Showing 48001 words to 51000 words out of 142410 words

Chapter 17 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

1002

Middle Ads

fadin abokin nan naka ne ai sai a solo baida mutunci.
Yace kada kice haka Khadija baki fahince shi bane amma abokina mutumin kirki ne wallahi ki bashi dama ku fahinci juna yanzu zai bugo waya godiya yake son yi maki akan taimakon da kikai mashi na bashi shara kuma yabi yaji dadin shawaran ki shine zai maki godiya akai.
Munyi sallama dashi ranan maryam tazo dakina wai a nan zata kwana saboda exam din da zatayi washegari yana da zafi ita kuma tana son tayi karatu a daren ranan.
Muna tsaka ga karatu wayana yayi kara na daga tare da karawa a kunne na muryan shi naji yana tambayana har yanzu baki barci bane.
Karatu mukeyi na bashi amsa yace OK dazun na kiraki in maki godiya kika kashe waya nace ina busy ne a lokacin.
Khadija ya kira sunana amsawa nayi ciki ciki yace please ki bani dama in maki godiya akan abinda kikai min shiru nayi na kasa magana.
Khadija kina jina nace ina jin ka mana sai naji tayi wani kasalalen murmushi yace in tambaye ke zaki ban amsa tsakani da Allah ?
Nace sosai makuwa idan har na sani may zai sa in boye maka tunda ba rike min baki zakayi ba.
Ajiyan zuciya naji ya sauke sai can yace may yasa kike son yawan bata min kina son ganin hasalana ni koda ban tashi hasala ba ?
Kin tsane ni kin ki jini baki kaunar ki ganin a cikin farin ciki why khadija why kika zabi wanan rayuwan a tsakanin mu.
Shiru nayi na kasa magana nauyin shi da kunyanshine suka kamani a lokaci daya na rasa may zance dashi don yadda yake magana bazakace shi din bane mai izza da jiji da kai.
Nasan kin san bawai son soyayya ne a tsakanin mu ba amma kuma kika zabi yin haka a gare ni ki fada min may ke sakina tsana na haka da yawa.
Dan murmushi nayi tare da fadin yaya Abdulsamad ke nan ni nasan babu dingo soyayya ma a tsakani mu tun farko sanan kuma ni ko in so ka ko da so ka ba abinda zai ragaka dashi duk dayane a wurin ka.
Ni dama ba kai na tsana halin ka na tsana da matar ka da bata san mutucin yan uwanka ba har hali ku ya juye iri daya da ita.
A yau in rayuka zai sauya kasan mutucin kan ka dana yan uwanka ka farga ka dawo yadda mahaifan ka suke son ganin ka da yan uwanka ka san darajan su da mutuncin su fiye da kowa.
Amma ni may zai sa na tsane ka kana a matsayin yayana aiko don mama zan so ka zanyi muamula dakai kamar kowa.
Don dama ba kinka nayi bani halin ka dai na tsana bani ba kowa ma zai so ya kulla halaka dakai ta yadda baka zata ba.
Murmushin da naji yayi yasani shiru yace khadija idan nace maki ashiri nake da in caza yanzun zaki yarda koma in ce dake din na canza a sanadiya ki.
Jin shi kawai nakeyi ta yaya ni zan iya canza mutum kamar Abdulsamad a lokaci daya haka.
Muryan shi naji yana fadin kina mamaki abinda na fada ne yanzu yace yes ke khadija kin tunatar dani abinda na manta acikin abinda nake dauka shirmay kukeyi ke da Yusuf a lokacin.
Nace ba abinda mukayi da har zai kawo sauyi gare ka haka da wuri sai dai idan dama Allah ya kaddara tamu din abin zai fito ma.
Kuma ina mai farin ciki da jin haka idan ya kasance gaskiya ne maganar ka da sai nafi kowa farin cikin haka a duniya.
Yace to ki fara farin ciki daga yau don ko kin sa iyayyena sun min abinda suka dade basu min ba a yau don haka khadija ban san ta yaya zan gode maki ba da tunatar dani da ki kayi ga abinda na manta hakki na ne yinsa a baya.
Koda da wasa ko gatse kika fada min wanan magana to ki sani your words inspired me har nakai ga samun kalmar albarka a bakin iyayyena yau abinda na dade baji ba a gun su.
Yau kin dawo min da farin cikin dana rasa da dadewa a tare dani kalman ki na ranan gare ni sun sa na dawo da natsuwana.
Ya kuma fara dawo min da respect da power na ga idon mutane dana rasa a baya wa yanda ya kamata ace komai wuya komai dadi ina tare dasu.
Ba zan iya kwantata maki dadin da naji ba yadda na kasance da yan uwana da abokai kai har ma da makwabta na ayau suna murna da zuwa gare su.
Don haka yazama dole in gode maki please khadija kada kiki fada min gaskiya a duk lokacin da kika ga na kauce ma hanya.
Murmushi nayi nace naji dadi kuma na tayaka murnan dawowa farin cikin ka gare ka don ko yau ranan kace ranan farin cikin ka.
Ka kuma gode ma Allah da bai sa ranan ya kasance ranan nadamar ka bace ya fargar dakai da wuri haka.
Allah ya kars shirya zukatan mu ni zan kashe karatu nakeyi ka tsayar dani don gobe zamu gama exam jibi gida zamu.
Da sauri yace jibi wata rana nace talata inda Allah ya kaimu da safe zan tafi gida don yin hutu a can.
Yace No kada ki tafi don Allah ranan ki jira in dawo akwai abinda nake son in shirya akan tafiyan ki nace Allah sarki dama ka hutar da kan ka don ni a shirye nake yanzun haka.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUBayan gama wayan mu dashi jikina ne yayi sanyi sosai a kan maganganun da yayi sai naji wani iri ba dadi a raina yadda mutum kamar Abdulsamad yake magana da ni haka acikin mutuunci da girmamawa.
Karatun da ban sake komawa gare shi ba ke nan cikin sanyin jiki da tunane barkatai barci ya dauke ni a wurin maryam dai batace dani kala ba a ranan.
Washegari bayan munyi sallah asuba zaune nake saman sallaya na nakasa motsawa abubuwa da yawa ne suke min yawo azuciya na.
Na dauko kura,ani na fara karatu don ka,idane duk safe sai nayi kafin in fita dakina sai dai idan ina cikin lalura a ranan.
Wayana yayi kara ban kula in duba mai kirana ba har sai da nakai karshe sanan na mayar da hankali da wayan da ke neman agaji kuma mai kiran bai fasa kira ba.
Yusuf ne ke kirana akai akai haka mamaki naji don bai taba kirana da safe irin haka ba ga kuma kiran dana gani yayi yawa.
Yasa nace lafiya wanan kiran haka da safe haka na tambayi kaina kiran ne ya kara shigowa again da sauri na dauka don kada ya kara katsewa a lokacin tare da fadin yaya Yusuf lafiya dai.
Naji yace ina kika shiga haka waya nata ringing baki daga ba nace ina zaune karatun kur,ani nake a lokacin yace da kyau yar mama da alama dai ke din babban malama ce hakan na dakyau wallahi.
Tambaya shi nayi lafiya kira yau da safe haka yace ina fa lafiya yar mama ta ruda min ogana kuma abokina nima umurni aka bani akan lallai in kiraki in fada maki don Allah kada ki tafi yau ko gobe ki bari mu shigo abuja gobe.
Katse shi nayi da fadin yaya Yusuf may zan mashi duk abinda nayi kona fada mai da ya faru wanan haka Allah ya kaddara a kan shi.
Sai mu godema Allah da yasa yayi saurin ganewa yasa kuma halin ya dore a gare shi haka kada yayi nadaman mazuru don jiya yakirana wai yana min godiya.
Ni abinda na fahinta shine rashin mai fada mashi gaskiya a tare dashi yadda ya dace yasa buzuwar matar shi ta samu galaba a kan shi haka sosai.
Yanzun kuma na tunar dashi Alhamdullahi tunda ya fahinci gaskiya har yayi niyar gyarawa da kanshi so ni yar barni don Allah ban son matsala ko wani abinda zai jawo ma karatuna matsala.
Dariya naji yayi yace duk mun san da hakan amma ki dan daga muna kafa kijira har mu dawo din please maryam ne ta wafce wayan a hannu na tana fadin insha Allahu zata jira ku dawo yace maryam mun gode da hakan.
Bayan ta kashe wayan na kalle ta nace akan may zan tsaya jiran su maryam ki tuna fa na gama abinda ya shigo dani abuja satin nan iyayyena kuma sun san da haka mai zaisa na kara kwana.
Wanan ba komai bane mai yuyuwa shima so yake ya saka maki da makan mancin abinda kikai mashi idan ya dawo.
Maryam bayi don ya saka min saboda Allah nayi haka tace dole ne tunda yana ganin kin cece shi daga halaka abinda wanan shi bai taba lurar dashi ba.
Don Allah kiyi hakkuri har su dawo din gobe ne fa kawai ba wasu kwana masu tsawo zaki kara ba hakan shiru nayi ban nata amasa ba sai dai zuciyana cike yake da tunanen dalilin da yasa yake son in tsaya sai sun dawo garin zan tafi.
Khadija godiya ya kamata kiyi ga abinda kikayi ya zama alheri gare shi wurin Allah nace nayi maryam kuma na gode ma Allah da haka ya kasance ta sanadina.
Amma maye dalilin shi na son ya tsayar dani wai sai ya dawo zan tafi tunda yasan bashi ke da ikona ba, tace dole akwai dalilin dayasa yace ki dan dakance su din yau da gobe ne fa kawai insha Allahu.
San nan kuma nasan dai dalili daya ne kawai don kin cancanci hakan a gare shi yanzu amma mu bari din har yazo muji.
Kila kuma dai sai kuma ta kama dariya a hasale nace don Allah dai ki bari karki bata min in ce na fasa tsayawan.
Shiru tayi do ganin yanayina daya sauya tasan zan iya abinda na fada din ita kuma bazata so ace na wuce ban jirashi ba.
Haka kawai naji kaina yana sarawa raina yamin mugin baci haka yasa na mike daga wurin na koma saman katifa na, na kwanta ina ci gaba da tunane a raina.

Wayan aminiyar ta takira cikin tashin hankali take mata bayani tana kuka wai samad din ta yana son juya mata baya a lokaci daya .
Don ma idon ta naga ala,amarin shi ne yasa tayi saurin ganewa da wuri ta kare da cewa na shiga uku madam tawa ta samay ne wallahi idan Samad ya fara neman mata ni yaya zanyi.
Tace haba ki kwantar da hankalin ki tunda akwai mafita zamu iya kaishi wurin mai rafanne yasan yadda ya lankwasa muna shi ko uwar shi indai mace ce ya dinga jin ko ganin ta kamar jaba.
Ke dai kada ki nuna mai kin fahince shi lankwasa shi zamu a cikin ruwan sanyi batare da wani hayaniya ba.
Wa ni tun yaushe nagama buda mai wuta wai fa satin nan har kaduna ya shiga ba tare da sani ba kinga ke nan abubuwan sun lalace don samad bai taba shawaran zuwa gida batare dani nabashi shawaran ya tafi ba ko shi sai idan ina da abinyi acan.
Don haka nayi mai kaca kaca kafin yatafi wai ma kin san may wanan zuwan don ki san komai ya fara lalacewa har sayayya yayi masu da zai tafi abinda ban taba gani ba tun zuwa na gidan nan.
Madam tace matsalan ki ke nan Nafisa baki da kwanciyan hankali idan abu yazo maki abishi a sannu sai kinyi hargowan nan naki da kika saba ko yaushe.
Don haka yanzu ki kwanta kamar komai bai faru ba yadda muka saba ta haka zamu fito mashi mu kara kaifin aikin mu a kansa don ba zamuyi sanyi muna kallo Samad ya kubuce muna ba don muna samu a wurin shi sosai.
Don haka ki kwantar da hankalin ki zan shigo gidan naki sai mu tsara yadda zamu shawo kan ala,amarin tace da ita
Madam hankalina baya kwanci don natsani in bude ido inga samad yana mu,amula koda na aiki ko na yan uwantaka da wata mace a duniyan nan musan man matan hausawa yan uwanshi.
Kada ki damu madam tace da ita zanzo gobe sai muyi magana a tsanake amma fa sai kin kwantar da hankalin ki .
Ajiyan zuciya ta sauke tana fadin zanyi kokari hakan suna gama waya ta sake kiran wata wai hajiya Auta da ke mata shige shige a kaduna.
Itama bayani tayi mata na halinda take ciki tace kada ta damu gobe zata je mata zaria wurin malamin da take zuwa tayi mashi bayanin halinda take ciki.
Daga nan kuma gida Niger ta kira tayi ma yar ta wace ke mata shige shige acan bayanin halin da take fuskanta daga Abdulsamad din yanzu tace kada ta damu za,a yi komai yadda ya dace.
Sai lokacin hankalinta ya kwanta don tana ganin kamar har anyi aikin mako don ta yi believe da aikin bokaya da malamanta sosai.
Shawaran da madam ta bata take so ta fara aiwatarwa indan ya dawo daga kadunan inda take sa ran dawowan shi yau din don tasan ba zai wuce kwana daya ba can tunda ba tare suka tafi ba.
Nikan nace Abdulsamad da sauran mazan dake cikin irin halin nan sun shiga uku ga matan su ruwan sha surukule abinci ma haka wurin kwanciya ma hakane Allah ya tsare ya kare ya shirya zukantan mu.
Baidawo ba ranan kamar yadda tayi tsamani abinda ya kara tayar mata da hankali ke nan ta kwana a cikin tashin hankali da damuwa.
Yana gurfane a gaban hajiya mama yana mata sallama zasu tafi inda take zaune akan kujera falon ta .
Akwai wani nauyi da kawaici dake tsakanin shi da mahaifiyar tashi tun farko kansancewar shi dan fari a gurin ta ba wani sakewa ko shakuwa mai yawa a tsakanin su tun farko don kawaici.
Ya dubeta sanan ya sunkuyar da kanshi tare da fadin hajiya mu zamu koma ke nan ta dan dubeshi ta kawar da kai gefe tace.
Allah ya kai lafiya mun gode da hindiman da akaimu Allah ya karams dukiya albarka cikin sauri suke hada baki da Yusuf wurin cewa amin hajiya mungode.
Sai dai kuma rufe bakin su yayi daidai da cewan ta yaya zancen iyali ka kuma har yanzu bamuji shawaran da ka yanke a kai ba kai suka dukar kasa gaba dayan su don basu zaci hajiya zata kawo wanan zancen ba a yanzu.
Taci gaba da fadin babangida kayiwa yarinyar nan adalci da diyan ka don ko sune ne jigon ka watarana kana ganin wanan abinda ka dauko na tallaban wata wace ko haihuwa bakuyi da ita ba zai haifa maka da mai ido gobe.
Yaran nan fa girma suke yi yanzu idan har suka san abinda kake yi ma uwar su kana ganin abin ba zai shafe ruwan ka ba wataran.
Yusuf ne ya kawar da shirun dakin bayan hajiya ta gama magana yace hajiya a dan bamu lokaci kadan don Allah akwai shirin da muke yi komai zai zama daidai bada dadewa ba da yardan Allah.
Sai dai a taya mu da addua da rokon Allah wanda shi muke bukata gare ku yanzu amma nan gaba kowa zai dara in Allah ya yarda.
Allah ya yarda tace dashi bata kara magana ba suka mike suna fadin zasu tafi ta bisu da addua wanda yasa zuciyar shi jin kamar an gafarta mashi a lokacin.
Abinda ya dade bai samu ba daga gare ta idan yazo da fada sukan rabu a gidan rayuka sukan baci sosai.
Tunda suka kama hanya ba wanda ya iya magana a cikin su kowa da abinda yake tunane aranshi saida sukai nisa Yusuf yace wanan abin yayi min dadi matuka.
Yau hajiya ta rakamu da addua tare da fatan alheri a gare mu abinda ta dade batai muna fatan alheri da sakin fuskan da muka samu gareta ba irin yau.
Murmushi yayi tare da kwantar da kan shi saman widow motar yana lumshe idon shi cikin jin wani irin yanayi a jikin shi.
Har suka iso Abuja kamar bai cikin motar gida ya wuce dashi direct inda ya samu gidan kamar yadda ya barshi Nafisa ce da yan uwanta suke yadda suke so su kadai a gidan babu kowa nashi a ciki.
Bayan sun gaisa ne ya haura zuwa sama dakin shi ya fara rage kayan jikin shi don ya dan watsa ruwa ya kwanta ya dauki lokaci a bayin kafin ya fito ya fara saka wasu kaya masu sauki a jikin shi don ya sha iska.
Yana saka kayan Nafisa ta shigo dakin bako sallama tana cewa kun dawo ashe yadan juyo ya kalleta ya mayar da hankali ga abinda yake yi din.
Ba laifi yau ta sa kaya masu dan kyau a jikin ta da alama kila tafita ne ko zata fita din don idan ba fita zatayi ba ita kwalliya bai damay ta ba haka take zama a gida ga kaya nan kamar ya kashe ta kuma bata kyauta wasan dadi.
Cike da sallo ta karaso gare shi ta amshi dan tawul din da yake tsane jiki dashi tana goge mai kai tare da fadin kaje gida hankalin ka ya kwanta ke nan ?

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login