Showing 132001 words to 135000 words out of 142410 words
fara.
Farin mu ba daya da ita na na fadi a tsiwace shi dai murmushi yayi kawai bai yi dogon magana ba sai Yusuf ne yace dani wai yanzu na fahinci gori motar nan ya bata maki rai sosai fa.
Wallahi ko daya raina bai baci ba don nasan rashin ilimi ne yasa ta fadi haka ba wai tasan ni ko wacece bane don ita halinta ne wanan.
Khadija kina son mota da sauri na dago kai ina kallon shi kamar bashi yayi maganan ba sai kuma na mayar da hankali na gurin yarinyar dake kokarin yayemin gyale dana yafa a kaina.
Yusuf yace ana tambayan ki wai kina son mota ne kai na girgiza nace ina yar tallaka dani ina zanje da mota ita mota ya dama a yanzu har take fankama da hakan.
Kiran sallah azahar aka fara yi Yusuf yace tau ashe har lokaci ya jane haka ban an kara ba zamu tafi da fatan kanwana ta huce ko ?
Murmushi nayi don ban son jan zance ina son fara aiwatar da shiri na akan buzuwa yanzu ina kokarin mika yarinyar gare su tare da fadin .
Sai ko yarinyar ta make a jikina taki zuwa karshe da na matsa da mikata sai tasa muna kuka tana lafewa a jikina.
Yusuf ya juya ya kalle shi tare da fadin yaya ke nan za ayi yace mutafi kawai anjima zan dawo in dauke ta in mai da ita gida.
Bazatai kuka na na tambaya da sauri yace ba gashi kin gani da idon ki ba taki zuwa wurin mu ku shiga da ita don ba gida zan tafi ba dama.
Haka suka ja motar su suka tafi yarinyar kuma bata damu da tafiyan su ba din muka shiga ciki da ita maryam bata nan sai da ta dawo ta samu ina bata indomie dana dafa mata tana ci.
Tambaya na tayi ina na samo yarinya haka diyar AA ne na bata amsa kai tsaye ido waje take kallona da mamaki a ina kika samota kuma ?
Shiya kawo ta na bata amsa in bata wanan in bata wancan har barci ya dauki yarinyar .
Ina da wasu set din ribon a jiye kana na a hankali na kama kan ta ina mata kitso tana barci .
Har na gama bata tashi ba na daura mata ribon din a kowani tukuwa yarinyar ba tashi don yadda nake kama mata kan a hankali.
Wayan shi ne Nafisa ta kira a gigice wai basu ga Banan ba a gida yace kamar ya ba a ganta ba may kike nufi.
Nan ta rikece mashi tana koro mashi bayanin yadda yanyala ta kirata daga gidan buki tana fada mata basu ga yar su ba wai.
Yace maganan banza ke nan duk inda suka kai min yarinya na su fito min da ita kafin in dawo gida ko rayuka ku su baci ya kashe wayan cikin hasala.
Ranan dai nafisa ta kirashi a waya yafi a kirga bai dauka ba kuma bai koma gidan ba kamar yadda suke jiran shi ya dawo duk ta fita hayacin ta yar ta ta bata a gidan.
Yanzu baiji kunyan idon ki ba khadija ya dauko yar shi ya kawo maki yar matar da tayi maki zagin wulakanci a saman hanya.
Wallahi da nice ba zan ko kalli inda yarinyar nan take ba balle ya bar min ita da sunan lalashi duk wanan abin fa sallon ba da hakkuri ne irin na maza.
Shi a dole matar shi ta saba maki ya wani dauko yarta ya kawo maki nan don ya nuna maki ya isa da gidan shi ko may ?
Dariya nayi nace ke ma kin san in dai wanan mutumin ne ba zai taba bani hakkuri ba bakina da nashi ba kuma kawo min yarinyar yayi ba nan .
Sun zo da itane tagani ta lakemin taki yarda su tafi da ita shine yabar ta har anjima zai zo wai ya dauke ta yace .
Tace bakin ji ba may ye na kawo maki ya kina makaranta kina fama da karatun ki ni dai nasan akwai wani abu a bayan wanan abin.
Tashin da yarinyar tayi ne tana kuka hankali na ya tashi na rarashe ta tea na hada mata tare da bata cup cake sai tayi shiru taci gaba da wasan ta.
Sai bayan magariba ya dawo daukan yarinyar ya bugo layina yana fadin gashi ya dawo in fito da yarinyar ya mayar da ita gida.
Tun daga nesa ya kura muna ido yana kallon mu cikin mamaki yadda yarinyar batai min kiuya ba har muka iso gurin tana ganin shi ta washe baki tana dariya.
Sai dai yana tara hannu tazo ta make tare da lafewa saman kafaduna ban san lokacin da murmushi ya subce min ba yace Banan yau fushi kike damu ne a gidan haka ?
Nace kasan yaro kamar kyanwa yake yana son a kyautata mashi ko da yaushe indai zai samu jiki gurin mutum .
Wanan ne kuma bata samu a gurin mu daga ni har uwar ba mazauna gida bane dukkan mu nace kuna daukan alhakin ta gashi babu ruwan ta wallahi.
Dan shafan ta da nakeyi daga tsaye yasa ta koma barci nace kaga tayi barci yanzu lalaba ka maida ita wurin uwar ta tun kan ta tashi tasa rikici.
Banji yace komai ba haka yasa na dago ido ina kallon shi sai naga yana wani lumshe ido yana kallon mu.
Da sauri na kawar da kai daga kallon shi kamar bangan shi ba muryan shi naji yana fadin .
Kun dace da Banan kamar kece uwar ta kenan goyo zai maki kyau sosai fa nace don Allah kakai yarinyar nan gida tun bata tashi tasa rikici ba.
Yace af koran mu kike yi don na fadi gaskiya gaskiya kuma da kama da ita kamar kece mahaifiyar ta fa.
Nace kaidai ka sani da jan magana a bayan idon uwar ta zaka iya fadin komai yanzu .
Tsoron idon uwarta nake ashe nace ai naga zahiri ne ranan don Allah ka karbe don hannuna ya fara tsami da daukan ta.
Miko jikin shi yayi don ya dauki yarinyar numfashin mu ne ya hade a guri daya nayi saurin ja da baya jikina yana rawa rigumay ta yayi a jikin shi yana fadin Thanks for today Banan da baban ta sun gode.
Yana kallon kan yarinyar da ya sha kitso fuskanta ya fito shar da goshin ta saboda kitson da akai mata din yace wayayi mata wanan kitso haka nace gun wa ka kawo ta.
Matsala na dake kenan tambaya a cikin tambaya halin ku na yan Africa leda na miko mai ciki da kayan ciye ciye nace a rika mata wanan idan ta tashi yai min godiya muka rabu yana cikin farin ciki da ya kasa boye wa.
Sai da ya wuce a zuciyana nace ko yaya akayi yazo da wanan yarinyar nan yanzu kuma may zai koma ya fada mata kai halin maza sai su wallahi maganan maryam ne ya dawo min a raina.
Ya na isa gida suna waje bakin get cirko cirko dasu sai da ya gama seta kan sa ya fito da yarinyar a kafadan shi.
Gaba daya suka nufo inda yake nafisa ta mika hannu zata karbi yarinyar ya gwauce ya wuce ta ba tare da yayi mata magana ba.
Sai da ya kwantar da yarinyar dake barci a saman gado ya juyo zai wuce ta tace ashe kaine kafita da yarinyar nan baka fada muna ba.
Ke ki fita min a ido banson maganan banza har kina da bakin tambaya na haka da kikasa kafa kikabar ta agidan tana kuka iidan wani abu ya samay ta fa.
Wallahi kasan su Yanyala na barwa ita amma sai suka bugo min waya suna fada min wai basu ganta ba.
Yace bari kiji akan yarinyar nan zan iya bata muku rai baki daya a gidan nan duk sanda kuka bari haka ya kara faruwa.
Kitson dake kan yarinyar dake barci saman gado take kallo muryan ta ne take tambayan shi a wurin mace kakai ta ke nan wani kallo yayi mata sai lokacin ya tuna da zata iya tambayan shi haka.
Kallon yarinyar yayi da take a kwance shar kamar zaiyi magana sai kuma yaja kafar shi ya wuce zuwa dakin shi.
Zuciyar shi a cunkushe yana jin bacin rai wanka yayi ya fito ya shirya gado ya koma ya kwanta da niyar taba aiki a laptop din shi .
Amma sai yasamu kan shi da jin kasala nan ya fara tunane abinda na fada masu yau tunane ya zurfafa dayi sosai har zuwa daukan yarinyar daje yi da yamman nan.
Ido ya lumshe yana tuna irin yanayin dayaji lokacin da muke hada jiki wurin amsan yarinyar yace a fili khadija khadija yana girgiza kai a hankali.
Bude idon shine yaga Nafisa tsaye tana mashi kallon tuhuma dakyat ta iya daga kafa zuwa wurin da yake kwance tace yaya naga yanayin ka gaba daya ya sauya ne ?
Samad ina kakai min yarinya yau wuni guda ace batai kuka ba nifa wanan abin ya daure min kai.
Gun wa kakai ta baka fada min ba yace muna gidan Yusuf da ita muna aiki shiyasa kika ga ban damu da kiran da kike min ba din tunda nasan yarinyar na wuri na.
Wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da zama a bakin gadon tana fadin sai yanzu hankalina ya kwanta wallahi.
Gobe da safe zan bar gidan nan zamu je gyara ma amarya gida juyowa yayi yana kallon ta tare da tambayan ta wai a wakike cikin wanan bukin ne don naga kin mayar dashi kamar bukin gidan ku .
Ga buki can za a yi a kaduna amma banji kina shirin zuwa ba sai wanan bukin da baki da wani dalili dashi kike maganan shi haka.
Tace bukin wa za ayi a kaduna din idan ma na sani bazan tafi ba wanan kai ya shafa don ni bai shafe ni ba yace haka kika ce tace kwarai kuwa.
Gyara kwanciyan shi yayi ya bata baya tace don kawai za ai bukin kannen Fati zan kwashi kafana in je don ban san ciwon kaina ba ko may ?
Mutanen da basu sona basu kauna na basuki su bude ido suji ance na mutu ba a yau din nan kake son in kusance su.
Ban son Fati ban kaunan ta da duk wani nata don su, , , enough Nafisa ya ishe ki ya isa haka baki zuwa ya isa wanan kalamin ba da Fati kikeyi ba dani kike yi don nima zurian gidan ne ko kin manta ne da hakan ?
A kusan tsatso daya muka fito da Fatin da kike aibantawa haka da yan uwan ta may Fati ta tare maki a duniyan nan da baki kaunar ta haka saboda wani bakin kishi naki can mara dalili.
Matan nan tun shigowan ki gidan nan kika dauki tsanar duniya kika dagwara mata katse shi tayi da fadin muka dai dagwara mata don bani kadai takewa abinda takeyi ba.
Yace matsalan ki daban nawa daban ko may Fati tayi min nimijin tane kuma uban diyan ta zan zauna da ita a ko wani irin hali.
Samad ni kake fada ma kai mijin Fati ne kuma uban diyan ta kake ni kake fadawa haka a gaba yace an fada maki kiyi abinda zakiyi.
Wani shuumi murmushi ta sauke tace dama maza haka kuke don kana takama da wanan dandanin da taima shine har kake ganin ta a mace take yanzu.
Kutawa tayi tafita daga dakin rai a bace ita samad zai kawo wa wani maganan wata matar shi can wai fati wai may yasa shirin ta akoda yaushe yake lalacewa ne idan tayi.
Tasan dai tanayi amma kuma maimakon yayi aiki yadda take so sai komai yazo ya lalace daga baya taki jinin fati da diyan ta a duniyan nan amma mace kamar kaska duk wanan abinda takeyi sai fatin ta dawo a rayuwan samad din.
Tana ganin taje gida tayi aiki akan kowa nashi amma kuma yanzu ta lura asiri bai cika kama samad din ba idan tayi ko tayi bai wani dadewa yana tasiri a jikin shi sai abin ya kare.
Kudi dai bata da matsalan shi ko nawane ta bukata tana samu a gurin samad din yanzu abinda tafi zargi shine mahaifiyar shi take lalata mata aikin ta don haka wanan karon da hajiya mama zata kara don na samad din mai sauki ne.
Don ko yanzu a tafin hannun ta yake don dai sai abinda tace dashi a gidan bai musa mata inba wani lokaci da yakan dan turza mata ba wai shi a dole ga namiji.
Tasha alwashin wanan karon sai taga bayan duk wani mai mata aiki ta bayan fage akan samad din zata raba shi da kowa nasa taga yarda uwan nashi zatayi.
Da haka barci ya dauke ta tana rungumay da yar diyar ta mumunan mafalkin da tayine ya falkan da ita sai gumi take hadawa a dakin duk da sanyin ac dake dakin alokacin.
Wacece wanan macen da tayi mafalki da ita samad din ta ya rike ma hannu yara na binsu a baya kodai don ta kwanta da zancen Fati ne a ranta tayi wana mafalkin haka.
Mace tare da samad din ta kaita kada tana fadin wanan ba gaskiya bane koma may ne gobe zata je wurin malamin ta a duba mata agani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
SEENABUGanin zamu dan huta har kwanaki yasa na yanke shawaran zuwa kaduna wurin Ya Amina in masu hutun dan break din da muka samu a can.
Bayan mun fito daga lectures ne na shigo na fara shirin tafiya kaduna maryam ma da tasa rai a gidan su zamu yi dan break din sai ganin ina shiri takeyi ta tambaye ni nake cewa kaduna zan tafi in duba ya Amina kin san hutun nan ban samu zuwa can ba.
Ranta ya baci amma na bata hakkuri akan wani lokaci ai zan tafi nayi Sa,a ina zuwa na samu mota ta cika saura mutum biyu.
Bamu dade ba motar ta bar tashan motar na da gudu sosai sai dai muna wuce maraba mun dan ba kauyen dage gaba baya kadan motar tamu ta tsaya.
Drivern yayi tsaki yana fitowa daga motar ya fita ya bude gaban motan ya dan taba ya dawo ya tayar taki tashi bude motar yayi yace mu fita daga waje mu sha iska zai duba motar.
Abu wasa wasa muna wurin har hudu na yamma motar bata gyaru ba raina duk ya baci nayi tunane kala kala a wurin tsaye.
Wasu motoci ne guda uku tafe a jere da gudu suka wulga a gaban mu, ina jin mutanen dake cikin motar suna fadin kai jama,a akwai dai motoci a duniyan nan hadadu wallahi duba motocin nan kamar su suka kera kan su don Allah.
Kuran motan da suke magana akai nabi da kallo sai naga motan suna dawowa baya a hankali zuwa inda muke kawar da ido na nayi daga kallon su na mayar da hankali na ga waya.
Muna charting da maryam ina fada mata abinda ya faru damu a hanyar jin muryan masu hiran nayi suna fadin wai Allah yaba wasu duniya duba mutanen cikin motar nan don Allah.
Daidai nan na dago ido na in ga abinda suke magana akai Yusuf ne yake kokarin fitowa daga motar tare da AA a daidai inda sukai parking yana kallon mu.
Yi nayi kamar ban gansu ba na dukar da kaina a kasa ina ba maryam amsa ya karaso yana gaida mutane tare da sallama suka amsa mai a mutunce suma don yadda yazo masu din.
Bayan ya gaisa dasu ne yake tambayan driver motar ce ta samu matsala yace wallahi Alhaji lafiya kalau kuma na fito da ita halin karfe ne kawai.
Wurina ya mayar da hankalinshi yana fadin khadija ina zaki haka a wanan lokacin bamu sani ba kuma ?
Ko kaina ban daga na kalle shi ba nace KD a takaice wata mata da muke mota daya ta dan manyanta matar dama akwai zuba don bakin ta bai huta ba tunda muka tsaya din.
Sai cewa tayi malam hala matar ka ce matar oga nane gashi can a cikin mota zaune tace haba.
Tun shigowan mu nasan yarinyar nan diyar manya ne ko kuma matar wani babba dama ina mamakin abinda ya shigo da ita motar hanya yanayin ta kawai ya nuna min haka.
Dago kai nayi ina kallon matar da mamaki karara a fuskana zan yi magana tace in kina ma Allah kiyi hakkuri kibi mijin ki yarinyar nan kila shiya sa motar tamu tsayawa haka nata tashi ba kin ko san girman tashi (yaji)ga diya mace wurin Allah.
Aiko jin haka sauran mutanen suka sa muna baki a lokaci daya ga abin dariya abin kuma haushi har da drivern suna ta bani hakkuri.
Drivern da kan shi ya dauko jakkata wanda dan karamin traveling bag ne na saka kaya na a ciki dama, driver ya dauka yakai wurin motar tasu.
Hannu Yusuf yasa a aljihun shi yaciro kudi yaba duk mutanen dake wurin dubu bibiyu wai su shiga wani mota