Showing 126001 words to 129000 words out of 165653 words
da taga Ana mata yasa ta fice daga gidan tana kuka.
Abie 2 na zaune ya zubama qofar falon idanu, su Abie suka shigo da sallama.
Abie ya amsa yana hawaye ya warema Rahma hannayensa.
Hannun Abie ta matse tana kallonsa ta ce“Abienah naje wajan Abie2 ? Me ya samesa yake kuka?â€
Abie ya matsa hannunta sosai cikin nashi, ya mata ra'da akunnenta.
“My Baby my heart eh jeki, shi ne yayan Ummul Aymana, congratulation my baby naji da'din samun jinin mahaifiyarki zaku rayu tare.â€
Rahma ta qamqame Abie ta ce“Ngd ngd ngd Rabin raina.â€
Ta sakeshi ta fashe da kuka da gudu ta nufi wajan Abie2.
Jikinsa ta fa'da ta 'kam'kameshi tana kuka, ta ce“Allah sarki Abie2 nah ashe dai Abien nawane, Alhmdllh! Allah na godema zan rayu da jinin mahaifiyata, Abie2 ina sonka don Allah ka kasance tare da mu har abdan bazan barka ka koma Iran ba bare akashemin kai. Naso na rayu da ummata nasan macace me kirki zata riritani zan mata shagwa'ba zan dinga tsokanarta na zubawa da gudu tana bina tana ku kamomin ita yarinyar nan batajin magana fa! Wlh ina son ummina ina son Abbana ina son Mustapah, ina son Abienah amman son Abienah ayanzu na daban ne duk son da nake musu na ha'damasa shine kowa nawa sai yanzu da na sameka Abie2, kai zan ba rabin 'kaunar Abienah.â€
Abie2 shima kukan yake ya rungumeta ya ce“Nima bazan tafi ba 'diyar albarka muna tare insha Allah, Abienki shine uwarmu shine ubanmu dole ki masa son so amman ai shine mahaifinki ko.â€
Abie zama yay gefensa ya tallafe kumatunsa da tafukan hannunsa ya zuba musu idanu yana kallonsu kamar Tv, bai hanasu kukan su ba sunata sambatunsu.
Rahma ta basa dariya sabida ta kasa amsa tambayar da Abie 2 ya mata.
Numfashi yaja yay gyaran murya ya ce.
“Toh dai kukan ya isa haka pls ai Baby bazata amsa maka tambaya ba, bari na baka tarihin ha'duwata da Ummul Aymana...â€
Abie nan ya tsakura masa labarin Aymana na ha'duwarsu da soyayyarsu da sadaukarwa da yama Aliyu zuwa haihuwar Rahma da basa ita da sukayi da 'daura aurensu da Abbu yay da kashe shi da Naja'atu tai, da dalilin zuwansa nan.
Abie2 ya ce“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abdul Majeed sannu kai kam na daban Allah ya halicce ka acikin mutane, wlh bansan Kalmar da zan gayamaka ba, komai ka wuce akiraka tsakanina da kai kawai nayi ta maka addu'a da fatan alkahir har numfashina yabar gangar jikina, ban ta'ba murna da farin ciki ba irin na yau naji da'din 'diyar albarka matarka ce ba namijin da ya cancanta ya zauna da ita matsayin mijinta sai kai, kaine uwata Kaine babanta yayanta 'kawarta komai nata.â€
Abie ya murmusa yana jinjina kansa, ya kamo hannun Rahma ya zare wayarsa cikin hannunta, yana latsawa.
Rahma ta kalleshi ta kalli Abie2.
Abie2 Yay murmushi ya ce.
'Diyar albarka 'dagani na wanko fuskaâ€
Rahma janye daga jikin Abie2 tana goge fuskarta.
Hanyar bedroom ya nufa.
Kallon Abie tai yana waya.
“Hello yauwa a ha'doma komai na breakfast akawo mana 'bangaran Abie2.â€
Katse kiran yay, ya danna number Abby morocco.
Ringing biyu aka 'daga.
Da hannu ya yafito Rahma yana 'daga mata gira, yana mata nuni tazo kusansa.
Kanta ta kauda ta 'daga kafa'da ta ce“Naqi awajan babana nake.â€
'Yar dariya yay yana kallonta cike da so ya fara amsa wayar.
“Hello Abby! Baku taso ba?â€
Daga can Abby ya amsa da.
“Ai jirginmu sai 10 na safe zai taso insha Allahu, ina rigiman manka?â€
Abie ya ce“Gatanan ta ha'du da babanta ta shareni ina kiranta.â€
Yanayin da ya yi mgna ya sanya Rahma juyowa ta kalleshi tana girgiza kanta.
Abby yay dariya ya ce“Wani uban kuma?
Abie ya ce“Wlh dattijon da yake gidana ashe yayan Ummu Aymana ne, daman najima ina zargin hakan ban dai tabbatar bane.â€
Abby ya ce“Masha Allah naji da'di yarinyar mu ta sake samun gata.â€
Sunyi 'Yar hira yaba Rahma wayan akunyace yau ta gaisa da Abby ba kamar daba, har yana tsokanarta.
Abie2 na fitowa Latifa na shigowa da 'katon tray shaqe da kayan breakfast, da sallama.
Leda ta shimfida saman carpet ta ajiye tray'n atsakiya ta gaishe da Abie2.
Abie ya ce“Yauwa Latifa fatan kunyi aikin da na baku?â€
Cike da ladabi ta ce.
“Eh Yalla'bai ai tin yaushe har 'kofar gate muka kaita.â€
Abie ya jinjina kansa ya ce“Masha Allah Ngd tashi kije.â€
Rahma da kallo take bin Latifa har fita.
Abie ya ce“Baby sakko mu karya, ha'dama.â€
Baki ta zumb'uro ta sauko kusan Abie2 ta zauna ta ce“Abie2 kaga Abie ya saka na kori ammi ai bai kyauta ba ko?â€
Kallonta Abie 2 ya yi cike da mamaki ya kalli Abie wanda ya zubama Rahma idanu yana mata kallon mamaki.
Abie2 ya ce“A'a baka kyauta ba me ta yi?â€
Abie ya harari Rahma ya ce“Uhmm! Wlh kashemin ita ta kusa na isko ta shaqeta da bana kusa ai shikenan.â€
Abie2 ya ce“Subahanallahi bata kyauta ba.â€
Rahma ta ha'da musu tea me kauri ta zuba musu farfesun kan rago kubus gefe ga soyayan dankalin turawa normal ba kwai.
Akunyace take ci sabida kallon da Abie yake mata.
Can ciki kuwa Jaddatu baccinsu suke cike da nutsuwa.
Yayin da Rayyana tana can kamar mahaukaciya sabuwar kamu.
Gidan nasu ta fa'do aguje tana ihu da kururuwa, Auntie Saro a kitchen tana ha'da breakfast taji ihun Rayyana.
Fitowa tai ta ce“Ke! Lafiya me ya faru na shiga uku.â€
Rayyana ta riqe Saro tana kuka ta ce.
“Ya sakeni Saki uku kawai dan na kamasa da 'yarsa suna alfasha wlh kamasa nayi yana tsotsarta, kawai dan na fa'data da bugu ya sakeni, don Allah Auntie ki temaka min na koma ina sonsa.â€
Saro ta ce“Ta faru ta qare nasan za'a rini bakyajin mgna 'kun'kurus tafaru ta kaqare, amman 'karya kike koda kin kamasu na yarda akwai 'boyayyan al'amari, ba wai yana alfasha da ita bane, wannan mutumin baka shedar 'dan Adam amman wlh ban yarda zai aikata zina ba, duk wanda ya kiyaye dokokin Allah da wuya ka sameshi cikin masu aikata alfasha, bare babban zunubi irin wannan.â€
Rayyana ta ce “Ya ce wai na isa na kashe masa mata uwarsa ta cemain wai Rahma matarsa ce ba 'yarsa ba, 'yan aiki aka saka suka min 'daukar 'yan wanki suka fiyo dani waje, yaushe Rahma ta zama matarsa?â€
Saro ta kamo hannunta suka shiga ciki zaunar da ita tai ta kawomata ruwan sanyi ta bata Tasha ta kamo hannunta ta ce“Abinda zan gayamaki anan shine kiyi hkr ki cire Abdulmajid aranki wlh najima da ciremiki shi arai, da nasan abinda kakiyi zaiyi wuya yaci gaba da zama dake daman irin ranan nan ya miki tanadi dan haka wlh karki kuskura kice zakibi malamai sbd ba aure tsakaninku Saki ukune kiyi hkr ki dage da istigfari ki tsarkake zuciyarki wlh za ki samu muji kiwa Allah ki Santa zuciyarki hkr ina jiye miki aikin da nasani irin wanda kikayi kwanaki ki manta da rayuwar da kikayi da shi ki fuskanci gabanki yanzu ki Kama kanki don Allah, daman can ALLAH ne ya 'kaddara akwai aure tsakaninku amman ai ba sa'an aurenki bane, sai dai kashhh! Damar da ya baki kikayi wasa da ita dan haka shawarata kiyi hkr ina jiye miki aikin da na Sani wlh idan kika je kika gingimo babban aiki ba hannuna ba 'kafata kiyi tawakali da mabuwayi gagara misali sai komai yazo miki a sauqi.â€
Rayyana sosai jikinta ya yi sanyi ta share hawayen fuskarta ta ce“Na miki alqawali zanyi aiki da shawaranki duk da ina masifar sonsa zan jure na Kama rayuwa sabuwa yanzu na kuma yarda ni ce na janyo kome ya faru dani zanyi qoqarin gyarawa.â€
Saro ta rungumeta ta ce.
“Naji da'di sosai Allah ya shige mana gaba adukkan lamarinmu.â€
“Ameen.â€
Rayyana ta amsa, nan ta kwanta sbd ciwon kan da take Saro ta tafi ta qarasa girkinta.
Can gidan Abie kuwa cikin farin ciki aka wuni,su Jaddatu da suka samu labarin Abie2 yayan Ummin Rahma ne, Rahma tana kusan Jaddatu wuni guda sai dai ta kasa sakewa irin na da, Abie kuwa ya fita sha'aninsa zuwa companynsa, su Meerah kuwa anata girke² tarbar baqi.
*Niger*
Misalin 'karfe 6 na yamma.
Ibtisam zaune, can gefe abinta tana qanqaran faratanta, har yanzu 'kirjinta zafi yake mata, haka la'bbanta basu idasa sacewa ba kamar yaune ya mata muguntar.
Tsaki taja ta ce“Mugun banza Allah sai ya saka min, ban yafe ba.â€
Laraba dasu Karime akan kunnansu abinda data fa'da.
Karime ta ce“Wlh zakici ubanki wannan mugun halin bazaki kaiki ko inaba sai nadama, kibi a sannu fitinanniya kawai.â€
Laraba kam batace uffan ba dan tana mgna Karime ta ce ita ta koya mata.
Taslim ta ce“Aunty Ibtisam anata shiryaki kina baqin hali wlh duk kyan amarcin naki zai zube ai.â€
Miqewa tai daman tana sanye da hijab ta ce“Na tafi gidan Dadda nan gidan ba mai 'kaunata.â€
Karime ta ce“Ai za ki dawo jeki Allah kiyaye.â€
Aydah ta biyo bayanta suka tafi.
Dab zasu karya kwanar gidan sai ga Ja'afar saman mashin yana tuqi yana waya sai murmushi yake, sanye yake da 'kananun kaya.
Sauran ka'dan ya bugeta yay saurin taka burki ya 'dago da niyar basu hkr dan baima lura da suba.
idanunsu ya ha'de waje 'daya.
Take Ja'afar ya ha'de fuska kicin² yana mata shegen kallon rainin wayo.
Ibtisam kuwa gabanta ya fa'di, tsoronsa ya shigeta ga wani irin kwarjini da ya mata, ya yi masifar kyau.
Kanta ta sadda k'asa tana Jan hannun Aydah zasu wuce.
Aydah ta ce“Yaya Ja'afar ina wuni lah! Gidanmu zaka? Mu kuma zamuje gidan Dadda.â€
Ja'afar ya Saki fuska ka'dan ya amsa gaisuwar ya ce“Aikenku akayi ne?â€
“A'a Auntie ce kawai zataje shi ne zan rakata.â€
“Ok.â€
ya ce yana kallon Ibtisam, ya ce“Wa kika tambaya? Ko zaman kanji kike?â€
Kallo 'daya ta masa ta sadda kanta 'kasa tana wasa yatsun hannunta ta ce“A'a zanje amsa abuneâ€
“Koma toh gida wlh na sake jin labarin kin fito kinsan halina, ware anan 'yar rainin hankali. Aydah na hanata Ku koma gida kinji yarinya me hankali, ki gaishemin da Nadra da Taslim.â€
Ibtisam ta saci kallonsa ta juya suka koma gida, ya kunna mashin 'dinsa yay gaba.
Da kuka ta shigo gidan tana fa'din“Yanzu Ana gani wannan baqin mugun zai kasheni da basin ciki baza'a raba aurenba.â€
Karime ta jefa mata takalmi ta ce“Anqi araba dan ubanki keda shi mutu ka raba uwad mugun hali. Aydah ya akayi kuka dawo?â€
“Umma da Ya Ja'afar muka ha'du ya koromu gida ya ce ba'a zuwa gidan Dadda wa ta tambaya tinda ba aukenta akayi ba mu dawo gida.â€
Laraba ta ce “dakyau wlh yayimin daidai.â€
Ibtisam d'aki ta shige tana turo baki.
Inna suna zazzaune Deluwa na girki anata hira.
Ja'afar ya shigo da sallama da qatuwar leda ahannunsa, ya beqama Inna Hansatu.
“Kai Masha Allah har an gama 'dinku nan?â€
Ja'afar ya ce“Eh innata ai Saidu bai wasa da cika alqawali, ki cire naki ki ba umma nata ga na Baaba a ajiye masa bari na watsa ruwa.â€
Ya fa'da yana sauke numfashi ya juya zuwa 'bangaransa.
Deluwa ta ce“Allah ya maka albarka Ja'afar ya tsare manat kai gabanka da bayanka.â€
Ya amsa da “Ameen umma.â€
Innah aka ranga'da gudu“Allah saka maka da alheri baqin buzuna.â€
Maimou ta ce“Wlh da nasani daman can nakai.â€
Deluwa ta ce“Su Sadiya kuwa can suka kai Ja'afar ya tamabyo musu.â€
Ja'afar yana fitowa daga wanka Ana kiran magarib yay alwala ya tafi masallaci.
*Gabon*
Bayan sallar magarib Aishatu ta sulale ta tafi gidan Rabi'ah.
Zaune take atsakar gida ta yi tagumi ta rasa abinda yake mata da'di arayuwatar,kamar amafarki taji sallamar Aishatu.
Da sauri ta 'dago kanta ta kalli hanyar shigowa gidan, ta ga ita ce.
Mamarta ta ji ta amsa sallamar.
Cike da jin kunyar Aishatun, tana fa'din.
“Aishatu kece agidan namu? Sannu da zuwa wuce ciki mana.â€
Aishatu fuska sake ta amsa kamar ba komai, ta nufo wajan Rabi'ah wacce ta kasa motsi kamar ruwa ya cinyeta.
Dakyar ta miqe tana cewa“Mushiga ciki.â€
Aishatu ta bita abaya ba tare da ta tanka mata ba.
Kai tsaye 'dakinta suka shiga, ta nuna mata gefen katifa.
Zama tai ta ce“Ya jikin? Allah ya raba lafiya, yauwa ba wai wata alaqa ta kawoni wajanki ba, a,a nazo na tunasar dakene, karki kuskura ki amince idan Ma'aruf yazo miki da mgnar zubar da ciki, kiji tsoron Allah kibar cikin nan ki haifeshi ba'a San me abinda aka Haifa zai iya zama ba, nan gaba, dan haka kuji da zunubin zinar ma, na barki lafiya.â€
Rabi'ah tai saurin riqe Aishatu tana kuka ta ce.
“Don Allah Aisha ki yafemin, naji kin yafemin ki sake yafemin.â€
Karki damu ai ni baki cuceniba, kanki kika cuta, wlh ba komai na yafe miki, duk meson Allah kaima ya dinga yafema kura-kuran-ka toh ka yafema mutum duk girman laifin da ya maka, dan haka ni ban riqeki ba.â€
Tana gama mgna ta janye jikinta ta fito.
Sallama ta ma mama ta tafiyarta.
A can Gabon kuwa da yamma Abie ya Kira motar ma'aikata masu kwasar kaya aka kwashe duk wani abun da ya sanya ya mallaakawa Rayyana aka kaimata gidansu, ta ci kuka kamar ranta zai fita, dakyar Saro ta lallasheta ta hkr.
Sai kusan Maghreb jirgin su Abby ya sauka Chad, Rahma murna bakinta ya kasa rufuwa, dadi takeji sosai batada iyaye amman 'yan uwan mahaifinta nada yawa ga yayan ummanta araye.
Abie yaba su Abby labarin komai akan Abie2 nan murna ta qaru, kowa kagani farin ciki yake.
Misalin 'karfe 9 na dare bayan sun gama cin abinci anyi gaishe-gaishe yaushe gamo, harda Abie2, zaune suke a falon anata hira Rahma sanye da riga da skirt maroon colour sun mata kyau sosai tana zaune ta jinjina kanta jikin Abby, Zainabu na shafa kanta, tana murmushi take cewa“Wai ni Rahamu takwaraki yanzu 'Yar kunya kukene?â€
Jaddatu ta sanya dabino abakinta ta ce“Humm bari wlh tin jiya da ta gane komai abu ya cakule taqi sakewa dani ni kuma wlh bazanyi surukunta da ita ba, takuramu zaiyi.â€
Abby ya yi dariya yana lakatar hancin Rahma ya ce“Gaskiya kam, yauwa Abdulmajid yanzu dai zamu tsayar da ranan biki sati uku insha Allah da zaran anyi sai mu wuce...â€
Ummiterh tai ihun murna kamar wata yarinya qarama, tana fa'din.
“Hakan ya yi daga gobe zan fara gyara 'diyata zan shiga kasuwa na siyo komai ba sai an 'dauko me gyara ba.â€
Zainabu ta ce“Ai keda Hanan daman zaku gyarata tinda kun Iya ni Ku barmin wani 'bangaran.â€
Hanan ta ce“Ummiterh gobe sai muahiga kasuwa insha Allah. â€
Jaddatu ta ce“Nima zan aiki Latifa akwai abinda zata siyomin na gyara 'diyata.â€
Abie ya yi wani irin murmushi na farin ciki ganin dukkansu kowa burinsa ya gyara masa babynsa, ya shafi sajansa ya ce“Masha Allah kowa burinsa ya gyara 'yar gidan Abie.â€
Rahma tai saurin kallonsa, idanunsu ya sarqe, ya kashe mata ido 'daya da 'daga mata gira, tai saurin sadda kanta, kunya kamar ta nutse 'kasa ta miqe jiki ba qwari ta nufi 'dakin Jaddatu.
Abie2 farin cikin Gatan da Rahma take Sha wajan dangin mahaifinsa ya sakashi kuka dakyar Abie ya rarrashe shi ya Kama hannunsa suka fita.
Abie kwance saman makeken gadonsa sai juyi yake kewar Rahma ta addabeshi yana ta kiranta yaqi d'agawa, dan lokaci tama yi bacci wanda tana jikin Jaddatu rungume.
Tsuki yaja yana caku'da sumar kansa ya furta.
“My baby pls kizo ko 'duminki naji.â€
Yajima kafin bacci ya sace shi.
★★★★★★ ★★★★★★
Bayan kwana 7
Tin randa su Abby suka zo rabon da Abie da Rahma su ke'be, wasan 'buya take da shi, idan zataje wajan Abie2 suyi fira sai ta tabbaatar baya gidan take tafiya, dan ta dawo 'kasa wajan Jaddatu.
Abie duk wayonsa da dubara ya kasa ke'bewa da Rahma, dan Jaddatu ma ta saka masa ido bata son ya b'ata musu shirinsu da suke fara mata yau tsawon kwana 6.
Wani irin tsumi Zainabu da Jaddatu suke mata, Ummiterh da Hanan kuwa gyaran jiki da turare suke mata, tun tuni ta fara canzawa jallabiya Jaddatu take sakata ta saka har 'kasa sannan kullun fuskarta akwai niqab, kome nata sun rufe mata hannunta safar hannun 'kafarta safar 'kafa, basa buqatar Abie yaga komai nata sai ran bikinsu.
Abie kamar ya yi kuka idan ya ha'du da Rahma a falo komai nata baya ganinsa sai idanunta.
Abie ya cika alqawali ya samoma Ja'afar gida 'dan 'karami me kyau 'daki uku da kitchen da toilet akwai 'yar 'karamar rumfa ta ajiye mota, gidan tsaf me kyau ya zuba musu komai aciki Masha Allah Allah ya biyasa da alkhairinsa.
Acan kuwa Niger yau take sallah, dan yau ake bikinsu Ja'afar idan kaga yadda ina ake hidimar biki abun sai ya burgeka, su Yahuza sun iso yin daren jiya, tare ake shagalin biki dasu.
Ja'afar ya ce baishagalin komai suna nan 'bangaransa da abokansa, ya samu gida me kyau ya Kama haya kasancewar ba jimawa zasuyi ya dai kamane kafin su tafi Ku'din wata 2 ya bada shi da ko wata bazai ba, can akaje aka shiryama Ibtisam kayanta daman katifa ce babbar sai carpet da labulaye da tarkacan kayan aiki, tinda daman Abie ya cema Tanko kar ya siyi kaya sosai zai zuba musu komai anan.
Yau Laraba baki yaqi rugowa sai sutturo ake sauyawa.
Ibtisam kuwa ansha kyau Masha Allah ba 'karya, an tauma ta taumu sai zuba take Tasha murza tayi wani irin kyau na ban mamaki. shegiyar ba gayyar 'kawayen da ta yi ko mutum daya duk Taslim ce ta gaiyato 'kawayenta, suke gwangwajewa.
Kowane 'bangare anyi bajinta dan Mal Adamu Sa ya yanka haka Tanko ko almajiran inguwa sunsan yau anyi biki na 'ya'yan gata.
Misalin 'karfe 8 aka gama shiryata don zuwa 'dakin mijinta, banda kuka ba abinda take.
Laraba da Tanko sun sata gaba da nasiha sun ja mata kunne sosai, Tanko ya ce“Don Allah ki zauna da mijinki lafiya kiyi nayi bari na bari don Allah ki fitar Dani kunya Ibisam ki temakeni ki zauna lafiya da mijinki.â€
Cikin kuka ta ce“Insha Allahu Baba.â€
Rungumeta yay ya sanya mata albarka.
Laraba ta qara da tata nasihar da sanya mata albarka kafin Karime, nan ta kamata suka fita tana ihun kiran Babanta da Anna.
Taslim ma.kuja take shi kenan ta rabu da 'yar uwarta.
Haka aka sakata mota suka tafi tana kuka kamar ranta zai fita, Karime na lallashinta, dan tasan kowace amarya tana tsintar kanta cikin wannan yanyi.
_Rahmerh ladingo😉_
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
5/3/22, 13:18 - You added Firdausi Yunus Ce
5/3/22, 17:51 - Buhainat: ```D A```
```91&92```
Gidane 'dan madedeci me kyau na talaka, ashafe da siminti ko ina 'dakuna guda biyune kowane akwai toilet avijinsa kitchen atsakar gida.
Karime na ri'ke da hannunta suka shigo falon, su Ramlat duk suna zazzaune suka tarbesu cikin sakin fuska, suka gaisa suka musu jagora har bedroom 'din.
Katiface inci shabiyu shimfi'de tsakiyar 'dakin an shimfi'da carpet, 'dakin sai 'kamshi yake.
Saman katifar Karime ta zaunar da ita akwai jama'ar ango sosai awajan.
Sadiya tana tsokanarta.
Yayarmu