Showing 39001 words to 42000 words out of 108894 words
qarasawa cikin toilet din ta nufeta lokacin tuni jikinta yasaki agurin ta zube jikin Cindy gaba daya Bata wani motsi.
Ihu Cindy tasaki tana Kiran sunanta da qarfin gaske cikin rudewa ganin Kamar Laylan Bata numfashi....
Kai tsaye shigowa yayi toilet din ya dauketa gabaki dayanta Yana cewa Cindy ta dauko Mata Kaya ta Sanya Mata.
A gado ya kwantarda ita ya juya ya bar dakin Cindy da duka jikinta ke rawa ta dauko wata doguwar Rigar bacci bataredama tasan abinda takeba ta Sanya Mata tafito ta fada Masa.
Dan shiru yayi Kamar Bai jiba Yana nazarin lafiyarsa idan yakuma hada jikinsa da natan Dan bayan fitowarsa Saida yaje yasha magani ya dawo.
Kallon A Abdoul daya iso Yana jiransa yayi Dan Dr Noah baya gari Dole asibiti za'a kaita.
Dakin yashiga ya daukota da kansa yakaita mota batareda ya lura da kayan da Cindyn tasanya mata Saida Suka Isa asibitin bayan an dauketa anyi ciki da ita A Abdoul ne ya kalli Cindy cikin Dan fada yace"
What was that??
Sauke Kai tayi saboda itama Saida Suka iso asibitin ta lura da abinda tasanyawa Laylan
Cikin damuwa da ban hankuri ta saci kallon inda Turaki ke zaune kamar baisan da tsayuwarsu agurinba murya na rawa tace"
I'm sorry sir I....
Abdoul kaita gida takawo wani kayan.
Daga Haka Bai qaraba ya duba agogon hannunsa Dan koma menene bayason su kwana a asibitin data farfado gida zasu koma.
Kaya kala uku ta dauko sbd gudun wani shirmen suka dawo asibitin lokacin har Laylan ta farko tana bacci Dan Haka drugs kawai suka karbo suka dawo gida.
Yana kwantar da ita ya bar qasan gabaki daya ya Haye sama Bai Kuma saukowaba har washe gari Babu Wanda yaga ya sauko breakfast Haka ya wuni Bai fito ba saidai A Abdoul daya damu sosai yayita kiransa karshe dayake Babu Wanda yake shiga samansa bayan A Abdoul shima tunda su Ms Na'ima Suka dawo qasar Bai qara bin hanyar saman ba Dan Haka hankalinsa ya tashi Sosai yayita Kiran wayar Ms Na'ima Bata dauka ba Dan Haka baida zabi bayan Kiran Anne.
Washe gari har dare ba Turakin ga wayayinsa a kashe Dole yanda Anne tace hakan zaiyi duk da yasan ran Turakin Zai baci Idan aka tura Masa Laylah dakinsa,
daddare yashigo babban palon qasa ya tambaya Cindy jikin Laylah ta tabbatar Masa da taji sauki sosai harma yau ta Dan fita taje makaranta.
Kira Masa ita yace Cindyn tayi
Ba jimawa sai gata tafito sanyeda doguwar jacket data Dora Kan kayan baccinta Dan tuni Tai Shirin bacci harma ta kwanta.
Cikin nutsuwa ya sanar da ita kwana biyu Turaki Bai fito ba wayoyinsa akashe shine Anne tace taje tadubosa tunda masu aikin gidan kaf basa zuwa gurin.
Shiru tayi tareda sauke kallonta daga kansa zuciyarta na harbawa da fargaban haduwarta dashi sbd abinda ya faru kwana biyu Wanda haramun ne gareta faruwar hakan,
Mijin yayarta Abokin mahaifinta duk da tsautsayine na ciwo da zuwan Abu Amma hakan ya tsaya Mata arai harta fara Jin kamar zamanta anan Bai kyautu ba duk da riqontane ake Amma sai tanajin tsoron zamanta nan Yana shigarta.
Kiran Anne ne yashigo wayarta tana dauka Kai tsaye Annen tace"
Laylah kije kidubo Mana Turakin ko lafiya hankalinmu duk ya tashi ga ba Wanda zai dubaso maza jeki kidubo Mana tun kafin Abu yayi nisa.
Jin hakan yasa gabanta faduwa ta dago ta kalli A Abdoul da duk yayi wani iri lokaci daya na rashin sanin halinda uban gidansa yake ciki Jin yake kamar yayi tsalle yagano lafiyar Turakin.
Da sauri ta juya ta nufi hanyar saman ta Haye gabanta na tsananta faduwa da sauri,
Bata taba ko kallon hanyar Master bedroom dinsaba sbd iyakacinta palon shima sai babban dalili idan ankirata kokuma taje Kai wani abin Dan Haka Bata taba kallon hanyar bedroom din nasa ba...
Tsayawa Tai bakin kofar tana Dan knocking kofar hannuwanta na Dan rawa,
Sake knocking takeyi tafara tsorata da Shirun itama Dan Haka taci gaba da bugawa tana jiran Jin motsi Amma shiru.
Rasa sanin abin Yi tayi ta daga wayarta da sauri ta saka Kiran Anne tana dauka Bata jira me Annen zatace ba tace"
Ba'a bude ba..
Laylah kishiga ki duba
Bari kawai nakira Abdoul ya hawo ya duba..
Komawa gefe tayi tana jiran tahowar Abdoul din sai gashi ya hayo da sauri ya qarasa dakin tareda knocking so daya ya Murda kofar yashige.
Sosai hankalinsa ya tashi da ganin yanayinda turakin yake Dake nuni da rashin lafiya sosai ataredashi saidai Kuma qarfin halinsa yasa Yana zaune Kan sofa tarin magungunansa birjik agabansa wainda yaketa faman Sha Amma erection dinsa yaqi sauka shiyasa ya nesanta kansa da fita ko Ina sbd kallo daya zakai Masa ka iya gano wani abin.
Ahankali ya dago idanuwansa dasukai wani iri yayiwa A Abdoul din daya shigo kallo daya ya dauke Kai yana bude Baki cikin dauriya yace"
Akwai damuwa ne?
Cikin tsananin kulawa da damuwa A Abdoul yace"
Hankalinmu ya tashi da rashin fitowarta Anne tabada izinin nashigo na duba,
Wayarsa yafara laluba Yana cewa"
Zankira Dr Allen yanzu na sanar dashi halinda kake ciki.
Juyawa yayi da sauri yafice Yana Nemo Numbern DR Allen.
Qasa ya sauko Laylah na biye dashi cikin sauri yace"
Ahada Black tea Mai zafi akai Masa Kar asanya sugar likita zaizo ya dubawa yanzu ba jimawa.
Gyada Kai kawai tayi jiki a Sanyaye
Ta nufi kitchen din da kanta ta Dora Masa tea din tana cewa siddika ta gasa Mata bread uku da kwai.
Tana gamawa ta hada a tray ta fito dasu ta nufi saman da tuni har A Abdoul yaje da gudun masifa yazo da Dr Noah duk da bashine likitansa na asalin lalurarsa ba Amma zai iya taimakawa.
Allurar da Dr Allen ya rubuto musu yanzu yanzun itace Dr Noah yayiwa Turakin tareda kallonsa cikin kulawa da nutsuwa yace"
Baka buqatan riqe kanka Haka sosai you have to let it out sbd zakaiwa kanka illa sosai tunda desire din tafara zuwane gadan gadan control nata zai fara wuya saidai Kuma saika lura sosai gurin having first sex din zai iya zuwa da tangarda.,
Amma dai for now Dole zaka daina kokarin dannewa lokacine yazo Dole zaka Bari abinda kakeji ya fita.
Dr Noah na fitowa tareda A Abdoul Dake Palo Yana jiransa Dan Bai shigaba tana shigowa daukeda tray din harma da fresh milk Mai sanyi kadan ta hado duk ta kawo.
Kallonta A Abdoul yayi Yana cewa"
Ki Kai Masa bedroom...
Ficewa sukai ganin dakin bude Kuma ganin Suma duk ciki Suka fito ya sanyata nufar dakin Kai tsaye tareda sallama Mai sauti Bata dagoba ta kutsa Kai dakin qamshin Bois elite na tashi tako Ina Yana rikita kanta da qafafunta Dake Dan rawa ta nufi table Dake dakin tafara kokarin ajiyewa.
Tunda tashigo Yana zaune a sofa Bai motsa ba bayan idanuwansa dasukai taushi Babu abinda ya zuba Mata Yana kallon yanda qafafuwanta ke hardewa
Tana dososhi ya dauke kallonsa daga gefenta gaba daya musamman qamshinta na Creed Dake tashi daga jikinta ahankali ahankali.
Tana ajewa cikin nutsuwa tace"
ALLAH yasauwaka yakawo afuwa.
Juyawa tayi ta fice tabar dakin da qamshinta dabaiyi qarfi da yawan nasa ba Amma hancinsa na Jin natan na shigarsa.
Da sanyin jiki tayi bacci hakama da safen da sanyin jiki ta tashi batareda tasan meya kawo Mata hakan ba Haka ta shirya ta tafi makaranta tagamo wuninta tadawo har lokacin batajin dadin ranta Sam.
Ms Na'ima lokacinda saqon Turaki na ticket da akai Mata booking na dowowarta yashigo wayarta tayi mamaki sosai saidai koda Laylah takirata ta sanar da ita bayada lafiya kwana biyu saita fasa dawowa Dan Bata Gama abinda takeba tunda ba wani abin zatai Masa idan tadawoba.
Kwana biyun sosai ciwonsa ya damu Laylah dake daukan hakan amatsayin kaga Wanda ya kyautata rayuwarta data mahaifinta dama ta Yar uwarta tagansa cikin Hali na ciwo.
Sam baya saukowa cin abinci yanzu saidai Cindy da A Abdoul yace anbawa damar Hawa Kai Masa abinci acan sbd har lokacin Ms Na'ima Bata dawoba.
Da wannan gidan yakoma kamar rayuwar kadaici takeyi sbd yanzu kowa Bata gani daga ita sai masu aiki take rayuwar gidan,
Kwata kwata ta daina ganin Turakin sbd ya yankewa kansa nesantarta sbd yanayin lafiyarsa ga Na'ima Bata dawoba Dan Haka yasaka kansa zama busy Sosai Sosai ko gidan Baya dawowa sai dare daya shigo Babu Mai sake ganinsa a qasa sai zai fita Kuma.
Ganin Haka ta maida hankalinta Kan karatunta itama ta rage zama gida sosai koyaushe tana makaranta ko gidansu Sofia.
Ahaka Ms Na'ima ta shanye kusan sati hudu kafin tadawo lokacin Turakin baya gari yayi tafiya Dan Haka sai gidan yadan dawo Mata daidai Amma hakanan takejin kewar su Anty Sa'adah.
Washe gari tana dawowa daga makaranta tana shigowa gida sai ganin Anne tayi A Palo zaune batasan lokacinda tasaki wata dariyar farin ciki ba tana qarasawa da sauri ta rungume Annen tana cewa"
Anty Sa'adah fa???
Da ido Annen ta nuna Mata bedroom dinta tana cewa"
Tana jiranki a dakinki hutawa takeyi.
Sakin Anne tayi ta nufi dakin ta tadda anty Sa'adah kwance kan gadonta tana bacci tayi wanka da alama Dan rigar jikinta bamai nauyi bace.
Kasa tada ita tayi ta aje handbag dinta tareda wayarta tana fadawa toilet da sauri tayo alwala tazo tayi sallah har lokacin anty Sa'adah Bata farka ba Dan Haka ta fito Takoma gurin Anne tana sake bayyanarda farin cikin zuwansu dayake Ms Na'ima Bata Nan tafita Koda suka iso.
#MAMUH#
[6/10, 9:18 AM] MG💋: *_Mamuhgee 22_*
Da kanta tashiga cikinsu Cindy sukai Abincin Daren gidan suna gamawa Takoma daki yin wanka ta tadda anty Sa'adah ta tashi
Cikin tsananin farin ciki ta qaraso gabanta tana cewa"
Anty Sa'adah sannu da tashi,
Kin gaji sosai ahanya.
Rungumeta Sa'adah tayi tana cewa"
Wannan Jin nauyin Yana Nan.
Dariya tayi tana qara rungume Anty Sa'adahn tace"
Nayi kewarki ganinki in person Sosai anty Sa'adah.
Sakinta Sa'adah tayi tana kallonta dakyau fuskarta daukeda murmushi da mamaki sosai a fili tace"
Masha Allah Laylah.
Murmushi Laylan tayi tana miqewa tsaye tace"
Zansa Miki qamshin abinci Bari nayo wanka Anty Sa'adah.
Toilet ta nufa tashige tayo wanka ta fito sanyeda bathrobe blue ta nufi gaban mirror ta goge jikinta sharp sharp ta shafa Mai da spray sai body mist ta nufi closet ta dauko Kaya ta saka Anty Sa'adah nata binta da kallo cikin burgewa da shaawa sbd duk yanda ta waye take ganin ta Gama zamowa wata shegiyar Ganin Laylah yasa ta shafawa kanta sbd laylah gabaki daya Babu abinda Bai Gama sauyawa nataba kwata kwata Bayan kunya da Jin nauyi Babu abinda ya rage na tsohuwar Laylah data sani,
Fatarta tagama gogewa Takoma asalin ta mahaifiyarta fara Sol
Hakama jikinta duk ya sauya,
Kayan Dake jikinta ta kalla lokacinda Laylan tagama sallar magriba ta zare Abayar sallarta
Rigane da wando na skinny jeans blue da black chiffon blouse da Bata kamata ba sai hula qarama akanta ta zuro slippers Suka fito cin abinci.
Ms Na'ima na dawowa ta tadda baqinda batai farin cikin zuwansu ba badan kowa ba sai Dan Sa'adah wadda batama San tanayiba
gabaki daya annurinta ya dauke Dan ma sbd Anne ta iya danne wani abin ta tarba Annen harma ta Dan daure taci abinci tareda su.
Sarai Anne ta fahimci rashin murnar zuwansu agun Na'imar Amma Bata damuba saima tausayinta data Dan ji wani bangaren Amma Kuma sanar da ita asalin kishiyar tata ayanzu ba alkhairi bane Dan zata cutatar da Laylan tunda suna guri daya.
Ganin yanayin Ms Na'ima baiwa Laylah Dadi ba sbd tasan Dan zuwan Anty Sa'adah ne duk da ta lura anty Sa'adahn ko ajikinta kamarma ba gidan mijinta tazo ba,
Sunyi fira a dakin Anne Amma dasuka koma dakinta firar Yan uwantaka suka bude Nan take sake Jin yanda su Momy suke Dan momyn takoma Nigeria ta Dade sosai Amma Takoma gurin Abban sbd ya farfado Amma baya iya komai Yana daga Nan kwance yanajin komai.
Farin ciki da godiyar Allah tahau Yi tareda bayyanarda zaquwarta tason zuwa gurin ganinsa tace"
Anty Sa'adah yaushe Zaki tambaya Momy sai muje muga Abban Dan Allah kafin ku koma.
Murmushi Sa'adah tayi tana cewa"
Ki fadawa Anne Zaki bimu kila ta yarda sbd daga Nan mu dama zamuje ganinsa.
Cikin zaquwa tace Zan fadawa Anne da mum Na'ima Inshallah zasu barni.
Da wani irin mamaki Sa'adah ta kalleta Jin takira Ms Na'ima da mum cikin zuciyarta dake cikeda mamaki da tausayi Tace"
Dake da ita Kuna cikin wani yanayi
Ita tana rainon Kishiya kema kina kiran Kishiya da sunan uwa.
Sai dare sosai suka Gama firar yaushe rabo da juna kafin Laylah takuma yowar wani wankan ta saka pyjamas dagama shafe shafenta tazo ta kwanta gefen Anty Sa'adah tareda shigewa bargo.
Washe gari da pyjamas dinta ta nufa dakin Ms Na'ima ta rarrasota ga fito sukai breakfast taredasu Annen da Anty Sa'adah da mamakin duniya na Ms Na'ima din yagama kasheta Dan kuwa qarara tsanartace bayyane da Ms Na'ima tun Bata tsarguba harta fara tsarguwa sbd tsoronta Ranarda Ms Na'iman zata gane waye Laylah agurinta komaima zai iya faruwa.
Bayan sunyi wanka Suka fito tareda anty Sa'adah da zata fita da ita yawo
Tana sanyeda long pencil skirt Ash da farar blouse sai kimono shrug data sanyi akai.
Yau Bata dauka Sofia ba daga ita sai Anty Sa'adah suka wuni suna yawo takaita gurare daban daban sai dare suka dawo Lokacin Anne ma ta fita Ms Na'ima ma daman bazata zaunaba tunda suna gidan hakama da gayya ta Hana masu aikin gidan suyiwa kowa abinci Laylah kawai akaiwa pancakes da akasan shi tafi ci yawanci da daddare batacin abinci Mai nauyi shiyasa jikinta yake yanda yake batai qiba ba.
Pancakes din sukaci suka kwanta Banda Anne da Dole akai Mata abinci kala biyu a Daren.
Washe gari ma yawo sosai sukai tareda Sofia Saida sukai kwana hudu suna fita kafin aka fara Shirin tafiyarsu dubo Abba harda ita murna gurinta da farin ciki Kamar me.
Ms Na'ima ba wani dogon zance tace aje da Laylan sbd a matse takeda su Annen su koma Dan Haka taje su tafi.
A Abdoul ne yayi musu komai na tafiyar a waya duk da baya gari suna Vegas tareda Turaki
Kai tsaye tareda Ms Na'ima aka siya tickets na tafiyar abisaga umarnin Turaki Amma taqi zuwa Dan Bata buqatan hada Hanya da duk inda Sa'adah take Dan zuciyarta ingiza take Dan Haka ta sharewarta taqi zuwa suka tafiyarsu.
Koda suka Isa LA jikin Laylah sanyi yayi sbd farin cikin yau zataga abbanta datai shekaru Bata ganiba...
A gidan Turakin Dake LA suka sauka duk da ba babbane sosai ba gidan zamansane shi kadai idan aiki ya kawosa Dan duka idan aka cire bedroom dinsa sauran dakuna biyu a agidan da makeken sitting room Dan gidan tsarin hutawane kawai.
Dayake Yana gari Dole a daki daya da ita da Anty Sa'adah suka sauka Anne Kuma a daki daya.
Baccin gajiya sukai kafin dasuka tashi sukai wanka sukaci abincinda cook yazo ya dafa musu sukai Shirin zuwa asibitin.
A Abdoul ne yazo da wata farar Audi8 ya daukesu zuwa asibiti Dan Turaki na gurin wani conference.
Sanye take da Riga da skirt na atampar Holland datai masifar Yi Mata kyau Wanda tuni ta manta rabonta dasu Dan Bata taba samun sakonsu ba tunda Babu Mai zuwa daga gida hakama itama batada Mai zuwan yanzun ma na Anty Sa'adah ce Kamar tasani taxo Mata dasu Dan idan zasu ganin Abba ta Sanya sbd koyaushe sukai video call taga qananun kayane jikin Laylan.
Batazo Mata da mayafi ba Dan Haka siririn qaramin gyaran Abayar rigar Anty Sa'adah ne a jikinta sai handbag dinta ta Lv da takarmin Versace Dake qafarta wedges.
Sa'adah ma lace ne ajikinta Riga da skirt daya fidda shape dinta dakyau saidai transparent gyalenta ya rufeta
Sai qamshin khumrahs din Amaryar kb masu dadin gaske Dake tashi jikinta.
A Abdoul ne yakaisu har kofar dakin Abban yakoma gefe ya bawa Anne Hanya tafara shiga kafin Sa'adah tabi bayanta sai Laylan daga baya wadda zuciyarta keta harbawa da qaguwar son ganin Abbanta.
Momy dake zaune tana amsa waya shigowarta kenan daga gidan da Turakin ya Kama Mata tana zama Sosai tashiga mamaki da farin cikin ganin Sa'adah Dan batama lura da Laylah dake bayanta ba sai daga baya...
Wani irin bugu zuciyarsu tayi dasukaga juna daga momyn har Laylan tayi saurin sauke kallonta daga Momy a matuqar ladapce da bayyanarda girman momyn agunta tace"
Momy Ina wuni?
Ya gida?
Akaron farko da momyn ta bude Baki ta Amsa gaisuwarta batareda takuma kallonta ba saita maida hankalinta Kan Anne suna gaisawa fuskarta daukeda murmushi Wanda duk na ganin Sa'adah ne data Gama sauyawa tana alfaharin ganin yarta akoyaushe yanzu sbd rayuwarta ta ingantu.
Laylah Kam qarasawa tayi gaban gadon Abbanta da idanuwansa suke bude Yana kallon sama takai hannunta dake rawa ta Dora Kan NASA tareda sake wani irin murmushin tsananin farin ciki hawaye nabin fuskarta
Ahankali ta furta"
Abbah.
Tana gani hawaye Suka biyo gefen idanuwansa da alama yajita yakuma ganta din
Da wani sabon farin cikin ta qanqame hannunsa tana fashewa da kuka Mara sauti tana share hawayensa Dake gangara tace"
Abbah nayi kewarka sosai
Allah yabaka lafiya katashi..
Anty Sa'adah ma qarasowa tayi cikin nutsuwa da kulawa idanuwanta na cika da hawayen tausayi da kewa tace"
Abba ya jikinka?
Allah zai baka lafiya Inshallah,
Zaka tashi kaga burinka na Auren Laylah da Turaki yacika kasamun Albarka ko akwance sbd na tabbatarda cikar burinka......
Tsit kowa yayi sbd subutar zancen da Sa'adah tayi gaban Laylah wadda itama dauke wutar tayi duk da zancen Bata wani fahimcesa illah ma saita Dan dago ta kalli Sa'adah da idanuwanta dake kaca kaca da hawayen farin cikin ganin Abbanta tace"
Anty Sa'adah Abbyana kukan farin cikin ganinmu..
Hawayen Abban ne suka ninka gudu alamar zancen Sa'adah ya shiga zuciyarsa sosai Kuma dukkaninsu sun gano hakan shiyasama Anne ta matso tayi Masa sannu tareda adduoi dakuma sake basa tabbacin Aure tsakanin Turaki da Laylah anyi shekaru yanzu kam saidai fatar alkhairi aciki.
Maganar Anne tasanya Laylah dagowa wannan karon tana kallonsu da kyau Dan yanzu zancen ya wuce subutar bakin Sa'adah da rudu tunda Anne tana fada.
Kan Momy ta maida kallonta zuciyarta na tsananin bugawa da tsoro da fargaba dama komai,
Dauke Kai akanta Momy tayi Kai tsaye ta juya zata bar dakin Laylah tayi saurin Shan gabanta tareda zubewa qasa idanuwanta na sauyawa ja murya na rawa tace"
Momy wallahi har abada bazan taba cutatar da Anty Sa'adah ba sbd ta wani bangaren kallon tamkar uwa nake Mata,
Har abada bazan taba kallon mijin anty Sa'adah da wani manufa ba daban bare hada wata muamala dashi ,
Momy wallahi ba......
Hannu momyn ta daga Mata tana sake dauke kallonta daga gefen Laylan tace"
Karki haramtawa kanki abinda yake halas gareki Dan Aure Kam Dake aka daura tun farko bada