Showing 51001 words to 54000 words out of 142410 words
Bai mata magana ba haka kuma bai saki fuskan shi ba har lokacin tace nayi mamakin zuwan ka gida a wanan lokacin bayan ba haka muka saba zuwa ba.
Yace banda daman zuwa ganin mahaifana sai mun tsara dake ko may ba haka nake nufi ba gani nayi ya kamata ace nasan da zuwan ka tun wuri ai.
Sai da ya soma tafiya yace yanzu na canza sallon tafiya ne ba dole bane sai naje dake indan zan tafi don kema idan zaki gida ba binki nakeyi ba ai.
Cikin yanayi mamaki tasha gaban shi tace may kake nufi da fadin ka canza tsarin ka yanzu yace komai ma don na fahinci baki kaunar yan uwana yanzu da ci gabana.
Na fahinci sakin fuskan da nake maki ne ya jawo min abubuwa da dama daga gare ki na koma nine mata kece miji a yanzu gidan nan.
Don zan tafi wurin iyayyena har kike tayar da jijiyoyin wuya wai jayi masu sayayya ke nawa nake baki idan tafiya gida ya kama ki.
Kuka ta sa mashi wai yayi mata gori kan abinda yake mata ita da iyayyen ta kallon ta kawai yayi ya fara kakabe gadon shi inda yake son ya kwanta cikin kuna rai.
Ta dawo bakin gadon bayan ya gama kakabewa ya kwanta ta zauna a bakin gadon tashi gaba tana kukan munafunci.
Sai da kukan ya ishe ne ya juyo gare ta yana fadin kukan ya isheni hakana in zaki gyara ki gyara dan gaba tace haba Samad may kake nufi da maganan da ka fada min.
Kana nufin ina hanaka yiwa yan uwanka alheri ke nan yace baki hanawa kikayi bakin ciki ga abinda zan dan kai masu a gaban kowa.
Tace kowa su wa baidai Yusuf bane gurin da sauran drivobin ka yace su ba mutane bane komai tace to kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allahu.
Nasan ban kyauta raina ne ya baci a lokacin bayin kaina bane ka sani son kane ya rufe min zuciya na.
Yadan dubeta yace don kina sona sai ki hanani yima iyayyena da iyalina alheri ko may kai min afuwa ba zan sake ba tana fitar da hawaye gwanin ban tausayi.
Nace naji ya wuce kuma kada ki sake yi min haka don ranki zai baci dani idan kin sake ina son in kwanta in huta ne haka yasa ta mike ta fita jiki a sabule da ita.
Mamaki take a zuciyar ta yau ita Samad ke da bakin fada mata haka da bakin shi babu shayi ko tsoron da yake gwada mata.
Tace zaka san koni waye idan na kulleka a wuri daya a karkshin ikona ba yan uwanka ba har iyayyenka da iyalin ka sai abinda nace maka a kan su.
Kwantawa yayi don ya huta amma ya kasa samun sukuni a lokacin saboda damuwa dayayi mashi yawa ga tunanen zuwa ya duba khadija ya damay shi ga kuma Nafisa da ta fita tana kuka yanzu a dakin.
Mun gama exam na dawo hostel tun jiya da na shigo ba fita ko kofan gida ba ina jin ya gidan nata parkin suna fita daya bayan daya a gidan.
Kwaciya na gyara ina jan tsoki haka kawai an tsayar dani don wani bukatan da ban sani ba an bata min lokaci na ga banza.
Da yanzu ina gida don tun da yamman jiya naso wucewa tunda ba wanj mugun nisa ke ga Abuja zuwa minna ba ko goma na dare zan iya tafiya gida idan na so.
Wayana yayi tsuwa ban yi saurin dagawa ba sai da na lalabo na dauka naga ya Aminace take kirana a lokacin .
Dauka nayi ina mata sallama bayan mun gaisa da ita ne take tambaya na kama hanya karya nayi mata nace ban gama ba sai gobe zan gama sai in tafi tace Allah ya kaimu.
Na tambaye ta ina su boy yaron ta tace sun shiga wurin mommy ta aike su can.
Nace ke dai da mommy sai Allah anty tace suna da kirkine mutanen akwaisu da so jamma,a sosai wallahi.
Dan murmushi nayi kawai tace ah ai na manta in fada maki mutumin ki fa yazo gida ya kawo wa iyayyen shi da matar shi alheri da yan uwa kowa yana ta mamakin sauyi da aka gani a gare shi.
Nace ah haba dai don Allah tace wallahi baki ga irin alherin da ya kawo masu bane khadija nima da na shiga gidan mommy take nuna min .
Nace shidai ya sani ai kila buzuwan matar shi ta barshi ya kawo masu ne tace bai ma zo da ita ba ai shika dai yazo wanan karon.
Nace kila shiyasa ya samu kawo masu alheri tace waya sani khadija Allah dai ya kyau ni ba kishiya nake gudu ba irin wa yan nan matan dake juye kan miji a lokaci daya ka rasa gane kan mijinka ne abin tsoro ai.
Nace da sauri No no ya Amina don Allah kada ki hada yaya da wanan mutumin don ba halin su daya ba ma tace saboda may shima ba namiji bane irin sa nace na fada maki ba daya suke ba ya Amina.
Tace Allah ya sauwaka nace amin tare da kawar da zancen nace idan naje gida may zance ma daddy tace nima ai zanzo kafin ku koma school idan anty hauwa ta haifu.
Don ina ganin tun last month ake sa ran haihuwan ta gata ta wuce lokacin ta nace ashe cikin ya tsufa haka ne muna gida zata haihu ke nan tace insha Allahu.
Mun gama waya mun kashe na ci gaba da tunanen hiran mu da ya Amina din murmushi nayi nace baki san komai ba yar uwa.
Zaki sha mamaki idan kin san nice mai shirya wanan plain din haka murmushi na dan sake nace ashe nima shu,umar kaina ne ban sani ba.
Kiran Yusuf ne ya shigo min yana tambayan ina ina nace hostel a takaice yace akwai mutane ne nace akwai su amma kadan yace gashi nan zuwa yanzu sai kazo nace dashi ya kashe wayan.
Maryam ta dawo daga wurin gyaran kai ta samay ni akwace take fadin ai na dauka barci kike yi nace na fara ya Amina ta tayar dani ga waya.
Nan nake bata labari hiran ya Amina dani tayi dariya tana bude tukuyan abincin mu tace bata san ke ce mai director ba yanzu na zuciyar shi.
Da sauri nace zuciyar shi fa kikace tace uhumm wai ke baki sani ba idan baso a tsakanin ku kina nufin zai ko kalle ki ne ma.
Shiru nayi ban bata amsa ba sai da ta zauna nace wai ke da tunanen ki ke nan akai mu tace bani ba kowa ma saboda kun dace dashi.
Nace baki ji ba ke nan don babu ta ida muka dace dashi wallahi ni ina ni ina wanan miskilin mara dariya da fara,a.
Zaiyi dariya wata rana sai kinyi mamaki zakice nace maki watarana amma fa idan kinyi nasaran canza shi din don kan ki ne zaki taimaka ba wani ba.
Nace a a gyara maganan ki dai maryam don ba gaskiya zuciyar ki take fada maki ba tayi murmushi ta soma cin abincin ta.
Yusuf ya kirani yace fito gani a waje ban bata lokaci ba na mike saboda na matsu inji abinda yasa suka tsayar dani garin har wanan lokaci.
Dan simple makeup nayi na fito a can nesa da mu na hango motar su a fake na karasa inda yake da sallama na gareshi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUA zoto na shika dai ne a cikin motar sai da na isa kusa ne naga sabanin haka ashe tare suke da dan baiwa yana zaune kamar kullun ya aza Laptop a cinyar shi yana dubawa.
A sanyaye nake nace dasu sannu ku da zuwa yaya hanya yaya mutanen gida kun barsu lafiya ?
Yusuf yace ke ce African ta gidi khadija tambaya haka a jere lokaci guda wani zamu fara amsa maki daga cikin wanda kika jero muna a lokaci daya ?
Nace amsa daya ya wadata gareni wanda nake fatan alheri a cikin shi yace to duka amsan ki alheri ne don duk Alhamdullahi gaba daya kowa na lafiya kuma hanya lafiya.
Murmushi nayi sai yace baki gaisa da oga na ba kuma aboki na dan satan kallon shi nayi nace ai bugu daya nayi maku gaba daya nashi gaisuwan daban ne kuma ?
Yace oga ne fa khadija kema kin sani ai dole gaisuwan manya ya zama daban da na saura nace a wurin ka yake daban don kace shi din ogan ka ne amma ni a wuri na duk daya kuke gare ni.
Eh to kya iya fadin haka yanzu amma dai nasan nan gaba bazaki fadi hakan ba dariya nayi nace saboda may kana ganin zanyi aiki a karkashin shi ne ko may , ?
In wanan kake tunane may zai kai lawya aiki a FCDI kuma sai in dai bukatan haka yataso mu a bukace mu a wurin muyi aikin mu mu bar wurin.
A a a ashe da babban lauya muke bamu sani ba haka nace cikin murmushi lawyer to be insha Allah ba ya juya gare shi yace kai kaji ashe da Barister muke bamu sani ba shike nan yanzu muyi abin mu ba kwabo muna da mai kare mu.
Nace wa ni ai nice ma zan tsaya sai na kama masu cinye ma gwaunati kudin filayen ta in daure mutum inga tsiyan kwashe kudi ana tura ma yan Niger suna cinyewa dama yan Nigeria kuke ba sai in maku sausaci a kai.
Sai lokacin ya dan sake murmushi yace ashe har kin fara hada evendece a kaina ban sani ba nace tun yaushe na fara hadawa zan tura babban kotun mu.
Dariya sukayi sosai gaba dayan su yace dama karatun da kike yi ke nan ashe nace kwarai don kama manyan bariyin gwaunati ba.
Yace ashe aiki ya ganki magana yake ba tare da ya dago kai ya kalle ni ba sai dakilan laptop da yake yi hankali kwance da gani abin ya zama mai jiki hakan.
Yusuf yace wai kin san ban taba sanin abinda kike karantawa bs ke nan sai yanzu na dan natsu nace shi nake karantawa ai Allah ya bada saa yace nace amin nagode.
Still bai dago kai ba yace wace zata kama ka kakewa addua haka kuma yace ai addua ya zama dole muyi mata shi fadi take yi kawai mutum ya taba kama kanshi da laifi ne.
To wai ni fa kun barni a cikin duhu yakamata ace yanzu ina gida kun tsayar dani a nan aikin oga ne haka khadija bai son ki bar garin nan yanzu ne yasa ya tsayar dake.
Kallon shi nayi sai faman aikin shi yake yi hankali a kwance bai dago ya kalle mu ba nace ni ai ba yar Niger bane da yake tarawa a gidan shi kamar almajirai.
Dama titi yake bi yana ba mabukata alheri da zai fi samun lada ga Allah da wanan ciyar da mayaudaran dayake yi zai fi mai Alheri sosai.
Rufe Laptop yayi tare da fadin wai ke maye matsalan ki da yan Niger ne cikin rashin sani nayi subul da baka nace kishi mana lokaci daya suka ce kishi nace wallahi.
Murmushi naga yayi yana lumshe ido Yusuf ko sai kallo na yake yana dariya shi ya bude idon shi yace kishi yana jijiga kai nace na kasata ba .
Sun zo suna kwashe muna dukiya suna raya kasan su da sunan aure nan ko barayi ne na zaune Yusuf yace a a kada ki gyara zancen kuma mana khadija yar mama.
Nace a in ba kishin kasata ba kishin may zanyi kuma Yusuf yace gashi a gaban ki kishin dai kike yi amma kada ki gyara kice kuma wai kasan ki.
Ikon Allah akan may zanyi kishin shi shi mijina ne ko wani nawa ba hadin kifi da kaska ai Yusuf yace waye kifin waye kasa yanzu.
Yace itace kaskan mana nine kifin ba ita ta lake min ba kana gani kuwa ido na waro waje nace ni din yace Yes kamar zanyi magana sai kuma na kalle su tare da fadin sai anjiman ku.
Ina juyawa da sauri Yusuf yake kirana ban tsaya ba ya fito daga motan ya sha gabana shiko yana ciki sai murmushi yake ba abinda ke mai yawo a rai sai kallaman kishin da nace.
Ya samu na tsaya yace ke ko daga wasa zaki mai da abin wani magana nace ina nuna shi bakiji may ya fada min bane yanzu wai ina like mai.
Yace ai wasa ne ko shima yasan baki like mai shiyasa ya juye maganan yace ke ce mai like mai yanzun bamu muka zo wuri ki ba wake nan kaskan a cikin mu ?
Bude motar yayi ya fito yana mika tare da nufo inda muke tsaye yana fadin wai may kaskan nan take fadi ne haka ka tsaya wani bata magana can.
Yusuf yace kin gani ba har ya kai ga fitowa a mota don ki yace ai ita ma ta fito don ni ko, kallon shi nayi na kauda kai na gefe daya.
Ya karasa takowa zuwa inda nake yace wai yaushe ne zaki tafi in samu in huta da wanan matsalar taki.
Nace nice yar matsalar yace gashi ko kina muns ko yanzu kai na girgiza kawai nace ba komai baka da laifi fito war maryam ya tsayar damu daga maganan .
Ta fito tana gaishe tare da masu yaya hanya da mutanen gida yusuf yace suna gaida ku tace kuna nan da miss barister ne yace wallahi kuwa kauna a kwai rigima ai.
Tace da kyat na shawo kan ta ta tsaya da yanzu tana gida baku samay ta ba Yusuf yace kin kyauta shi dai tunda ta fito bai mata magana ba ko gaisuwan da tayi bai karba ta ba sai ma daure fuska da ya kara yi yanzu.
Yaushe ne zata wuce Yusuf ya tambayi maryam tace bataki ko yanzu wanan ta bar gari ba ta isa da dare da sauri shi yayi magana da fadin No bako a cikin daren nan ba kan gaskiya.
Nace may ye a hanya da zaka ce ba da daren nan ba zan isa ko lafiya yace No sai gobe za a zo a kai ki har gida.
Nace a a kada ku wahal da kan ku motar kasuwa
nake shiga yanzun ma shi zan bi in Allah ya yarda bani kadai ba kowa dake wurin yayi mamakin maganan shi da yace.
Ba zan yardan ba ki bi motar haya ke kadai idan wani abu yaje ya samay ki fa a hanya ki sani a wani hali don haka ki shirya gobe zan turo malam sani ya kaiki gida da safe.
Ido gaba dayan mu muka tsura mashi da yake maganan kamar wani uba da yar shi ko miji da matar shi yadda ya hakikance yana fada a hasale dani.
Zan yi magana Yusuf yace ya gama yanke hukunci akai Allah ya kai mu gobe din ai yau da gobe duk na Allah ne ko amma ki bi motar haya wani abu yaje ya samar mashi ke a hanya kuma ?
Maryam ne tayi dariya nikan hararan shi nayi mai dani gida yace a dake Yusuf yace to bissimillah muje in sauke ka ko ya juya ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba kuma.
Sai Yusuf ne ya tsaya yana ce muna yar mama ni zan tafi ban sani ba ko zamu sake haduwa ga wanan ayi ma kanne tsara ba dashi ya mika ma maryam sai kuma ya sake ciro wasu yana miko min wai na karba.
Kai na girgiza mai nace daka barshi don ni ina da kudin mota a hannu na tsaraba kuma ai kowa yasan makaran ta naje basu expecting din tsaraba a wuri na.
Yace daga wanan time din sai ki fara masu tsaraba baki san tsaraba ko ga babba yana da muhinmanci ba ne mutuka kauna na.
Dole ya mika min na karba tare da mashi godiya har dan Baiwa ya fara mashi horn a mota yace Allah sada mu da alherin sa nace amin yaya Yusuf ya juya ya tafi sai da suka shige muka koma ciki.
Maryam bata shigo daki ba don haka ni kadai na shiga na adana kudin tare da cire rigar da nasaka a jikina.
Can ta shigo ta hada muna abinda zamu ci ina kwance a wurin tunane ya addabe ni a raina har ta gama tace inzo muci don na idar da sallah a lokaci.
Sai da muka zauna cin abincin ne muka fara hira da ita take tuna min maganan shi da yayi dazun tare da fadin guy din ya hadu wallahi
Daure fuska nayi nace a naki ganin kike ganin haka amma ni mai zaisa in sawa raina abinda nasan ba mai yuyuwa bane gare ni ai ko a mafalki wallahi.
Ko dai baki san ko shi waye bane yasa kike wanan magana haka shima dai Yusuf ai yanayi ne don wasa kawai amma ba gaskiya bane so kima daina wanan zancen