba dasuke gabanta.

Kunun abbanta tafara damawa kafin ta soya doya tadafa ruwan Lipton ta juye a qaramin flask ta Kai Palo tadawo ta dauki na abbanta takai masa.

Cikin dauriya tayi aikin gyaran koina ta zauna tana bawa Abban abinci,
Daga fuskarsa Yana iya Jin hucin zafin jikinta dake hurowa
Take jikinsa yayi matuqar sanyi zuciyarsa ta narke da tausayin kansu dagashi har itan
Ya zuba Mata idonuwansa dasuka sauya Yana danne hawayen Dake kokarin gangaro Masa Dan karya qara Mata damuwa akan wannan halin datake cikin.

Tana Gama basa ta gyarasa ta fice zuwa gyaran palon Momy da dakunansu,

Daqyar tagama gyaran ta dauki kasko ta fita tasamo garwashi maqota tadawo ta zuba turaren wutar kadan ta aje palon Saida ya Kama koina har dakunansu kafin ta dauka takaiwa abbanta shima ya samu tadawo da kaskon tsakar gida ta aje.

Kicin taje ta zaunda Kan kujera ta janyo abincinta tafara ci taji Bata iyacin ta dauki Kofi taje ta debo kunun babanta kadan ta zauna acan tasaka kanta Sha Dole sbd Kar ciwon yafi qarfin hakan.

Tana gamawa cikin magunan abbanta ta dudduba tasamo paracetamol Wanda Yaya abdullahi ke ajewa Dan kansa shima ta balla biyu Tasha ta fito Abban na binta da kallo zuciyarsa na sake shiga hali na damuwa.

Shanyar Momy ta kashe tayi ciki dasu ta aje gefen kujera ta zauna qasa Dan tana lumshe fararen idanuwanta dasukai duhu ga jiri datake Dan gani.

Mintuna biyar ta dauka zaune agurin kafin ta miqe ta Kashi kayan ta dauko dutsan guga daga dakin anty Sa'adah tayi palon Abba sbd acan take guga Dan palon Momy tanada center carpet  bayan tayils din dake qasan batason a Kona Mata carpet shikuma palon abban tayils dinne kawai Dan Haka acan take gugar duk zafi kuwa ahaka take gugar ita zufa Abban zufa.

Qatuwar daddumar baqin Abban ta shimfida tazauna akai tafara gugar.

Har Saida Suka tashi daga barci suka fito gurin Sha daya kafin tagama gugar ta kwaso ta fito suna Palo zaune Momy tagama cin abinci tana waya da umma Jamila hamshaqiyar yayarta Mai abun duniya Kamar yanda take fada.

Anty Sa'adah dake Shan ruwan Lipton har lokacin tafara kalla cikin kulawa tace"

Anty Sa'adah antashi lfy?

Lfy kalau Laylah,
Gama abunda kike wani guri Zaki rakani
Yau umma Jamila nanan zuwa inason binta daga can yafimun kusa da hanyar makaranta sbd exams din zamu fara kinsanni da yawan bacci anan duk exam sainayi latti.

Ahankali ta gyada Kai tana sakewa anty Sa'adahn murmushi tace"

Allah yabaki sa'a Anty Sa'adah.

Satar kallon gefen Momy tayi kafin ta qarasa kadan gefenta cikin nutsuwa da girmamawa tace"

Barka da fitowa Momy.

Hannu kawai momyn ta iya amsa Mata dashi kafin tasaki murmushi ta juya ta shige dakin momyn da kayan gugar
tana shiga ta ajiye Kan gado ta bude Yar qaramar wardrobe din momyn ta jere Mata kayan tas ta cire na Anty Sa'adah ta aje gefe tafara gyaran gadon da momyn ta tashi
tana gamawa ta nufi toilet din dakin shima ta wanke kafin ta dauki kayan Anty Sa'adah din tafito dasu takai Mata nata dakin.

Ganin alamar yau momyn Bata fita yasa ta nufi dakinta takoma ta Dan kwanta Dan kanta Kamar zai tsage ga zazzabi.

Baccin wahalane ya dauketa har batasan yayi nisa ba Saida taji Ana tasata da qarfi
Bude idanuwanta tayi tana kallon anty Sa'adah dake tsaye kanta shirye cikin Riga da skirt na embellished atampa dark brown da gyale Sai qamshi takeyi abunta tace"

Laylah maza tashi muje
Yi sauri na tare Mana Mai napep a kofar gida yanzu zamu dawo ba jimawa.

Tashi Laylan tayi tana miqewa tsaye tace"

Bari na fadawa Momy to.

Aa muje kawai tasani.

Jan hannun laylan tayi suka fito dama da Dan hijabinta a jikinta
Sam anty Sa'adah Bata wani damu data bari ta Dan gyaggyaraba kafin fitar itadai tunda ba tube Laylan takeba bata damuba.

Suna fitowa palon Momy na zaune har lokacin tanata wayoyinta anty Sa'adah tajata suka fice har lokacin Bata saki hannuntaba.

Napep suka Shiga Saida suka hau titi ta kalli Sa'adah din tace"

Anty Sa'adah Ina zamuje ne?

Dariya anty Sa'adah tayi tana Ciro wayarta daga handbag dinta da ake Kira taga Kiran Nasir ne Mai nemanta taqi dauka ta maida wayar jakar tana cewa"

Umma Jamila zatazo muje na karbo dinki kafin mudawo tagama yininta muna dawowa wucewa kawai zamuyi nida ita.

Ahankali ta dauke kallonta daga kan anty Sa'adah din tana maidawa Kan Hanya tareda sauke boyayyan numfashi.

Anty Sa'adah da Baki daukoni munfitoba ai sbd aikin abinci da wasu ayyukan duk gasucan nabari,
Umma Jamila ma banajin komai Akan yanda takemun ba komai bane tunda ta haifeni nesa ma
Dan Allah mu koma gidan Anty Sa'adah.

Wani kallo anty Sa'adah din Tai Mata tana sakin tsokin mamaki tace"

Bazamu koma din ba saina karbo abunda muka fito karbowa.

Shiru kawai Laylan tayi tana sauraren fadan anty Sa'adah din akanta duk da dai tasan duk yanda takeda tauri da danne Abu tareda boyewa duk umma Jamila tazo gidan sai idanuwanta sunyi kwanan rashin bacci da wani Hali ranar sbd tsanar da umma Jamila din take Mata itada abbanta Dan kuwa da dama shi kansa idan tazo gidan sai ya zubda hawayen boye akan 'yarsa Laylah Dan kuwa bayyananniyar tsana tayiwa Laylah da Abban duk da shi kullum maganarta ya girbi cin amanarsa gashinan yagani.

Suna isowa shagon Mai dinkin yacewa anty Sa'adah Bai kammala ba
Dama hakan takeson ji Dan Haka ta nema guri Suka zauna tace ya kammala zata jirasa.

Kallonta Laylah tayi tana kallon agogon shagon cikin nutsuwa tace"

Anty Sa'adah karfe daya saura
Ni Zan koma gida
Kinga ban Dora abinci ba Kuma kada Momy tanason wani aikin bana Nan ga Abb....

quiet please Laylah,
Bazan barki ki komaba Zaki jira nagama tunda Nina fito Dake zamu koma tare so just sit quietly muyi zaman jira,
Fushin Momy na rashin aikinki yafi Miki zuwan umma Jamila so dubu.

Shiru tayi sbd Bata iya hayaniya ba bare tayita magiya saidai hankalinta gabaki daya Yana Kan abbanta da momyn,
Dan kuwa har cikin ranta qaunar uwa takewa momyn shiyasa Bata qaunar ta Bata Mata Rai.
ga zazzabin dake cinta har lokacin.

Zama yayi zama sune har la'asar Basu koma gidaba sai qarfe biyar Adaidaita sahu ta ajesu kofar gida
Anty Sa'adah ce agaba taba bayanta riqeda ledar kayan anty Sa'adah din suka shigo da sallama tun daga tsakar tasan Bata kyautaba qin dawowa da wuri sbd Yar dattin da gidan yayi na iska da aka danyi kamar za'ai ruwa.

Kallon inda su momyn suke zaune tsakar gida Kan babbar daddumar baqin girman momyn sun Gama cin abincin da aka kawo musu daga gidan umma Jamila din tunda yau baai abinciba Nan gidan suna magana hankali kwanci saidai shigowarsu yasa bacin ran da umma Jamilan ke dannewa tasowa ta kalli Laylah bayan ta amsa gaisuwar Sa'adah data zauna gefenta tana daukan ruwan robar swan Dake gurin ta bude tana sha
Tace"

Zainab haryanzu kin kasa gane illar jini,
Shi Abu idan akace a jininka yake to saifa iko na ubangiji,
Kinada 'ya mace budurwa a gabanki da kikewa fatar samun miji na hutawa da Jin Dadi kike Bari suna fita tare da yarinyar nan?
Ta Yaya kike tunanin namiji daya zai kallesu idanuwansa su kasa tsolewa da wannan kodaddiyar fatar ta jinin gado,
Mahaifiyarta da mahaifinta akwai wani gadon dasuka bar Mata bayan na jinin cin Amana ne,
Magana daya itace na soke fitar Sa'adah da laylan daga yau karna ji ko a labari wannan umarni nane,

Shine kina zaune zata saka qafa ta fice  ko aikin abinci Babu idanma kinyi baqin kunya Dole kece da tsufanki Zaki shiga kicin girka abinci
Ke kenan Haka rayuwarki zata qare a bautar Mahmud da 'yarsa bakya tunanin Taki Yar?
To Allah ya kyauta,
Sa'adah ma Inshallah saiki fara shiri ki fadawa Mahmud din babban 'dan Alhaji Sadiqu commissioner Dake aikin Lawyer a Lagos munyi mgna da  alhajin zasuzo neman aurenta
Allah yayi Kinga tasamu miji gidan Jin Dadi da arziki Kar aja wani lokaci ayi Mata auren tasamu ta tafi gidanta inda zatai irin rayuwar da kike Mata fatar samu
Kema Kinga kin samu nutsuwa shikenan Babu Wanda zakiwa wahalar nema saiki zauna abinda yazo kibasu Wanda baizoba saisu dangana shida 'yarsa.

Idanma bazaki iyaba Ni bayan auren Sa'adah din kiban laylan Dan masu aikina duk sun isheni wlh
Saina ringa biyanki kudin aikinta Kuna dawainiyar dashi kin huta ya komaima.

Momyn dai batace komaiba sai kayan wayarta datake dubawa tana hada Kan wani lissafi
Saidai fuskarta sosai ya bayyanarda farin cikin zancen mijin Sa'adah din da akai takumayi na'am da maganar auren saidai maganar Laylah batace kala ba duk da tariga tasan cewa tabbas Sa'adah tayi aure zamanta daga ita saisu Laylah din bazai musu dadiba su dukan Dan tasan zamanta a gidan zai iya karanci Dan kuwa zata saka kanta busy ne da yawon kasuwanci ta ringa Hana kanta zaman gidan

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login