Showing 159001 words to 162000 words out of 165653 words
Ibtiama take cike da mamaki wai daman yarinyar batasan tanada ciki ba abun ya fito qiri² kuma mijinta bai gayamata ba?
Bari tai sai da ta qare wayan ta ce.
“Wai ibtisam kina nufin qiba ce ta kumbura miki ciki hakan?â€
Ibtisam tai dariya ta ce.
“Eh wlh Umma.â€
Falmata ta ce“Gsky bakida wayo Ibtisam toh wlh kibar shasancin nan cikine cake fa! Kina ganin abu haka kice qiba? Ai wlh bakya bina bashin rantsuwa cikin nan naki hakai wata shidda.â€
Ibtiama ta firfito da manyan idanunta ta dafe 'kirjinta ta ce.
“Ni umma? A'a wlh ai me ciki kullun baida lfy baya cin abinci ni kuma lau nake.â€
Falmata ta ce.
“Lallai sabida bakya laulayi shi kenan? Sai akace miki kowace mace take laulayi? Ai wlh wata sai dai ki ganta da cikinta kamar nakin nan, wata kuma tin ranan da Allah ya bata toh zai fara nuna alama, har sai yayi k'wari ita da lafiya. wata kuma sai ya kai wata zuwa wata biyu take fara laulayi wata kuma idan ta fara laulayi abin ba sauqi sai ta sauke wata ba laulayi amman bata son namiji ya kusanceta wata kuma k'amshinsa ne bataso wata kuma fad'a da yawan b'acin rai, ba ta yadda ciki baya zuwar ma mace dan haka ki dawo haiyacinki ciki gareki, Wanda inada tabbacin zai kai 6 ko 5.â€
Ibtisam tai tagumi sai yanzu ta tuna ita fa dudu jininta biyu a nan garin idan hakane kuwa hakane cikinta watansa 6.
Shiru tai kamar ruwa ya cinyeta ta kasa magana.
Koda Ja'afar yazo d'aukanta yaga ta sauya sosai yana driving ya kamo hannunta yana murzawa ya ce.
“Mah Love me ya farune?â€
Ibtisam ta silalo hawayen da taru cikin idanunta ta kalleshi ta ce.
“Mon Amour Ashe ba qiba bace cikine gareni.â€
Ja'afar yay murmushi ya ce.
“Au wai da baki saniba matar Ja'afar?
Ai wlh nasani ina kallonki ne naga iya wayon Mon cherie, yanzu dai kin gane ko? Ai ni ba sakarai bane wata shidda bakiyi period ba wlh nasani ganin bakya ciwo ba laulayi na qara dagewa wajan kulawa dake da abinda yake cikinki wallahi ina sonku fiye da kaina addu'ata Allah ya sauke min ke lafiya.â€
Kuka ta fashe da shi tana rungumeshi.
“Hahaha Beby bari kuka ko bakyason haihuwar?â€
Ibtisma ta girgiza kanta ta ce.
“Mon amour ina mamakine sam da ban tab'a ankarewa ba.â€
Ja'afar ya sake gyara mata kwanci jikinsa ya ce“Ai yanzu an Ankara dake dan haka Allah zamuma godiya gobe sai mufara zuwa asibiti duk da nasan zamusha fad'a.â€
Murmushi tai bata sake mgna ba dan ganin abun take a Almara.
Yau aka d'aura auren Rayyana akan sadaki mai daraja, ayau kuma ta tare agidanta, Wanda lokacin da za'a tafi da ita kuka take tamkar budurwa sabida yadda auntie Saro ta tsaya tsayin daka wajan gayara da mata nasiha tasan abinda take ta Kama kanta karta kuskura tace zatayi irin rayuwar da tai agidan Abie.
Tabbas ta d'auki nasihar tayi alqawalin ruwa da iska zata masa biyayya.
B'angaran uwar gida aka kai Rayyana, hajiya Sha'wanatu batada matsala har tsokanar Rayyana tayi, sosai 'yan uwan Rayyana suka yaba da halin Sha'awanatu.
Daga can suka nufi b'angaran hajiya Zakiya me d'akin tsaka toh ita ma ba laifi.
Kowa ya yaba dagin Rayyana ba laifi duk da bai kai rabin² gidan Abie ba amman fa gidan ya had'u.
Wajan k'arfe 10 na dare ya had'asu b'angaran hajiya Sha'awanatu ya musu nasiha akan su zauna lafiya kamar baya baya son yaji wata fitina ta billo kowa yaba d'an uwansa girma.
Alhj baisan dawan garinba cewar Rayyana bata tab'a sanin namiji ba ashekarunta sai da yaje kutsawa aguje yaji Abu gark'ame.
Ai kusan haukacemata yay lokacin da yaji zamzam ya kuma samu ya tila ya shige tasha zantuttuka ba laifi da kyaututtuka.
Rayyana tasha wuya matuqa girmanta bai hanata kuka ba.
Amman fa washegari tasha lele ko nan da can Alhj ya kasa fita dakyar yaje ya gaido iyalinsa.
Cikin kwana ukun da yayi wajanta matasan sosai sukaga rawan k'afan da yake akan amarayan tasa sai sukaji ba dad'i.
Rayyana kulawa take samu wajan alhj Nafi'u abun ba'acewa komai sai yanzu tasan tayi aure kuma aurema na mijin da yake sonta.
★★★
Bayan wasun 'yan kwanaki.
Gabon.
Alhamdulillahi za'ace b'angaran su Aishatu Ma'aruf kamar wasa harakan gwanjo ta amshesa yana samu ba laifi har an gyara masa motarsa da wuta taci abinda taci, komai na rufin asiri bai gagaresu ba.
Yau tin safe Rabi'ah ta tashi da naqud'a ganin ba'a wani kulata sosai agidan ta shige uwar d'aka tana shan azaba.
Ai wuya da tayi wuya ta shiga kiran mahaifiyarta.
Arikice suka nufi hospital.
Murtala ne ya kira Ma'aruf ya gayamasa halin da ake ciki akan Rabi'ah bazata haihu da kanta ba sai an mata cs.
Yana gayama Aishatu hankalinta ya tashi harda kukan tausayama Rabi'ah dan ayanzu tausayi take bata tasna tata k'addarace hakan.
Tin safe suke can har akayi aiki aka fito da yaron kyakkyawa fari Tass k'aton gaske sak Ma'aruf kamar anyi kakinsa a tofar.
Aishatu tinda ta kalli yaron ta k'ara yarda ba wanda ya isa ya goge zanen k'addarasa aduniya.
Amman abin tashin hankalin Rabi'ah har dare ya fara bata farfad'oba hankalin kowa ya tashi sosai.
Aishatu tana maqale da yaron ta kasa zuwa gida ba yanda Ma'aruf baiba amman taqi ya hasala yayi ya tafi ya barta.
Misali 10 na dare Rabi'ah ta farfad'o Aishatu ta fara nema.
Aishatu tana rungume da yaron ta riqe hannun Rabi'ah t ace.
“Ga ni Rabi'ah ga yaronki Masha Allah. â€
Rabi'ah cikin fitar hayyaci ta ce.
“Don Allah ki temaka ki basa abincinsa ajikina,kuma na baki shi kyauta dan Allah ki yafemin wlh bazan gaji da naiman yafiyarki ba.â€
Aishatu ta rufe mata baki ta ce.
“Na yafe miki duniya da lahira ba yauba tsaya abasa nono mama temaka min na basa dan Allah. â€
Mahaifiyar Rabi'ah tana mamakin shin Aishatun nan wace irice ne?
Taimakawa sukayi wajan bawa yaron nono ya Kama yana Sha.
Rabi'ah tana zubar da hawaye ta shafi kan yaron ta ce.
“Allah ya maka albarka ya rayaka, Allah yasa kazama wani Abu aduniya Allah yasa duniya tai alfahari dakai ka yafemin ka qara nema min gafara wajan mahaifinka, Aishatu ki riqeshi amana dan Allah karyasan bake bace mahaifiyarsa...â€
Aishatu ta rufe mata baki tana girgiza kanta.
Shaquwa sukaga tanayi mama ta fita aguje kiran doctor kamar jiran fitarta take numfashin Rabi'ah ya tsaya cak bakinta na motsawa sam bakajin abinda take fad'a.
Aishatu idanu ta zuba mata ganin bata motsi jikinta ya d'auki rawa.
Dr yana dubawa ya ce.
“Kullun nafsin za'ikatul maut. Allah ya mata rasuwa kuyi hkr.â€
Aishatu nan ta zube k'asa asume.
Mama kanta abun ya girgiza k'asa ta zauna dab'as ta dafe kanta wasu hawaye mai zafi ya zubo mata tana fad'in.
“Rabi'ah wallahi na yafe miki duk qamar da make nuna miki sabida ki gyara rayuwarki ba dan na tsaneki ba.â€
Murta ya d'auki yaron Wanda har lokacin yana shan nonon uwarsa.
Idanu ya shafema Rabi'ah yana kuka kamar yaro.
Dr dakyar ya ceton ran Aishatu Wanda aka Kira Ma'aruf mutuwar Rabi'ah ta girgizasa matuqa.
Washegari da safe aka basu gawar Rabi'ah aka sallace ta aka kaita gidan gaskiya yaron na wajan Aishatu wani magani na gargajiya aka had'a mata ta Sha take ruwan nono yazo.
Aishatu bayan kwana uku ta saka aka tara dukkan families nasu ta musu bayanin abinda ya faru Wanda ta b'oye wani abun ta ce dai k'addarace kawai ta had'asu agidanta wani lokaci abisa kuskure cikin dare ya dawo daga tafiya Rabi'ah tazo tayata kwana har hakan ta faru Ashe rabone.
Kowa hakan ya d'auki maganar yamata addu'ar Allah ya bata ikon riqe yaron da amana mahaifiyasar Allah ya jiqanta.
Randa akayi sadakan sati aka sakawa yaron suna Umar Farook.
Kafin Arab'in yaro yayi mulmul sabida Gatan da yake samu Ma'aruf Allah ya jarabesa da son yaron ga wani irin bud'i da yake shigo musu Masha Allah.
★★★
Ibtisam cikinta na cikawa wata takwas Ja'afar ya shiriya musu zuwa Niger ya kaita haihuwa kwanansa biyar ya juyo wanda da zarna ta haihu zai dawo.
Toh masha Allah tana samun kulawa sosai cikin ya tsufa zama dakyar tashi dakyar an bata sati biyu Wanda ba lallai taci satin ba ma.
*Tchad*
Masha Allah Abie sunje Morocco sun memo auren Meerah an basu Wanda basu baro qasar ba sai da aka d'aura auren aka basu amaryasu.
anan gidan Abie akayi taron biki abin sai Wanda yagani b'angaran Abie2 aka zuba sabbin kaya dole idan ka shiga wajan ya burgeka, sai da Meerah tai kimanin kwana uku kenan da tarewar amman Abie2 ya kasa tab'ata, sai da tai kusan sati yaje ya zage ya fuskanceta aka b'arji amarci ya sameta cikakkan buduwar ta samu tattalin so fiye da yadda zan kwatanta Ashe Abie2 ya Iya love, cikin sati biyu sun murje sunyi qiba suna shan love kullun Rahma sai tazo ta zubama Abie2 shagwab'a ya lallab'ata kafin ta tafi.
Abie ya ce bayason Abie2 ya yi komai ya huta akan wuyar da yaci aduniya kusan shekaru ashirin da biyar.
Amman yaqi ya fara fita aiki companyn Ja'afar.
Rahma kuwa cikinta wata bakwai da 'yan kwanaki qalilan amman Masha Allah kace yau zata haihu dan tayi girman ciki.
Wata irin kulawa suke samu ita abin cikinta soyayyarsu da Abie sai qara hauhawa take.
Zaune take a falon nasu na qasa wanda suka tare d'akin k'asa.
Saman carpet tana cin mutumin nata strawberry.
Sanye take da doguwar riga shara-shara.
Idanunta akan TV.
Jin motsi ta waiga.
Abie ta gani cikin shirin fita ya ha'da cikin wasu irin kayan Pakistan masu uban tsad'a yana baza k'amshi ba abinda yafi burgeta irin hular kansa da takalmin k'afarsa da glass d'in da yake manne akan kyakkyawar fuskarsa.
K'ananun kyawawan idanunta ta qura masa tana kallon tsadadiyar agogon da take d'aure a tsintaiyar hannunsa, yana dubawa.
Qarasowa yay gabanta ya rusuna yana sakar mata tattausan murmushi ya shafi fuskarta ya d'ora hannunsa saman k'aton cikinta ya shafa ya rusuna ya kai guiwowinsa k'asa ya sunkuya ya sumbaci cikin ya ce.
“My babies ya kuke?â€
Ya d'ago yana d'aga mata gira ya ce.
“My ruhi ya dai kina son sanin Inda Abienki zaije koh?â€
Ashagwab'e ta turo bakinta gaba tana sanya masa strawberry abakinsa ta ce.
“Wayyo My Abieh kayi kyau sosai zan bika, dan Allah karma bari matan banzan su kalle min kai kaji...â€
Wani irin ihu ta Saki lokacin da taji marata wani abu ya sokaeta kamar allura ta damqe damtsam hannun Abie.
Arikice Abie ya ce.
“No! My Baby meye haka idan bakyaso nafita na barki zan jira har kiyi bacci OK?â€
Rahma bayanta taji ya riqe cikinta yay wani irin murd'awa take taji yaron cikin na zillo ga azabar da marata take cikin seconds goma har zufa ta karyo mata, cikin fitar hayyaci ta ce.
“Wayyo Abie zan mutu bayana marata cikina wallahi ba wasa nake ba, ka kaini wajan Jaddatu.â€
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Babyna ko naqudace ai lokacinki baiba na shiga uku.â€.
Ya qarashe mganr yana ciccib'arta sama ya nufo babban falon, yana kiranta Babyna kiyi haquri yanzu zamuje asibiti qila juyawar yarone.â€
Hahaha Abie inaga zaka zama ubane fa yau
Whtspp number😊
_*+22796515805*_
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
6/7/22, 19:48 - Buhainat: ```D A```
```106```
_Rahmerh Ladingo😉_
*ALHAMDULILLAHIðŸ™ðŸ¼* Masoya Ngode sai mun ha'du JIKAR BULAMA, nan kusa kujirani da zafinsa zai fito, Tabbas wannan tafiya ta daban ce.😹 tabbas idan kin karanta Dattijon Arziqi toh JIKAR BULAMA ya shafeshi a dad'i da soyayyar cikinsa da darusan cikinsa da makirci da darasi da komai fatana ku biyoni muje zuwa, wannan da zafinsa yake tafe sannu-sannu nake tafiyar da salona, bana takurawa bana gaggawa amman na tabbata za ki/ka ku anfana wannan shine burina wa makaranta.ðŸ‘ðŸ½
Ya ALLAH duk labarin da ya kasance babu darasi acikinsa ko fad'akarwa karka bani ikon rubuta shi.ðŸ™ðŸ¼
Jaddatu zaune tana kallon tashar Aljazeera, tana Jan casbi taga Abie d'auke da Rahma hakalinsa a tashe yana doso falon.
Jaddatu ta miqe tana fad'in.
“Innalilalhi wa'inna ilaihir raji'un! Abdul me ya faru da Rahma?â€
Gabanta ya iso ya ce“Ummi ki kwantar da hankalinki inaga juyin cikina ta ce maratan da bayan da cikinta suke mata ciwo...â€
Jaddatu ta matso tana kallon Rahma ta ce.
“Maza muje asibiti haihuwace ba juyawar ciki bane.â€
abie bai jiraba me zatace yay gaba cikin sauri jin yadda Rahma ta cikuikuiyeshi tana kiransa.
“Abie! Marata bayana.â€
Sannu kawai yake mata.
Jaddatu ta kiraUmmu Adnan da Latifa sukanzo cikin sauri suna zubewa gabanta.
“Yawwa Maza zo ki had'ado kaya ki samemu mota, Latifa ke kuma kiyi qoqarin had'ama farfesun hanta da k'oda da kunnun madara.â€
Ta k'arashe mgnar tana gyara mayafin kanta tana tokara sandarta ta nufi k'ofar fita.
Ummu Adnan ta shiga ta had'o kayan haihuwa wanda daman su suka jera a d'akin da yake kallon na Rahma da Abie, ta had'o komai ta fito ta rufama Jaddatu baya.
Meerah ta fito da niyar shiga wajan Rahma taga ko lafiya yau bata shigo, ta hango Abie d'auke da Rahma ya nufi parking spaces.
Cikin tashin hankali ta bisa tana tambayarsa.
“Abie me ya sameta?â€
Abie ya ce“Inaga haihuwace.â€
Meerah ta koma ciki da gudu ta d'auki wayanta, ta Kira Abue2 ta sheda masa zasu asibiti Rahma na naquda.
Abraham daga nesa ya hango Abie d'auke da Rahma, yay saurin isa rumfar ajiye motocin ya fito da wata baqar Jeep.
Baya shigar da ita shima ya shi ya zauna yana rungume da ita.
Meerah da Ummu Adnan suna gaba Jaddatu baya wajansu Abie suka d'unguma zuwa hospital.
Sosai suke tausaya ma Rahma ganin irin azabar da take Sha, sai damqe Abie da Jaddatu take tana cizon lips d'inta, Abie sai sannu yake mata.
Suna isa asibitin aka amsheta cikin gaggawa aka nufi labor room da ita, Wanda Abie yaji tamkar ya bita suyi naqudan tare.
Jaddatu suna zazzaune sunyi jugum² suna zaman jira.
Abie ya aksa zaune ya kasa tsaye sai kai kome yake.
Jaddatu ta kalleshi ta ce.
“Don Allah Abdul ka zauna, adsu'armu kawai take buqata.â€
Goshinsa ya dafe yana hango yadda aka shiga da ita labor room.
Dab da ita ya zauna yana danna casbi da yake maqale atsarsa, bai iya cewa komai ba.
Abie2 ya iso suka gaisa da Jaddatu ya zauna kusan Abie1 yana fad'in Allah ya bud'e idanu lafiya.
Jaddatu da Meerah suka amsa da.
“Ameen.â€
Abie aqasan labb'ansa ya amsa da Amin.
Kusan awa biyu Rahma tana famar naquda, taci uwar azaba kafin Allah ya sauketa lafiya, ta haifo yaranta kyawawa mace da namiji, macan babu abinda ya rabata da Rahma har 'kananun idanunta sak, haka namijin ba abinda ya rabasa da Abie, ma'ana dai yaran baki d'aya Abie ne macan ce ta 'dauko idanun Rahma.
Yaran bakwaini ne 'yan mitsi² dasu, suna fitowa duniya bayan agyarasu aka sakasu a kwalba, aka kaisu wajan da za'a dinga kula dasu tsakaninsu da Rahma sai idan zata shayar dasu, sai da aka gama shirya Rahma tsaf baccin wuya ya d'auketa kafin aje sanar dasu Abie.
Lokacin da nurse ta fito bada albishir Rahma ta haihu, Abie na hangota jikinsa ya d'auki rawa bakinsa na makyarkyata ya ce.
“Ya don Allah har yanzu?â€
Nurse tai murnushi ta ce.
“Alhmdllh! Aqa'idar asibitin nan bama sanar da kowa nasa ya haihu sai an gyara yara da uwarsu sai mu fito mu sanar yadda zakaga naka cikin farin ciki.
Madam ta sauka lafiya ta samu mace da namiji amman suna kwalba sabida basu isa haihuwa ba.â€
Abie ya ce.
“Alhmdllh! Allah Kaine abin godiya da ka azurtani da Yara biyu lokaci d'aya haqiqa kinada babban tukuici.â€
Jaddatu ta rangad'a gud'a ta ce.
“Alhdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!! Yau Rahma ta saukewa Abdul Yara biyu.â€
Sai ta fashe da kuka, Abie ya rungumeta yana murmushi ya ce.
“Ummi don Allah ki daina kukan haka muje anuna mana yaran.â€
Abie2 ya ce.
“Masha Allah, D'iyar albarka tai k'ok'ari sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa.â€
Meerah tana kallonsa ta amsa da.
“Ameen ya Allah.â€
Wajan Rahma Nurse ta fara kaisu.
Kwance take tsaf abinta tana bacci, tamkar ba ita bace ta gama yaqi.
Abie ba kunyar kowa ya isa ya zauna bakin gadon ya riqo hannayenta yana murzawa ya rankwafo dab da fuskarta ya sumbaci goshinta ya ce.
“My baby sannu Allah ya miki albarka ya baki lafiyar shayarwa, Ngd sosai baby Ummi kinyi qoqari Allah ya albarkaci yaranmu.â€
Su Abie2 suka amsa da.
“Ameen.â€
Jaddatu zauwa tai ta rungumeta tana saka mata albarka, ita kam baccinta take bata San me suke ba.
Jaddatu ta Kira Latifa awaya ta ce maza tayi sauri ta kawo farfesun Rahma ta samu taci.
Wajan yaran aka kaisu masha Allah kayawun yaran abun kallone 'yan k'ananu dasu.
Abie yay musu addu'a tare da kiran sallah ya rad'a musu suna.
Namijin Abdulwahab suan mahaifinsa macan UmmulAymana.
Duk yadda zan fad'i dad'i da farin cikin Abie da zuri'arsa suke ciki akan wannan haihuwar toh bazan gayi daidai ba sabida gabaki d'aya kafofin sadarwa ba Inda Abie baiyi shelar haihuwar ba, kowa murna yake tayasa jama'a nesa dana kusa kiransa sukeyi taya murna.
Ja'afar har iyayansa ya Kira ya gayamusu suka Kira Abie sukayi masa barka harda Tanko hakan ba qaramin kima ya qarama Ja'afar wajan Abie b dan aduniya Wanda zai nun k'aunarsa da yaransa ko Rahma da Jaddatu toh ba qaramin masoyinsa yake kallonsa ba.
Kusan kullun asibitin cike take ga abokan arziqi mazu zuwa ganin Rahma da yaranta Wanda aqalla yanzu kusan kwana goma kenan, yaran suna samun kulawa sosai Rahma Allah ya jarabceta da son yaranta matuqa ba kamar macan da tai irin idanun mahaifiyarta.
*Niger*
Misalin k'arfe d'aya na rana Ibtisam zaune ta bararaje, tana cin wake da shinkafar da akayi, tana ci tana turo baki.
Laraba ta ce.
“Wai baqin ran me kikeyi yau Ibtisam? Me aka miki? Ji yadda kike cin abincin kamar dole kodai bakya so ne?â€
Ibtisam ta qaqalo murmushin k'arfi tai ta ce.
“Kai Anna wlh ni bawani baqin rai da nakeyi kawai banajin dad'in yanayin ne.â€
Anna tai shiru kamar batasan naquda ta fara.
“Taslim ku qare cin abincin kije ki kirawo mun Dadda.â€
Taslim ta amsa da.
“Toh Anna.â€
Ibtisam ta yamutsa fuska tana ciza lips ta ce.
“Me zata miki Anna? Ni kamar ma natafi can.â€
Laraba ta ce“A'a ki zauna ai zatazo.â€
Ibtisam batace komai ba tana tura Wake da shinkafar kamar dole.
Suna gamawa Taslim ta tafi gidan Dadda kiranta.
Kamar wasa Taslim na fita naquda ta tasoma Ibtisam gadan-gadan, ai kafin su Dadda suzo Laraba ta Kira Tanko a waya yazo da mai taxi suka nufi asibiti.
Cikin hukuncin Allah suna zuwa Ibtisam bata huce 30 minutes ba Allah ya sauketa lafiya ta haifo k'aton d'anta mai Kama d Ja'afar sak har baqin ba abunda ya bari.
Wai kai karkuso kuga murna wajansu Inna Hansatu mai waina, Mal Adamu tsabar farin ciki shi ya Kira Ja'afar ya gayamasa.
Ja'afar rasa idan zai saka kansa yay dan murna lokacin da Mahmoud ya tura masa hoton yaron.
Tabbas wannan zuri'a sunyi farin cikin haihuwar Ibtisam.
Ita kanta tana mamakin dangin Ja'afar haka suke son Ja'afar.
Tin ranan Ja'afar ya fara shirin tafiya su Harisu sukace