Showing 102001 words to 105000 words out of 165653 words

Chapter 35 - DATTIJON ARZIKI

Start ads

Rahma   

15 Aug 2025

852

Middle Ads

'kasan 'kafafunsa suka zube suna godiya, da masa addu'u sabida ku'dine wanda dukkansu kowa zai ishesa sabgogin bikinsa har agama ba wanda ya nemi wani abun.â€
Sallama yay musu jin ana shirin tayar da sallah nan masallacin gidansa.
Laraba baki da hanci ta Saki tana kallon uban 'daurin ku'din da Abie yaba mazan ita banda ita ko meyasa ya hanata?
Abie ya ce“Ai sai mu hanzarta zuwa masallaci kar atayar da sallah da mun fito sai muwuce airport nayi rakiya.â€
Cike da murna dukkansu suka fito domin zuwa masallaci daman sunada alwala.
Ibtisam kuwa tinda ta kalli Abie ta sadda kanta bata 'dago ba saida ta ga ya shige ciki ta miqe tana zubar da hawaye, ta nufi cikin, amman bata shiga ba sai da ya fito ta nufo ciki nan taci Karo dasu Abie 2 zasu masallaci.
Jikin Laraba ta fa'do ta fashe da kuka mai cin rai tana fa'din.“Amatsayinki na mahaifiyata kimin addu'a Allah ya yayemin abinda yake damuna dan Allah.â€
Laraba ta ce“Ibtisam ki dawo hankalinki tashi kiyi sallah da sun dawo zamu wuce ni ina hutune.
Kinga mutumin nan ya rabamusu uban ku'di wlh ko sisin kwabo abi ban ba, ikon Allah.â€
Ibtisam ta ce “Balarabe ko?â€
Laraba ta ce“Eh amman nasan Babanki zai bani.â€
Ibtisam ta share hawayenta ta miqe tayo alwala daman tana sanye da hijib madedeci tahau darduma ta tayar da sallah.
Abie ana idar da sallah ya shige moto tare da securities suka fice.
Yahaya ne ya kaisu Ja'afar airport Abie 2 'dan rakiya, shi daau Yahuza, suna nan sai da jirginsu ya cira sama suka nufi gida.
Ja'afar da Ibtisam wajan zamansu 'daya amman ko kallo bata ishesa ba, sabgogin gabansa yake.

*Gabon*
Aishatu sosai jikinta yake rawa gabanta yana fa'duwa, ganin paper 'din hannunsa tasan sakinta yay.
Danne abinda takeji tai ta sanya hannunta wanda yake rawa ta amsa tana fa'din.
“Allah yasa haka yafi alkhairi.â€
Ta 'karashe mgnar zata zauna, taji ya fizgota ta fa'do jikinsa ya rungumeta ta baya, ya 'dora ha'bar akan kafa'darta, cikin kwantar da murya ya ce“Yanzu don Allah kinason na sakeki?â€
Fizge jikinta tai tana nunasa da 'yar yatsa ta ce“Karka raina min hankali mana, kana nufin ba sakin nawa kayi ba?â€
Sake damqota yay ya rungumeta ya ce“Wlh bazan iya sakin ki ba! Don Allah ki yafemin zan dai barki har lokacin da za ki sauko dawo gida wlh Allah ban ta'ba zina ba, abinda dai da na fa'da Munnira shine gaskiya wlh bana haiyacina komai ya faru ki fahimceni dan Allah.â€
Jikinta ta janye ta zauna tana bu'de takardar, da abinda ta fara cin karo ya sanyaya mata jikinta.
BAN HKR MY AISHERðŸ‘ðŸ½ðŸ˜­

HMM! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki.
INA SON
KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA my Aisher.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan tab'a canjawa a kan hakan ba, don Allah ki yafemin my dawo kamar da nayi miki alqawalin zama dake bisa amana, ina sonki my Aisher.â€

Ajiyar zuciya ta sauke a'boye amman azahiri tai kicin² da fuska ta miqe ta shige toilet ta banko 'kofar.
Murmushi yay ya juya ya tafi.
Rabi'ah wasa² tana cikin tashin hankali duk ta fige ta lalace komai baya mata da'di, sai tayi yin'kurin zuwa ganin Aishatu sai ta fasa gabanta na fa'duwa amman ta 'dauki alqawalin zuwa dubata da neman gafarata idan abun ya lafa.

*Niger*
Inna Hansatu an kasa zaune an kasa tsaye anata murna Ja'afar da babansa zasu zo, an yanke zabbi guda uku manya anyi farfesu an dafa macaroni da shankafa, an gyara musu salad da kwai anyi kunun gyad'a kai abun Masha Allah.
Sadiya tazo ta Kama mata girkin da Deluwa Maimou ta 'kwal'kwale gidansu tasa tana turaren wuta abin gwanin ban sha'awa ta share 'dakin Ja'afar ta goge an canza zanin katifa, Mahmoud ya wanke wanda yake kwana Asama.

Can ma Dadda da yaran sunzo sun gayara gidansu Laraba, Taslim Masha Allah, ta share 'dakunan ta goge ta kunna turaren wata, Dadda ta sayo zakatu biyu aka yanka ita da Taslim suka 'Dora girkin.
Dadda tana mota miyar Taslim ta ce“Don Allah Dadda ki daina zatayi 'karni fa!â€
Aydah tai dariya tana fa'din.
Kince Dadda bata iya girki ba.â€
Dadda ta ce“Barta Aydah 'Yar ashatta ko uwata ta gwadamin girki bari na kammala muci kuji.â€
Taslim tai dariya ta ce“Yo abinda duk Rabin miyar nice ni da nafi Auntie Ibtisam ma iya girki.â€
Dadda tace“Ai shagwa'bar ta barta iya girki ja'ira ai Ja'afar zai ga tab'ara.â€
Dariya sukayi bayan sun kammala firkin bayan Maghreb sunyi sallah Dadda ta zuba musu sukaci suka 'koshi dam nan suka Kama hira dan Dadda na tare dasu sa iyayansu sun zo sai ta wucce gida.
Inna Hanssatu zaune an kakkame an sha wanka masha Allah ga 'kunshin gargajiya ansha 'kafa da hannu, gida ko ina sai baza 'kamshi yake.
Deluwa ma ansha kwalliya ba laifi tana 'kofar 'dakinta da yaranta.
Abinci Hansatu ta raba, Mahmoud na gefe ta kirasa.
“Mahamoud! Zo 'dauki naka kai da 'yan uwanka, Maimouna zo kema ga naku. Deluwa matso muci.â€
Maimou ta ce“Yaufa akwai kwasar ganima, bari muci kafin su Baaba su zo suci su rage muci sauran.â€
Inna Hansatu ta ce“Ai sai kici uwar cikin ci tinda ubanki ya bayar da ku'di.â€
Deluwa tai gum da bakinta tana gun abincinta kar ta tofa tasha gori.

*Morocco*
Wata dattijuwa ce zaune a'kalla zata kai shekaru sittin da biyu, sai wata 'yar matashiya wacce bazata wuce shekaru 28 ba sai dattijo zai kai shekaru saba'in yana waya cikin harshen larabaci yana sakin murmushi.
Sai wasu kyawawan twins maza zasu kai shekaru 9.
Falon kawai zaka kalla kasan an tara dukiya.
Tv suke kallo tashar Aljazeera ana labarai, yayin da yaran nan game suke a wata Tv plasma suna tsereran jirgi.

Ummiterh ta ce“ Yaro kuzo ga Abien Ummi yau mu ko neman mu baiba wai sai mun koma can gidanmu, don Allah tinda Abbunku bayanan ai gwara mu cashe anan ko?â€
Ai kuwa aguje suka nufo mahaifiyar tasu suna dariya, suka rungumeta suka bata Sumba suka miqe suka isa suka kewaye kakan nasu suna cewa ya basu wayan su gaisa da Abien ummi.
Zainabu dattijuwar ta kaima Ummiterh duka ta ce“Zahra bakyajin mgna wlh ke wai bakisan kin girma ba?â€
Ummiterh tai dariya ta Abby kace uncle Abdul mun kusa zuwa Tchad. â€
Wayar ya bek'o mata yana murmushi ya ce“Abdul Zahra da mayya ce idan ta kamaka kasheka zatayi.â€
Abie daga can wanda yay luf bayan mota suna hanyar zuwa gida agajiye yake lilis ga yunwa ga bacci tin fitar azuhur bai dawoba sai yanzu kusan tara na dare, duk da tseraiya lokacin da take tsakaninsu.
Gyaran murya yay ya ce“Ai ni ummiterh ba ruwana dake matuqar bazaki koma gidanki ba, kinga na gaji ga bacci yunwa duk nakeji zamuyi mgna gobe OK?â€
Ummiterh ta ce“Toh naji ga Twins na nemanka.â€
“Ok ban Ammi muyi mgna sai ki bani su.â€
Ammi ta basa sukayi mgna ta basa yaran suka ta'ba hira ya dates kiran.â€
Abby ya ce“Toh fah lokaci ya yi Abdulmajid matarsa yakeso ta tare Allah ya jiqan Aliyu.â€
Ya shafe 'kwallar idanunsa.
Zainabu ta ce“Hakan yafi ai amman ina dalili ace sai ta gama karatu ai da sauranta dukanta Rahma nawa take, yanzu zata San mune muka haifi mahaifinta.â€
Ummiterh ta share 'kwalla ta ce“Damuwata da batasan suwaye 'yan uwan Ummul Aymana ba, duk da an barsa amatsayin kune Abby amman ai dole zata san gaskiya, 'yan uwan mamarta an kashesu a yaqi wasu kuma har yau ba'asan Inda suke ba.â€
Abby ya ce“Zahra kin fiye mgna ai dukkanmu zamu tafi Tchad dole ayi komai agabanmu har bikin sai anyi zamu dawo Abdulmajid haka ya ce shi da Rahamu, amman ke ki tambayo mijinki idan y'a barki.â€
Ummiterh ta zumb'uro baki gaba ta ce“Ai zai barni ma.â€

*Tchad*
Zazzaune suke a falon tin bayan da suka gama abincin dare.
Rayyana acin ubansu kwalliya, sai baza k'amshi take.
Rahma sanye da wata riga maroon color ta yi kyau sosai rigar tabi jikinta kanta ko 'dan kwali babu, amman ta tuf'ke gashinta, ta yi kyau sosai duk rigar simple ce.
Doorbell aka danna Rayyana zuwat ta miqe ta tafi.
Rahma ta bita da kallo.
Hanan ta ce“Ummi! Ashe su Jaddatu Zainabu sun kusa zuwa?â€
Jaddatu ta kur'bi shayi ta dire cup 'din ta ce“Eh munyi mgna da Abbyn Ummiterh.â€
Hanan tai dariya ta ce“Kenan zata fashe? Anata min 'kumbiya² nasan komai wlh.â€
Rahma ta rungume Jaddatu tana murna ta ce“Jaddati Ashe shiyasa 'dazu ummiterh ta kirani tana cemin tayi mafarki tazo Abienah ya korata kuji sharri.â€
Dariya sukayi Jaddatu tana cewa “Ki share ummiterh ja'irace uwar banza.â€
Rayyana tana bud'e 'kofar Abie ya bayyana.
Taso rungumeshi ganin yanayin yadda ya tsare gida.
Murmushi tai masa ta Kama hannunsa ta ce“Habiby barka da zuwa, fatan dai kana lfy? Ya gajiya? Wlh duk na damu tin azuhur da ka fita sai yanzu, hope lafiyarka k'alau?â€
Ta 'karashe mgnar cikin nuna tsantsar damuwa idanunta har ya kawo ruwa.
Abie ganin yadda ta nuna damuwarta da shi yasa ya kamo 'dayan hannunta yana murmushi ya ce“Lafiya lau ai daman dai kinsan nakan zarta hakan wani sa'ain hope kowa lfy?â€
Kai ta jinjina ya Saki hannun suka jera falon.
Rahma na jin takunsu ta waiwayo idanunta suka sauka akan nashi, tai saurin ha'de face ta juya kanta, tana 'ka'kalo murmushin yaqe ta Kama hannun Iman tana fa'din.
“Baby gobe za'a mana zanen henna me kyau kina so?â€
Cikin murna Iman ta ce “Eh Auntie ina so.â€
Murmushi Rahma tai ta sumbaci goshinta, ta kalli Jaddatu ta ce“Kema kina so ko Jaddati?â€
Jaddatu ta ce“Allah rabani da abin kunya, ko ran aurenki ai irin na tsofaffi zanyi.â€
Dariya suka sanya, sallamar Abie ta katse musu dariyarsu.
Jaddatu ta ce“Abien Rahma sai yanzu? Sannu.â€
Kusan Jaddatun ya zaune yana amsar gaisuwar Hanan Iman na masa oyoyo ta zauna zaman cinyarsa.
Rahma ta dake ba tare da ta kalleshi ba ta ce“Abie sannu da zuwa.â€
Taja bakinta ta tsuke.
Abie ya amsa yana tambayarta“Baby kinci abinci?â€
Kai ta 'daga ha'di da cewa“Ehâ€
Rayyana sama ta haye domin ha'da masa ruwan wanka.
Hanan ta ce“Yayana ashe mun kusa baqi?â€
Murmusawa yay ya ce“Wannan ummiterh 'karamar uwata akwai baki kamar aku. Hanan iyayan gulma mijinki dai ya kusa saukowa daga daji atattara atafi.â€
Rahma kallonsa take cike da mugun sonsa da 'kaunarsa, take kallon yadda 'kananun la'bbansa ke motsawa yana mgna anutse.
Karaf idanunsa ya fa'da cikin nata, kauda kanta tai tana Kama hannun jiddatu, cikin saita nutsuwarta take fa'din“Jaddatu kalli faratanki sun fara tsayi.â€
Abie kallonta yake cike da mamakin yadda ta sharesa, tana sambgogin gabanta.
Miqewa yay ya ce“Ummi na shiga zan watsa ruwa na kwanta sai da safe.â€
Jafdatu ta ce“Abinci fa Abdul? â€
Sajansa ya shafa ya kafe Rahma da idanu ya ce“Rayyana zata kawomin Ummi nagaji ne. Babyna sai da safe bye.â€
Ya 'karashe mgnar yana juyawa ya fara tafiya.
Rahma ko kallonsa batayi ba, tana cigaba da hirata da Jaddatu.

Ya na shiga Rayyana tana 'ko'karin fitowa, sukaci karo.
“Wayyo sorry ban ganka ba! Shiga kayi wanka sai muje kaci abainci.â€
Kai ya jinjina ya ce“Ngd ki kawo min nan nayi ko spoon 3 nayi, ki ha'domin coffee mai da'di please.â€
Cikin murna ta ce“Ok an gama afito lafiya.â€
Ta sumbaci hannunsa ta fice, shi kuma ya shiga bedroom.
Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom.

Rahma sai kallon Rayyana take tana kai komo wajan ha'dawa Abie abinda zaici, ta jima tana dafa coffee kafin ta juye cikin cup glass me kyau, taje man dining area ta ha'do komai a tray ta haye sama.
Abie ya jima yana wanka kafin ya fito da towel 'daure a 'kugunsa, qaramin towel yana goge jikinsa.
a falonsa ta ajiye tray'n saman center table, ta zauna jiransa salin halinsa batayi gangancin shiga bedroom ba.


Acan Niger kuwa 'karfe 9 na dare jorginsu ya sauka, taxi suka shiga Mal Adamu da Ja'afar taxi 'dinsu daban kasancewar su ba 'daya ba.
Fa'din farin farin ciki wajan Inna Hansatu ba'a magana ganin yadda Ja'afar ya qara zama qato ga wani irin haske da baqar fatar sa ta yi.
Can ma Dadda kamar ta goya Ibtisam ganin yadda ta ciko ta sake fari.
Ammaan sai taga Ibtisam 'din Sam batada walwala.
Bayan sunci sun sha Dadda ta qarama Laraba da Tanko ban gajiya ta ce.
“Ta miqe ta ce“Ibtisam zo muje can gidana mu kwana sai musha hira.â€
Aikuwa kamar jira take ta miqe cike da zumu'di ta ce“Daman akwai labaein da zan baki Dadda...â€
Tanko ya ce“Mama ki 'kyaleta ba Inda zata.â€
Dadda ta ce “Toh shikenan mai 'diya.â€
Tanko ya ce“A'a ba haka bane zan miki bayani gobe insha Allah.â€
Dadda ta musu sallama ta tafi Ibtisam ta fashe da kuka ta nufi 'daki tana fa'din.
“Ni daman ba'a 'kaunata.â€
Laraba ta ce“Oh Allah ni Laraba naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba! Tanko yarinyar nan anya tana hankalinta kuwa? Wlh inaga kamar bata dawo hankalinta ba?â€
Tsuki yaja ya ce“Dallah rufemin baki tin ban wulaqantaki cikin 'diyanki ba! Wa yaja duk abinda yake faruwa?â€
Muqus Laraba tai bata sake mgna ba.

Ja'afar tsabar gajiya yana gama con abinci yay wanka ya rama sallah ya kwanta, yanajin Mahmoud na basa labari yay banza da shi dan buqatar hutu yake.

A can Tchad kuwa Rahma ganin Rayyana ta koma sama 'dauke da tray wani irin abu ya tirniqe Rahma ta kasa control kanta ta miqe tama Jaddatu da Hanan sallama, daman Meerah ta jima da tafiya.
Dab da zata iso 'kofar falon Abie ta ji mgnar Rayyana tana fa'din.
Please My Habiby ka 'dan qara spoon 'daya kaji,daure don Allah haaaa na saka maka.â€
Wani dammm! Rahma taji 'kirjinta ya buga da sauri, ta rumtse idanunta wani irin zafi takeji wanda yake tasowa daga 'kasan zuciyarta.
Shirun da taji hakan ya tabbatar mata Abie ya bu'de sweet 'din bakinsa Ammi na basa abinci aciki 'kilama ta dinga lashe masa wanda ya 'bata masa baki.
Da Sauri ta bu'de idanunta ta dafe bango ta fara tafiya taji sautin muryar Rayyana tana tafa hannu ta ce “Bravo! habibina muahhhhhhh! Toh amshi coffee ka Sha.â€
Zamewa Rahma tai 'kasa dab'as ta wanda sai da bayanta ya bugu da qofar falon wacce take rufe ta bada sautin alamun an bugu da ita, ta saki 'dan qara tana dafe 'kugunta tare da cewa“Ushhhhhhhh! Bayana.â€
tana toshe bakinta kar ajita...........

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/29/22, 16:56 - Buhainat: ```D A```

```77&78```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

Washegari Abie ya na fitowa daga masallaci, ya biya dan tashin Rayyana ya isko tana sallah, ya ji da'di sosai ya zauna ta idar suka gaisa ya ce“Yauwa zanje Cameron amman ayau zamu jiyo komin dare, 'karfe 8 flight 'dinmu zai tashi.â€
Ya 'karashe mganr yana miqewa.
Rayyana ta ce“Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, zanyi missing 'dinka. Please zanje gida idan ka amince da rana don Allah habiby?â€
Abie ya 'dan kalleta ya ce.
“Ameen amin Shkuran, Ok kije ba damuwa, agishe da su Saratu.â€
Godiya tai masa harda rakoso bakin 'kofa riqe da hannunsa.

Zaune ya isko Rahma sanye da jallabiyarsa fara 'kal sabuwa ta mata kyau ta yane kanta da hiraminsa tana karatun Qur'ani.
Sosai hakan ya masa da'di ya shiga ya watso ruwa, ya fito 'daure da towel a'kugunsa, yana goge murdadd'an jikinsa mai cike da gargasa, Masha Allah Abie yanada kyan fata Sam bazaka ta'ba cewa ya yi shekaru 40 ba bare 50 cif.
Rahma tana gama karatun ta 'daga hannu tana addu'a tana zubar da hawaye.
Bayanta ya sunkaya ya'dauka Qur'ani ya kaita ma'ajiyarta ya dawo ya zauna bayanta ya sanya hannayensa ya zuro ya ha'de da nata yana amsawa da “Ameen Ya Allah Babyna.â€
Rahma yadda Abie ya kanainayeta ya rungumeta, danshin ruwan jikinsa na shigarta yana goga mata sajan fuskar shi, agefen fuskarta yasa bakinta ya bara farawa, tsikar jikinta sai yamm take, dakyar ta 'karasa addu'ar tana hawaye suka shafa.
Ya juyo da ita gabansa ya na wasa da hawayen fuskarta.
Rahma idanunta ta runtse sbd kallon Abie fa'duwar gaba yake sakata Sam bata Saba ganin ba Riga ba, duk da tasan yanada babban 'kirji batasan cike yakeda gashi haka ba.
Can 'kasan maqoshi ya furta“Ya Salam! My Baby yanzu ni kam me na miki? Daga masallaci nake fa! Please Ruhina ki daina min asaran hawayenki na tuba, Oya fa'damin me nayi yanzu zo na shanye hawayen sai naji dalili. Oya sanya hannunki ki zagaye bayana rungumeni gam kinji My Baby.“
Ya 'karashe mgnar yana tallabo fuskarta da dukkan hannunsa biyu, ya mata qurr da shanyayyun idanunsa, baisan wani irin so yake mata ba, jinta yake tabbas idan babu ita bazai ta'ba rayuwaba.
Rahma sanya hannunta duka biyu ta yi ta zagaye bayansa, ta rungumesa gam, tana fa'din“Abie nah me yasa nakeson koda yaushe na kasance da kai kuma ajikin ki? Bayan nasan hakan bai dace ba amman na kasa Hana kaina, Abie wane irin so nake maka don Allah?â€
Ta idar da mgnar cikin shasheqar kukan zallar shagwa'ba.
Abie ya ra'da mata akunnenta.
“My baby kul kiyi kuka maza had'e hawayenki, banson kukanki farin cikin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login