Showing 135001 words to 138000 words out of 165653 words
manta kowa da kome Abienta na da take kallonsa.
“Abie goyani don Allah.â€
Ta fa'da ashagwa'be.
Bayansa ya goyata yana dariya yana dab da shiga bedroom yaji bugun 'kofar falon murya Jaddatu da kanta tana kiransa.
“Kai! Abdul Majid! Ni zakawa iya shege bu'dema yarinya k'ofa wlh ba ruwana da girmanka sai wanwanka maka Mari aiki zaka maidamana baya?â€
Rahma ta zazzaro idanunta gabanta na fa'duwa cikin murya kuka ta ce“Abie kagani ko ka jamana sauke ni kaje ka kwanta sai nayi 'karya nace kanka yake ciwo dakyar kaci abinci.â€
Abie ya ce“Oho! Baby 'karya ciwo idan kuma nayi ciwon da gaske na mutu na barki ya....â€
Wani irin ihu Rahma tai tana beqa kanta ta wuyansa tana ha'de bakinsu, ta qamqameshi, hakan yayi daidai da bu'de 'kofar da Jaddatu da Hanan sukayi aguje suka shigo jin ihun Rahma.......
_Sai kuma Allah ya kamu bayan sallah zamu qarasa idan Allah ya ban iko wandan kuka min uzuri kuka gane nagode wanda baku fahimceni ba ma banga laifinku ba ku'di kuka biya, duk ina muku fatan alkhair._
_Rahmerh ladingo😉_
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
5/6/22, 18:01 - Buhainat: ```D A```
```95```
_Rahmerh ladingo😉_
*Eid Mubarak.*
_Tak'abbalullahu minna wa min kum_
Jaddatu da mugun sauri taja burki, tai tsaye cak, sai kuma tai azamar juyawa, har tana neman fa'duwa.
Hanan tai sauri riqota sabida ita tuntuni ta juyar da kanta, sakammakon ganin bakin Abie da Rahma ha'de waje 'daya, kuma tana kwance gadon bayansa ta bayansa ta beqo kanta, yanayin ya bada wani irin salo, me buegewa, yadda suke adunqule waje 'daya. kuma alamu ya nuna Sam basuji shigowar su Jaddatu 'dakin ba.
Dan zatonsu wani abun ya samu Abie shiyasa Rahma ta saki ihuuu abinda ya rikitasu kenan suka shigo basu jiraba an bu'de musu qofa ba.
Jaddatu ta qara rintse idanunta, tana fa'din.
“Kai innalillahi! Wallahi Abdul yaushe ya 'batamin yarinya haka sbd Allah kidiba kiga tana bayansa amman fuskarta ha'de da ta shi, ai sai wuyanta ya karye, ni bu'de min qofa na wuce wallahi zan ha'du da shi naji tun yaushe ya b'atamin yarinya da wannan shirmen banzan...â€
Hanan ta zube qasa tana 'kyal'kyala dariya, harda riqe cikinta, tana fa'din.
Sbd Allah Ummi mutun da matarsa, yo me naki aciki?â€
Mgnar Hanan ta janyo hankalinsu Abie.
Rahma tai sauri zare bakinta daga na Abie, ta 'dago kanta tana kallon bakin 'kofar falon.
Muguwar kunya ta kamata, ganin Jaddatu ta basu baya,tana surfama Hanan masifa akan ta bu'de mata qofa ta tafi, ita sai ta tsaya ta kwana wajansu, tinda bazata tafi ba.
Cike da muguwar kunya ta diro daga bayan Abie ta shige bedroom 'dinsa aguje tana sakin kukan takaicin ahalin da Jaddatu da Hanan suka gansu.
Saman bed ta fa'da ta shige bargo tsabar kunya, dan gani take ita kam bazata sake yarda ta sake ha'da idanu da Jaddatu ba.
Abie ya dafe goshinsa yana me jin kunyar Jaddatu, ga kukan da yaji babyn nasa ta fashe da shi.
Cikin dakiya ya nufo wajan su Jaddatu yana zura hannayensa cikin aljihun wandon baccin sa.
“Wlh Hanan idan baki bu'damin k'ofa ba, zan ci qaniyarki fa! Ni mahaukaciya za ki sakani gaba kina min dariya..?â€
Abie ya iso wajan yana murmushin qarfin hali, ya ce“Wai Ummi me ya farune?â€
Ya 'karashe tambayar yana zaro hannunsa waje ya riqe Jaddatu, ya Kama handle 'din qofar, yana kallon Hanan, wacce har yanzu dariya take tana kallon shi.
Ido 'daya ya kashe Mata, ya ce“Allah ya shiryeki Hanan, Ummi muje kiyi hkr wlh ba abinda kike tunani bane yanzu zan kawo miki 'yarki.â€
Jaddatu tai mutuwar tsaye, tana kallon Abie, rashin kunya qiri-qiri.
Fuska ta ha'de ta ce“Bud'e min 'kofa na wuce, ai ba damuwa kai da matarka, idan ma ka ce a daina gyaran da ake Mata tazo kenan ai shikenan tinda daman ka ce baka son ayi wani biki ka riqeta kawai...â€
Abie yay murmushi ya ce“Tuba nake ya mahaifiyata, wlh minti biyar bazata qaraba zan kawo miki ita muje.â€
Jaddatu bata sake magna ba, ya bu'de qofar yana riqe da hannunta suka fito, Hanan ta miqe ta biyo bayansu tana qyalqala dariya.
Sannu ahankali Abie ya sakko Jaddatu qasa, bai zame da ita ko ina ba sai bedroom 'dinta, ya samu ya lalla'bata, Hanan na musu dariya.
A qudundune ya iskota cikin bargo tana famar kuka.
Saman gadon ya haye ya janye bargon da ta rufa,ya sanya hannayensa dukkan ya 'dagota ya 'dorata saman cinyarsa ya tallabo fuskarta, ya tsirama kyakkyawar fuskarta manyan kyawawan idanunsa, cike da matsanaiciyar 'kaunarta, iska ya hura mata saman idanunta da qofar hancinta, ya matso fuskarshi dab da tata, yana goga mata kwantaccan sajansa, ha'di da hura mata iskar bakinsa mai fitar sanyin qamshi.
Yay mgna can qasa cikin kwantar da murya.
“Please mn my Baby. toh meye ma na kukan? Ni bana son kukanki yi hkr ta shi muje na rakaki.â€
Ya qarasa mgnar cike da sigar lallashi, yana zura harshensa saman fuskarta yana lasar hawayen da yake silalowa kan fuskarta.
Qamqameshi tai, cike da shagwab'a ta ce“Rabin raina! Kunya Jaddatu nakeyi, kwance gadon bayanka ta ganin, bayan haka bakina na cikin naka, lokacin da kamin zancan mutuwa bansan lokacin da na aikata hakan ba.â€
Labb'anta ya sumbata ya Mata ra'da akunnenta yana sake qamqameta yana shafa bayan.
Zabura tai tana qasa da kanta cike da kunya ta girgiza kanta, tana me wasa da yatsun hannunta.
Dariya yay ya miqe tsaye ya sakko daga saman bed, ya kamo hannayenta ya ce“Oya My baby love.â€
Ba musu Rahma ta sakko ya gyara Mata fuskarta yana maqale da hannunta suka fito falon.
Kallon so ya mata ya ce“Ko na goyaki?â€
Shagwab'e fuska tai ta maqale kafad'a ta ce“Abie ni dai da mun kusa sauka ka barni ka dawo zan qarasa kaji?â€
“Ok Baby love naji ai dole naji Ruhina.â€
Rahma tai murmushi tana qara damqe hannunsa cikin nata, tana jin sonsa na qara shigar dukkan wata gab'a ta jikinta.
anutse suke tafiya yana kasheta da kalamai masu sanyin dad'i.
Dab da zazu sauko, ta zame hannunta ta qara gaba.
Kai ya girgiza ya juya yana fa'din.
“Ruhina kiyi mafarkina.â€
Rahma cike da kunya ta shigo bedroom 'din tana rarraba idanunt, jin har lokacin Jaddatu na masifa.
Hanan ta ce“Ummi sai kiyi hkr gata tazo, Ummi ai nazata Chan zaki kwana?â€
Rahma taji kamar ta nutse dan kunya, ta wuce sumsum batayi mgma ba tai shirin bacci, tai kwanciyarta kusan Jaddatu.
Jaddatu ta ce“Zanga ta imda zaku sake ha'duwa tinda ke sakaryace, ina gyaraki kina zuwa yana lalubeki koh?â€
Rahma ta runtse idanunta, aranta tana fad'in.
“Innalillahi! Abie ka jamin ya zanyi? Ashe ban masa zance Abie 2 da Meerah ba.â€
Hanan dariya kawai take abinta, Rahma kuwa ta cure waje 'daya kamar ruwa ya cinyeta.
Abie kuwa ransa fess ya kwanta, ba jimawa bacci ya 'daukesa, sbd tashin da yake so ya yi na cikin dare.
★★★★★★
*Bayan kwana 5*
Niger
Duk tsayin kwanakin nan Ja'afar bai sake kusantar Ibtisam ba, yana kulawa da ita, sosai har ta warke ras ganin bai sake neman komai wajanta ba, ta saki jikinta da shi, sbd yadda yake bata kulawa, ga yanayin yadda yake romantic nata, bai wuce iyaka sai ta Fara rage tunanin Abie Sam yanzu bai dameta ba kamar da, datake wuni tana tunaninsa.
Tsaye yake a 'kofar falo cikin shirinsa mai k'ayatarwa, 'kananun kaya jikinsa ya yi masifar kyau, sai baza 'kamshi yake, yana amsa waya.
“Eh Abie insha Allah gobe muke tasowa.â€
Daga chan Abie Wanda yake harabar asibitin Rahma, ya amsa da.
“Ok Ja'afar Allah ya kawoku lfy, an shirya komai agidanku, insha Allah idan kazo kahuta sai muyi mgnar aikin ka, tinda kace bazaka cigaba da karatu ba!â€
Cike da girmamawa Ja'afar ya ce.
“Ok Abie insha Allah Ngd Allah ya qara rufa maka asiri, sai munzo.â€
Abie ya amsa da “Ameen ya Allah Ja'afar.â€
Katse kiran Ja'afar yay bayan ya masa sallama, ya kalli qofar jin takun Ibtisam.
Sanye take cikin wani danqarere lace, amman ba wai me ku'di dayawaba daidai wadaida ne, baqine me adon pink ya Mata kyau sosai 'dinki Riga da zani.
Idanu suka ha'da tai saurin kauda kanta, tana murmushi qasa², ganin yadda yake kallonta kamar zai lasheta, amman ya wani waske yana shan 'kamshi.
Dab da shi ta tsaya kamar zata shige jikinsa, ta 'dan kalleshi ta ce“Mon amour na shirya.â€
Hancita yaja, ya matsota jikinsa, ya rankwafo, dab da fuskarta, ya 'dago kanta bai tsaya wani batuba ya ha'de bakinsu ya sumbaceta, tare da tsotsar harshenta.
Ibtisam ta zare bakinta ashagwa'be ta ce.
“Don Allah muje kaji.â€
Da yake miskilan na kusa bai sake mgna ba, ya Kama hannunta suka fito ya rufe qofar falon, suka tafi.
Keke napep suka hau.
Tafe suke acikin keke napep, Ja'afar yana latsa wayarsa, message suke da wani abokin Haroun.
Kallonsa Ibtisam tai ta ce“Mon amour ina zamu fara zuwa?â€
Kallon yay ya shafi sajansa ya ce.
“Uhmm! Gidanmu mn, daga Chan sai ki wuce da dare zanje na kawoki.â€
Hannunsa ta kamo tana wasa da yatsun hannun tana murmushi.
Kallonta kawai yake, yadda ta dawo Ibtisam d'insa ta da.
Murmushi yay aransa ya ce“Mon cœur anji maza anyi hankali.
A 'kofar gidan Mal Adamu keke napep ta ajiyesu, Ja'afar ya biyasa ku'dinsa suka shiga.
Acikin soron qofar Ibtisam ta riqe hannun Ja'afar tana sunne kanta, ta ce“Mon Amour inajin kunyar Inna wlh.â€
'Yar dariya yay, ya rungumota ya ce“Tabbas dole kiji kunyarta 'danta kin Nuna bakya sonsa, yanzu kuma ya kaiki duniya ta daban kin dawo haiyacinki...â€
Da sauri ta sanya hannunta ta rufe masa baki, tana narai² da idanu ta ce“Please Mon amour za'a gamun muje.â€
Fuskarta ya shafa ya saketa tai saurin yin gaba, cike da kunyar irin yadda yake nuna mata tsantsar 'kauna, tin Randa suka zama abu d'aya.
Inna Hansatu mai waina, suna zazzaune a rumfa tsakar gida, anata hira hankalinta wajan lissafain ku'din wainarta, taji sallamar Ja'afar da Ibtisam.
Deluwa ta amsa sallamar cikin sakin tana fad'in.
“Sannunku da zuwa kune da rana tsakiya?â€
Ja'afar ya ce“Eh wlh umma mun fito sallama ne.â€
Inna ta ce“Au ashe gobene tafiya Allah sarki baqin buzuna.â€
Ibtisam ta tsuguna tana gaishesu cikin girmamawa.
Inna ta amsa fuska sake tana bata hannunta, ta qarasa ta zauna kusanta cike da jin nauyinta.
Maimou ta ce“Ya Ja'afar kamar nabiku, auntie Ibtisam ko nazo mu tafi ne?â€
Ibtisam kanta 'kasa ta murmusa ta ce“Eh Maimou.â€
Ja'afar ya ce“Ina wasa dakene?â€
Inna ta ce“Maida wuqar yayarta take tsokana ah toh.â€
Deluwa tai dariya ta ce“A'a fa kinsan halin Maimuna idan ta samu zuwan yi zatayi.â€
Ja'afar ya miqe ya ce.
“Bari naje wajan Baaba na dawo, sai ki tafi Chan gidan.â€
Ibrisam kanta a 'kasa ta amsa da.
“Tohâ€
Inna ta ce“Kaga kuwa abincinsa can yanzu za'a kai, jeka da shi.â€
Ja'afar ya amsa da.
“Toh innah.â€
Yana fita innah ta miqe da kanta ta zuboma Ibti abinci, dakyar tai hannu biyu sbd tsabar kunya da takeji, Maimou na janta da hira.
Sai kusan qarfe uku Ja'afar yazo ya rakata gidansu, daga can ya shiga sabgogin shi tare dasu Harisu dan tare zasu koma.
Laraba tinda Ibtisam tazo da kallo take binta, ganin cikin kwanaki 6 ta yi kyau tsaf abinta, fatarta taqara murjewa, kamar ma ta yi 'kiba haka take gani.
Taslim tai dariya tana kallon Laraba ta ce“Kai Anna sai kallon Auntie Ibti kikeyi halan ta canza ne?â€
Aydha tai tsalaf ta ce“Eh wlh ta yi kyau abinta.â€
Ibtisam ta zabga Mata harara ta ce“Ni ban son baqin surutu fa! Wai nayi kyau.â€
Laraba ta ce“Wlh sai yau da naganki hankalina ya kwanta, kinga yadda kika sauya kuwa? Allah ya qara Baku zaman lfy da kwanciyar hankali, dan Allah Ibtiam ki kwantar da hankalinki, kibi mijinki sau da 'kafa, kinga 'kasar wasu zakuje banda iskancin nan da kika tsira na baya ni dai wlh ba ruwana.â€
Ibtisma ta zumb'uro baki gaba ta ce.
“Anna ki daina tunamin wlh tallahi ba yin kaina bane alokacin, kuma ai komai ya wuce insha Allahu zanma roqeshi gafara, da zaran mun isa lafiya.â€
Ta 'karasa mgnar tana goge hawayen da suka silalo kan fuskarta.
Taslim ta ce“Ai wlh auntie kinyi dacen miji dan Allah Ku zauna lfy kinji?â€
Ibti tai murmushi ita kunya ma takeji sbd Taslim ta fita hangen nesa.
“Anna bari naje gidan Dadda na dawo.“
“Toh ki gaisheta Karime kuwa jibi zata tafi kije kuyi sallama.â€
Tanko ne ya shigo bakinsa d'auke da sallama.
Ibtisam ta miqe aguje ta tarbesa tana rungumesa cikin murna ta ce“Baba nayi kewarka dayawa.â€
Tanko ya saki baki da hanci yana kallon Ibtisam, da gaske yaga tayi kyau sosai harda 'yar 'kiba ma.
Hannunta ya kamo yana washe baki.
“Kai masha Allah Ibtin babanta naji dad'in ganinki haka sosai Allah ya qara muku zaman lafiya, ince dai ba matsa masa kikayi ba, akan ya kawoki ba koh?â€
Tana maqale da hamnunsa ta ce“A'a Baba, wlh shi ya ce muzo muyi bankwana gobe zamu tafi Tchad. â€
Kai masha Allah, naji dad'i Allah ya Baku zaman lfy ya kaiku lfy, dan Allah ki nutsu kisan bautar Allah kikaje yi, sannan dan Allah karki jamana abin kunya bake ba bawan Allah nan kinga kinada auren wani akanki, kiji tsoron Allah aduk Inda kike ki tuna idan bakya ganinsa shi yana ganki.â€
Ibtisam ta ce“Wallahi Baba na muku alqawali ba bainda zai faru sai alkahiri, insha Allah. â€
Tanko ya ce“Alhmdllh naji dad'i sosai Allah ya miki albarka, ya albarkaci aurenku.â€
Laraba ta amsa da
“Ameen ya Allah. â€
Ibtisam bayan iyayanta sun gama mata nasha mai shiga jiki ita da Aydah da Taslim suka tafi gidan Dadda domin mata sallama.
Ja'afar sai kusan 9 na dare suka tafi gidansu, bayan sunyi sallama da dukkan 'yan Uwa da abokanan arzik'i.
Su na isa gida suka fara shirin tafiya dan gidan bus zasu kwana 'karfe 4 na asuba bus d'insu zata tashi zuwa damagaram.
Bayan sun gama dukkan shirinsu sukayi wanna suka shirya.
Ja'afar ya kalli Ibtisam na hamma.
Hannunta ya kamo yana murzawa ya ce“Muje toh ai zakiyi bacci a can.â€
Langwab'ewa tai ajikinsa ta ce“Ai ba wani bacci hayaniya ta yi yawa awajan Mon Amour.â€
Murmushi yay iya labb'ansa yaja hancinta ya ce“Oya muje dare fa ya yi kar murasa abin hawa.â€
Manyan idanunta ta zaro waje tana 'Dora hannunta saman 'kirjinsa ta kallesa ta ce“Mon Amour Wlh na manta fa! Ai shi kenan muje 'din wlh bacci inaji kamar me.â€
Fuskarta ya tallafo da hannunsa 'daya, 'dayan a 'kugunta yana Mata wani shu'umin kallo Wanda ya saka taji fa'duwar gaba, ta lumshe idanunta tana tura kanta tsakiyar 'kirjinsa.
Bakinta ya sumbata ya Mata ra'da akunnenta.
“Je t'aime bébé, kinci bashi dayawa fa! Zaki biya a Tchad. â€
Ibtisam ta 'kwace jikinta ta koma baya tana maqale kafa'da.
Kai ya girgiza yana zura hannunsa cikin aljihun wandonsa, ya fita kiran adaidaita sahu.
Aikuwa suna zuwa gidan bus (3stv) ya rakata 'bangaran mata ya wuce wajan maza, bata jimaba bacci ya 'dauketa duk da kuwa qaran TV bai hanata baccinta ba.
★★★★★★
Washegari misalin 4:30 na asubah bus d'insu ta 'daga daga Tahoua.
Tchad
Duk tsayin wannan kwanakin da gaske Jaddatu ta hana Abie ganin Rahma ta amshe wayanta ko awaya basa ha'duwa, hakan ba qaramin takura rayuwarsu yay ba su duka biyun sunyi missing 'din junansu, Rahma kuwa tai alk'awalin bazata bi kowace hanya ba dan ganin Abien, zata hkr har ayi bikin tinda yazo.
Jaddatu Abie2 kawai take Kira a waya taba Rahma su gaisa, ko idan yazo gaishe da Jaddatun ta basa umarnin shiga wajan Rahma susha hirasu nan kawai take samun sassauci, Abby da zainabu sunata dariya dan sunga Jaddatu abun na gaske ne.
*Gabon*
Ma'aruf duk yabi ya rame, ya sakawa kansa damuwar abinda sukayi da Rabi'ah, Uwa uba ga ciki ajikinta, abun ya tab'asa sosai ga shi Aishatu ta ce yabar komai ahannunta, haka ya barwa Allah ikon sa.
Cikin shirinta ta fito tayi kyau tsaf sai uwar ramar da take damunta.
Hajiya ta kalleta ta ce“Aishatu wai me kike nufi da Ma'aruf ne? Toh wlh yau gidanki za ki koma kya qarasa warkewa agidanki, shifa Aisha zaman aure 'dan hkr ne, wlh duk macan da bata iya hkr da mijinta tabbas bazata iya zama da kowa aduniya ba, Ma'aruf fa 'dan uwanki ne koda wani abun ya miki hkr zakiyi ki yafe masa sannan idan Wanda zakiyi qoqarin sanya shi hanyane ki jajirce kiga ya bari ne, ba wai ki guje shi ba, ke da yake 'dan uwanki kin guje shi ina kuma bare?â€
Aishatu ta zauna kusan mahaifiyarta ta kamo hannunta ta ce“Insha Allahu zan koma ni bai min wani abu na gujewa kawai naji haushine wani lamari da ya faru amman insha Allah na yafe masa kuma idan na koma zanzo na muku bayani wlh :kaddarace kuma bata wuce kan kowa, zan shairya cikin kwanakinnan kafin sati biyu zan koma, bari na qara warwarewa.â€
Kallonta mahaifiyarta tai ta ce“Ni bazan matsa miki naji tsakaninki da mijinki ba, dan haka Ku gyara tsakaninku Allah ka'de fitina tsakaninku.â€
Aishatu ta amsa da.
“Ameen Uwa tagari sai na dawo.â€
Kai tsaye Aishatu tana fita ta hau taxi ta tafi gidansu Rabi'ah dan bata yarda da ita ba, tana gudun ta zubar da cikin.
Rabi'ah zaune tsakiyar falonsu qasa tana shan iska, sanye da doguwar Riga atamfa, duk ta rame sai uban fari tai cikin ba qaramin laulayi take sakata ba.
Hannunta riqe da cup tana shan ruwan tsamiya.
Aishatu ta shigo gidan da sallama.
Maman Rabi'ah ta amsa tana shanyar kayan da almajirinsu ya wanke ya bari igiyar ta cika.
“Ah Aishatu kece da rana haka?â€
Aishatu ta rusuna ta gaisheta tana ajiye baqar ledar hannunta, ta amshi shanyar tanayi.
“Wlh nice mama ina Rabi'ah kuwa?â€
“Tana ciki kawo nayi dan Allah Aisha ki bari kema ba lafiyar kirki gareki ba.â€
A'a mama zanyi.â€
Bayan ta qarasa ta Mata jagora suka shiga d'akin.
Rabi'ah jin murya Aishatu ya saka duk ta diririce.
Dakyar ta amsa sallamar tsabar kunyarta.
Aishatu ta zauna kusan Rabi'ah ta ajiye ledar ta ce“Rabi'ah barka da rana ya jikin?â€
Rabi'ah ta fashe da kuka ta rungume Aishatu tana kuka mai cin rai ayanzu arayuwarta ba abinda tafi so irin mutuwa duk da tasan bata tanadi abinda za'ace taso mutuwa ayanzu ba.
Aishatu ta janye ta matsa gefe tana tab'e baki, ta ce“Uhmm! Nazo na sake garga'dinki ne wlh karki kuskura ki zubar da cikin nan, yadda bakiji kunyar abinda kukayi ba har Allah ya Baku kyauta toh idan dai Allah ya yarda sai kun haifesa ya taka doron k'asa, sbd bakusan me zai zama ba nan gaba ko ta zama ba, dan haka kuji tsoron Allah karki zubar da cikin nan.â€
Rabi'ah ta ce“Insha Allahu dan Allah Aisha ki yafemin.â€
Baki Aishatu ta tab'e ta ce“Wlh da ban yafe muku ba Sam bazaku tab'a sake ganina arayiwarku ba, ni na tafi Allah ya qara lafiya.â€
Rabi'ah kunya ta hanata rakiya tana kallon Aishatu har ta fita.
Sallama ta ma Maman Rabi'ah ta tafi.
Tana fita Rabi'ah ta fasa kuka me cin rai tana qara nadama abin da tayi, tabbas ta yarda son zuciya b'acinta.
★★★
Rayyana