Showing 90001 words to 93000 words out of 165653 words
karka ganta ka 'batama kowa na gidan rai, amman yarinyar ta min nisa ruwan haka ya dinga dukanmu dakyar na kamota tana kyalkyala dariya.
Ba'a fi awa 'daya ba zazza'bi ya rufeni hankalinka a tashe mukaje asibiti gwajin farko akace inada ciki wata 4 sakammakon razanar da nayi ina cewa ban yarda ba ya ina goya zanyi ciki wallahi bazan yarda ba sai an zubar, daidai wajan akayi wata irin tsawa na tashi a bacci, don Allah Abie kayi hkr da lafazina wlh abinda ya firgitani kenan duk da nasan sharrin mafarkine amman na ru'de naji tsoro sosai ne.â€
Ta 'karashe mgnar cikin shasheqar kuka tana kallonsa cike da tsoron hukuncin da zai 'dauka 'kilama, dukanta zaiyi, ya ce ta haukace.
'Kananun kyawawan idanunta ta xaro waje cike da mamaki tana kallon ikon Allah, ganin Abienta na sakin 'kayataccan murmushi wani irin zallar farin ciki take gani akan fuskarshi idan batayi 'karya ba sai ta ce rabon da taga irin wannan murmushin akan fuskarshi tin tana 'yar shekaru 12 tin Jaddi Cheri, sunan da take kiran abdulwahab mahaifin Abie kenan.
Mamaki sosai Abien yake bata lokacin da yake sumbatar kumatunta, ya zura hannunsa cikin rigarta yana shafa lafaffan cikinta yana kallonta.
Wani iri ta dingaji a 'dan gigice ta riqe hannunsa ta marerecewa, idanunta ya fara tara ruwa ta kirasa“Abie Rabin raina.â€
Juyawa yay ya shiga bedroom 'dinsa ya murza key ya nufi 'katon bed 'dinsa da ita har yanzu yana shafa cikinta yana wani irin murmushi sam labarin ya mantar da shi tashin hanklin da Rafeek ya jefasa.
Rahma ta lumshe idanunta tana tura kanta cikin 'kirjinsa tana shaqar dadda'dan 'kamshin sa tana sauke ajiyar zuciya.
Tsakiyar gadon ya kwantar da ita, ya nufi fridge wanda yake nan cikin bedroom 'dinsa, ya bu'de ya 'dauko fresh milk me sanyi wacce ya siyo 'dazu ya 'dauki cup ya tsiyaya sai da ya cika cup 'din ya rufe sauran ya maida fridge ya nufo gadon.
Zama yay ya 'dagota tana kallonsa ya tallafo fuskarta ya kafa mata cup abaki.
“Oya Baby sha kiji sanyi azuciyarki zan fa'da miki fassara mafarkinki.â€
Ya 'karashe mgnar yana sakar mata tattausan murmushi, wanda ya sanya jikinta qarasa mutuwa murus.
Hannunta ta 'dora saman nashi ta fara sha anutse, tasha fiye da rabi ta janye bakinta tana langwa'bar da kanta.
“Abie ya isa.â€
“No! Baby shanye ji cikin ki kwalam ba komai, laifin Baby Ummu Aymana ne (Fifie)
Ta sanya mamarta ruwa ya daketa harda zazza'bi daga nan aka gano 'kaninta ko 'kanwarta Allah masani.â€
Ya 'karashe mgnar yana murmushi hannunsa saman lafaffan cikinta yana shafawa anutse, still idanunsa cikin nata yana bata fresh milk 'din.
Baki 'daya Rahma 'kusosun kanta sun kwance ta rasa gane kan Abie 'dinta 'karshe idanunta ta kulle ta shanye fresh milk 'din, ya kwantar da ita ya mayar da cup saman fridge, sai lokacin idanunsa suka sauka akan wayarsa wacce aka gaji da Alo² aka kashe.
Sumar kansa ya shafa ya 'dauki wayar da take yashe saman carpet yay 'yar siririyar dariya ya kashe wutar 'dakin ya, kunna ta gefen gado ya hauro saman bed 'din ya kwanta nesa da Rahma yana murmushi yay dialing number 'dazun, yana kiran Rahma “Babyna zo nan.â€
Ashagwa'be ta rarrafa jikin Abie ta shige jikinsa luf ta qamqameshi.
Blanket ya ja musu ya rufesu ruf kansu kawai ya bari awaje, hannunsa 'daya ya sanya ya zagayeta 'dayan manne da wayarsa.
Bugu biyu aka 'daga.
Murmushi ya saki me taushi ya ce“Afuwan ihun Babyna ne ya rikitani 'dazun hope kana lafiya? Pls Tarno flight gobe zuwa Tchad insha Allah nake so?â€
Daga can wani kyakkyawan baturene babba zai kai warin Abie ya maida masa cikin harahen nasu.
“Ok Abdul an gama 'karfe nawa?â€
Abie ya murmusa yana kallon fuskarta ta 'dan hasken 'kwan gefen gadon ya 'daga mata gira ganin ta kafesa da idanu, ya ce.
“Da yamma muyi kwana hanya ya kasance na samu sallar juma'a jibin insha Allah a Tchad. â€
Tarno ya amsa da “Ok an gama yadda kakeso hakan zayi kun gama samun flight amman kwana Canada zakuyi.â€
Sallama sukayi da Abie.
Wayar ya kashe baki 'daya ya ajiye saman bedside drawer, ya sake shigar da Rahma jikinsa ya kirata can 'kasan maqoshi, dab da fuskarta har hancinsu na gamuwa, suna shaqar numfashin junansu.
“Baby Ummin Abienta!â€
Rahma wani yammm ta ji ta sake qamqameshi ashagwa'be ta kirasa.
“Abie nah! Ka fassaramin mafarkin kaji?â€
Hancinta ya sumbata ya tallabo fuskarta suna kallon juna, bakinsa dab da kunnenta cikin kwantar da murya ya ce“Ruhin Abie mijinki kikayi mafarki kuma nasan insha Allah cikin tarin yaran da zaku haifane Allah ya nuna miki ukun da cikon na hu'dun.
Ni shaquwar da take tsakaninmu ce ta sanya kikaga fuskata amman azahiri mijinki na sunna kiga gani.â€
Rahma ta sauke ajiyar zuciya ta shafo sajan Abie ta tura hannunta cikin sumar kansa me taushi tana caku'dawa, ashagwa'be ta ce “Abie naga hotonsa pls Rabin raina kaji?â€
Ta 'karashe mgnar tana sumbatar goshinsa tana kallon jajayen lips 'dinsa tai saurin 'dora bakinta saman nashi ta sakar masa Sumba ta janye tana kwantar da kanta saman kansa ta kirasa “Abie nah!â€
Sai ta rushe da kuka.
Abie ya furta “Ya Ilahi! Babyna menene? Taho zo nan.â€
Ya 'karashe mgnar ya 'daukarta dukkanta ya 'dorata saman faffa'dan 'kirjinsa ya 'kam'kameta yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, ya tura hannunsa cikin dogon gashin kanta yana yamutswa asannu.
Ra'da ya mata akunnenta“Abinda kikeso na tare dake Baby shima sonki yake kamar zai mutu sbd masifar sonki da 'kaunarki, gobe zamu wuce bazan sake baki waya ba sai kin tare, kina son ganin mijinki?â€
Asakalce ta 'daga kanta tana tura hannunta cikin gashin kansa.
“Ok yaushe kikeso?â€
Ra'da ta masa akunnensa “Wayyo Abie Rabin raina duk kunyarka nakeji ni bazan iya gayaba ka sanya min rana da kanka.â€
Murmushi yay ya kamo hannunta ya sumbata yana cizon 'karamar yatsarta ta saki 'yar qara tana 'kyal'kyala dariya ta qamqameshi.
“Nan da kwana 6 insha Allah zai bayyana gareki OK? Ko kinfi son sai bayan biki? Nafiso ki gansa idan kinji bai miki ba zan rabaku na baki farin cikin ki.â€
Rahma taji damm! Gabanta ya fa'di dan ji take rabuwa da Abie kamar rabuwa da numfashinta ne, amman tasan dole zata rabu da shi ji take inama ace Ab'ie ya halata gareta, gani take Abienta yafi dukkan mazan duniya komai da ake buqata wajan namiji, ita hakan take ganin Abienta.
Daurewa tai ta yi murmushin yaqe ta ce“Allah ya kaimu.â€
Hancinta yaja ya ce“Ameen Baby ummina.â€
Manne suke waje 'daya Abie na shafa gashinta ha'di da Sosa mata ta yi luf samansa, tanajin daman su dauwama ahakan, tana jinjinawa Ammi Rayyana ta yi dacen miji.
Hannunta ta tura cikin gashinsa tana shafawa.
Saukar numfashinta ya ji alamun ta yi bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya fara qoqarin kwantar da ita taqi ta maqaleshi.
Dariya yay ya sake mata masauki a 'kirjinsa, yana shafa bayanta, ya karanto musu addu'ar bacci.
'Karfe 3 na dare ya farka daga dadda'dan baccin da ya sace shi, ya samu ya janye jikinsa daga nata ya shiga bathroom ya 'dauro alwala.
Sallar nafila da ta zame masa jiki ya yi bayan ya idar ya yi karatun Qur'ani wanda saida aka Kira sallar asubah ya rufe Qur'anin ya miqe ya gabatar da sallar raka'atanil fajir yana idarwa yay addu'a ya miqe ya gyarama Rahma kwanciya ya sumbaceta a kumatu ya lullu'beta, dan ta yaye zanin rufar taje qarshen bed 'din duk girmansa.
'Karfe 6 ya dawo daga masallaci.
Zaune ya iskota saman darduma sanye da jallabiyarsa milk colour ta yafa mayafinta tana karatun Qur'ani.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ji da'di har ransa.
Kai tsaye saman bed ya wuce ya kwanta yana 'daukan remote ya rage gudun A/C.
Idanunsa akan Rahma yana sauraron dadda'dar muryata, suratul Yasin take karantawa.
Tana kai 'karshe tai addu'a ta shafa ta miqe ta linke darduma ta mayar dasu ma'ajiyarsu har Qur'anin.
Kallon Abie tai tana langwa'bar da kanta ta gaishesa.
“Abie nah Sabahul khair.â€
Abie ya beqa mata hannu ta taho da sassarfa, ya kamata ta hauro saman bed 'din ya janyota jikinsa ya rungume gam ya sumbaci goshinta ya ce“Baby kin tashi lfy? Ya rigima da shagwa'ba magen Abientaâ€
Kai ta 'daga masa tana 'yar dariya.
Lullu'besu yay da blanket ya ra'da mata “Muje na ha'da miki tea sai muzo mu kwanta.â€
Ashagwa'be ta ce“A'a Abie ai kasan sai da rana nake breakfast, kafin mu tashi Meerah ta gama mana komai, ko naje na girka mana?â€
Hannunsa ya'dora saman lips 'dinta yana shafawa ya ce“No! Baby oya bacci.â€
'Yar dariya tai ta shige jikinsa ta cusa kanta kafa'darsa tana shaqar qamshinsa.
Haka wani irin dadda'dan bacci ya 'daukesu manne da junansu.
A can kuwa 'bangaran Rafeek ya shiga tashin hankali jin Rahma ta kashe wayarsa adaren ya Kira Anee dakyar ta samu ta lalla'bashi, akan gobe zata rakashi Gideons da yamma idan ta taso daga makaranta.
*Gabon*
Har garin Allah ya waye Aishatu ba farfa'do ba, dukkan illahirin families 'dinsu hankalinsu tashe yake.
Banda baqin ruwan tea da hajiya take matsawa Ma'aruf ya sha ba abinda yake iya sakawa acikinsa. Kwana ya yi yana sallah yana istigfari akan babban zunubin da ya aikata na zina.
Misalin 'karfe 3 na yamma, 'yan gidansu duk suna waje azaune Ma'aruf ya kasa ya tsare yana bakin gadon Aishatu azaune, yana riqe da hannunta me drip yana zubar da hawaye.
Motsi ya ji hannun ya fara ya kalleta agigice cikin murna har ya bu'de baki zai kirata sai ya tuni ayanzu ba wanda ta tsana bata son gani sama da shi.
'Ko'karin janye hannunsa yake cikin nata dan ya danna 'yar na'uran da zata janyo hankalin likitocin.
Ya ji tana furta.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ya Allah karka tasheni daga wannan dogon baccin da nake idan dai har gaskiya ne abinda ya faru ba mafarki nake ba ya Allah ka 'dauki raina na huta...â€
Ma'aruf ya rufe mata baki yana kuka ya ce“Aishatu don Allah bu'de idanunki muyi mgna kiyi hkr karki tonamin asiri na rantse miki da Allah ban ta'ba zani ba sai jiya itama wallahil azeem bansan yadda akayi ba nayita ki yarda dani don Allah ki bu'de idanun...â€
Wata irin bangaza ta masa idanunta arufe tana qara rufesu.
Ta sake hanka'dashi wanda sai da wajan cs 'dinta ya amsa ta saki ihu tana riqe wajan cikin kuka ta ce“Fita anan na tsaneka bana son ganinka wallahi idan baka fita ba zan zan baka mamaki na tsaneku tsana mafi muni macita amana azzalamai, daman kai na jima ina fa'da maka kai mazinaci ne kana musamin Allah ya isa tsakanina daku, ina 'dan cikina? Kun kashe shi ku?â€
Ta tambaye shi cikin tsawa har yanzu bata bu'de idanunta ba, sai wani irin numfashi take ja jikinta na wani irin 'bari tamkar me farfa'diya.
Ma'aruf na'uran ya danna da 'karfi sai ga likitoci sun shigo aguje.
Temakon gaggawa suka dinga bata allurai Dr ya mata nan take bacci ya 'dauketa.
Dr ya dinga ma Ma'aruf fa'da.
“Me ka fa'da mata wanda ya haddasa jininta sake hawa? Wlh sai kunbi ahankali ayi nesa da abinda bata 'kaunar gani.â€
Ma'aruf ya share hawayen fuskarshi ya ce“Ok Dr insha Allahu za'a kiyaye Ngd.â€
Wajan iyayan nasu ya fito yana sheda musu ta farfa'do amman an mata alluran bacci. Hamdalah sukayi duk suka 'dunguma 'dakin da take suka mata addu'a.
Hudah da Kabeera sunzo dubata har kuka sukayi jin an ciro yaron bai qarasa isa haihuwa ba.
Rabi'ah zaune ta rabka tagumi tana zubar da hawaye tana mgna qasa-qasa.
“Don Allah Aishatu ki yafemin nasan na tafka kuskure mafi girma, cin amanar wadda ta yarda dani, mu hu'du muka tasa amman cikinsu kifin sona da yarda dani fiye da Hudah da Kabeerah, amman nice me 'kyashinki da ha'intarki, naqi aure sbd yadda kika 'kwa'daitamin mijinki kike 'kodashi da yabonsa sai naji duk duniya banda wanda nakeso sama da shi.
Wani 'bangaran Aishatu kece kika janyo akaso 100 kaso 90% laifinki ne ni laifina cin amanarki, da son abinda duniya da ya min yawa har na fa'da bin maza, har yau na kasa samun hamsha'kin me ku'di daidai Ma'aruf, abinda ya saka kenan na biyo masa ta bayan gida, ki yafemin Aishatu don Allah. â€
Ta 'karashe mgnar cikin kuka, Rabi'ah kuka na gaba....
*Tchad*
Tin bayan la'asar Ja'afar suka zo nan gidan Abie wajan iyayan nasu suna fira cike da nisha'di.
Sanye Ja'afar yake da wani yadi me kyau milk colour ya yi kyau sosai sai baza 'kamshi yake.
Cikin tsokana ya ce“Baaba ya kamata a'danaka a motar nan gaskiya har Abie 2 ma.â€
Abie 2 yay dariya ya ce“Ai kuwa sai ka tashi muje zagaya ce. Amman tinda kuka dawo ka gaishe da Jaddatu kuwa? wato (Ummi) ?â€
Ja'afar ya ce“Eh mana Abie munje mu dukkanmu amman bari naje na gaisheta yanzu.â€
Tanko ya ce“Yauwa Allah ya maka albarka kuje ku gaisheta.â€
Abie y murmusa ya ce“Yauwa jeka ka fito sai mufita.â€
Ja'afar ya amsa da “Toh Harisu kuzo muje.â€
Rayyana zaune ansha uban 'kunshi bai qarasa bushewa ba, ga me kitso zauna na mata tin wajan 'karfe 2 Rahma ta kirata da wayar Abie cewar zasu taso da yamma amman kwanan Canada zasuyi sai gobe zasu shigo.
Kallo 'daya zaka mata kasan tana cikin farin ciki.
Ibtisam gefenta zaune tana kallon kitson ya mata kyau sosai.
Jaddatu ikon Allah take kallo tana mamkin ko dai Abdul na son matarsa har ya iya kiranta ya sheda mata zuwansa sai kwalliya take?
Hanan ta ce“Aunty Rayyana wlh kinyi kyau tsaf abinki iyeee! Lallai anaji da Yayana wlh.â€
Jaddatu zatayi mgna taji qaran doorbell taga Latifa ta tafi bu'dewa.
“Rayyana wai Abien Rahma da kansa ya kiraki ya sheda miki zuwansu?â€
Rayyana haushin Jaddatu ya cikata amman ta waske ta ce“Eh Ummina ya ce amusu girke² amman ai tinda sai gobe zasu shigo yau bai kamata ayiba ko?â€.
Sallamar su Ja'afar ta hana Jaddatu amsawa Rayyana mgnarta.
Jaddatu ta amsa fuska asake tana fa'din.
“Lale marhabun da Ja'afar yaron kirki, Latifa akawo musu abun motsa baki.â€
Ja'afar kallo 'daya yama Ibtisam ya ha'de face ya kauda kansa.
'Kasa suka zube suna gaishet ta amsa fuska asake tana tambayarsu gida.
Ibtisam ta ce“Harisu Yahuza ina yininku?â€
Amsawa sukayi fuska asake suna tambayarta Laraba.
Rayyana ta zungureta ta ce“Mijin fa?â€
Baki ta zum'buro gaba ta ce“Jiya dukana ya yi fa!â€
Jaddatu ta ce“Ke kuma wayonki kenan? Dan uwaki shi mijin naki bazaki gaida sa ba? Kiga ni bana son iya shege, ke uwar 'dakin Nata fassara mata, dan na gano abokanansa kawai ta gaisar.â€
Rayyana ta gintse dariyarta ta gayama Ibtisam abinda Jaddatu ta fa'da.
Kunya taji ta ce“Ja'afar ina wuni.â€
Kallon arziqi bata ishesa ba.
Latifa ta kawo musu lemo da ruwa ta zuzzuba musu, basu jimaba suka fito, dan Ja'afar takaicin Ibtisam ya ishesa.
Ibtisam ta kalli Rayyana ta ce“Wai Aunty suwaye zasu zo kiketa kwalliya ha kinga kuwa yadda kikayi kyau?â€
Dariya Rayyana tai ta ce“Mijina da 'yarsa na jikin hoton can da naga kina yawan kallonsu.â€
Ibtisam wani 'kululun baqin ciki taji ya tsaya mata amaqoshi.
Afakaice ta ta'be baki ta ce“Oh! Su ne? Allah ya kawosu lafiya.â€
Rayyana ta amsa da “Ameen ya Allah, ina Auntie Laraba kuwa?â€
Ibtisam ta miqe ta ce“Bari na dubota...â€
Acan Espagne kuwa su Rahma ba qaramin barci sukayi ba, sai shabiyu na Rana suka farka, bayan sunyi breakfast Abie ya fita, bai jimaba ya dawo, bayan azuhur.
Zaune ya isko Rahma da Meerah suna mgna akan tafiyarsu.
Meerah ta masa barka da zuwa.
Abie ya ce“Fatan kunyi sallah?â€
Kai Rahma ta 'daga. Meerah ta miqe ta nufi sashenta dan ta 'dan huta sbd har girkin Rana ta kammala.
Ashagwa'be ta ce“Abie ina son ci gaba da zama da Meerah aduk inda nake ta ce zata bimu bata son amayar da ita 'kauyensu can Morocco muna tare insha Allahu kaji?â€
Gira ya 'daga mata ya beqa mata kumatunsa.
Matsowa tai ta shige jikinsa ta sumbaci kumatunsa tana dariya.
'Kam'kameta yay yana sauke numfashi da harshen Hausa ya ce.
“Ina sonki ina 'kaunarki Babyna muahhhhhh.â€
Ya sumbaci ha'barta.
Idanu ta tsura masa ta shagwa'be fuska tana shafa sajansa ta ce“Abie me kace don Allah ai kasan ban iyaba?â€
Hancinta yaja ya ce“Na ce kinci abinci.“
Kai ta girgiza ta sake shigewa jikinsa tana jan gemunsa ashagwa'be ta ce“Wallahi Abie kalaman sunfi wannan tambayar yawa.
Dariya yay ya ce“Mgnar Meerah ne na ce idan tafi son zuwa Chad ba damuwa ni har na hagoma Abienki 2 mata wlh.â€
Cikin murna ta maqale Abie tana murna ta ce“Kira min shi mu gaisa daga nan sai Jaddatu sai Ammi.â€
Wayar ya bata ta kira Abien suna hira...
Misalin 'karfe 6 na yamma jirginsu Rahma ya 'daga zuwa Canada, dan dole sai sun kwana a Canada.......
*Ba maammaki zuwa yamma na 'karo muku, amman fa sai kun samba'do comments and Sharhi. Ngd mach love masoya.*
_Rahmerh ladingo😉_
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/16/22, 17:36 - Buhainat: ```D A```
```67&68```
_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Tafiya ce me dogon zango sukayi acikin jirgin. Rahma da Meerah wajansu 'daya, layin manya Abie na ta hannun damarsu, yana lure da dukkan motsinsu sosai Meerah da Rahma suke hirasu cikin annushuwa. Meerah sun 'danci abinci, Rahma kuwa taqi sai da Abie ya taso ya lalla'bata ta sha tea, ya koma wajansa.
Tsakiyar dare jirginsu ya sauka aka kaisu hotel 'din saukar baqi ta airport 'din, wanda ke'bantaccan wajene na manyan masu fa'da aji irin su Abie aka saukesu.
Abie 'dakinsa daban Rahma da Meerah nasu 'dayane. Sai da Abie ya sanyata gaba taci abinci dakyar tana zuba masa shagwa'ba, ya lalla'bata taci kafin ya fita ya tafi 'dakinsa.
Rahma duk sai taji kewar Abienta jiya 'daya da ta kwana manne da shi wata irin muguwar shaquwa ta shiga tsakaninsu haka kawai takejin Abienta shine rayuwarta baki 'daya.
Kwance take tana juyi duk yadda taso bacci ta kasa yinsa, zazza'bi taji na son rufeta ga marata na ciwo, wani irin juyi tai tana sauke numfashi ha'di da riqe marata wacce ta 'kulle mata ahankali cikin siririyar muryata ta ce“Aushhhhh cikina Abie nah banda lafiya kana ina?â€
Ta 'kare mgnar kamar zatayi kuka.
Idanunta ta sauke akan Meerah ta ga tana sharara baccinta cikin kwanciyar hankali.
Fuska ta yamutsa, ta miqewa tai sauko daga saman bed 'din tana zagaya 'dakin, sai matsar 'kwalla take, dogon gashinta ya sauka har tsakiyar bayanta, Rabi ya rufe mata gefen fuskarta.
Tv ta kunna ta zauna saman kujera tana yamutsa fuska.
Du'kewa tai tana riqe marata da tai mata wani irin mugun mur'dawa ta saki qara me 'karfi wanda ya tayar da Meerah daga bacci.
Saukowa tai agigice ta nufo wajan Rahma ta kamota ta zauna ta zauna kusanta tana tambayarta.
“Rahma lafiya kuwa? Me ya sameki ko akira Abie?â€
Da sauri ta 'daga kanta tana zubar hawaye.
Meerah ta miqe ta