Showing 99001 words to 102000 words out of 108894 words

Chapter 34 - NOOR ALBI COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

38

Middle Ads

tareda cewa"

Bazaki ko'inaba kina hankalina zai rabu biyu.
Ki jira idan kin haihu zakije gidan kafin ki koma US.

Riqe hannunsa tayi hawaye na ballewa daga idanuwanta tana kokarin tausar zuciyarta Amma takasa sai kawai kuka Mai qaramin sauti ya balle Mata.

Abbah bazai gane halinda zuciyarta take cikiba,
Tana tsananin sonsa Amma take nesanta kanta dashi sbd tashin hankalin da ake ciki,
Idan tana gidan bazasu taba samun damar magance komaiba har a zauna lafiya,
Gashi saidai taji qamshinsa kawai idan yashigo gurin Anne
zuciyarta na galabaituwa da hakan Wanda shima tasan Yana damuwa da hakan shiyasa bama zai iya tsayawa ayi gyaran ba,

Ita kanta kullum da kwanan tunanin Yana tareda mum Na'ima take
Shedan ya Hana zuciyarta sakat Dan Haka takeson tafiya gidan.

Kukanta yasashi zuba Mata ido Yana kallonta cikin qunci da damuwar ganinta ahalin ya janyota jikinsa ahankali ya rungume sbd baisan Me zai fada mataba,
Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan Bata kusa dashi ko Dan sbd irin wannan fitintinun na Na'ima..

Ahankali ya dagota daga jikinsa tareda Kai bakinsa yayi kissing idonta Dake tsiyayar hawaye ya kalleta ya bude Baki cikin Taushin murya yace"

Ya isa hawayen,
Zakije gida Amma Na'ima na Jin sauki aka dawo da ita gida Zaki dawo kin yarda?

Gyada Kai tayi tana tsayar da hawayenta cikin sanyin jikin kewarsa da zatai.

Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi tana Jin dumin hannunsa daya sauka cikin rigarta ya Dora Kan cikinta..

Lumshe ido tayi Ahankali tareda Kai hannuwanta biyu ta kamo fuskarsa takai bakinta Kan NASA ta Dora tareda Kama lips dinta ta tsotsa kafin ta zira harshenta cikin bakin ta kamo harshensa shima ta fara tsotsa.

Lumshe ido yayi tareda matso da ita jikinsa sosai ya karbe kissing din yanayi.

Sosai sukai kissing juna kafin ya saketa Suka ya miqe tsaye tareda daukanta yakaita toilet.

Da kansa ya tayata brush tayi tagama tayo wanka ya tayata shiryawa cikin doguwar riga purple Mai haske suka fito shirye tsaf suka nufa dining.

Suna zama Anne na dawowa Dan Haka kusan atare sukai breakfast din tana Binsu da kallon ikon Allah sbd gabaki daya yau Kam sun manta da Jin nauyinta sbd kewan junan da zasuyi...

Duk tabi tayi wani sukuku komai batajin dadinsa Jin takeyi tamkar zata rabu da 'barin jikinta,
Ga fargabar abinda zata tadda acan,
Ga fargabar yanda zata hada Ido da mahaifinta da qaton ciki a gabanta.,
Dan Haka duk tabi tayi sanyi.

Baiso tafiyar tata ba Amma damuwarta akan son tafiyar yasa yabarta taje din saidai yasan kwana uku zatai zaizo da kansa ya taho da ita yakuma sanarda Mahmoud ba maganar saki har abada a tarihinsa da matarsa Zainab LAYLAH.

Anne dataji maganar tafiyar Bata hanaba sbd Laylan dama tana buqatan matsawa daga wannan fitintinun kafin asamu a sauko da Na'iman sbd wannan damuwar da tashe tashen hankulan zai iya kawo musu damuwa akan cikin Laylah
Basa fata,basa buri Allah dai ya saukar musu da ita lafiya.

Dan Haka itace da kanta ta qarasa hada kayan Laylan sbd tuni A Abdoul ya siya musu tickets itada Ruky Dan Haka qarfe biyu da mintuna aka kaisu airport Suka wuce kafin Turakin yasamu komawa asibiti.



*******Yamma sosai jirginsu ya sauka suka fito Ruky na janyeda akwatinta
Ita hanbag ce kawai rataye a hannunta qarama.

Anty Sa'adah ce tazo daukansu Airport din da lafiyayyar motar Abbansu E-class da Turakin ya siya Masa.

Takowa suke ahankali zuwa gurin motar bayan Anty Sa'adah din ta tarbosu ta zubawa Laylah Ido cikin tsananin farin ciki da murnar ganinta da lafiyayyan cikinta dake bayyanarda tayi gaba yanzu saidai abita da kallon burgewa,

Fatarta da yanayin rayuwarta sun sauya gabaki daya tako Ina,
Komai nata Mai tsari da kudi ne na masu da akwai,
Kallo daya zakai Mata kasan Matar babban mutum Mai abun duniya ce sbd komai nata ya nuna Dan Haka sai murmushi anty Sa'adah keyi tana cewa"

Laylah zamtowa uwa shine babban abin farin cikin danake tayaki murna akansa yanzu.

Dan dago Kai tayi ta kalli Anty Sa'adah din dake tuqi tana maganar sai taji nauyin maganar ta kamata ta saki murmushin yaqe batareda tace komaiba.

Fira suke sama sama har Suka Kama ha Yar gidan qatoton gidan Turaki Dake garin ta waiwayo ta kalli Sa'adah a natse tace"

Anty Sa'adah gidan Zan zauna gurinku.

Dariya anty Sa'adah tayi tana karya kwanar titin da zasu shiga da motar tace"

Tun dawowarmu Muna sabon gidan Abba Turakin sbd wancan namu An rushe ana sabon gini.

Shiru tayi daidai Lokacinda suka iso bakin tangamemen gate din gidan Sa'adah tayi horn Mai gadi ya wangale musu gate din Suka shige.

Gabantane yafara faduwa tana shiga wani yanayi na fargaba duk da ta Saba da komai na dangin Momy Amma wannan karon Jin take fargaba Tai Mata yawa sbd batasan Yaya zasu karbi lamarintaba da cikin dake jikinta ita da akaje da ita da sunan riqo gata tadawo da cikin Mai gida a jikinta.

Babban sashensu Suka nufa Kai tsaye Laylan na tafiya jiki mace zucuyarta bugawa kawai takeyi Amma a natse take Kamar koyaushe.

Babban palon Suka fara shiga da sallama Wanda shine palon farko kafin kashiga kofar da zata kaika palon abbansu da bedroom dinsa da toilet dinsa aciki,

Gefe daya Kuma hanyace da zata kaika wani palon da dakunan Momy Dana Sa'adah suke ciki kowa da toilet dinsa sai wani qaramin dakin kusa da lafiyayyan kitchen dinsu na gidan masu abun duniya Wanda yake na Mai aikinsu ce hadiza.

Suna shigowa babban palon da Abban Dake zaune suka fara cin Karo Yana karatu a jarida idonsa sanyeda farin medical glass ya dago cikin tsananin farin cikin zuwan laylansa ya kallesu Yana sakarwa Laylah murmushi fararen haqoransa a bayyane Dan Bai lura da cikinba farko sbd idonsa akan fuskarta ya sauka Yana cewa"

Barka da zuwa Laylan......

Cikin dake gabanta ya sanyashi qarasa kalmar a rarrabe Yana kallon cikin dakyau.

Tabbatarda cikine a jikinta ya sanyashi kallon Sa'adah daketa washe bakinta cikin farin cikin murnar zuwan 'yar uwarta taga yanda Abban ke raba Ido jikinsa na neman yin sanyi tayi saurin cewa"

Abbah wancan takardan Daman na Laylah ne su Anne sun sani Suma tun lokacin..

Akaro na farko da Abban yaji kunyar yarsa Laylan Dan shi kunyama abin yazo Masa dashi sbd yagama sakawa ransa Raba auren sbd zaunawa yayi yai tunanin Turakin bazai taba karban Laylah Amatsayin matabe duba da shaquwarsa da Zainab uwarta dakuma duba da shine yabiya sadakin aurensu Dan Haka tako wane bangare Laylah dai bazata taba wuce wani matsayinba Bayan na 'yar cikinsa dazai ringa kallonta.....

Yanzu Kuma ga wannan al'amari ya bullo,
Kenan Koda yayi Masa maganar rubuwar shine yasa Bai Masa amsaba Kuma tun lokacin yake ignoring calls dinsa koma ya dauka baya Bari suyi doguwar magana sbd karya Kuma kawo masa zancen rabuwar kenan¿?

Wani murmushin farin cikine ya saukar Masa,Allah sarki Turaki nawa Ashe 'yar Zainab ce zata zama uwar yayansa shiyasa Allah ya kaddaro musu duk wannan qaddarar sbd wannan Rabon na haihuwa tsakanin Turakin da Laylah.

Kallon Laylah yayi da duk tagama muzanta jikinta yayi Sanyi cikin farin ciki yace"

Qaraso gurin Abbanki Mana Laylah..

Allah sarki Laylan Abbah,
ALLAH na gode maka daka ingantamun rayuwarsu kafin nabar duniya nagani.

Jiki mace har idonta na cikowa da hawayen kunya ta qaraso gurin Abban ta zauna ya riqo hannunta Yana kallonta yafara jero Mata addua tareda sannu da hanya.

Cikin Jin nauyi take amsawa tareda gaidasa.

Shigowar Abdullahi ne cikin farin cikin zuwan laylan ya qaraso Yana Mata sannu da zuwa yana kallonta cikeda kulawa da kauna.

Duk yanda takejin nauyin Saida suka matsa Suka rage Mata Jin nauyin tafara sakewa kafin suka tashi sukayi ciki.

Momy na zaune a Palo Kan lafiyayyar sofa tana waya da tsadaddiyar wayarta sbd yanzu Kam duniya tafara zauna musu tunda Turaki ya sake musu abun duniya suna Jin dadinsu shiyasa yanzu gidan koyaushe Yan uwanta suna hanyar zuwa.

Batasan da zuwan laylanba sbd Sa'adah Bata sanar Mata ba tunda itama yau din tasamu labarin zuwan na Laylan bayanma sun Isa airport kafin su baro A Abdoul ya sanar Mata.

Ido ta zubawa Laylan akaro na farko tayiwa cikinta kallon mintuna kafin ta dauke kanta daga kansu tana kokarin cigaba da amsa wayar saidai Sam taji takasa wayar ta kashe tareda aje wayar gefe tana sauke numfashi....


Momy Ina wuni?" Muryar Laylah data qaraso gabanta ta fada cikin sanyin murya.

Shiru tafara Yi kafin ta daga Kai ahankali batareda ta juyo ta kalli Laylan ba.

Sanin Babu abinda zata qara amsawa koda takuma wata gaisuwar yasa Sa'adah janta Suka nufi dakinta dake tsare da komai na Jin Dadi da kwanciyar hankali.

Zaunawa tayi bakin gado tana sauke numfashi sbd kwanciyar hankalin data gudo Nan Dan tasamu batajin zata samu din sbd kewansa da tunaninsa bazasu Bari ba.
##MAMUH#
[7/4, 7:29 PM] MG💋: *_Mamuhgee 54_*
Wanka tayi tareda alwala ta fito daureda towel Mai girma kanta sanyeda hula ta qaraso kujeran dakin ta zauna tareda daukan wayarta dake Hasken shigowan Kira Kuma vidcall ne Dan Haka ta waiwaya ta kalli kofar da anty Sa'adah ta fice kafin ta dauki kiran.

Kallonta yake yanda koyaushe fatarta take fresh,
Ya maida idanuwansa ahankali ya kalli wuyanta dayaga kaman yayi tsayi ya Dan dauke idonsa akai anatse yace"

Haryanxu kinajin damuwa ne?
Yaya gidan?
Zaki iya zama?
Ba matsalan komai?

Ajiyar zuciya ta sauke tareda kallonsa tana kokarin sake fuska sbd tasan tambayarsa ta yanayin rayuwarta dasu Momy yake mgn akai sbd duk da Bata taba sanar dashi irin Rayuwar data taso acikiba sbd koma yayane bata buqatan kowa yasani idan har ba Momynce ta nuna irin zaman dasukeba sbd har abada ita bazata daina daukan momyn matsayin uwa ba.

Sai data nuna Masa Babu komai hankalinta yafara kwanciya tukuna Suka Gama wayar tasamu ta shirya cikin doguwar Riga da hula Mara nauyi sai qamshin turarenta daya Gama cika dakin har Yana Isa Palo da sanyin qamshinsa Mai nutsuwa.

Sallah tayi tana idarwa Ruky da aka sauke dakin hadiza Mai aikinsu tashigo dakin daukeda fruits da aka shiryawa Laylan masu sanyi da tsafta ta aje Mata tareda kallonta cikin girmamawa tace"

Ma za'a dafa madaran ne?Naga basu dashi a fridge na duba.

No kibarshi Fruits dinma sun Isa Inshallah.

Ok Ma.

Juyawa tayi ta fice daga dakin daidai anty Sa'adah tashigo Mata da abinci lafiyayye data dafo Mata da kanta tana cewa"

Ko a aje Miki a dining abincin?

Murmushi tasake tana cewa"

Anty Sa'adah abincin mafa basai kin dauko da kankiba Ruky zata dauko,
Dan Allah ki daina aikin
Gatanan ta ki ringa sakata zatayi komai.

Abincin tafara daukan spoon ta saka cikin plate din fried rice da aka sakawa hanta da qananun Naman kaza sosai ta diba kadan tana kaiwa bakinta tafara ci ahankali sbd ba wani sosai takeson Naman kazaba tunda tasamu cikin Amma sbd kokarin anty Sa'adah taci sosai ba laifi tana gamawa suka fito A rakube ta wuce palon abbanta sbd ganin Momy Dake zaune palon tana amsa waya sbd Yan uwanta yanzu kowa yanayi da ita tunda sunyi arziki.

A palon abbanta tayi dare suna magana tsakaninta da Abbanta ya tambayayeta yanayin zamanta da Ms Na'ima yanzu datasan komai.

Sanar dashi komai tayi saidai Bata sanar Masa yanda Ms Na'iman ta gansu da Abban ba.

Sosai Abban yayi Mata nasiha Yana sake tunatar da ita mahimmanci hakuri da tawakkali akan komai tunda gashinan hakuri da barwa Allah komai yakawo haske da sauyi Mai girma a rayuwarta.

Ko data dawo ciki kowa ya shige Dan Haka Kai tsaye dakin anty Sa'adah ta Isa ta tube tayi Shirin bacci ta Isa bakin gadon ta kwanta gefe daya tana Dan dafe cikinta dake motsi.

Washe gari tunda safe kamar yanda ta Saba tana budurwa Bayan sallar asuba ta fito ta nufi dakin Momy tayi knocking ahankali tareda Murda kofar tashiga taganta zaune Kan daddumar sallah ta qarasa har gefenta ta Danyi kasa da kai kadan sbd bazata iya durqusawaba cikin ladabi da girmamawa tace"

Barka da asuba Momy,
Antashi lfy?

Batareda ta waiwayo ta kalletaba ta gyada Kai ahankali alamar amsawa tana cigaba da Jan carbin hannunta.

Juyowa tayi ta fito sbd tasan iyakacinsu kenan.

Daki Takoma ta zauna bakin gado tana kunna wayarta da Abbahh ya koya Mata kashewa duk zata kwanta daga bayan Nan sbd Kar aringa damunta alokacinda take bacci ga yanayinta Kuma.

Tana kunnawa Kiran Anne yafara shigowa ta gyara zama suna wayar harda tambayar jikin mum Na'ima tayi Anne tace taji sauki sosai ba laifi.

Suna gamawa Abbahh na Kira ta kalli wayar zuciyarta na samun nutsuwar ganin kiransa ta daga wayar tareda komawa ta kwanta jikin gadon tana amsa sunanta na asali daya kirata dashi.

Bacci Takoma bayan Gama wayarta da Abban Bata farkaba sai guraren 11 lokacin Ruky tagama Mata komai na abubuwan datasan tana breakfast dasu
Anty Sa'adah kuwa sai kulawa takeyi da komai data shafi Laylahn sbd har cikin ranta Jin so da kaunar cikin take itama harma takejin inama Allah zai nuna Mata ranarda zata raini nata cikin harma ta Haifa idan tanada rabo.

Momy kuwa da wuri ta shirya ta fice daga gidan sbd ganin kamar yarta takoma itace naiwar Laylah yanzu tunda suna zaune gidan mijinta,
Hakan ke son saka 'daci cikin ranta Dan Haka ta shirya ta fita Bata dawo gidanba sai magriba sbd qarin Bata kaunar Yan uwanta ko daya yazo gidan a yanzu,
Duk sukazo sukaga Laylah da ciki zasu tada hayaniya da Rigima ne kawai shiyasa duk qarin fitarta sbd idan batanan karsu zo.

Washe gari ma Haka ta wuni gurin harkokinta a cikin gari sai dare tadawo.

Itadai Laylah koyaushe tana tareda abbanta da anty Sa'adah dasuke debe Mata kewa da Bata tsananin kulawa da kauna,

Wata tsananin shaquwa da sabuwar kauna suke nuna Laylan da cikinta Wanda wasu lokutan sai taji jikinta na yin sanyi har hawaye takeyi idan taga yanda anty Sa'adah ke Mata ta.

Ta bangaren abbanta koyaushe sake tunatar da ita yakeyi karta taba riqe abinda Momy ke Mata a ranta sbd koma menene itace ta zauna dasu alokacinda suke basuda kowa Kuma tunda Bata taba cutatar da itaba shi ko ahakan Yana godiya.

Da wannan take sake girmama momyn duk da duk wani girma da kaunar momyn datake sbd itace ta Haifa Anty Sa'adah,wadda takewa kallon uwa awani bangaren.


******Ms Na'ima taji sauki sosai tadawo hayyacinta hakan yasa Zinat ta sakata taqi Kara ko kwana asibitin sbd Kar a zurfafa bincike akanta agano batada hankali cikakke
Dan Haka Kai tsaye Ms Na'iman ta tattara ta tafiyarta gidan Haj zinat batareda ta sanarda Turakin ba Saida Dr faruk yakirasa ya sanar dashi cewan ta tafiyanta.

Cikin nutsuwa Turakin yace"

Ba damuwa tunda tasamu lafiya,
Kawai dai ayi gaggawar bincika syringe din da aka samu gurin bincika sanadin gobarar sbd ba daya bane Wanda aka samu kusan gudan biyar ne,
Inason sani menene takeyi da alluran koma wane irine.

Inshallah Allah sir Turaki Muna Kan bincikawa cikin qanqanin lokaci zamu Gama dubawa,

Sai maganar results din Ms Sa'adah shima ya fito tana tareda _Leukemia_ Sir and tayi nisa.....

Shiru Turaki yayi cikin wani yanayi Mai girma daya taba zuciyarsa..

Mahmoud da momyn Sa'adah din yafara Jin sun tsaya Masa arai kafin A Abdoul dinsa daya Riga yasan maganar Dake tsakaninsu Bayan yasan A Abdoul dinsa Bai taba soyayya da kowace mace ba sai akan Sa'adahn...

Gangaro da tunaninsa yayi akan tasa Matar da batada kowane makusanci bayan Sa'adahn take yaji zuciyarsa ta karye da labarin.

Cikin nutsuwa ya bude Baki yace"

Menene nisanta??

Ajiyar zuciya Dr faruk ya sauke cikin sanyin jiki shima yace"

Tayi nisa sosai sbd inaga ta Jima tana samun symptoms dinta Amma Bata saniba inaga kokuma tasani Bata tana zuwa ganin likita ba.

Dr faruk ka shirya Mata ganin likitan cancer dayakeda qwarewa da sani sosai akowace qasar yake cikin gaggawa zai duba ta.

Inshallah Allah Turaki zanfara aikin hakan ayau dinnan.

Yana Gama waya da Dr faruk kasa sanar da kowa yayi sbd Babu Wanda abun bazai tababa acikin mutanen Nan Dan Haka yasa A Abdoul yayi masu booking tickets na tafiya.


Na'ima yafara Kira dan jinta itama Amma taqi daga wayar yana kashewa massage dinta yashigo wayarsa cewar zata zauna gurin Zinat kafin agyara Mata sashenta Dan Haka yabarta tasamu nutsuwa anan din kafin kwana biyu.

Yana gama karanta massage din ya kashe wayarsa ya aje gefe Yana sake shiga nazarin rayuwar Sa'adah da Allah yabawa kyakkawar zuciya Ashe tanada tata qaddarar agabanta itama.


Haj Zinat data turawa Turaki massage din ta ajiye wayar Na'iman a gafe tareda kallon siddika Data dauko Mata wayar daga daki Na'ima na wanka tace"

Tafiya zamuyi gobe tunda safen Kuma goben zamu dawo karki kuskura Koda Wasa wani yasan munyi tafiya munbar garin Abuja a goben.

Kallonta siddika tayi cikin tsoron fadar abinda ke bakinta tace"

Akwai yiyuwar Anne zata iya zuwa Nan din dubata idan tazo mezance Mata?

Wani mugun kallo Haj Zinat tayi kafin tace"

Kice munje asibiti kokuma kice munje siyan kayan sawar Na'iman tunda kusan komai ya kone.

Gyada Kai siddika tayi tareda juyawa tabar gurin Takoma daki.

Waya Haj Zinat ta dauka ta lalubo wata number tasaka Kira
Ana dauka tace"

Komai ya zama ready kufara wucewa yau zamu sameku goben acan.

Kashe wayar tayi tareda miqewa daukeda wayarta data Na'ima ta nufi dakinda Na'iman take tana shiga ta aje Mata tata wayar ta fito.

Bata fadawa Na'iman komaiba Saida tasa aka siya musu tickets din tafiya da daddare sun fara cin abincin Na'iman na zaune tarasa meyake Mata Dadi acikin Rai,
Bata cikin nutsuwa zuciya data ruhi
Qunci da damuwa takeji sosai wanda ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi,

Zinat ta kalleta cikin son sake cakuda Mata qwaqwalwa ta gyara zama ta kalleta dakyau cikin yanayi na bayyanarda damuwa tace"

Na'ima ki nutsu kiji sauran gaskiyar da aka rufemu baibai akanta sbd yaudara da son zuciya irin na Anne Dan wlh itace taci mafi girman Amana a lamarin..

Ba cikin shege neba a jikin Laylah,
Ciki dai Dan halak ne,
Dan cin Amana, Dan zamba cikin aminci,
Laylah itace asalin matar Ba Sa'adah ba.......

Abincin Dake bakin Ms Na'ima ne ya dawo Mata da qarfi tana sakin wani tari Mai qarfin gaske ta dauki cup da sauri zata Sha ruwa Haj Zinat ta jefa Mata wata qaramar qwaya aciki batareda ta Ankara ba takai ruwan bakinta Tasha tanajin zuciyarta na balbalowa da wuta....

Wurgi tayi da cup na glass yafashe ta kalli zinat da idanuwanta dake neman sauyawa tace"

Wlh bazai yiyuba,

Laylan ce Matar Turakin?

Kishiya ta ake nufin na Raina?

Ba gaskia bane sbd yamata ciki ne zasu boye mutuncinsa suce ita matarsace Amma qaryane,
Bazai yiyuba tana matarsa shekaru masu tsayi bansaniba......

Riqota Zinat tayi Dan qarasa yamutsa kanta da qwayar data Bata tace"

Gskiyar kenan Na'ima,
Laylah matar Turaki ce Kuma uwar yayansa tunda gatanan da cikinsa a jikinta,

Abin haushi da baqin ciki ke yanzu ba lallai ki haihuba tunda qwayoyin ciwonki sunada qarfi zasu iya lalata qwayoyin haihuwarki Dan Haka bazaki taba yardaba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login