Showing 63001 words to 66000 words out of 165653 words
la'bbanta yay yana jan siririn dogon hancinta, ya manna mata kiss saman idanunta.
Ya nufi bedroom.
'Kananun kyawawan idanunta ta bu'de tabi bayansa da kallo tana sakin murmushi.
Sai da ya shiga ta ce“Abiena tin fa kana ciremin sarqar 'kafata na tashi.â€
Cikin bargon ta shige tana shaqo 'kamshinsa mai sakawa taji nutsuwa.
Abie alwala ya 'dauro lokacin da ya fito ana kiran sallar la'asar.
Kallonta yay ya ga ta rufe dukkan jikinta.
Fita yay zuwa masallaci idan ya dawo sai ya tasheta.
Yana fita ta miqe zauna, tana miqa ta sauko, bathroom ta shiga ta cika bathtub da ruwan 'dumi ta shige ciki ta kwanta.
Ta jima sosai kafin tai wanka ta fito, ta 'daura alwala.
'Daure da towel ta fito tana riqe da kayanta.
Motsi Abie taji afalo duk sai ta rikice.
'Katuwar wardrobe 'dinsa ta bu'de wacce take shaqe da sutturo iri² 'bangaran jallabiya ta kalla ta ciro wata ruwan toka sabuwa dal tai saurin sakawa jikinta ba tare da ta cire towel 'din ba, hirami ta janyo shima sabo ta rufe masa wardrobe 'dinsa.
Turarensa ta fesa ta cire towel 'din ta ajiye saman bed ta hau darduma ta tayar da sallah..
Abie na zaune falo yana waya, ya kai 20 minutes kafin ya gama ya miqe ya nufo bedroom 'din.
Ta gama sallar karatun Qur'an take.
Murmushi yay ganin kayansa jikinta sunyi mata kyau sosai, duk da rigar ta mata mugun yawa.
Bai mata mgna ba ganin tana karatu, ya shiga ha'da kayansa, kala 4 ya 'dauka sai na bacci kala 2 sbd kwana 2 ne zaiyi ya juyo. Sai da ya gama shirya kayansa cikin 'karamar trolley ya 'dauki duk abinda zaiyi anfani da shi, ya zauna saman kujera yana duba saqonnin email.
Rahma anutse ta gama karatunta tai addu'a ta shafa ta miqe ta maida Qur'an wajansa, ta linke dardumar ta ajiye ta muhalinta, ta gyarama Abie bed 'dinsa tsab.
Awarwaronta da sarqar wuya da ta qafa ta kwashe ta nufi wajan Abie.
Kusansa ta zauna, ashagwa'be ta ce.
“Abie rabin raina ina bacci ka ciremin kwaliyata, maida min toh.â€
Kallonta yay ya kwaikwayi mgnarta.
Kumatunsa ya beqa mata.
Tasan me yake nufi.
Fuskarshi ta riqe ta manna 'dan 'karamin bakinta saman kumatunsa ta sumbata, itama ta basa kumci.
Sansanyar Sumba ya mata akumatunta,wacce ta maqale masa ta tura kanta cikin 'kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Anutse ya sanya mata sarqar da awarwaron ya sanya mata ta qafar ya sumbaci 'kafar, 'dan kunnen ya sanya mata, yana gyara mata bichons 'kananun 'yan kunnen wanda ya kasance tilla ukune jera akunnenta, biyun sai ta saka 'yan mitsi² 'yan kunne na gold.
Ashagwa'be ta riqe hannunsa tana fa'din “Aushhhhh! Abiena zafi kawai ka cire min toh.†hura mata wajan yay yana shafawa ahankali ya ce.
“No! Baby sunyi kyau barsu idan naje Australia zan siyo miki mask kyau na diamond.
Baby ki kace gobe kike son wucewa ko?â€
Cikin murna ta amsa tana kallon 'dan 'karamin jajayen la'bbansa tana langwa'bar da kanta.
Kallo 'daya yay mata yay saurin Janyeta jikinsa ya na miqar da ita tsaye, yana murmushi sbd ya lura da ita ba abinda take so irin tai ta ma sa kiss le'bensa.
Hannunta ya kama ya 'dauki wayarta suka fara tafiya.
Ashgwa'be ta ce“Abiena bakece komai ba?â€
Kwaikwayonta yay ya 'dora da cewa“Za ki tafi baby ummina muje kici abinci.â€
Asakalce ta ce“Wayyo Abiena wlh banjin yunwa pls ka barni nayi fira bankwana da kai.â€
Kallonta yay ya kashe mata ido 'daya yana sakar mata 'kayataccan murmushi.
Baki ta turo.
'Kasa suka sauko tana maqale da hannunsa.
Jaddatu da Hanan suka bisu da kallo.
Jaddatu da gaza gani ta ce“Oh! Yau shagwa'bar saka kayan Abienki ne?â€
Rahma ta ce“Eh kuma dasu zan zauna har gobe wlh bazan cire ba.â€
Dariya Jaddatu tai ta ce“Ma Sha Allah MATAR manya 'yar manya.â€
Hanan ta kalleta Jaddatu ta ce“Wlh Hanan masifar gulma gareki ai fatan alkhairi nai mata kuma 'diyar Abdul Majeed ai 'Yar manyan mutane ce.â€
Abie baice komai ba yaja suka tafi kan dinning area, zaunar da ita yay.
Ya shiga ha'da mata lafiyayyan girkin.
Ashagwa'be Rahma ta ce“Abiena kanaji matar manyan mutane ce ni, halan ba yaro bane mijin nawa rabin raina ni dai gaskiya bazan xauna da babba idan ma irin halinka gareshi.â€
Rankwafowa yay ya sumbaci la'bbanta da gashin idanunta wanda suke gazar².
Akunnenta ya ra'da mata.
“Babyna bazaki iya son duk abinda na baki ba? OK ai mun gama mgna nace idan bakyaso dole zai sakeki.â€
Ya 'dago ha'barta yana sakar mata tsadaddan murmushi.
Kanta ta samu da fa'duwar gaba ta shafi fuskar Abie tana Jan tsinin karan hancinsa, tai raurau da ido tana son ta yi mgna ta kasa.
Kumatunsa ya bata.
Ahankali ta manna masa Sumba tana kwantar da kanta kafa'darsa.
Da kansa ya ciyar da ita yana mata waqa mai da'din gaske wacce tin tana yarinyar 'yar shekaru 3 idan yana mata take samun nutsuwa sosai.
Ai kuwa sai gata tana 'kyal'kyala dariya ta 'dare saman cinyarsa tana kallon bakinsa yadda yake waqar cikin 'kwarewa.
Misalin 'karfe 6 su Abie suka gama shirin tafiya, sosai sai da yaba Raiyana kulawa, da barmusu duk abin buqata, da wanda za'a tarbi malamin da zaizo mai maganin aljannu, kafi yabar gidan.
Rahma harda kukanta Abie ya samu dakyar ya lallasheta ya ce zai biya wajanta ya kwana kafin ya dawo Chad.
Har airport Rahma tai rakiya, su Baba Tsalha Harisu Yahuza Mal Adamu Abie 2 duk suna airport, sai da jirgin su ya cira sama suka nufo gida.
Mal Adamu da Abie na rarrashin Rahma tanata kuka kamar Abien ya tafi kenan.
Acikin jirgi kuwa Ja'afar bai ta'ba hawa jirgin sama ba aman cikin ikon Allah sam baiyi 'kauyanci ba, sbd aganinsa komai sa kaine.
Sa'bani Laraba da ta dinga 'kurma ihu tana fa'dun.
“Wlh ni daman nasan duk abinda aka ha'da da yaron nan Jafaru sai an ha'du da masifu acikinsa.... Wayyo Allah kaina na juyawa zanyi amai...â€
Tanko cike datakaicin ya ishesa ya buge mata baki, ganin jama'a na kallonsu.
Kasancewar kusan Abie suke dan dukkansu Vip ya biya musu.
Kai Abie ya girgiza yana mamakin halaiyar Laraba.
Tanko fa'da ya fara mata kamar ya ari baki.
“Wlh badan jirgin ya tashi ba, da mun FASA tafiyar nan Ja'afar ya isa ya kula da matarsa, tinda ko munje ba mune zamu bata lfy ba, Allah ne zai bata, haba ina anfanin zabur da kima cikin jama'ah...â€
Abie ne ya ajiye jaridar hannunsa yay gyaran murna.
Tanko yaja bakinsa yay shiru.
Anutse Abie ya ce“ kayi hkr harda rashin sabo.â€
Tanko ya ce“Shi kenan Alhaji Ngd sosai Allah ya biyaka da gidan aljanna.â€
Abie ya amsa da “Ameen.â€
Ya 'dauki jaridarsa yana karantawa.
Ja'afar takaicin Laraba kamar zai kashesa, duba da yadda larabawa da turawa suke kallonta suna dariya.
'Karamin tsaki yaja a 'boye ya na mamakin halaiyar Laraban, wai shine yake janyo musu musifu.
Kallon Ibtisam yay yana riqe da ita jikinsa, bata iya ko 'daga 'Yar yatsarta sbd alluran da aka mata,shiyasa tai lamo jikinsa tana famar zaro idanunta cizonsa take so ta yi ta kasa sbd batada kuzari ko guntu atare da ita.
Hancinta yaja ta hararesa tana zaro masa idanu.
Guntin murmushi yay yana 'daga mata gira.
Karaf akan idon Laraba, wacce ta takure waje 'daya.
Ta ce“Lah ha ilah illallahu! Me zan gani Jafaru iskancin da yasa ka nace ka biyo mu kenan? Yarinyar ba lafiya keke neman koya mata iskanci? Toh meye idan ba iskanci ba 'daga ma mace gira....â€
Wawan bugo Tanko ya kaima bakin Laraba tai saurin kaucewa tana rufe bakin nata.
Abie kunya ta saka bai 'dago kansa ba yana mamakin matar matuqa.
Ja'afar ransa ya 'baci sosai amman yay shiru bai ce komai ba.
Tanko cikin kwantar da murya yaba Ja'afar hkr.
Ya kalli Abie ya ce“Don Allah Alhaji daga munje an bata 'daki idan zaka dawo zamu biyoka wlh MATAR nan bazata bari azauna lafiya ba acan shi ka'dai zai iya jinyar matarsa daman ai ba yarda take damu ba.â€
Abie ba tare dare da ya yi mgana ba ya jinjina kansa hakan ma ya yi.
Rahma ma tana can tana shirin tafiya Espagne gobe insha Allah.
Sai tsakiyar dare suka shigo 'kasar Australia.
Tinda airport Ja'afar yasan lallai wannan 'kasar babbar 'kasa cikin manyan 'kasashen duniya.
Laraba 'kauyanci 'kiri² ta dinga nunawa.
Wasu manyan motoci guda biyu akazo tarbarsu da ita.
Lallai Abie babban mutum ne wanda duniya ta san da zaman sa.
Ba hotel suka nufa ba, wani tamfatsetsan gidane wanda yake mallakin Abie 'din.
Tinda wajan gidan zakaji sha'awar ina ma ka kasance acikinsa.
Suna shiga falon wanda ya gaji da ha'du suka zazzauna.
Pa 'din Abie nan Australia ya shiga musu sannu da zuwa bayan ya jido kayansu.
Abie ya ce “Nadeer yanzu dare ya yi sosai zuwa gobe sai muje asibitin kaje kaima ka kwanta sai da safe.â€
Cikin girmamawa Pa Nadeer ya amsa “Allah ya huta gajiya Oga.â€
Babban kukan Abie wanda idan yana 'kasar shine ya shirya musu daddan girki nan falon saman carpet ya shimfi'da wata babbar lade mai kyau ya jera musu abincin.
Sai da sukaci suka nat Abie yama Tanko da Laraba jagora Inda zasu kwana.
Yazo yama su Ja'afar wanda Ibtisam 'din bacci take.
Abie ya ce“Kaje da abinci idan ta farka cikin dare sai ka lalla'ba ka bata, ka dinga kiyayewa kar ka ajiye duk abinda kasan idan ta gansa zata iya 'dauka ta buga maka.â€
Ja'afar yay godiya yana qara ganin kima da darajar Abie 'din.
Abie bayan ya rufe falon ya shige bedroom 'dinsa mai girman gaske ta tsaru. Wanka yay ya 'dauro alwala ya shirya yana baza 'kamshi ya Rama sallar magarib da isha, ya miqe ya fara nafila.
Ja'afar ma hakance bayan ya kwantar da Ibtisam yay wanka ya rama sallah ya shiga nafila dan tin rada ya dawo haicinsa bai sake cikakken baccin dare ba sosai.
Abie sai 'karfe uku ya gama bayan ya jima yana ma Allah kirari yama mahaifinsa da Ummu Aymana and Aliyu addu'a, ya miqe ya cire jallabiyar ya sanya kayan bacci kwaso wayoyinsa yana dubawa kasancewar layinsa na Australia har biyu.
Ganin kiran Rahma yay har miss calls 6 a'dayar layin miss calls 7 da message 2.
'Kwan filar 'dakin ya kashe ya bar na gefen gadon ya 'Kara gudun Ac kasancewarsa mutum mai son sanyi sosai. kwanciya yay yana dafe goshinsa Allah ka'dai yasan halin da take ciki.
Message 'din ya duba.
_ðŸ˜â€œAbiena Allah yasa kana lfy ina kiranka ka qi ka 'dauka na kasa bacci ina son naji lafiyarka, ya gajiya? I miss you so much Abiena.😢_
Kansa ya dafe yana fa'din.“Oh! Babyna ina fa lfy gajiya ce kawai.
Bai kirata ba ya tura mata message.
_😔“Wayyo Babyna yi hkr Abienki ya gaji ne, sosai ina lfy, gobe zan kiraki nasan yanzu kinyi bacci, kina maqale cikin zuciyata ban manta dake ba, gajiya ta saka ban kira ki ba, miss you too baby ummina.😘_
Dr Moha ya kira sukayi mgna akan gobe suna shigo asibitin.
Har tsawon 5 minutes yana jiranta shiru yay murmushi daman yasan ta yi bacci.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanta ya rufe rabin jikinsa da blanket, ba jimawa bacci yay awon gaba da shi.
Ja'afar uku bata qarasa ba, ya kammala ibadarsa ya miqe da jallabiyar ya kwanta yana rage hasken 'dakin.
Jikinsa ya jayota ya rungumeta tsam yana kallon kyakkyawar fuskarta, yana shafa gashin kanta wanda bai fiye yawa ba.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanto musu.
Yaji Ibtisam ta fara motsi sai yaji ta shige cikin 'kirjinsa sosai ta 'kan'kame shi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya sake matseta gam yana shafa bayanta alamar lallashi.
Cikin baccin gajiyar da ya 'daukei shi yaji wata irin iska mai 'karfi kamar guguwa.
Azabure ya bu'de idanunsa bakinsa 'dauke da addu'a.
Abienda idanunsa suka gane masa'ne ya yi masifar gigitashi.....!!
_💃ðŸ»'Yar Ajin Tubarkallah🥰_
_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/2/22, 22:41 - Buhainat: ```D A```
```47&48``
_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Sosai Ja'afar yake zaro idanunsa, wanda suka numa zallar tsoronsa akan abin al'ajabin da ya gani.
Duk da ya kasance jarumin namiji marar tsoro amman lamarin na yau ya yi mugun tsorata shi, wanda ya nemi addu'ar da yake cikin bakinsa lokacin da ya farka amman ya kasa, sakkamkon abinda yake tsaye gabansa.
Yawun bakinsa ya ji ya 'kame baki 'daya. Da sauri ya rarumo Ibtisam ya rungumeta gam a 'kirjinsa, yana kallon ikon ubangiji.
Yaron nan makaho da ya temakawa sanye da wasu irin kaya ya yi shiga irin ta 'ya'yan sarauta, sandar da take hannunsa kallo 'daya zaka mata kasan ta zinarince.
Sai wasu irin manyan halittu masu 'kirar 'karfafa, kallo 'daya zaka musu kasan ba mutane bane.
Gabansa ya 'karaso yaga cikin halittun biyu wanda yafi tsayi da girman ya beqa dogon hannunsa wata lafiyayyar kujera ta lu'u-lu-u ya ajiye agabansa sai walqiya take ya zauna dab da gadonsu.
Cikin sansanyar murya ya ce.
“Assalamu alaikum Ja'afar.â€
Ja'afar 'yar zufar da ta karyo masa ya goge yana sake rungume Ibtisam jikinsa.
Numfashi mai 'karfi ya fizgo cikin jarumtarsa ya amsa.
“Wa'alaika salam, bawan Allah ba kai bane wanda na tsallaka saman titi? Shin ya akayi kazo nan? Sannan wannan halittun fa!?â€
Hussain yay murmushi ya ce.
“Ya kai bawan Allah Ja'afar haqiqa nine wanda ka temakawa, ni musulmi ne mu 'yan biyune 'dan uwana Hassan ba ruwansa da rayuwar bil'adam, ni kuma haka na taso da son bil'adam, da son temaka musu amman na 'kwarai fa!ni ba mutum bane aqalla yanzu inada shekaru dubu 'daya da 'dari biyu da goma sha 'daya da kwana 17 yau cif aduniya.
Najima ban samu wanda ya temaka min ba irinka, tinda nazo duniya cikin wannan shekarun nawa kaine mutum na tara da ya temakeni cikin mutane duk da ba wai ina buqatar temakon ba, inayine kawai dan ware bil'adam irinku masu Neman temako, mu tarbi inda mukasan zaku wuce da zaran kun temaka mana sai muma mu temakeku. Akwai wa'danda zakaga suna cikin halin neman temako ko wata gagarumar matsala,muke fitowa mu tarbesu mu nuna atemake ko abinci ko sutura ko halin rashin lafiya ko Neman sadaka ko atsallakamu titi, kawai sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, wataran harda mari ana nuna mana 'kyama bayan mu'din cikin jansin mu ma babbar sarauta garemu mun gama samun duniya lahira muke nema. Amman duk da haka ni ban ta'ba 'daukan fansa ba akan kowa temakon ne kawai bazan ma wanda bai min ba, idan ka mareni nasan agaba zaka ha'du da daidai kai sabida nawa mahaifin bazan ta'ba cutar da bil'adam ba. â€
Ja'afar sosai yake atsorace amman ya jure yana kallon Hussain ya ce.
“Ai ni kuma aganina ban maka wani temako ba da ya cancanta ka sakamin, ai ba komai yiwa kaine toh da me zaka sakamin?â€
Hussain yay murmushi yace bari kaga yanzu na dawo asalina.â€
Yana qarashe mgnar yay wata irin girgiza take ya riki'de ya dawo Hussain 'dinsa sak babba kuma cikakken aljani.
Ja'afar ya ce.
“Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahamnir rahim.â€
Hussain ya ce “Ai banzo da niyar cutar da kai ba, zan temaka maka akan matarka dan wlh kafin Ku samu maganin da zai warka da ita zaku jima duk da ba abinda ya gagari Allah.â€
Ja'afar jin ya ce Ibtisam zaima magni cikin murya ya ce“Amman da naji da'di.â€
Hussain ya ce“Insha Allah 'dago kanta.â€
Ja'afar jikinsa na rawa ya 'dago kan Ibtisam, Hussain ya beqa hannun ya dafe goshinta.
Wani irin haske hannunsa ya fara idanunsa arufe bakinsa na motsawa.
Kusan 30 minutes, ahakan, kafin Ibtisam ta fara wata irin rawa jiki da kyarrrma numfashinta na sama da 'kasa.
“Karka ji tsoro Ja'afar sai mun cika awa 'daya cif.â€
Kai kawai Ja'afar yake 'dagawa.
Sosai ya girgiza da lamarin yadda Ibtisam take zanzana.
Sandar hannunsa ya 'daga ya fara karatu yana tofawa, wanda goshinsa ya fara fitar da zufa, ya buga atsakiyar kan Ibtisam, wanda atake ta 'kurama ihu ha'di da fa'din “Wayyo Allah nah! Ja'afar ka cuceni, zan mutu ban nemi gafara iyayena ba! Na tsaneka bana sonka...!â€
Sai kuma tai shiru tana sauke numfashi alamun bacci.
Hussain ya ce“Alhmdllh! Tana farkawa bacci lafiya zata farka sai dai baccin zai jima zata ita kwana da wuni ahaka karka damu tana tashi komai ya wuce Insha Allah, dan haka karku kaita asibiti dan batada wata matsala yanzun, na barku lfy ina muku fatan alkhair ki bi sannu ka saddo 'kasa ka 'kas'kantar da kanka ka lallashi yarinyar ka bata kulawa karka yi girman kai cikin lamarin sannan karka yi fushi ka biye mata ka yanke hukunci cikin fushi duk zakuyi nadama daga baya, idan kunbi son zuciya, da kuma 'bacin rai, ka riqe mganata ka rungumi matarka tana sonka da zaran ka ajiye jiji da kanka ka lallasheta komai zai wuce fatan alkhairi .â€
Ja'afar da'di ya rasa inda zai tsoma ransa sai godiya yake ma Hussain.
Iska da guguwa mai 'karfi wacce tafi ta farko ita ce ta turniqe 'dakin kafin giftawar idanu sun 'bace.
Kumaa daidai lokacin ake kiran sallar asubah.
Ja'afar ya kwantar da Ibtisam ya zuba mata idanu cikin farin ciki wai ta warke.
Miqewa yay ya shiga toilet yay wanka ya 'dauro alwala ya fito ya sanya jallabiya ya tayar da sallar raka'atanil fajir.
Abie amakare ya farka dan lokacin an fara sallah, masallaci, agaggauce yay wanka ya 'dauro alwala yay sallah.
Bayan ya gama ya fara azkhar.
Bayan ya idar ya miqe ya fito falo yana Jan cazbi.
Da mamaki yake kallon Ja'afar da Tanko zaune falo suna magana cikin zallar farin ciki wanda ya ga Laraba sai washe haqora take.
Sallama yay musu suka gaisa cikin mutuntaka.
Abie ya ce“Ya dai ko an samu wani ci gabane wajan Ibtisam?â€
Cikin farin ciki Tanko ya ce.
“Alhaji daman zaman jiranka muke bai kamata kana hutawa atasheka ba,Allah ya dubi kirkin ka da temakon ka, ya ragema wahala, jiya cikin ikon Allah cikin tsakiyar dare......â€
Tsaff ya labartawa Abie yadda Ja'afar ya labarta masa daga kan temakon da yawa yaron makaho zuwa zauwarsa da abinda yama Ibtisam zuwa ihunta da kiran sunan Ja'afar da tai da yadda Hussain ya ce da zaran ta farka zata tashi normal kar aje asibiti abari har ta farka.
Abie ya sauke ajiyar zuciya zaiyi magna kiran Rahma ya shigo wayarsa.
Bai 'daga ba ya kallesu ya ce.
“Ma Sha Allah Alhamdllh! Abu ya yi kyau toh ba damuwa zamu jira muga farkawar tata amman duk da haka zamuje aqara dubata idan ta tashi.â€
Ja'afar cikin murna ya ce“Abie Allah ya qara girma da bu'di.â€
Abie ya 'daga wayar yana amsawa da “Ameen ya Allah Ja'afar.“
Wayar ya kai kunnensa yana miqewa ya nufi bedroom 'dinsa.
Zazzafan numfashi ya sakar mata ta cikin wayar ha'di da sauke ajiyar zuciya, cikin sansanyan murya ya mata sallama.
“Assalamu alaiki Ya Baby Ummina.â€
Rahma