Showing 27001 words to 30000 words out of 142410 words
yanzun kake yi ba buzuwan matar ka da dangin ta sun ishe ka.
Hajiya kiyi hakkuri nima a wurin yariyar nan Yusuf ya jiyo muna shine nace ba a fada min ba tunda har zaki je zaria ki kwana biyu haka ba karamin rashi kika yi ba.
Tace wace yarinya ke nan kake magana a kanta yace yarinyar da kika hadamu da ita kwanaki muka taho abuja sai dai yarinyar bata da kunya ban gane inda maganan ta ya dosa ba.
Au khadija kake nufi ko wa yace ina ganin sunanta ke nan Yusuf ya hadu da ita take fada mai yaban layin ta na kirata tana karanta min shirmay .
Tace Ladi ce matar kawun ka Allah ya karbi abinshi shine nazo ita khadijan kuma ta damu da nine shiyasa tasan damuwa na har taji.
Yanzun kai bakaji kunya ba ace wai har khadija zata ji zance na kai bakaji ba haduwan ka da yarinyar gaba daya ya canza muna kai kana ko tuna makomar ka ga Allah.
Bani ba ba mahaifinka ba duk kayi watsi da alamarin kowa kana ganin buzuwa da yan uwan ta sun isheka rayuwan duniya.
Mu din dai da kake gudu din mune dai iyayyen naka har gobe zance guda ne abin nan da ka guje mu akan shi yana nan yana jiran ka .
Sannan da kake kiran khadija mara kunya ita ma ka sa mata tsanar ne na babu gaira babu dalili saboda da tafi karfin matar son naka ko may .
Zai yi magana ta kashe wayan ta ta kyale shi ranshi yaji ya baci sosai da maganan hajiya yasan akan Fati take wanan fushin haka dashi to shi may ye laifin shi a ciki.
Hajiya suna gama waya binta ta kira tana tambayan ta ko sunyi waya da khadija tace mama ta kura tana tambaya na ke nace kin tafi zariya an maki rasuwa acan zaki kwana biyu.
Tace oho yanzu yayan ku ya kira waya wai sin hadu da yusuf take fada mai a wurin ta suke jin an min rasuwa don baida kunya har khadija taji abu ya samay ni tana jajantawa amma shi bai ji ba.
Sai kokarin son ya zagi yar mutane yake wai bata da kunya shi waya fishi rashin kunya yanzu shida ya nuna muna ba komai muke a gare shi ba.
Sun gama da binta gulma ya ci binta sai ga kiranta ina shirin kwaciya ya shigo min.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUBayan mun gama waya da ita naji raina ya baci sai a lokacin na gode ma Allah da ban goge number shi ba a wayana kira nayi har sau biyu bai daga ba sai na tura mashi sako masu zafi na kashe wayan.
Don nasan zai gani da safe in ma kwanciya yayi a lokacin haka yasa na danji zafin da nake ji ya rage min da kyat barci ya dauke ni a ranan.
Har na rufe ido sai nayi wayana yana kara na dauka a zatona shine yaga sakona ya kira wayan sai dai ba number daya kirani daya kira dashi bane.
Nace ummhumm ina jin ka naji ance haka ake karba kiran wanda baka sani ba na sheda muryan Yusuf din nace yayana kaine a na dauka wani ne.
Yace nice injin ruwa bai saki jin zazzabi ba dariya nayi nace ai na watsa ruwan zafi a jikina yace good dama na kiraki ne don mutumin ki ya karbi number ki a hannu na nasan zai iya kiranki kada ki biye ma halinshi don Allah don bansan abinda zai kiraki ya fada maki ba koda yake yace akan maganan hajiya mama zai kiraki yaji don Allah , , ,
Na katse shi da fadin ai ya kirani ko har munyi tsiyan shi ya dauka kowa nema yake a gare shi ko yaushe ni kuma na wanke shi tass.
Da karfi naji yace haba don Allah nace wallahi na kwashe komai na fada mai har text din da na tura mai mai zafi yace amma baki kyauta ba wallahi.
Nace saboda may zai mun hadi yace khadija kin san kuwa kece mukee son kizama weapon din mu wurin yakan buzuwa nan gaba.
Don Allah ki dinga sausautar harshen ki gare shi nace wa ni ni ina ruwa da shi da zan zama muku makami a gare shi da buzuwan shi.
Dariya yayi yace ke ko ke dashi khadija ke da komai da zaki yakar muna buzuwa don kin cancanci yin hakan.
Ni din yayana yace kwarai kuwa kauna na sai dai idan mun hadu zan maki bayani yadda zaki gane nace to shike nan tunda haka ka fada yace bani na fada ba umurni nima aka bani kan hakan .
Yace sai dai idan mun hadu din zan maki bayanin komai nace Allah ya kaimu ina saurarenka da haka muka yi sallama dashi ya barni da tulin tunane a zuciyana.
Da safe zarah ce take buga min kofa jin bugun kofan na tashi na bude daki tana tsaye kofan dakin nawa ganin tana son shigowa na bata hanya ta shiga daga ciki.
Tambaya na tayi ko da safe zan fita nace ai kemakin sani yanzu haka shiri nakeyi kada in makara take cewa dani zata fita amma wai za a kawo mata sako shine take son in karba.
Nace zarah fitan kuma zakiyi yanzu tayi dan guntun tsaki tana fadin eh wani friend dina zaiyi tafiya nake son inje muyi sallama dashi.
Zarah ba zaki wankan ki fada ki zauna ki abinda iyayyenn mu suka kawo mu yi ba wanan dabiar da kika dauko bai da amfani gare ki nan gaba.
Ta dan yi murmushi ta nufi wurin da taga na aje plate din abin ci da tukunya tana bude bayan ta bude ta dago tana dariya tace an fada maki yadda bakin san wayen kai ba haka kowa yake yanzu da anganki kamar may wayayen kai .
Nace in dai irin wanan wayen wane kada Allah ya nufe ni da yin shi ina neman tsarin Allah ga irin wanan dabian naku Allah kuma ya shirye ku ku gane gaskiya.
Ta juya ta debi arish a plate ta zauna ta fara ci ni kuma ina ta shirina nace kiyi ki gama gada ki makarar dani anan don banson in makara.
Tayi murmushi tana kai abinci a bakin ta sai da ta hade tace wanan halin naki na ina kika fito karatu ina zaki karatu sai ke khadija.
Khady look at you me kika rasa ke kanki jarin kanki ne amma kin tsaya kina wahal da kanki haka har kina wani girki tunda safe kamar wata matar aure amma waike nacin karatu sai wahala kike haka.
Wallahi da zaki yarda akwai wanda zan hada ki dashi cikin kwana biyu kiyi clean ke baki daukan misali a kwaina khady da haka nake ?
Amma yanzu gani tunda hanya ya bude min mai na rasa na rayuwa atare da ni amma ke gaki da abin kawo kudi kina ta faman kumshe shi a jikin ki ta fada tana dariyan shakiyanci.
Ni dai ina tsaye ina mata kallon mamaki da huduban shedan da take min har kuryan dakina ta dauka nasihan ta ya na shigana ne ganin yadda na tsaya ina kallon ta.
Tace ina son ki fahimci wani abu tsarin rayuwa yanzu ya canza ki shigo kawai a dama dake yarinya.
Nace cikin murmushi zarah baki fance ni batsarin rayuwa ta daban yake da naki ban sanya ma zuciyana kwadayi ko son jin dadi a ko wani irin yanayi ba don haka kada kiyi tsammanin guntun huduban ki zaiyi tasiri a raina .
Ni da kika ganin nan ina da mutunci na kuma nasan ciwon kaina dana iyayyena kada kiyi tsammanin kananan kwarin da kike bi zasu iya rudana da wani abu.
Shi jin dadi lokaci indan lokaci yayi sai inji amma ba ta hanyar wullakata kai yadda kukeyi din nan ba kema idan da zakiji sharata da kin watsar da wanan rayuwan ki rungumi abinda ya kawo ki Abuja.
Su kansu mazan da kuke bi aida karatun suke amfana yanzu bance maki ban saurayi ko rayuwa ba sai dai in gajarce maki ni indan zanyi mai tsabta da sanin ciwon kai zanyi amma bana kwanan gida irin naku ba.
Baki zarah ta tabe min tana dariya ta saba da nasihana kullun wanda ita a ganin ta ni har yanzu ban waye ba ban san ciwon kaina ba bansan ta kan duniya ba kuma.
Nace keyi dariya amma ni idan zan faso gari ba irin wa yan nan kanana kwari masu gurbata rayuwa zan tsaya dububa ba sai wanda ya san kanshi da mutuncin kanshi.
Ta mike bayan ta gama ci dama ina magana ina kallon agogona ne kada in makara tace ina son ki fahince ni a yanzu ba a samun irin wa yan nan mazan da kike hasashe kinga ko zaki shawa wuya wurin neman su.
A naki ganin ke nan zarah amma muna nan dake zakice na fada maki watarana ta miko min key din ta nace kenan yauma till down zakiyi tace yo may za a fasa kuma.
Ta fita na rufo kofana muka fito tare da ita a titi muka raba hanya tana neman lift ni kuma na nufi cikin makaranta ina mamakin wanan rayuwa da zarah ta daukan ma kanta.
Itama yar minna ce kama na dalilin haduwan mu ke nan da ita don ko a minnan ba unguwa daya muke ba su suna zama a cancaga ne ni kuma muna tsakiyan gari.
Kasancewar mu yan gari daya yasa muka zama kamar yan uwa da ita da farko halin ta mai kyaune kafin idon ta ya bude da bin mazan abuja.
Sai lokacin muka raba hannu da ita amma hakan baisa mun daina kula junan mu ba kamar baya sai dai ban taba yarda naci abinda take samuwa ba daga wurin yawon banzanta ba.
Tun abin na damun ta har yazo ya daina damun ta ta daina ba sai wanan da iyayyen ta suka kulla suka aiko mata yanzun tana ganin tafi karfin shi ita shine ta kawo min inyi amfani dashi.
Tun asuba yake tayar da ita ta tashi tayi sallah amma tana kwance tana barcin ta har yagaji yatayar da ita da karfin tsiya ta zauna tana mustsukan ido alaman barcin bai isheta ba har lokacin yana ganin ta tashine yasa shi fita daga dakin azaton shi zata tashi tayi sallah.
Ya fita zuwa dakin motsa jikin shi da yakeyi duk safe inda kuma yake aje wasu kayan amfanin shi jiya anan yabar wayan shi yana canji ya je ya kwanta yana tunanen rashin son ibadan da batayi.
Ya gama komai na motsa jiki da yakanyi da safe ya wuce zuwa inda wayan shi yake jone ya dauko din ka idan shine sai takwas yake bude waya da safe.
Budan wayan yasa sakon da suka taru mai shigowa ya gane su wanda farko budewa nawa ne ya shigo da farkon.
Mamaki yayi don ba suna sai lamba ga dogon sako kuma da maishi ya turo mashi kamar kada ya karanta tunda baisan mai sakon ba sai kuma wata zuciya tace dashi karanta kaji mana abinda sakon ya kumsa kila mai amfani ne gare ka.
Fara karanta sakon ne yaji ranshi ya baci don ya fahinci inda sakon ya fito don ganin farkon rubutun nawa kamar haka
Mijin buzuwa a zaton ka zaka iya rabani da hajiya mamane ko ka zubar min da mutucina da take gani kayi kuskure wallahi kuma kayi karya don bakina da naka ban fada ma hajiya mama tana gida an mata rasuwa ba.
Ga wanda yasan mutuncinta yasan darajan ta na fadawa shida ya tambaye ni ko ina da labarin su bakai da buzuwa wace bata da daraja da galihu tasa ka zubar da matan ka da yayan ka da kowa naka kana ganin tsohuwar buzuwa tana maka rudi da huduban shedan kullun.
Kai bari ma kaji wallahi wanan buzuwar ta zubar ma da kima da komai naka a idon duniya tunda kiri kiri ta mai dakai mijin hajiya.
Ga mutum har mutum amma baida ta cewa saboda mace macen kuma buzuwa wace bata san Allah how dear you kaida mace bata bari ka zauna dako matar sunnan ka har kake da bakin yi mun hadi a wurin mama, , , ,
Jikin shi har rawa yakeyi da yake karata text din kasa kai kashen rubutun daki ya nufa da sauri da zuman ya shiga yai wanka ya fita ya samu Yusuf shida yaja mashi rene da wullakanci wurin yar karamar yarinya harta iya turo mashi text din banza haka.
Sai yayi magani na a garin sai yasa na raina kaina may nike dashi may nake takama dashi da zan iya yimai cin fuska haka ina aibanta shi shi da matar shi.
Waya ya fada min maganan da sukayi da hajiyan su hajiyan ne zata fada min kowa komai dai may nene sai ya rena min wayo sai na gane banda wayo yau a garin nan duk inda na shige sai ya tononi a cikin garin nan yayi min wulkanci
Sai dai yana shiga dakin su kuma sai bacin ran nashi ya karu ganin Nafisa kwance tana barcin ta hankali kwace rashi ne ya kara baci ya tuna abinda nace a text dina.
Bai san lokacin da ya isa wurin ta yakai mata mugun maka a tsakar bayan ta ba ta mike firgigit tana fadin Samad may nayi maka ?
Tsawa ya daka mata yace wanan abin zai hada ni dake ke sai yaushe ne zaki rike ibada a zuciyar ki ne yaja tsuki ya shige wanka.
Da sauri ya watsa ya fito ranan ya fito bai wani dauki dogon lokaci ba ya shirya ya fita daga gidan koda ta fito ta samu baya gidan.
Tun a mota ya kira Yusuf yana fadin kana inane yanzu?
Gani gidana ya bashi amsa OK kajirani ganin zuwa yanzu gidan yace eh mamaki Yusuf yaji yana tunanen mai zai kawo Samad gidan shi wanan lokacin haka.
Don ka idar shine sai takwas yake fitowa ko takwas da rabi ware hannu yayi alaman shi ya sani ya mike ya shiga wanka kada yai mashi girshi.
Yana shiri ya sake bugo mai waya gashi kofa gidan shi ya fito ya karasa ya fito ya samay shi don ko driver bai fito dashi ba Yusuf din na gani haka ya rufo gidan nashi ya fito ya samay shi.
Anan ya bude mai mota ya shiga yarufe sai ya dauki hanya batare da yasan inda zasu nufa ba sai yaga ya miki mashi wayan shi duban wayan yake da mamaki yake fadin na maye wanan kuma ?
Ka duba mana cewa fuska a daure ya karbi wayan ya fara karantawa a hankali yana sake murmushi ya gaba yana mika mai wayan yace kai amma wanan yarinyar takai jaruma wallahi haduwan zai zama abin shaawa ga mai kallo.
May ne kace yanzun kai baka ga abin jin haushi ba a nan yace ban gani ba sai ma wani abin da na hango na daban tsakanin ka da beauty din.
Yau sai nanu namata ita ba kowa bane a garin nan sai na wullakanta ta a garin nan dariya yayi sosai yace da kaima kan ka wallahi da ka tozarta kan kuwa.
Wai kaiko kaga yadda kukai balain dacewa da yarinyar nan kuwa wallahi ni abin naku burgeni yake yi idan kuna yi har wani dadi nake ji.
May kake nufi ne wai yace abinda idona ya hango min mana a kai saidai fatan alheri amma zancen ka ci mata mutunci bai taso ba ko kaje ka tozartata duk ba wanan a tsakanin ku ko kamanta da hikimar hajiya na hada ka da wanan yarinyar ne ko kana nufin kai baka gane hakan ba.
To bari kaji Khadija itace zata iya fitar dakai daga zargin da ake maka na cewa Nafisa ta gama dakai da cewan da ake saboda ita ka kasa zama da Fati.
Akan wani dalili zata fitar dani ta yaya din zata fitar dani yace muje zuwa nan gaba zaka sani idan lokacin hakan yayi yanzo ina zamu ne kadauko ni tunda safe haka.
Wurin ta zamu in gwada mata ita din ba kowa bace ya kwashe mai da dariya yace ta zama kowan ke nan tunda har zaka iya biye ma shirmay ta na mata.
Bai kara magana ba sai juya kan motar yayi zuwa office din su ya shige bai tsaya jiran Yusuf din ba.
Anan malam musa driver ya tsayar dashi yana fadin yana da magana dashi na siri da yake son suyi a tsakanin su yace da malam sani din wani abu ya faru ne yace eh to sai dai maganan nason siri gaskiya yace dashi babu damuwa kasa may ni a gida da yamma idan mun tashi.
Ga haka suka bar zancen da malam sani din sai dai ya barshi da tunane a zuciyar shi ko akan may yake bukatan kebewa dashi bai sani ba ya san dai abune mai muhinmanci sosai.
Shiko gogan acikin office maganan da sukayi da Yusuf ne yake ta mashi yawo arai wai zata zama mai garkuwa a kan matsalan shi da Fati da Nafisa