Showing 3001 words to 6000 words out of 165653 words
mai tsananin Kama da shi ta bayyana, tana fitar da numfashi, cike da nutsuwar da ta daddage ta sakawa kanta adole.
Kanta ya d'ora saman cinyarsa, ya tattare mata dogon gashinta, ya d'aure shi ya saka mata ribbons.
Har yanzu murmushi yake, yana kallon kyakkyawar fuskarta sosai suke tsananin kama.
Juyi ta fara ta shige jikinsa ta tura kanta tsakiyar k'irjinsa, tana sauke numfashi cikin nutsuwa, wanda ba k'aramin namijin k'ok'ari ta yi ba, tare da temakon daddad'an k'amshinsa wanda ya saka taji nutsuwar gasken lokaci d'aya. Cikin sanyin mgnarta ta kirasa, da amon muryata mai zak'in gaske.
“Abie nah!â€
“Na'am Baby ummina!â€
Shiru yaji sai sauke masa hucin numfashinta take atsakiyar k'irjinsa, wanda yake jiyo bugun zuciyarta da sauri², alamar baccinta take.
Duk'o da kansa yay, ya sumbaci kumatunta da goshinta, ya mayar da kanta saman pillow ya kwantar, ya runguma mata Teddy d'inta, ya lullub'eta kamar yadda ya iskota, ya mik'e ya nufi k'ofar fita. Taku d'aya biyu uku, ya juyo.
Cikin daddad'ar muryashi ya ce.
“Ya ubangiji ka tsaremin 'yata ka bata miji nagari wanda zai sota da dukkan zuciyarsa, tsakaninsa da Allah badan abinda na mallaka ba! ya kulamin da ita fiye da yadda nake kulawa da ita, Ameen ya Rabbil Al'amin.â€
Ya amsa ya juya ya bud'e k'ofar ya fice ya rufo mata k'ofar, ya zura hannayensa cikin aljihu ya fara takunsa mai nagarta ya shiga taka steps da bibbiyu cikin kuzari da lafiya.
'Bangaran Raiyana kuwa bayan Abdul Majeed ya korata, part d'inta ta tafi cike da tsoron abinda zai biyo baya.
Cikin tashin hankali ta Kira auntie Saro, da harshen larabci take magana hankalinta atashe.
“Hello Auntie Saro kina ji, wlh mutumin nan sai nayi da gaske fa! Haba! Dan ni na nuna masa so haka kawai sai ya tauyemin hakk'ina akan k'udirin banzan shi, na kasa gane inda ya saka gaba, fafur yak'i amince min, mace da aka sani da Jan aji ni nake kai kaina wajansa amman shirune, inaga fa da gaske baida lafiya b'oyewa yake dan kar duniya ta sheda. Yo idan ba haka ba, ayadda nai masa tijara yau tabbas da ya rufar min ta k'arfi, aure wata 3 ace namiji bai kusance ka ba.â€
Daga can wacce aka kira da Auntie Saro wata jibgegiyar macace, 'yar kimanin 37 years zaune ta hakimce tana yagar cinyar kaza, tana korawa da sansanyan drink, ko uban sanyin nan da ake zubawa ba taji.
Tanada kyau sosai farace tass. Kallo d'aga zaka mata kasan shuwa arab ce, ga tsantsar kama nan ita da Raiyana. Sake yagar cinyar kazan tai ta ce“
“Kai! Raiyana bakida hankali Ashe? Sbd Allah bak'in ciki zaki mana? Badai kina sonsa ba ya kuma aureki darajar mahifiyarsa da son da kike masa, ki tuna irin bak'ar wahalar da mukaci kafin ki shigo gidan, sannan ki tuna ya ce miki zaki basa lokaci sosai koda kunyi aure kafin ya waiwayeki, kika ce kin amince. Meye damuwa tinda kina gidan? Sannan gamu cikin daula? Haba ki tausaya mana mn, wlh nasan zai waiwayeki kinsan manyan mutane bai cika zama ba, sannan ya gindaya miki sharud'a kafin aurenku amman yau duk kin manta sabida kinci kin k'oshi yanzu abinda yake gabanki.... Bari kiji wani abun....â€
Tsaf cikin wayo da siyasa ta samu ta ciyo kan Raiyana, har ta ajiye k'udirinta na sai Abdul Majeed ya kusance ta adole sai yanzu ta tuna sharud'ansa na duk yanayi da taga suna ciki zatayi hkr ta amsa da eh.
A hawa na 1 yaci karo da Raiyana ta fito daga bedroom d'inta tsaf ta sake shigar kaya.
Ko kallon arzik'i bata ishesa ba ya sa kai yabi ta kusanta zai wuce.
Gabansa ta Sha tana washe baki kamar ba ita bace tagama gaggaya masa bak'ak'en maganganu ba!
“Abein ummi sai yanzu za'a fita? Allah ya tsare ya bada sa'ar abinda akaje yi. Ina ummi ko bata farka ba? Dan naji Ammi na fad'in shayi ta sha kad'ai.â€
Ta k'arashe mgnar kamar zata rungume shi.
Da sauri ya kauce yana watsa mata kallon kin raina min hankali.
Sai kuma ya saki lallausan murmushi aransa yace“Shi fa yak'i d'an zambane, kamar ba d'azu ta gama sunan tijara ba.
Kallonta yay ya ce“Eh bacci take idan ta tashi ki kula pls har ta ci abinci sai kuzaga gari ta motsa jikinta, bye.â€
Ya tafiyarsa.
Yawun kwad'ayinta ta had'iye, ta bisa da kallo, tana ciza lips.
Ummin Adnan ta shigo da sallama ta rusuna da harshen larabci ta ce“Barka da warhaka Jaddatu Rahamu.â€
Latifa ta rusuna can nesa ta ce“Jaddatu ga ummin Adnan d'in zan iya tafiya zuwa aikina? Ko na tsaya anan ko matsae k'afa na miki kafin Rahma ta farka?â€
Jaddatu Rahamu ta kalleta, ta d'aga sandar hannunta ta kwad'awa Latifa ta goce ta mik'e aguje ta nufi hanyar kitchen, tana fad'in.
“Yau shi kenan banda izinin walawa, sai na fad'awa Rahma ta shiga tsakanimu, wanga tsohuwa Allah shi shiryeta.â€
Ta k'arashe mgnar tana bin hanyar da zata kaita kitchen.
“Kiyi hak'uri Jaddatu.â€
Cewar Ummin Adnan.
Jaddatu Rahamu ta kurb'i shayi ta ce“Ummin Adnan nasan ke ba munafuka bace, don Allah me Latifa tace ne da yarensu na Hausa? Shiyasa na ce bana sonta amman Rahma ta matsa wai abarta tanada kirki, yau tsawom kwana 6 banga kirkin da take min ba, bayan sace-sace da lek'e-lek'e acikin gida.â€
Ummin Adnan ta danne dariyata ta ce“Allah ya wuci zuciyarki Jaddatu kiyi hkr za'a mata fad'a, yabonki tai da hausa ba zagi ba.â€
Jaddatu ta ce“Ai ke na yarda dake je ki d'auko min wayana ad'aki na kira Abien Rahma.â€
Cikin girmamawa ta mik'e zata tafi sallamar sa ta kard'e wajan tare da sansanyan k'amshin turAddu'asa.
Ummin Adnan ta zube tana gaishesa cikin girmamawa.
Ya amsa fuska a sake ta mik'e.
Jaddatu Rahamu ta ce “Kije ma aikin ki tinda ya fito.
Da “Tohâ€
Ta amsa ta koma wajan aikinta.
“Wai duk sanyin ne Abein Rahma?â€
Cike da ladaba ya zube k'asan k'afafunta yana gasheta.
Cike da sakin fuska ta amsa, tana fad'in.
“Fatan kana lfy?â€
Kai ya jinjina ya ce“Alhmdllh! Ala kullun halin Ummi. Bari na fita na makara sosai inada meeting bayan azuhur.â€
Addu'a tai masa ya sumbaceta agoshi ya fice.
Tin daga nesa securities suka tsinkayo shi, har rigai² suka wajan bud'e masa mota.
Cike da girmama ma'aikatan wajan mutum 7 kowa da aikinsa Kama daga mai kula da lambu da mai kula su talato talato d'awisu jimuna tantabaru aku da sauran abin kiwo. Masu gadi mai wanki mai bawa flowers ruwa, dukkansu suka gashesa cike da girmamawa.
Fuskar shi sake dukkansu ya bek'a musu hannu suka gaisa. Cike da dattaku cikin muryasa mai taushi ya ce.
“Am! Yahuzaya anjima idan ummina ta farka daga bacci zaka kaita wajan shak'atawa, k'ila da amminta pls waje mai kyau ok?â€
Cike da girmamawa ya rusana yace “Ok Yallab'ai insha Allahu.â€
Kai ya jinjina ya nuna Abbas da Khaleefa cikin securities d'insa ya ce“Yauwa Abbas and Khaleefa ku jira ummina ta farka zaku fita da ita awannan farar mota.â€
Cikin girmamawa suka masa.
Ya shiga bayan bak'ar motar securities biyu suna gaban motar kusan direba.
Jarida Abie ya d'auka ya fara karantawa.
Tin kafin direba ya iso d'aya daga cikin masu gadin au 2 ya na sanye da uniform ya wangale musu k'atoton gate mai girman gaske, kalarsa golden.
Rahma da take tsaye ta k'urama motar Abie ido har lokacin da motar sulale ta fice daga gidan.
Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfin gaske, hawaye na silalowa daga cikin k'ananun idanunta masu matuk'ar haske, wanda b'acin rai ya saka ya canza Kala.
Sosai hawayen ke zarya saman kyakkyawar fuskarta, ta rufe glass d'in window tana Jan labulen, taja k'afafunta dakyar ta koma ta zube saman Royal bed d'inta, tana sakin wahalallan kuka, mai tsuma zuciya.
“Allah sarki Abiena, Ya Allah kaima ya baka mata ta gari wacce zata kular min da kai tasan darajarka ta zauna dakai akowane hali, ya Allah ka saka Abie mai lafiya ne ba gaskiya bane abinda take fad'amaka, na tsani Raiyana tinda har bataga girmanka ba take maka rashin kunya.â€
Su na fita daga gidan Abie yacema direba.
“_*Hôpital de la Renaissance*_â€.
Direba ya amsa cikin girmamawa“Ok Yallab'ai.â€
*Niger*
💃ðŸ»TAHOUA lele birnin adar.
Unguwan ( *Geban zogi*)........... Billahi akwai k'ura😹ðŸƒðŸ»â€â™€ï¸
*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*
TSINTACCIYA
Nimcyluv
SULTAN
mss flower
BAK'AR FATA
AUTAR MANYA
Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218
*Real Ladingo+22796515805* For more information😇
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu baðŸ™ðŸ¼.*_
2/2/22, 09:18 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_
*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_
*🔥FITATTU HUƊU🔥*
_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
_*cнapтer 5&6*_
Gidane ginin jar k'asa mai d'auke da d'aki biyu k'wal, sai d'an filin da baida larewa.
Matashiyar budurwa ce ta fito daga band'aki rik'e da bokiti, alamar wanka ta yi, jikinta na d'igar da ruwa, sai turo baki gaba take tana game jikinta waje d'aya alamar sanyi take ji.
'yar kimanin shekaru 17 ahaife, kyakkyawa fara mai kyan sura ba laifi, komai na jikinta ubangiji ya tsara mata shi daidai ita, ba abinda yake mata kyau irin wushiryata da dimples d'inta idan tana murmushi, tanada gashi babu laifi yanada d'an yawa, gata mai yawan fara'a da son mutane, ga kirki.
Wata fara mata zata kai shekaru 40 alamunta zatayi fad'a tana bakacen masara da zasuyi girkin dare wajan sarrafa tuwan tsaki da ita.
Da harara tabita ta ce“Wallahi Ibtisam idan kika min jajen mura zakici ubanki tinda jarabarki bata k'arewa, daga wancan ciwon ki kwanta wancan, mu kullun kud'inmu wajan miki magani yake k'arewa, gaki ba wani tsayayyan saurayi mai zuciyar kulawa dake...â€
Tanko da yake shigowa cikin gidan yay caraf ya ce“Eh kekuma lashe money ba! Wlh Laraba ki rabani da mugun hali karki b'atamin yarinya, shiyasa Yaya Karime ta ce na turata wajanta, wlh na kusa d'auketa kiji da k'ananun 'yaran tinda baki iya mgna ba! Ya zaki dinga jayoma d'iya budurwa kamar Ibtisam jaraba? Kinsan tasirin bakin uwa jikin d'anta? Sannan kice kina son rayuwarta ta yi albarka? Kike mgnar saurayi Ja'afar ai namijin duniyane inace duk mafi yawan siyan maganin bawan Allah nan shi ke siya? Dan haka dan Allah ya masa bud'i na abin aure idan yaje bid'ar ya dawo zan basa Ibtisam, sabida nasan ba zata tozarta ba.â€
Laraba taja tsaki tana had'e gira sama da ta k'asa, ta ce“Ai kaji hamm wannan yaron mai bak'ar zuciya da girman kan tsiya kamar ba d'an Malam Adamu mai panpo ba, da Hansatu mai waina ba, yaron da zai shiga duniya zamu jira? Wlh da wannan gwara kawai taje wajan Yaya Karime d'in.â€
Tanko ya girgiza kansa ya ce“Allah ya sawwaqa.â€
Ibtisam ta ajiye bokitin tana langwab'ar da kanta gefe,ta shagwab'e fuska tana diddira k'afafunta cikin zazzak'ar muryanta ta ce“Baba ni dai Ku sakamun albarka, zata bini, ni ba inda zanje Cameron ta yi nisa ni dai ina sonku ba zanyi nesa daku ba.â€
Tanko ya ce“Insha Allahu albarka na tare dake.†tsalle tai ta shiga d'akin da yake mallakinsu ita da k'anninta, ta shirya domin zuwa wajan sahibinta.
“Tanko ni sai ka tsinemin nabi duniya kaji.†ko takanta bai bi ba ya shiga cikin d'akin domin d'aukar abinda ya kawo shi.
Unguwan Moray Gidane na jar k'asa shima, wanda yake d'akuke da dakuna hud'u acikinsa.
Na farko yanada kewayensa, daban yayin da sauran suke game a kewaye d'aya. Na Malam Adamu sai na inna Hansatu mai waina da na Sailuba Deluwa.
Gida sai shige da fice ake 'yan siyan waina, inna mai waina macace 'yar kimanin shekaru 45 kyakkyawace bak'ar buzuwa, mai shegen surutu da son kud'in tsiya, amman ta iya neman na kanta.
Deluwa tana gefe tana kallon ikon Allah, inna ta washe baki sai labarin tafiyar da Ja'afar zaiyi take fad'awa duk wanda ya shigo.
“Dan Allah Ku jira na k'arasa bawa Hashimu jinya yake bai jima awaje.
Ni kuwa Hashimu na ce Anya ta rasulu ba ciwon daji bane kuwa?â€
Hashimu haushinta yaji sosai yaga me ruwanta da lamarinsu daga zuwa siyan waina?
“A'aâ€
Kawai ya ce bai sake tanka mata ba, dan yana jin shayin Ja'afar da sai ya gayamata mgna, toh gayen ne ba sauqi mugun tsoron sa ake, shegen k'arfine da shi, ga saurin hannu, bugu d'aya idan yama sai ka kai k'asa.
har ta basa wainarsa ya tafi bai kulataba ta gama surutun .
Cikin sauri yake had'a kod'add'un kayansa, wad'anda suke wanke tass sunsha turare, ya zuba cikin jakarsa ta matafiya wacce ta d'an ji jiki.
Matashine d'an kimanin shekaru 28 bak'ine kyakkyawa mai manyan idanu masu haske, akwai dogon hanci, yanada fad'in fuska kad'an, wacce take zagaye da saje mai kyau.
labb'ansa bak'ak'e kamar mai shan sigari, yanada yalwatacciyar sumar kai da ta ido haka gira, yanada tsayi sosai ingarma namijine sosai yanada cikar zati, mai k'iran k'arfafa jikinsa duk a mummurd'e.
Ma sha Allah yanada kyau sosai duk da yana bak'i kyawunsa na musamman ne, ga kwarjini da farin jinin 'yan mata har mazan ma, nason abuta da shi, matsalarsa shi d'an ra'ayine, ko za'a mallaka masa duniya idan abu bai masa ba, toh an wuce wajan.
Sosai 'ya'yan masu kud'i suke rubibinsa da masa kyaututuka amman ko sau d'aya bai amsa ba bai kuma basu dama, Ibtisam har kusan kasheta wata yarinya tai zata taketa da mota akansa sbd itace zab'insa.
shiru² ne bai fiye mgna ba sam arayuwarsa, yasan neman na kasan bai k'arasa kartuba sabida rashin larewa duk yadda yake da masifar ilimi tinda ya yi (BAC) har sau 3 bai samuba ya watsar sabida zuciyar masifa yakeda, sam baison raini ko zaka mallaka masa duniya, ya sani sarai aikinsu ake siyarwa 'ya'yan masu kud'i shiyasa yake masifar jin haushin masu kud'i, sun tara sunacin gumusun suda 'ya'yansu bai ishesu ba ilimin nasu ma sai an siyar musu, shiyasa sam baya alak'a da mai kud'i.
Ganin karatun bai d'oreba ya shiga neman kud'insa sana'a kowace iri indai ta halal ce yi yake, ba ruwansa da girman kai, raini ne bai so.
Ya idar da shirinsa yana sanye da k'ananun kaya sun masa kyau duk da ba sabbi bane, amman sun amshi murd'add'an jikinsa.
Yana tsakiya da fesa turare ta fad'o d'akin kamar an jefota.
Jikinsa ta zube ta k'ank'ameshi tana sakin kuka mai cin rai.
Wata irin zazzafar iska ya feso daga bakinsa, yana ciza bak'ak'en lips d'insa, ya d'ago da kanta ya kafamawa kyakkyawar fuskanta, manyan fitinannun idanunsa, komai baice ba ya zagaye bayenta da hannayensa, yana bugawa asannu, alamar lallashi.
Kuka take harda shashek'a.
Wani irin fitinannan numfashi ya fizgo dakyat, ya fesar, cikin kamalarsa, da muryasa mai fitar da amon dad'i cikin tausasa murya ya kira“Mon cÅ“ur!â€
Wani irin zirrrrr yarrrr Ibtisam taji adukkan illahirin jikinta, wanda sai da tai saurin nutsa kanta tsakiyar faffad'an k'irjinsa.
Cikin shashek'ar kuka ta amsa“ Na'am Mon Amour.â€
Cikin kunnenta ya rad'a mata kina sona?â€
Kai tsaye tace“Har na koma wajan mahaliccina Mon Amour ina sonka.â€
Wani guntin smile ya saki wanda ya bayyana fararen hak'oransa, ya kuma k'awata masa kyawun fuskar ta shi, ya janyeta jikinsa ya kamo hannunta suka zauna gefen yamutsatsar katifarsa.
Ya ce“Abdan muna tare ko wata uku nayi idan na samo kud'in auremu zan dawo muyi aure sai mu koma ok?â€
Kai ta jinjina tana kwantar da kanta saman cinyarsa tana mak'ale da hannunsa cikin nata.
Ahankali ta shiga jero masa kyawawan addu'o'i yana amsawa da Ameen can k'asan labb'ansa.
Kod'ad'iyar wayarsa kira Itel ta d'auki ringing.
Ganin sunan ya saka shi d'aukan kiran yana sallama.
Ko me akace oho ya amsa da “Ok 15 minutes ina zuwa.â€
Ibtisam ta sanya masa kuka tana shigewa jikinsa.
“Pls my Ibtisam.â€
Dakyat ya iya furta hakan yana d'ago da kanta ya shiga shanye mata hawayen fuskarta da harshensa yana buga bayanta.
Kiss ya mata agoshinta, bayan ya zuk'e hawayen ahankali ya furta“Na baki amanar kanki Mon cÅ“ur, ki kularmin da kanki, zan kular miki da kaina.â€
Cikin kukan dake son taso mata ta ce“Namaka alk'awali duk runtsi Mon Amour zan rik'ema amanata.â€
Labb'anta ya sumbata ya mik'ar da ita, kud'in wajansa ya raba abiyu ya bata raba ya ce“Kiyi buk'atunki zan turo miki wasu da zaran mun isa lafiya na samu akin k'wadago mai kawo kud'i, sai ki sai waya da layi muna mgna kafin na dawo...â€
Ya k'arashe mgnar yana jan dogon numfashin uwar mgnar da ya yi dan dan ita kawai take saka shi dogon sharhi.
Ibtisam ta langwab'ar da kai gefe ta girgiza kai ta ce“A'a mon amour ka bar shi kaga wasu ma na kawomaka jiya aka kawoma Anna kud'in adashe sai na sato rabi na kawo maka....â€
Wani mugun kallo ya watsa mata, wanda yasa ta mak'ale sauran mgnar bakinta, ta sadda kanta k'asa tana wasa da yatsar hannunsa.
Janye hannunsa yay ya Kama harshen hijab d'inta ya d'aure mata kud'in wajansa, ya d'ago fuskarta cikin kakkausar murya ya ce“D'ago kanki kalleni.â€
Ya k'arashe mgnar yana tsura mata fitinannun idanunsa.
Ibtisam tsoronsa ya kamata sabida bai tab'a mata hakan ba.
Cikin rauni ta d'ago ta sauke k'wayar idanunta cikin fitinannun idanunsa.
Runtse Nata idanun tai tana fad'in.
Mon amour kayi hkr wlh ban tab'a satar mata kud'iba sai yau dan na baka.â€
Labb'anta ya kamo ya murza ta Saki qara tana k'amk'ameshi.
“Ni ba lusarin namiji bane da har zaki sato kud'i agidanku ki kawo min karki kuma tab'a abinda ba'a baki ba, maza jeki mayar dasu idan kika d'aukeso bana son munafukin mutum, nasani ba halinki bane kinyi dan nine, amman karki kuma, sannan banda kula samari ok?†Ya k'arashe mgnar yana zaro zoben azurfar hannunsa na k'aramar yatsarsa kasancewar zoben 2, ya kamo farin hannunta ya sanya mata a yatsarta, ya sumbaci yatsar me zoben, ya ce“Amanata kinji.â€
Ibtisam tace“Insha Allahu mon amour kuma zance Anna tai hkr na mata laifi amman bazan kuma ba. â€
“Yauwa matana muje toh.â€
Hannunta ya kamata suka fito har waje ya rakota ya ce“Ki kwance kud'in harshen hijib.â€
Hawaye ya fara bin kyakkyawar fuskarta ya had'e raina yana zura hannayensa cikin aljihun jeans d'insa ya ce“Ok na fasa tafiyar mu zauna acikin talaucin har iyayanki su gaji da jirana su aurama wani ke, daga nan ciwon zuciya ya kasheni ko?â€
Da sauri ta Saki murmushi tana girgiza kai ta ce“Mon amour fatan alkahiri inata jirnka kaj?â€
Wani sansanyan kallo mai tsayawa azuciya ya mata ya ce“Je t'aime mon cÅ“ur bye.â€
Da gudu tabar wajan tana sakin kuka.
Goshinsa ya dafe ya furta“Ya Rabbi!â€
Gida ya koma ya d'auko kayansa ya rufe k'ofarsa kasancewar k'annensa mazan duk suna school.
Cikin sa'a yanzu ba kowa sai inna da Deluwa da k'annensa biyu mata masu aure