Showing 87001 words to 90000 words out of 165653 words

Chapter 30 - DATTIJON ARZIKI

Start ads

Rahma   

15 Aug 2025

859

Middle Ads

shi ma tana can gidansu Aishar wajan bikin. wanda cikin lokaci qalilin gidan yanayin fuskokin su ya canza zuwa damuwa.
Mama Adiya ta shiga tashin hankali harda kuka ta shedawa su Munnira.
Munnira ta ce“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Aishar dai mama?â€
“Eh ita dai muje muga halin da za'a fito da ita.â€
Hajiyar Ma'aruf hankalinta idan ya yi dubu ya tashi, ga Ma'aruf ya sakata gaba yana kuka.
Hajiya Ma'aruf ta kira Alhaji babba ta sheda masa abinda yake faruwa ya ce su fito baki 'daya suka 'dunguma zuwa asibitin.
Haka suka tafi hankalinsu atashe harda uwani me aikin Aishatu.
Kai komo kawai suke suna jiran fitowar Aishatu.
Ana kiran la'asar aka fito da ita, aka kaita 'dakin hutu.
Ma'aruf jin anyi nasara ciro yaron ita tana lfy sai dai jininta ya hau sosai tana buqatar hutu, dan har yanzu bata farfa'do ba. Dr ya ce akiyaye duk abinda zata gani ya 'bata mata ranta.
Koda suka shiga wajanta bata San wanda yake kanta ba.
Akaba su gawar yaron da ba'a gama masa halitta ba.
Ma'aruf yana kuka aka binne yaron da shi acan babban gida.

*Espagne*
Kiran sallar la'asar ya tashi Abie daga dadda'dan baccin da ya 'dauke shi.
Wanka yay ya fice masallaci.
Rahma kwance ta yi 'dai'-daya baccinta take shararawa.
Har Abie ya dawo daga masallaci, ya zauna a falon ya kunna Tv yana amsa waya ya ga shiru bata fito ba, ya miqe ya nufi bedroom 'dinta.
Kwance take tana sharara bacci.
Bathroom ya wuce ya ha'da mata ruwan wanka masu 'dumi.
Zama yay bakin bed ya janye blanket 'din jikinta, ya rankwafo yana kallon kyakkyawar fuskarta.
Ya sanya hannunsa ya gyara mata gashinta, wanda ya rufe mata fuska.
Anutse ya tattarashi ya 'dago kanta ya 'Dora saman cinyarsa ya kitse mata gashin a 'daya ya saka ribbon, ya sumbaci tsakiyar kanta, ya shafi gefen fuskarta, ya 'dora bakinsa kan kunnenta ya kirata“Baby Ummi! Oya tashi anyi sallah.â€
Ya qarashe mgnar yana cizon fatar kunnenta.
Idanunta ta bu'de tar tana kallonsa, ta turo 'dan 'karamin bakinta gaba.
Murmushi yay ya kwantar da kanta saman pillow, ya kamo lallausan hannunta ya miqar da ita zaune ya 'dauke cak kamar 'yar baby ya shiga bathroom da ita, ya direta ya ce“Oya wanka azo ayi sallah, aci abinci OK Babyna?â€
Kai ta 'daga tana shigewa jikinsa tai lamo, ta 'dago kanta tana kallon kyakkyawar fuskarshi, tana 'kif² da qananun idanunta masu matuqar masa kyau, da sanyasa shauki.
'Yar dariya yay ya ce“Uhmmm! Baby mage oya wanka lokacin sallah zai shige, idan kin gama kome sai ki shige jikin Abienki kiyi luf ba me hanaki Ok.â€
Janyewa tai ta amsa da “Toh Abie Rabin raina.â€
Hancinta yaja ya fita ya rufo mata 'kofar toilet 'din.
Kayan jikinta ta cire ta shige cikin ruwan 'dumin, wanda yake fitar da wami irin 'kamshi.

Abie yana fitowa falon ana danna doorbell 'din falo.
Ya nufi hanyar falon.
Yana bu'dewa suka ha'da idanu da Anee. Cike da girmamawa ta duqa ta gaishesa ya amsa fuska asake, yana fa'din.
“Anee an taso? Ma Sha Allah wuce sai ki shige tana 'dakinta.â€
Amsawa tai da “Toh Abie Allah qara girma.â€
Kai ya jinjina ya bata hanya ta wuce ya rufe qofar.
Zama yay yana kallon tashar CNN.
Meerah ya kira ta kawo masa dabino ya bata umarni ta dafa masa shayi.

Anee sanyin da'din 'kamshin bedroom 'din Rahma ya saka lumshe idanu tana fa'din.
“Uhmm! Habibty Rahma son sanyi da qamshi.â€
Ta qarashe mgnar tana zama tana jiran Rahma jin qaran ruwa a toilet.
Sosai Rahma tai wanka, ta 'dauro alwala, ta fito, 'daure da towel.
'Kananun kyawawan idanunta ta waro ganin Anee ta iso gareta tana fa'din.
“Oyoyo my Anee ashe za ki dawo?â€
Anee tai dariya ta ce“Dakata! Mage karki fa'domin ajiki ki jiqani da ruwna jikinki.â€
Murmushi tai tana goge jikinta da qaramin towel, ta ce“Daman kin samu babyn Abie zatayi hugging 'dinki ma.â€
Dariya sukayi.
Agaggauce ta shafa lotion ta saka riga da wando Pakistan orange colour sun mata kyau tsaf ta fesa turare ta yane kanta da mayafin ta tayar da sallar la'asar.
Tana idarwa bayan ta yi addu'a ta miqe ta zauna kusan Anee tana sauke numfashi jin kanta na ciwo.
Anee ta ce“Rafeek fa school ya iskeni sai munzo naqi wlh bakiga yadda ya damu ba, akanki Habibty ya ce yana kiranki baya sumunki, switch of.â€
Rahma ta dafe goshinta, tana kallon Anee ta yamutsa fuska ta ce“Wayan inaga Abie ya kasheta ne, pls kici ya ban lokaci kinga Chad zamu koma da Abie ya ce ba yanzu zanci gaba da karuta ba, ni ban iya musu da Abie na ba! Ya ce tarewa zanyi kwanan nan gidan mijina, so kinga abun ya tabbata babu damar naci gaba da alaqa da Rafeek duk da daman sanin matsayina ya saka ban sakar masa fuska sosai, kawai kimina fatan alkhairi wlh bazan qi za'bin Abie na ba, za'binsa tin bansan kaina ba nasan yanada dalilinsa mai qarfi na aurar dani da wuri.â€
Anee ta jinjina kanta ta ce“Gaskiya my Rahmerh kinada hankali da hangen nesa da biyayya wa Abienki Allah ya saka miki da khairan, ya kuma baki ladan biyayya insha Allahu bazakiyi kuka ba, amman zanyi kewarki idan kin tafi.â€
Rahma ta rungumeta tana buga bayanta tana zubar da hawaye dan har acikin ranta batajin son mijin nata kowaye, sai dai zatama Abie biyayya haka tana son karatunta hkr kawai tai dan ta farantawa Abie ransa.
Hawayen fuskarta ta goge ta ce“Anee muje muyi dinner. â€
Anee ta miqe tana fa'din.
“Nima yau nayi naki banci komai ba.â€
Murmushi Rahma tai tana cire mayafin kanta ta ajiye saman bed, suka fito.

Abie zaune yana cin dabino yana kur'bar shayi yaji motsinsu, bai waigo ba idanunsa kan Tv wayarsa ta 'dauki ringing.
Rahma ta kalleshi tana zama kusansa ta zare dabinon hannunsa takai bakinta tana kallonsa yana amsa waya.
Kallonta ya yi, yay saurin kai hannunsa wanda ta janye dabinon ya ta'ba goshinta ya ji zafi.
“Ya Salam! Baby ba lafiya.â€
Ya furta yana shafa gefen fuskarta, ya miqe yana fa'din.
“Eh Kamal aha'da su kamar yadda nace 'din pls anjima zuwa dare zan kiraka yanzu inada babban uzuri zanba baby magani.â€
Ya qarashe mganr yana tafiya.
Rahma da idanu ta bisa tana murmushi.
Hannun Anee ta kama suka tafi kan dining area.

Abienta ta fara zubama ta zubama Anee kafin tai serving 'din kanta.
Suna tsakar cin abuncin ya iso yaja kuje ya zauna, ya bu'de plate.
Sosai sukaci alfatat 'din wanda yaji niqaqen nama, suka Sha lemon inabi.
Abie ya bata magani ta Sha suka dawo falo suka zauna Rahma ta canza channel, Abie ya shirya ya tafi makarantar su Rahma, ita da Anee su na zaune suna hirasu harda Meerah.

*Tchad*
Misalin 'karfe 8 na dare Ja'afar zaune gaban Mal Adamu, suna mgna Abie 2 na gefe, casbi ahannunsa yana ja.
Ja'afar sanye yake da 'kananun kaya, wanda suka masa kyau, kasancewarsa namiji me qirar qarfafa, sun fito da mur'daddan jikinsa sai baza 'kamshi yake.
Mal Adamu ya ce.
“Wlh har na rasa bakin da zan godema bawan Allah'n nan, ya kaiku 'kasar waje neman magani an dace yanzu kuma takardun karatunka yake nema dan samomaka aiki ko cigaban karatunka? Allah ya masa albarka ya karashe da dukkan abin sharri.â€
Abie 2 da Tanko suka amsa da “Ameen.â€
Ja'afar ya ce“Eh Baaba inaga karatun yake so cigaba, ni kuma sam ya fita araina gwara kawai aikin 'kasa² dai-dai ruwa dai-dai tsaki. Yanzu idan yazo dole tare zamuje Niger tinda takardon na can.â€
Mal Adamu ya ce “Toh toh ba laifi Ja'afar Allah ya maka albarka.â€
Tanko ya ce“Mal Adamu inaga idan muje ayi biki sai kawai yazo da matarsa, ko ta zauna can idan ya yi 'yan watanni sai ya dinga zuwa, inaga zaifi ko?“
Ja'afar ya kalli Tanko da sauri sai dai ya sadda kansa.
Mal Adamu ya ce“A'a wannan ba mgna bace, ya za'ayi biki yabar matarsa ya taho? Ai insha Allah tare zasu taho Allah ya tabbatar mana da alkhairi.â€
Suka amsa da “Ameen.â€
Abie 2 yay gyaran murya ya ce.
“Abdulmajid ya ce ku qara hkr Rahma batajin da'di tana kan shan magani, da zaran ta gama likita ya qara bincikar lafiyarta zasu dawo.â€
Mal Adamu ya ce“Allah sarki, Allah ya qara mata lfy, ya maidosu lfy.â€
Abie 2 da Tanko suka amsa da “Ameen.â€
Ja'afar ya miqe ya musu sallama ya fito yana karka'da 'dan makullin motarsa.

Ibtisam ya hango tana zagaye tana kalle² a compound 'din gidan.
Cike da mamaki yake kallonta, yana nazarin anya yarinyar nan tana lafiya lau kuwa?
Ganin ta nufi rumfar shaqatawa ya tsaya yana kallon ikon Allah har ta shige ta zauna.
Wajanta ya nufa fuska ba walwala, yana takunsa mai cike da 'kasaita.
Kallonta yay ta sadda kanta tana wasa da zabon hannunta, bata ma san ya shigo ba.
Cikin tsawa ya ce“Ke! Tashi koma ciki uban me kikeyi anan?â€
Ibtisam firgigit tai ta dawo daga duniyar tunanin Abie.
Kallonsa tai ta ga yadda ya tamqe fuska ba alamun wasa.
Baki ta zum'buro gaba ta ce“Haka kawai nazo inajin yanayi me da'di sai ka korani...â€
Wata iriyan damqa yay mata ya miqar da ita tsaye, wadda ta sanyata sakin ihu jikinta ya 'dauki rawa ganin yadda fuskarsa take amurtuke.
Cikin mugunta ya matse 'kugunta da kakkausar murya ya ce“Maza wuce ciki ni sa'anki ne?â€
Ya tambaya yana murza mata fatar baki, ta saki kuka tana girgiza kanta ta ce“Don Allah kayi hkr zan shiga gidan.â€
Hanka'data yay waje cikin tsawa ya ce“Wuce na sake ganin kin fito ahaka ke marar kunya.â€
Da gudu ta nufi cikin gidan, tana kuka.

Tsuki yaja ya tafi ya shiga motarsa ya fizgeta aguje ya nufi gate yana huci, yana 'kudirtawa tabbas sai ya mata horo me tsanani zata dawo hayyacinta.

Zazzaune suke afalon anata hira Rayyana wacce taje cikin farin ciki sbd wayar da sukayi 'dazu da Rahma awayar Abie jin yadda Rahma ta sake tana bata labarinba, suna tafe har ita cikin satin nan, ta kwantar da hankalinta Abie na sonta bazai rabu da ita ko meye ta mata ta yafe mata.
Shi ne fa Rayyana taji hankalinta ya kwanta dan tasan Rahma 'yar lelen Abie ce tinda tana sonta toh Abie ma zai sota. Ta zage tana basu labarin wata kakarsu wacce take Sudan, idan kana son kaci dariyata ka samo kyankyaso koda mataccene ka ajiye wajan da zata gani har rawar banjo take tsabar tsoro.
Idan ta fa'da da larabci sai ta fassara da hausa sbd Laraba wacce ta dage tana tiqar dariya, oh! Mutane basu iya samun waje ba.🤔
Jaddatu ikon Allah take kallo yadda Rayyana ta saki jikinta tana bada labari, ita ko kunyar abinda ta aikata bataji, har ta manta.
Hanan dariya take harda riqe cikinta ta ce“Wlh Rayyana da ace anan garin take ko dan naga rawar banjo zamuje mu samo kyankyason mu ajiye agabanta.â€

Rayyana ta ce“Wlh Hanan anyi muguwa kice rawar banjo kike son gani?â€
Dariya sukayi Jaddatu ta ce“Kai wlh mutane ba kunya ko ka'dan koda yake ance tabarmar kunya da hauka ake na'deta.â€
Rayyana ta gane da ita take ta basar da ita taci gaba da labarinta.
Ibtisam ce ta shigo tana kuka.
Laraba ta ce“Ke fa bakida hankali wlh meye haka kike musu ihu agida? Kinsan dai jajayen mutane basa son hayaniya dan Allah ki bari.â€
Jikin Laraba ta zube tana rage kukan nata ta ce’Yo ba wancan mugun bane ya mur'demin hannu haka kawai ban masa komai ba, dan naje wata rumfa mai shegen kyau na zauan.â€
Rayyana ta ce“Waye Ibtisam?â€
“Ja'afar mana.â€
Rayyana ta ce“Oh! Abin na masoyana ba ruwana qila akwai abinda kika masa.â€
Jaddatu ta ce“Me ya faru ne take kuka iyayan jin hausa?â€
Latifa da take 'daukar tray'n da ta yanko Jaddatu kankana ta gintse dariyartatai maza ta wuce kar abin ya shafet.
Rayyana ta gane sarai Jaddatu habaici ta mata ta fa'da mata abinda Ibtisam ta fa'da.
Jaddatu ta ce“Wannan yarinyar zatayi ruwan marasa kunya qila ta masa rashin kunyane ai kome bazai gagareta ba tinda ta iya biyosa daga wata qasa tin kafin aurensu.â€
Rayyana dai bata sake mgna ganin Ibtisam da Laraba suna kallonta sai kawai ta waske ta ce“Ta ce qila kin masa laifi ne.â€
Ibtisam ta miqe idanunta akan hoton Abie ta nufi hanyar kitchen inda 'dakinsu yake tana share hawaye, tana kisima wani qudiri aranta ta nan kawai takejin zata iya samun Abie.

*Gabon*
Har goma na dare Aishatu bata farfa'do ba daga dogowar suman da tai, hankaalin iyayanta da 'yan uwanta ya tashi. Ma'aruf daman ba'acewa komai, shi hankalinsa qololuwar tashi ne yay, ko baqin ruwa har yanzu ya kasa Sha, hajiyarsa ba yadda batayi da shi ba amman yaqi ya ce sai yaga tashin Aishatu.
Amman doctor ya basu tabbacin zata farka akowane lokaci.
'Bangaran Rabi'ah kuwa tinda take bata ta'ba tsanar kanta da bin mazan da take ba sai yau, ji take kamar ta da'bawa cikinta wuqa amman idan ta tuna makomarta wajan Allah sai ta fasa.
Tinda ta dawo daga sallah sai istigfari take taji har Abadan bazata sake zina ba ta tuba da zuciya 'daya ta fasa dukkan halaiyarta, abinda ta yanke ta qudurta aranta tanaga shine daidai shi zatayi, bata ta'ba sanin cin amana idan an kamala haka take sai yau ta yi tirrr da Allah wadaran halaiyarta.

*Espagne*
Anee sai da sukayi sallar isha sukayi lunch kafin Rahma ta saka direba ya kaita gida.
Har lokacin Abie bai dawo ba, Rahma ta cika da kewarsa ga bata san inda ya ajiye mata wayanta ba!
Koda yazo ta yi fushi dakyar ya lallasheta sai da ya Kira mata Jaddatu sukayi fire sosai da Hanan kafin 'yan Morocco su ummiterh daga qarshe Rayyana.
Misalin 12 na dare, hadari ya ha'du sosai garin sai wata irin cida ake ga tsawa mai figitarwa.
Rafeek kwance saman lafiyayyan gadonsa yana juyi banda tunanin Rahma ba abunda yake, adaidai wannan lokacin, mugun sonta yake kamar me, ga shi yana kiranta baya samunta.
Sake gwada kiran number nata yay duk da yasan ba lallai ta shiga ba.
Cikin sa'a ya ji wayan na ringing ya zabura ya miqe zaune cikin farin ciki.
Dai-dai lokacin Abie na kwance saman 'katon Royal bed 'dinsa ya shige cikin lallausan bargo, yana latsa wayan Rahma, kiran ya shigo.
Sunan Rafeek ya ga yana yawo saman screen 'din wayan.
'Kirjinsa ya ji ya buga dammm!
Picking call 'din yay, baiyi mgna ba, ya kara wayar kunnensa.
Daga can Rafeek ya sauke ajiyar zuciya,cikin sansanyar murya mai da'di ya kirata.
“Baby cute! I miss you I love you, ya jikin naki? Wlh na kasa bacci tunaninki na azabtar dani, 'dazu na matsawa Anee ta rakoni gidanku taqi, hope kinji sauqi? Pls ki ban dama na bayyana wajan Abie sbd naga baida wata Matsala wlh ina sonki ina son mallakarki nan kusa, hello baby cute kina jina kuwa ko network ne?â€
Abie tsabar tashin hankali har zufa take tsatsafo masa duk kuwa sanyin A/C da yake cikin 'dakin zuciyarsa wani irin tsalle take tamkar zata faso 'kirjinsa ta fito waje, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi sam bai san abin na yaron ya kai haka ba!
Wayar ya kashe baki 'dayanta, yana ciza jajayen lips 'dinsa, yana jin wani irin 'daci acikin bakinsa.
Wayarsa ya janyo wacce take ajiye akan bedside drawer, hannunsa na rawa ya Danna wata number ya kira bugu 'daya aka 'daga.
Dai-dai lokacin da zaiyi mgna ya ji Ana bugun 'kofarsa da 'karfin gaske.
Jin muryar Rahma tana kiransa tana shasheqar kuka yay saurin jifa da wayar hannunsa ya miqe jikinsa na rawa ya diro daga saman bed 'din ya nufi 'kofar...!
Washhhh! Wlh ina ciwon kai nai muku typing 'din nan.

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/16/22, 11:30 - Buhainat: ```D A```

```65&66```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

```WANNAN PAGEN SADAUKARWANE GA MUM SAYYED DA MMN ABDULWAHAB AND KHADIJA WLH NAJI DA'DIN COMMENTS 'DINKU NA JIYA TNX SO MUCH ACI GABA DA GASHI GUYS, YANZU AKA SOMA ANZO WAJAN.😉```
Kofar Abie ya murza key ya bu'de hankalinsa atashe.
Kafa'dunta ya riqe yana girgizawa, “Babyna me ya faru dake? Tsoron tsawa ko Baby?â€
Rahma ta girgiza kanta ta fa'do jikinsa tana qamqameshi gam, jikinta sai rawa yake, tana kuka ta ha'da uwar zufa.
Arikice ya 'dago fuskarta yana bubbuga kumataunta, ya tsura mata idanu, yana tambayarta “Baby menene? Me ya faru dake pls nutsu ki fa'damin kalleni tare kike da Abienki ba abinda zai sameki insha Allah. Menene Baby?â€
Rahma ta qamqamshi gam ko 'kwa'kwaran motsi ta hanasa, sai kuka take.
“Oh! Ya Rabbi! Baby tsoron ruwane ko cida? Nasan dai ba wani zai iya shigo mana gida ba, toh menene Baby? Oya muje 'dakin naki mugani.â€
Ya qarashe mgnar yana qoqarin 'ban'bareta daga jikinsa, taqi ta maqaleshi gam.
“Baby ki tsaya mana karki kadamu, nutsu ki min bayani OK? â€
Kai ta 'daga ya janyeta daga jikinsa ya kama hannunta don su shiga bedroom 'dinta ta'ki ta qamqameshi.
Cak ya cirata sama kamar 'yar baby ya nufi bedroom 'dinta da ita.
Cikin kuka ta ce.
“Abie kar muje 'dakina wlh tsoro nakeji awajanka zan kwana mummunan mafarki nayi, wanda ko 'kasar arna abin baya faru kuma bazai ta'ba faruwa ba.â€
Ta 'karashe mgnar cikin kuka.
Abie galala ya saki baki yana kallonta ya tsaya da tafiyar cak, fuskarta ya tsirawa idanu, cikin kwantar da murya ya ce“Ok fa'damin wannan wani irin mafarkine baby? Kina nufin bakiyi addu'a ba lokacin da kika farka kika dinga kuka da famar kiran Abie?â€
Ya mata tambayar yana 'dago ha'barta ya ce“Kalleni Baby.â€
Yadda ta ga fuskar shi ba wasa ya sanya ta ha'diye kukanta tana kallonsa ahankali ta motsa la'bbanta ta ce.
“Wlh nayi addu'a Abienah kawai na gigice da mafarkin ne.â€
“Ok fa'damin wane irin mafarkine? Fa'damin idan ba haka ba sauka kije 'dakin ki kiyi addu'a ki kwanta bi khair insha Allah. â€
Rahma ta qara maqaleshi ta sadda kanta cike da jin nauyin Abien ta bu'de 'dan 'karamin bakinta ahankali ta ce.
“Abie zan fa'da maka, wai mafarki nayi ni da kai muna cikin wani irin 'kawataccan lambu, ko ina franni ne tsanwa shar, wasu irin dawakai farare tass na zagaye damu, sai wasu mata masu farin kaya suna hidima damu, da wasu yara maza kyawawa biyu basu fi shekara 3 ba, sai wata 'Yar baby 'yar wata 10 amman tana tafiya irin ta yaran da basu jima da koyan tafiya ba, amman akwaita yawo ko ina shiga take a lambun, haka duk inda zaka tafi kana maqale da ita ko ina gashinta har gadon bayanta, kamarmu 'daya da ita, wai kuma inada cikin tsawon wata 4 duk bamu san da shi ba sai yau anata zabga ruwa babyn ta fita aguje sakamamakon Meerah da ta bu'de 'kofar ta manta bata rufe ba, ta fice hankalina atashe na bita aguje sbd tsoron

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login