Showing 108001 words to 111000 words out of 165653 words
sosai billahi.â€
Rafeek wani suman da'din jin sautin murya Rahma ya kusa yi, cikin zumu'di ya ce“Baby cute shi ne kika tafi kika barni da kewarki ko? Kinsan irin halin da na shiga? Yanzu ma nazo gidansu Anee ne, naji ko tanada labarin ki, sai ga shi nazo a sa'a Alhmdllh! Ykk baby cute nah?â€
Rahma daga can ta zazzaro kyawawan 'kananun idanunta, ta ce“Rafeek! Ykk? Wlh tafiyar kai tsaye ta sameni shiyasa.â€
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Na azabtu wlh baby cute, pls ki ban dama na fito neman aurenki bazan hanaki karatu ba.â€
Rahma ta ce“Kayi hkr zan nemeka idan buqatar hakan ta taso, amatsayin yanzu matar wani ce ni mahaifina ya 'dauramin aure kuma bazan bijire masa ba, pls karka kirani muyi hkr kawai.â€
Tana gama mgnar ta katse kiran ha'di da kashe wayar baki 'daya.
Rafeek jin Rahma ta katse kiran ya sake kiranta hankalinsa a tashe, amman switch of.
Anee ta amashi wayarta tana fa'din.
“Abinda nakeson kwatanta maka kenan, kayi hkr Rahma tanama mahaifinta biyayya sosai ba lallai ta saurareka ba.â€
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya akan fuskarshi.
Ya ce“Me yasa zatayi min haka? Ban wayarki na 'dauki number tata.â€
Anee ta girgiza kanta ta ce“'kilama sbd kai aka canza mata layi, sbd Rahma bata tsayawa da maza kai ka'dai naga tana kulawa.â€
Haka ya tafi ransa a 'bace gani yake kamar taci amanarsa ne. Anee ta shiga gida tana sake gwada number Rahma bata shiga.
A can kuwa Chad Rahma wayan ta ajiye saman center table, ta sanya hijab har 'kasa ta sauka 'kasa ta nufi 'bangaran Abie 2.
Auntie Saro zaune a falo tana ma Umaima 'yarta gyaran gashi ta shigo da sallama.
Auntie Saro ta amsa tana kallon Rayyana, cike da mamaki ganinta ba akwai, Umaima ta miqe ta rungumeta tana mata sannu da zuwa.
Rayyana ta zauna kusan Saro tana murmushi ta gaisheta.
Auntie Saro ta amsa ba yabo ba fallasa.
Rayyana ta ce“Kai Auntie wai meye kike ciccin magani?â€
Saro ta ce“Umaima jeki waje ki qarasa aikinmu.â€
Fita tai ta fuskanci Rayyana ta ce.
“Wai ya na ganki haka ziqau? Ko ya hkr ne?â€
Rayyana ta 'kyal'kyale da dariya ta ce“Lah! Wlh ya yafemin baiyi fushi ba, jiya 'dakina ya raba dare.â€
Auntie Saro ta ce“Ikon Allah! Shi kuwa wane irin mutum ne kina nufin ya sauke miki nauyin da yake kansa?â€
Rayyana akayi fari da idanu, ta ce“A'a amman ya kusa.â€
Saro ta ce“Humm! Raiyanatu kenan toh Allah ya jishemu alkhairi.â€
“Ameen Auntie wlh ba wata matsala, yanzu ma shiyasa aka kawoni ya ce kar nayi driving da kaina, ga sakonki ya ce na siyo muku tsaraba ni kuma na kawo miki ku'din.â€
Auntie Saro ta amsa tana jinjina kai tabbas akwai abinda yake jira kafin ya sallameta sam bata yardaba, wai ya hkr.
Saro ta ce“Masha Allah mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi.â€
Rayyana ta amsa da “Ameen.â€
Nan suka fara hira duniya.
Abie zaune yana kallon Tv casbi a hannunsa, Rahmatoubulie ta bu'de 'kofar ta shigo da sallama.
Abie2 ya amsa yana fa'din.
“Diyar albarka kece yanzu da Rana?â€
Murmushi Rahma tai ta zauna kusansa tana gaishesa ta ce“Abie inata kewarka mun jima bamuyi hira ba sosai azahiri sai a waya.â€
Dariya yay ya ce“Aikuwa dai 'diyar albarka, Abienki ya yi tafiya ko?â€
“Eh Abie2 amman yau Latifa bata zo ta gyarama falo ba? Bari idan naje zan turota, ko Meerah.â€
'Yar dariya yay ya ce“Yanzu nan ina wata dau'da?â€
Rahma ta ce“Abie2 bakaga wayana ba me kyau irin waccan Abienah ya siya min bari na 'dauko kagani.â€
Ta miqe kafin ya yi mgna ta fice.
Abie2 ya girgiza kansa yana murmushi.
Acan Niger
Da yamma su innah Hansatu suka tafi ganin Ibtisam.
Zaune suke a tsakiyar gidan, Taslim ta 'dora girkin yamma, Ibtisam zaune kusan Laraba, su Aydah na sabgogin gabansu.
Ramadan ya kalli Ibtisam ya ce“Wai aunty meke damunki kalli yadda kika zuge?â€
Laraba ta ce“Kaikuwa Ramadan dukama yaushe ta warke.
Ibtisam ta ce“Ni kaga ba abinda yake damuna kawai yanayin rayuwane...â€
Sallamar su innah hansatu ya katse mata mgna.
Laraba ta amsa tana fa'din.
Marabanku da zuwa, Ibtisam 'dauko babbar tabarma.â€
Ibtisam ta miqe tana Jan tsuki aranta taje ta kawo tabarmar da shimfi'da suka zauna ta duqa ta gaishesu.
Deluwa ta ce“Sannu ya jikin? Allah ya qara sauqi.â€
Ibtisam ta amsa da“Ameen.â€
Ta miqe ta nufi 'daki, innah ta bita kallo ganin yarinyar fuska ba walwala.
Yaran dukansu suka gaishesu.
Laraba ta zubo musu ruwan sabuwar Randa me sanyi, ta zauna suka gaggaisa, innah batayi tunanin Laraba zata tarbesu haka ba.
Ibtisam kuwa haushinsu takeji shiyasa ta shige 'daki sai da zasu tafi ta fito ta rakasu har bakin titi suka samu abin hawa.
Da dare bayan sallar isha Map Adamu yazo har nan gidansu Ibtisam shi da Tanko suka tsayar da ranan biki sati uku masu zuwa.
Yana zuwa gida ya gayama Ja'afar akan ya fara ha'da kayan lefe biki sati uku masu zuwa. Da toh ya amsa dan bai Iya jayayya da mahaifinsa.
Acan Chad kuwa Rayyana bayan la'asar tazo, da ita aka ahiga kitchen tana temakawa Ummu Adnan da Latifa wajan girki, ta ha'da lemuka masu dad'i na 'ya'yan itatuwa, sai bayan maghrib suka kammala kome aka jera saman dining area, aka shiga wanka.
har 8 na dare Abie bai shigo gari ba.
Zazzune suke akan dining suna cin abinci, sai qara apoon kakeji.
Rahma ta sauko tana tafiya jikinta sanyi qarai, sanye take wani jeans 'din da Riga irin me yankaken hannu, tanada igiyoyi na 'daurewa wanda suke jere ta 'dauresu baqace jeans 'din kuwa blue ne, ta raba kanta gida biyu ta 'daure, shigar tai mata kyau, sai baza 'kamshi take.
Meerah ta kalla zaune 'kasan carpet tana cin abinci.
Meerah ta ce“Madam tin wajan uku na yamma da kika haye sama sai yanzu?â€
Rahma ta yamutsa fuska ta ce“Wlh fa! Duk banjin da'dine Abienah shiru har yanzu.â€
Ta nufi kan dining area 'din.
Da idanu take binsu kowa cin abinsa yake.
Idanu suka ha'da da Rayyana Rahma Sam batada niyar mata mgna ko tambayar yaushe ta dawo dan basu ha'duba.
Kujera taja ta zauna, kusan Jaddatu.
Tana fa'din.
“Shine kuke zubama cikinku abinci Abienah baya gari baza a tsaya aga dawowarsa ba.â€
Ta 'karasa mgnar ashagwa'be tana murgu'da 'dan qaramin bakinta.
Jaddatu ta ce“Eh lallai fa! Abien naki idan yayi tafiyar wuni sai ta kaisa sati haka kawai sai mu hana cikinmu abinci.â€
Hanan tai dariya tana yagar cinyar kaza.
Rahma ta ce“Ngd Jaddatu ba kome ai sai kuje kuyi taci, ni dai nasan komin dare zai dawo.â€
Ta 'karashe mgnar tana tsiyayar lemon 'ya'yan itatuwa ta sha.
Rayyana ta ce“Ummi kici abinci mana pls.â€
Kai Rahma ta girgiza ta miqe tabar musu wajan, ta zauna falo.
Har goma na dare bai zoba Rahma ta haye sama ta shige 'bangaran Abien ta murza key na falo ta shige bedroom ta kunna turaren wuta ta fesa na feshe ta haye saman Royal bed 'dinsa ta 'kure gudun Ac ta shige lallausan bargo tana latsa wayanta, sai da taji bacci sosai yazo ta ajiye wayan kusan kanta, ba jimawa bacci ya 'dauketa.
Shabiyu saura su Abie suka shigo Chad.
Koda suka shigo gida shabiyu ta gota.
Parlor'n shiru ba kowa ya murza key, ganin dare ya yi ya kashe 'kwayayen wutar falon ya haye sama.
Key ya zaro ya bu'de 'kofar falon, ya shigo bakinsa 'dauke da sallama.
Ya maida 'kofar ya murza key.
Dadda'dan 'kamshi ya baibaye 'kofofin hancinsa, ya lumshe idanunsa ya bu'de ya nufi bedroom.
Yana bu'de 'kofar wani 'kamshi ya daki hancinsa, idanunsa suka sauka saman kyakkyawar fuskarta bargon da ta rufa ya yaye tana rungume da pillow wayarta dab da fuskarta saman pillow'n.
Ajiyar zuciya ya sauke ya maida 'kofar ya rufe ya tako har tsakiyar 'dakin.
Remote 'din Ac ya 'dauka ya rage gudun Ac. Zama yay bakin bed ya rankwafo ya sumbaci kumatunta da la'bbanta ya shafi fuskarta ya ce“Allah sarki abar 'kaunata, kewar Abienki ko?â€
Cikin baccin tai juyi bakinta ya motsa ta ce“Uhmm! Baby Abienah.â€
Idanu Abie ya zaro yana 'kunshe dariya sa, bai san lokacin da haye saman bed 'din ba, ya janye pillow ya shige jikinta, yana kanainayeta da faffa'dan 'kirjinsa, ya manna bakinsa saman kunnenta cikin siririyar murya ya furta.
“Na'am Babyn Babyn ta.â€
Ya sumbaci gefen fuskarta.
Ji yay ta 'kam'kameshi gam tana jujuya fuskarta 'kasan wuyansa, cikin mayen bacci ta ce“Please Baby Abie rigimata ka dawo.â€
Abie duk ya sukurkuce ya furta“Ya Salam! My baby sunan ya min sosai ga ni gabanki ajikin Abienki kike ba mafarki bane kike.â€
Shiru bata motsaba ya gane mafarki take baccinta ya yi nisa, kwantar da ita yay ya sumbaci goshinta, ya sauko daga saman bed 'din.
Kayansa ya cire ya 'daura towel ya nufi bathroom.
Sosai yay wanka ya fito ya shirya kasan cikin wasu lallausan kayan bacci ya fesa turare, ya zauna bakin gadon yana qarema jeans 'din Rahma kallo na jikinta da rigar sun masa kyau, ya so ciremata ya saka mata kayan baccinta na jiya da yaga ta wanke, harda nasa.
Matsowa yay sosai ya janye rigarta farin shafaffan cikinta ya bayyana, ya sanya hannunsa saman cikin ya shafa, ya furta.
“Ya Allah! My Baby tunanin Abie ya hanata cin komai haka ta kwanta baiwar Allah. â€
Ya 'karashe mgnar yana janye hannunsa daga saman cikinta ya miqe ya bu'de 'kofa ya fice.
'Kasa ya sauko, ya nufi kitchen dan yasan Rahma bazata ta'ba cin abinci yanzu ba.
Ruwan zafi ya 'dora ya ha'da mata tea ya zuba uwar madara Nido da Milo, babban cup glass ya cika ya 'dauki cake wanda bai yankewa agidan.
Sama ya koma ya ajiye saman 'dan 'karamin table ya zauna ya sanya hannunsa ya 'dauketa ca'dak ya 'dora saman cinyarsa.
Tallabo fuskarta yay yana shafawa yana kiran sunan, bakinsa dab da fuskarta.
“My Baby ummina! Oya bu'de idanunki ga Babynki.â€
Ya fad'a yana 'daukar cup 'din ya kur'bi tea 'din ya bud'a bakinta ahankali ya 'dora bakinsa saman nata ya shiga juye mata tea 'din yana shafa gashinta.
Rahma ta jima da tashi tai muqus kamar mai bacci jin Abienta na bata tea daga bakinsa ya sanya ta shiga ha'diya, tamkar mai baccin.
Abie ya ce“My Baby wane irin bacci kikeyi haka yau?â€
Ya fa'da yana sake kur'bar tea 'din ya ha'de bakinsu ya juyemata tana ha'diya.
Murmushi Abie yay sabida ya gano ta farka.
Cake ya gutsira ya tauna ya ha'de bakinsu ya tura mata, yaji ta shiga tsotsewa tana ha'diyewa.
Kamar wasa sai da Abie ya gama ciyar da ita ta hanyar 'dura mata sai da taji ta 'koshi,ta bu'de idanunta ta 'kyal'kyale da dariya tana ruqumqumeshi tana kallonsa.
Abie ya ce“My Baby ai kin kyauta, na fasan idanunki biyu, tunda naji kina ha'dawa da harshena kina tsotsa sai kin jima kafin ki saki.â€
Kumatunsa ta sumbata, tana Jan gemunsa tana tatta'ba sajansa.
Ashagwa'be ta ce“Baby Abienah I miss you so much ka rungumeni kewarka yau ta kusa kasheni.â€
Abie ya sake matseta jikinsa ya tallabo fuskarta ya ce“Wallahi da tunaninki na wuni acikin zuciyata, kamar zan zauce Babyna.â€
Cikin farin ciki ta qara shigewa jikinsa sai kuma ta sakeshi tana saukowa 'kasa ta Kama hannunsa ta ce“Baby Abienah muje kaci abinci pls.â€
Wayo ya mata ya ce“Babyna naci mana ai saida naci na hayo sama.â€
Kai ta langwa'bar ta ce“Baby toh coffee? â€
Sanin sai ta sauka 'kasa ta dafo masa ya ce“Ruhina nasha ai da naje dafo miki tea na data nasha acan.â€
Ajiyar zuciya ta sauke ta Saki hannunsa ta 'dauki cup 'din da ta Sha tea da sauran cake ta fitar falo ta dawo ta shiga toilet tai brush ta fito ta hauro saman bed 'din ta zauna kusa da Abie wanda ta isko yana duba wayanta.
Wani kallo ya watsa mata wanda ya sanya hantar cikinta ka'dawa.
“Baby Anee kika Kira ko Rafeek?â€
Jikinsa ta shige ta ce“Wlh Abie Anee na Kira ni banda number sa, ka kirata kaji na manta banyi saving number ba.â€
Ajiyar zuciya Abie ya sauke ya ce“Kashe wuta kizo mu kwanta dare ya yi.â€
Sauka tai ta kashe wutar duhu ya bayyana, Abie ya kunna 'kwan fitilar gefen gadon, ta hayo ya janyota jikinsa ya ce“Baby kayan bacci fa?â€
Shigewa jikinsa ta yi ta ce“A'a Abie ni banso Abie marata ciwo.â€
Ta fa'da ashagwa'be.
Ruf ya rufesu da lallausan bargo cikin siririyar murya ya ce.
“Haba!? Mugani My baby. â€
Rigar ta janye tana kallonsa ta 'dan hasken.
Hannunsa ya 'dora saman cikinta ya zarce mara ya shafa ahankali, ta 'kam'kameshi tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin wata irin murya ya kirata.
“My baby ummina!â€
Yadda ya kirata da yadda yake shashafa mata Mara yasa ta Saki wata irin shashe'ka ta sauke ajiyar zuciya.
Akunnenta ya ra'da mata “Babyna mijinki da jibi zai bayyana da uzuri ya taso masa yanzu sai nan da kwana 8 insha Allah, ya ce ki shirya tarbarsa, alambu zaiyi shigar fararen kaya, shaddah me maiqo 'dinkin manya anyin aiki da bluen zare zai maqala baqin glass a fuskarshi zai sanya rufaffan takalmi sai agogon silver 'daure atsintsiyar hannunsa, dogone mai fa'din 'kirji yanada yalwar sumar kai kamar bai kwana biyu ba, saman kilishi zaki sameshi a zaune an jramasa kayan marmari agabansa.â€
Ya 'karashe mgnar yana zare hannunsa daga marata ya tallabo fuskarta ya ce“Baby kina jina?â€
Kai ta 'daga tana zubar da hawaye ta ce“Abie ba shi nake soba kai nake so wallahi.â€
Ta rushe da kuka.
Abie ya matseta jikinsa ya ce“My Baby naji ni kikeso yanzu a 'kaddara ba nine mahaifinki ba za ki iya zama dani matsayin mijinki?â€
'Kirjinta taji ya buga damm! Tai saurin kallonsa ta ce“Wayyo Baby wallahi da nafi kowa murna toh amman bazan samu hakan ba, tinda hakan zai nuna cewar ni shegiyace tsintata kayi, gwara na zauna yadda Allah ya tsara kana matsayin ubana.â€
Sumbatar la'bbanta yay ya ce“Ai zallar kamar da muke dake ya isa ya nuna miki ke 'din jinina ce kull na kuma jin kina ha'damin kanki alayin shegu.â€
Qamqameshi tai tana dariya ta ce“Yo ai kawai ina fa'dane, Baby ina sonka kaji wai kowane uba da 'yarsa haka sukeyi kamar ni da kai um Baby Abienah.â€
Abie ya ce“Naji My heart nima ina sonki ina 'kaunarki. No! Baby ko shugaban arnan duniya bazai haka ba da 'yarsa ta cikinsa, bare Abienki cikakken musulmi.â€
Rahma ta ce“Toh Baby Abienah...â€
“Shiiiiiit! My baby nan da kwana takwas Babyna ta san waye Abienta gareta daga ranna za'a fara shirin bikin ki wata 'daya kawai za'a saka. oya bacci Abar sona ina sonki My Baby â€
Rahma ta qamqameshi duk da magnar Abien ta kasa gane me yake nufi.
Bakinsa ta lalubo tana Sha abinta anutse har lumshe idanu take.
Abie bai hanata bata ya shiga shafa kanta, yana wasa da gashinta har bacci yay nasarar 'daukarsu.
★★★★★★ ★★★★★★
Bayan kwana 8
*Gabon*
Aishatu tana ta samun sauqi agidansu, Ma'aruf kullun sai yazo sau uku safe rana dare, Aishatu har yau bata sakar masa fuska ya jiki ma sai idan agaban iyayanta take take amsawa.
Yau gidan nasu shiru ba kowa sai ita da Uwani, wacce ta dawo nan wajan Aishatun da zama.
Kwance take saman doguwar kujera idanunta arufe kuma ba bacci take ba.
'Kamshin turarensa ta fara shaqa kafin sallamarsa ta iso konnenta.
Adaqile ta amsa ba tare da bu'de idanunta ba.
Uwani da take gefe zaune qasan saman carpet ta gaishesa.
Amsawa yay yana tamabayarta.
“Ina 'yan gidan?â€
Ya 'karashe tambayar yana zama kusan Aishatu.
“Sun tafi sunan Najwa.â€
Ta basa amsa tana miqewa ta fice.
Ma'aruf ya ce“Oh! Na manta wlh.â€
Ya 'karashe mgnar yana 'dago Aishatu.
Fizgewa tai zata miqe ya matseta jikinsa, yana mata ra'da akunnenta.
Sallama sukaji murya da sukaji ne ya sanye suka 'dago da sauri.
Rabi'ah tsaye ta jema ta rame tayi fari fat kamar batada jini ajikinta.
Aishatu ta 'dauke kanta ta miqe zata nufi bedroom Rabi'ah ta bita aguje tasha gabanta ta zube ta riqe qafafunta tana kuka ta ce“Don Allah ki yafemin wallahi tinda na zalumceki na kasa nutsuwa banda lafiya.â€
Aishatu ta fizge 'kafarta tace“Kanki kika zalumta bani ba kije na yafe miki Allah ya yafemu baki 'daya, amma bani bake, don Allah karki sake zuwa Inda nake.†tana gama mgna ta shiga bedroom ta murza key.
Rabi'ah wacce tinda ta shaqi turaren Ma'aruf taji kanta na juyawa zuciyarta na tashi, ta toshe hanci ta ce.
“Ngd daman ban cancanci zama da mutanan qwaraiba.â€
Juyowa tai domin taba Ma'aruf hkr taga wayam baya nan.
Miqewa tai ta fito zuciyarta na mugun tashi jiri na 'dibarta.
A'kofar gidan ta zube tana kelaya amai kamar zata zubar da kayan cikinta.
Haka ta daure ta samu abin hawa ta koma gida zazza'bi ya rufeta wuni tai tana amai hankalin mahaifiyarta ya tashi ta Kira yayansu Rabi'ah da yake yanada 'Yar motarsa suka kwasheta zuba asibiti.
Gwajin farko likita ya sanar dasu tana 'dauke da ciki na kwana goma Sha shidda.
Ba Rabi'ah ba yayanta ma zuciyarsa ta kusa bugawa, bare mamarsu da ta kasa cewa komai har sukazo gida ta kasa magana.
Rabi'ah ji tai duniyar na juya mata komai ya tsaya mata cak...
Mamarta da yayanta suka shiga jibgarta kamar Allah ya aiko akan ta fa'da musu wa ya mata ciki yaushe ta fara bin maza basuda labari?
Rabi'ah tana kuka ta ce“Wlh idan na fa'da tsinemin zakiyi mama dan Allah kuyi hkr...â€
Wani wawan bugo Murtala ya mata sai gata qasa a sume...
Acan Chad kuwa cikin kwankin da suka shu'de Abie baya samun zama kullun yana tafiya Rahma tayi kewar har ta gaji sam baya zama sai ya yi kwana biyu baya gari Rahma ta dawo bacci 'dakinsa, cikin kwanakin sau biyu suka kwana tare.
Rayyana kuwa ta ajiye hankalinta shariyar da Rahma take mata ta watsar abin baya damunta kowa sabgarsa yake, tinda taji Rahma nada miji yana tafe ta dinga janyota ajikinta tana koya mata kissa da kisisina Rahma kallonta take sbd tasan idan mutum na sonka ba sai ka zaqe masa ba dayawa, bare ita bata son mijin umarnin Abienta take bi.
Abie kuwa da Rayyana banda gaisuwa irin ta da ba abinda yake ha'dasu da Abie sbd bayama zama yanzu.
Yau tin safe Rahma take cikin zullumin ganin mijin nata ita Sam bata sonsa amman tasan Abie ubantane bazata samesa ba matsayin miji ba.
Kowa agidan yau yasan mijin Rahma zai bayyana, Rayyana tafi kowa farin ciki ita ce da kanta ta kira me makeup tai ma Rahma an mata zanen Jan lalle me shegen kyau, anyi girke-girke da lemuka kala².
Misalin biyar da Rabi aka shirya komai a can lambu kamar yadda Abie ya bada umarni tin jiya da zaiyi tafiya.
Idan ka kalli Rahma sai ka qara kallon sabida wani irin kyau da ta yi.
Misakin 'karfe 6 na yamma Zazzaune suke a falon, Rahma tana sanye da doguwar riga milk colour, an 'kawatata da adon sequence stones masu 'dan banza kyawu.
Rayyana sai washe baki take ta ce“Ummi amman me yasa Abienki ya za'bi surikinmu yaje Lambu?â€
Rahma tai murmushi ta