Showing 141001 words to 142410 words out of 142410 words

Chapter 48 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

50

Middle Ads

bar gidan ba sai dare so sai muka koma gida tare da ya Amina da dawowan su ke nan daga gidan jere.
Wanka nayi na kwanta don raina a bace yake da kowa nayi dana sanin zuwan danayi kadunan a yau da nake ganin ana son kula min sheri wurin matan da nake jin nauyin su.
Shi kuma munafukin bai fada masu ba gaskiya bane dan ya kullamin sheri kawai a wurin su komay yake nufi oho zan gani idan ana kula abinda ba alaka ne a cikin sa.
Da safe tun safe su zainab suna gidan mu ana sha,anin buki a cikin gida mu muna shirin namu event din.
Unguwar yacika da baki nakusa dana nesa ko ina mutum ya duba motane na masu zuwa daurin aure a haka muka ratso tarun mazan har kafana yana hardewa.
Kamar ance in daga kai can na hangoshi tsakiyan mutane daga nesa muka watsa ma juna harara mun shiga ciki zakace a gidan ne ake buki don jama, a da suka cika gidan.
Nan na kara yarda ba karamin alaka ke tsakan gidajen biyu ba mun zauna ke nan massage ya shigo a wayana na dauka ina dubawa.
Kina da hankali kuwa da zaki ratso wanan taron maza haka da dan gyale karami.
Haushi naji har cikin raina na mayar mashi da amsa ina ruwan ka da ni ka fara tsare matan ka kafin ka fito sa ido waje.
Yarinyar dani kike wasa ida na kara ganin ki haka a garin nan sai na bata maki rai .
Kaji min mutum da sa idon tsiya kai waye da kake son saka min doka na rubata mashi.
Ya sake rubuto min barin shigo ciki in nuna maki ko ni waye a gaban su mommu da hajiyan mu yanzu.
Ban bashi amsa ba don tsoro ya kamani kada bakina yaja min jin kuya sai hira muke a falon hajiya mama ban yi aune ba sai ganin mutum nayi ya shigo falon.
Da sauri na noke kaina kasa ina hajiyan mu ya tambaya cikin daure fuska take dakin yayi tsit kamar ba kowa a ciki lokacin.
Sai zainab ne tace mai yanzu ta shiga dauko abu a ciki sai gata ta fito yace a hada muna abinci akwai bakin da suka zo daga Abuja yanzu.
Kai babangida shine kaki fada da wuri a cire masu tun farko ai da ko matar ka sai kasa ta aje masu yace ni kaina wai bata aje min ba tace.
Kai wanan irin abu naku damay yayi kama ace ana buki a gidan ku bazaka aje ma mijin ka abinda zaici ba sai ya tambaya mama ta fada cikin bacin rai.
Nan ya fice daga falon na sauke ajiyan zuciya muna zaune kafin wani lokaci an hada masu aka kai ina jin mommy da mama suna ta fadan abinda banji dadin shi ba kan fatin.
Mun dage bukin mu sai washe gari don hidimar bukin da yayi yawa a gidan dole muka dage namu din sai washe gari four na yamma zamuyi inda nasa rai ya wuce a lokacin don Sunday ne dole ya koma aiki na manta akwai hutu Monday da za ayi.
Kamar yadda muka tsara zamuyi four mun gama shiri a cikin dogayen riguna bakake gaba dayan mu sai zainab ne tasaka fari kwal a cikin mu.
Mun gyara wurin dakyau kawaye na zuwa guda guda har wurin ya dan cika mu mata zalla ne a gurin muna gidan Fati ta dawo daga gidan su daukan abu.
Maryam ta zuba mata ido tana kallon ta ina gefe ni kuma ina kallon maryam din bata tsaya ba ta fice ta barmu a gidan .
A falon su ne zamuyi event din so ba wasu maza a gurin sai wanda zai muna dj da aka dauko bayan yan bayane aka fara gudanar da event din gwanin ban shaawa.
Mun sake sosai don mu kadai ne a gidan haka ya bamu daman sakewa yadda muke so a gidan kira ake guda guda mu fito mu taya zainab din murna a fili muna fitowa har akazo kaina na fito na fara takawa kamar ance in daga kai sama tsaye yake da waya a kunnen shi yana saukowa kasa.
Da sauri na rage rawan na fita fiilin suka sa ihun basu yarda ba don time din da ake ba kowa baiyi ba na fita.
Gyaran muryan da yayi daga bayan mu ne yasa kowa dake wurin ya natsu sai da ya fita muka koma abinda mukeyi din wayana naji yana kugi da sauri na ciro a jakkana ina dubawa fito nan waje yace dani.
Sai na basar da sakon naki fita wani sakon ne ya kara shigo min again ki fito ko inzo wuei in samay ki cikin bacin rai na fito cike da rashin mutuncin wanan takuran haka da yake min.
Ina fitowa na duba ban ganshi ba sai naji horn a gabana na gane yana cikin motar shi zaune wurin na nufa na samay shi zaune a motan.
Shigo yace min nace bazan shiga ba nan yayi min nace dashi kai tsaye yace ki shigo tun ban fito ba wallahi ban shiga nace kai tsaye yana fitowa na fara ja da baya baya har nakai jikin wani mota na tsaya.
Ashe karya rashin kunya kike yi may kika rubuto min jiya tsakanin mu bai wuce tako daya ba nace may ka gani ya tako kenan zuwa gare ni binta tafito daga ciki tana kwala min kira.
Da sauri ya ja baya na sauke ajiyan zuciya kirana ta kara yi ya juya a fusace yana cewa da ita stupid wanan kira haka fa kamar makauniya.
Ta juya simi simi zata wuce nace jirani muje Binta yace bace min da gani ta wuce ba ko waige ta shige ciki da sauri ya dawo da kallon shi gare ni da zuman nufo ni na zille da gudu na bar wurin.
Sai gab da magariba muka gama muka kwashe kayan lokacin har ishai yayi kai tsaye gidan ya Amina muka nufa ni da maryam.
Binta mamaki ne ya cika ta ta kasa sakin jikin ta na abinda ta gani yana aukuwa tsakanina da dan uwan nasu sai da sukaje gida ne take fada ma zainab abinda ta gani.
Zainab tace nima naso in fahinci hakan tun ranan da taje waje tayi mai magana a hostel din su amma koma may ye zan binkici yaya yusuf inji ko akwai wani abu a tsakanin na su.
Wai har khadija taban tausayi wallahi ina zata iya da Nafisa anty Fati da take babba yaya ta iya da ita balle khadija da take karama ?
Zainab tace ai abin badaga nan yake ba in fada maki sai ko kiga khadija ta iya zama da ita tsab balle khadija da take da baki.
Magana may naji kuna yi haka baku kwanta ba muryan hajiya mama ne a dakin nasu take tambayan su zainab tace a a magana mukeyi kawai.
Binta tace mama wani abin mamaki na gani yau wallahi yayan mu tare da khadija nagani sun ban mamaki don akwai wani abu a tsakani su nake gani.
Koma may ye a tsakanin su Allah ya tabbatar muna da alheri shi muke fata ga kowan ku yanzu ta fice ta bar masu dakin cikin sanyin jiki.
Kodai dama hajiyan mu tasan da wani abu a tsakanin su ne ga yadda tayi magana yanzu kamar tana da masaniya akan abinda nagani.
Kokarin rungumay khadijan fa naga yanayi sai dai ita khadijan kamar a tsorace take a lokacin kai Binta banda sheri fa.
Au kin dauka karya nake yi ai koma may gobe zan tambayi khadija din don nasan ba zata boye muna komai ba inji Binta.
Zainab tace yau zan tambayi yaya Yusuf idan ya kira ni inji don shi zai san komai akan haka ?
Washegari Mun sha barcin gajiya don haka bamu tashi da wuri ba gashi ina son zuwa hidan kakanin yaran Ya Amina in duba yaran dake can.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login