Showing 138001 words to 141000 words out of 142410 words
a sayo maku kada tazo nan ta takura.
Dariya nayi nace da kin hutar da kanki don maryam suna masu kudi ne kawai amma bata da matsalan komai wallahi komai da kika san muna ci tana son shi.
Allah ya kawo ta lafiya nace amin daga haka had barci ya dauke ni nayi mafalkin ga mutane sun taru ina kuka haka yasa na kasa barci har safe nakai a hakan.
Haka na tashi da safe a cikin damuwa ina tsoron in fadi wani abu mumuna ya faru dani da gari ya karasa wayewa nace da anty zan fita bakin titi in ba da sadaka.
Bata tsaya tambaya na ba na fita zuwa titin in da nayi saa na hadu da wata mata mabukayi tana neman abinda zataci da yaran ta na bata dubu biyu tana min addua na juyo zuwa gida.
Ban yi nisa ba ina karyo kwanan unguwar mu tun daga nesa na gane A A tafe a cikin kayan motsa jiki yana judging shi da su mutum biyu a bayan shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUKawar da kaina nayi gefe kamar ban ganshi ba ko ban san shi ba karfin gudun ya rage ya dinga sarsarfa zuwa wurina yayin da ni kuma nake sauri in shige get din gidan Ya Amina din.
Ke ji mana yace bai juyo ba sai saurin da nakeyi na kara harda dan gudu nashige ciki tsayawa yayi ya rike west din shi da hannun shi biyu yana dan murmushi.
Yadda na shigo gidan kamar wacce aka koro yasa Ya Amina fadin ke lafiyan ki kuwa nace ina waigen kofan shigowa lafiya sauri nake na bar wayana daki.
Ajiyan zuciya ta sauke ta kalli kofan sai ta juyo ta kalli inda na shiga ta tabe baki na dade a ciki zaune kafin in fito danaji shiru.
Wanan kaaton da soja yaje daya fi mai yya more karfin shi a can nace ina dagawa wanka nayi na fito na shirya na fito falo.
Na samu yaAmina bata falon sai gata ta fito daga uwar dakin ta tana fadin zan dan shiga gidan su mommy akwai aikin da zamuyi da safe nan kin san ance ka rama alheri ga mai maka.
Dana haifi Na,ima mutanen nan baki ga irin alheri da sukai min ba wallahi banda abin basu in ba ta haka zan maryar masu da alherin su ba gare ni.
Adawo lafiya nace mata ina lafewa saman kujera tare da danna wayana ta juyo tana fadin idan ban fito da wuri ba sai ki dora girkin abinda zamuci da rana kada bakuwan ki tazo ta samu ba abinci.
A kwai komai a kitchen da zaki buka wanda babu ki buga min waya ko ki fita ki samu nan bakin layi sai kin dawo nace da ita tafice daga gidan.
Ban dade ba barci mai nauyi ya dauke ni a guri firgigit na tashi daga zaune don mafalkin hajiya mama da nayi ta sani gaba tana min murmushi.
Firgigita na falka daidai lokacin da ta mika hannu zata share min hawayen dake bin fuska na ina mamakin wanan mafalkin da nake yi tsakanin jiya da yau.
Na dade zaune a gurin kafin in mike in shiga kitchen ban ankara ba ashe har shadayan rana ya gwauta ban sani ba a gurguje na dora muna girki ina yi ina duban time.
Wayana naji yana ruri daga falon inda nasa chagi da sauri na nufi gurin maryam ne a layin na dauka ba ko sallama naji tana fadin wani unguwa zan ce a kawo ni nace GRA na fada mata sunan layin mu.
Isowan ta yayi daidai da gama girki na na fito na tare ta a waje muka rungumay juna muna dariya tare da shigewa ciki sai bin gidan takeyi da kallo.
Falo muka shiga na karbi jakkanta nakai dakina da na gyara na dawo falin ina dariya tambaya na tayi ina ya Amina nace humm kin san sune kan buki tun safe ta shiga wai aiki a family house din su AA.
Nikan na matsu in san wanan uwar gidan nashi abin tausayi na kallo ta nace may abin tausayi a ciki an fada maki tana cikin wani hali ne ?
Khadija labarin dasu Binta suka bamu nata ne ai matar abin tausayi ne wallahi malama kice dama gulma ya kawo ki ba taya zainab murna ba.
Sannan ita fa Fatin nan halin tane haka shiyasa mutane suke mata kallon abin tausayi tana da sanyi hali da rashin nuna kulawa ga abu shiyasa mutane ke fadi haka.
Amma ni ina ganin lafiya kalau take da mijin ta yanzu don ban kara jin wani maganan haushi ya faru ba koda yake idan ma ya faru ni ina zan sani.
Mikewa nayi na shiga kitchen na fito mata da abinda zata ci mun dade muna hira har bayan azahar muka mike zuwa sallah.
Ina idarwa wayana na karan kira ya shigo min na dauka da sauri Zainab ce a layin gaisawa mukayi take fadin khady har yanzu baki shigo ba mana bamu shirya komai ba fa ke ake jira.
Nace gani nan da maryam ta iso dazun tana hutawa ne amma mai zai sa sai nazo kuyi duk abinda kuka ga ya dace mana zainab.
Look indan ba zaki zo ba ni ganin nan zuwa dayani in gaida maryam da zuwa don binta sun fita sai kin zo din nace Allah ya gani yanzu kunyan shiga gidan su nakeyi.
Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai gasu tare da Binta sun shigo da murna suna taron maryam din nace ga gandoki muje buki ta iso daga ina fata mata kawai tace gata nan zuwa ai.
Wayan zainab ne yayi kara ta dauka da murmushi tana mikewa wurin da muke din Binta tace ango yayi kira ke nan dariya nayi nace au shine ake gudun muji yadda ake soyewan ta dan waigo tana fadin wallahi yayana ne ai ba wani soyewan da muke yi ke dai.
Munafuncin banza sai ki fada masu su da basu sani ba nikan nasan komai ai yanzun tana dauka yake tambayan ta tana inane haka waya ke ta ringing bata dauka ba?
Tace nazo wurin kawar mune Khadija da tazo nan makwabtan mu ba nisa damu murmushi yayi yace khadijan na kusa ne ki bata waya tace eh sai gata tazo tana miko min wayan.
Yayana ashe kwanan nan zakayi wuf da kawata gaskiya munyi murna sosai Allah ya sa albarka ga alamarin.
Ameen khadija Allah yasa ayi namu da naku a lokaci daya ya fadi da sauri nace dani dawa kuma ai ni ban ko tsayar da miji ba balle aje ga zancen aure .
A yadda muke magana dashi yasa dukan su zuba min ido a cikin tuhuma sai kuma ga maryam tace kice ina gaida shi ina taya shi murna.
Ga mayam tana tayaka murnan samun zukekiya kamar zainab na fada cikin zolaya yace haba yaushe tazo nace yau din nan ina fada mata jiya tace da ita za, ayi komai shine ta taso yau aba maryam din waya yace.
A lokacin da nake mika wa maryam waya binta tace wai tsaya nifa ban gane ba ?
Dama kun san shi ne ko may maryam ta karbi wayan tana fadin yaya Yusuf ashe wani abin arziki ya samu kuma munyi murana sosai wallahi.
Yace ya gode ta mika wa zainab wayan ta zainab din ta juya tana make murya muka sa mata dariya wai tsaya don Allah dama kun san yaya Yusuf ne khadija ?
Mun san shi mana farin sani kuwa kallon da tati min ne yasa na gyara zancen da fadin ai a sanadin ku ne muka san shi kin manta ne.
Zainab ne ta juyo tana fadin wai yana waje yana jiran mu mu fito gaskiya something is fishing here don ina mamaki har da gidan ku yaya Yusuf wai ya sani.
A yadda nasan yaya Yusuf bamai yawan magana ba ne da zai san ku haka farat daya dariyan da maryam keyi ne yasa ta mayar da hankalin ta gare ta.
Mikewa mukayi zuwa wajen inda yace yake a waje bakin get muka samay shi ya fito daga motar shi gaidashi muka fara yi muna tayashi murna.
Yace in Allah ya yarda khadija na fada maki da naku za ayi bukin mu nace don Allah yayana kabar zancen nan wai dawa zaka hada nine halan.
Koma da waye kin fi kowa sani don yanzu lokaci yayi da kowa zai sani na gaji da wanan wasan boyar naku maryam tace ashe ka gane su yaya ?
Maganan mu ya daure ma su Binta kai nace cikin daure fuska don Allah yayana abar zancen nan anan kada kasa in koma yau Abuja.
Yace an gama ama watarana ai dole kowa zai sani nace wai asan may da kake ta fadin haka yace ai na bar zancen tunda baki son matana ta sani ko ?
May kuka shirya zakuyi ne goben nayi saurin cewa ba wani bidia zamuyi mai yawa ba kawai dan get together zamu da kawayen mu su ma su sheda.
A ina zakuyi ke nan binta tayi tsagal tace yaya a kama muna holl a gamji kawai muje can mu cashe da sauri nace a, a wallahi nan dai kusa zamu samu wani gida muyi event din mu wanan ai kya jira har aure yazo.
Zainab tace ga gidan yayan mu nan ai ya ishe mu muyi komai don ko falon gidan kunga babba ne sai dai in ba zai bari ba kun san shi da rashin son hayaniya.
Cabdi akan may zai hanamu shi da matar shi tayi buki na banza ma a ranan fa Yusuf yace to shike nan kunji madam ta gama maga dole ko zai yarda da hakan.
Balle ma ai bazai hanaku yi ba a gidan sai ka fada mai da kanka Binta tace yace kedai ki bar zancen tunda kin ji khadija tayi magana ai an gama.
Yayi muna sallama yace zai tafi idan munyi list din abinda muke so sai mu turo mai amma ga wanan ya ciro kudi a motar shi yana miko min wai mu fara amfani dashi.
Kai na kada nace a a yayana kudin nan sunyi yawa wallahi bafa wani abu mai yawa zamuyi ba a wurin just friends din mune zamu hada su tayamu murna.
Binta tayi saurin mika hannu tana karban kudin wai din may zance sunyi yawa inda wani ma a karo.
Murmushi yayi yana fadin khadija dama nasan halin ki ba karba zakiyi ba amma ita kaunar nan nawa da tasan dadi kashin kudi kinga ta karbe da sauri ai.
Duk muka sa dariya ya wuce ya barmu a gurin nan gardama ya kaure muna akan abinda zamuyi sai zainab tace ba fa wanan ba shi yayan mu yasan gidan shi zamuyi event din gobe ?
Maryam tace ai mashi magana mana aji ko zai bari indan bai bari ai da wurin yi da yawa bashi kadai ke da gida ba khadija baki san halin yayan mu bane da masifa.
Amma mu gwada kiran shi mu gani yanzu da sauri binta tace wa zaiyi magana idan mun kirashi din maryam tace a ba khadija tayi.
Kira Binta tayi ta miko min wayan kafin in magana kamar ba zai dauka ba sai can aka daga yace wake magana ?
Malam gidan ka muke son aro gobe zamu danyi get together ne da kawayen mu na engament din Zainab yace kuna da hankali kuwa ?
May zakuyi wa wasa ko kun manta matar shi mutuwa tayi kada ko fara gigin yin wanan abin na fada maku wai ma wake magana ne ya tambaya.
Nan sani ba nace na kashe wayan da sauri Binta tace ke zaki ja muna masifan shi ne baki san shi bane wallahi .
Maryam tace yanzu yaya ke nan don maganan yaya AA gaskiya ne fa tunda mutuwa matar shi tayi binta tace humm ummm wallahi sai munyi shekara nawa da mutuwar matan shi yanzu.
Zainab tace mommy zamu fadawa ita kadai ne zatace ayi ya yarda ayi don kun san hajiyan mu ba zatai magana ba don haka muje wurin ta kawai.
Da sauri nace wa nikan sai kun dawo maji yadda kukayi amma nikan gaskiya ban iya zuwa wurin mommy kan wanan magana.
A take Zainab ta nuna min bataji dadin haka ba don nine hope din ta yanzu kuma nace ban zuwa dole na yarda muje wurin mommy din .
Mun koma ciki na dan gyara jikina muka fito muka tunkari gidan nasu a dakin mommy muka yada zango bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan sai dai bamu je aurin hajiya mama ba sai mun fito.
Ni da maryam a kasa muka zube muna gaida mommy cikin fara,a take amsa muna tare da tambayan mu munzo lafiya ?
Ta kalli maryam tace wanan ne kuka zo asibiti ranan tare ko nace itace mommy tace yarinyar nada kirki wallahi ku yi hakkuri da junan ku kun ji nace to mommy mun gode.
Binta ce ta fara mata bayanin abinda ke tafe damu mommy tace shiko dai abinda ba a gari daya ake ba may zai sa ya hanaku yin farin ciki ai wanan farin ciki ne ga kowa.
Ya barku kawai kuyi abin ku tunda ba wani abu can zakuyi ba dan taruwa ne kawai mommy ayi addu,a binta ta fada wani addua kuma binta abinda za a tara yan mata.
Kada ki kawo min wanan karyan naki yanzu dai ku bari zan ganshi in mashi magana kafin goben ya kyale ku kuyi abinku tunda shima yusuf din baiki ba.
Zamu daga mi bar dakin mommy tace khadija an kusa gama karatun ko nace mommy da dan saura kadan insha Allahu.
To ai mu mun matsu ki karasa ansan abinda ake ciki don na matsu in kai ga sarakuwa irin ki sai dai ki matsa da addu, a fa don Nafisa ba wasa.
Mun fito wurin mommy dakin hajiya mama muka nufa muka gaida ita da fara,a take fadin ikon Allah ashe Allah ya nufa ayi dake sai gashi kin zo garin.
Dan dariya nayi ciki ciki nace wallahi mama basu fada min ba zuwa kawai nayi duba ya Amina don na dade ban zo ba tace ina zakizo wanan karatun naku mai wuyan sha, ani Allah yasa dai a gama lafiya nace amin mama nagode.
Muka shige dakin su Binta suna ta faman buga ma abokan su waya kan event din mu dai muna gefe muna jin su.
Hajiya mama ne ta kwala ma binta kira tafita tadan jima sai gata ta dawo tana fadin ga su yaya AA nan sun shigo yanzu kuzo ku gaida su.
Nace daga inda nake kwance ku tafi kawai ni ina nan ba inda zanje sai kun dawo su fita sai ga zainab wai mama tace muzo mu gaisa da yayan su.
Dole na fito muka gaida su na tsaya can baya daga kofa maryam ne ta dan fita fili sosai yace kinzo lafiya maryam ?
Ai ba ita daya tazo ba ga diyana nan a bayan ta ai ina kun san ta khadija itama jiya tazo daga Abujan kasan acen take karatun ta.
Mama wanan diyar taki mara kunya ce baki ga inda ta tsaya tana gaida mutane ba daga nesa gaisuwan ma sai da kika roka mana tazo.
A a ban yarda ba kai kadai naji ka fadi haka ga khadija amma khadija ai tana da tarbiya ko dan hararan shi nayi daga inda nake lokacin da yake maganan.
Mommy ce tashigo dakin inda shigowanta baisa mama ta fasa maganan ta ba tace kai ai kowa ba daidai yake ba saboda murdaden halin ka.
Mommy tace may kuma yayi yanzu da shigowan shi yaya tace haka kawai zai saka min diya a gaba daga gaida shi wai bata da kunya.
Ina shi kunyan ne gare shi yaya ki barsu kawai don sun fi kusa idan kika shiga maganan nan kunya zakiyi .
Au to haka zancen yake to Allah ya tabbatar muna da alheri da nafi kowa farin ciki da hakan kuwa da sauri nace mama ba haka zancen yake ba mugune shi kawai nama rasa may zance dasu a wurin.
Dariya mommy sukayi tace na fada maki barsu kawai su gama boye boyen su kyaji may ke nan watarana.
Mommy ai ba sai watarana ba gashi sun nuna a gaban ku ai yanzu kowa ya sani haka da kika gansu muke fama dasu wallahi ko maryam ?
Yana tambayan maryam din tace mama kyale su haka suke ko yaushe ba a shiga tsakanin su don ko an shiga zasu dawo su shirya ba a sani ba.
Ji nayi wurin bai dauka na da sauri na koma ciki ina jin wani bacin rai tare dani ban san yaya suka kwashe a falon ba na daiji binta ta shigo tana murna wai an mashi magana yace muyi.
Suna murnan su nikan raina a bace yake da maryam da yusuf har da mommy data biye masu din.
Sai da kyat na saita kaina na dan koma normal kada a fahince ni bamu