Showing 54001 words to 57000 words out of 142410 words

Chapter 19 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

29

Middle Ads

don Allah.
Wayana dake gefe ne yayi kara ban gani don wayan a silent take lokacin sai maryam ne ta gani take ce kamar kiran ki ake a waya fa sai nayi saurin juya don in duba.
Tashi nayi na dauko wayan mai kiranane yaban mamaki tunda basu dade da barin wuri na ba, daukan wayan nayi na kara a kunne na da sallama yace fito gani waje.
Da mamaki nabi wayan da kallo muryan shi naji yana fadin kin ji abinda nace nace eh maryam na kalla da ta tsareni da idanuwan ta nace a sanyaya wai shine a waje .
Ta kwashe da wanin irin dariya bance da ita kala ba komai ba na zura rigana na fita zuwa jin may ya kawo shi kuma.
Ina fita na hango motan shi dan nisa kadan damu na karasa wurin na samu ya fito da kafa daya a waje yana duba abu a cikin motar na iso wurin.
Ina wuni ya dan juyo ya kalle ni yace zagaya ki shiga dan jin nayi bai zagaya ba kamar yadda ya umurce ni dayi ya sake dagowa bayan ya rufe cabinet din motar yana fadin baki ba ne dole na zagaya kamar yadda ya umurce ni din dayi.
Bayan na shiga naga ya tayar da motar ya bar gurin down hostel din ya halba motan muka hau expresse ba wanda yayi magana a motan sai dai gaba na yana dan fadi don ban san ina muka nufa dashi ba.
Mun dan yi nisa da gurin ya juyo ya kalle ni yana fadin maman ki ita kadai ne a gurin mahaifin ki ?
Mamakin tambayan nashi nayi sai ban iya bashi amsa ba na kawar da kaina gefe yace ina magana kin kyale ni nace akan may zakai mun wanan tambayan haka.
Yace don na isa na tambaya yasa na tambaye ki OK idan kana son sani sai kaje ka gani da idon ka ai.
Kan nen ki nawane dariya tambayan ya bani sosai nace yau ni naga ikon Allah to kannen na biyar ne na bashi amsa tare da kawar da kaina.
Ok kawai yace mukaci gaba da tafiya sai wani katon Plaza muka tsaya ya juyo yana fadin bissimillah fito mu shiga yace.
Ban ki ba na fito muka shiga shagon sai faman gaida shi masu shagon keyi layin kayan sawa muka nufa yana gaba ina bayan shi.
Abin ya ban mamaki yadda naga yana jidan kaya a wurin ya ban mamaki ya koma layin kayan yara sai lokacin ya juyo ya tambaye ni shekarun su nawa ne kallon shi nayi nace a kwai sha uku da sha daya sai takwas da shidda mutum biyu.
Maza da mata ne ya kara tambaya nace maza uku mata biyu sai yaran yaya na biyu yan she kara takwas da shidda maza.
Bayan mun gama wurin takalma muka nufa muka zaba sai layin zanuwa nan ya zaba da dama ya zaba sai ya duba kudi ya gani yake daukan mafi tsada a wurin.
Ya sa yaron shagon ya tura yakai yace a samu trolley masu kyau a saka mai kayan a ciki muka bar shagon hanyar down hostel muka nufa sai lokacin hankalina ya kwanta.
Bayan ya tsaya da motar nayi kokarin budewa naji ta a rufe gam na juyo na dan kalle shi naga shima ni yake kallo a lokacin sai na kawar da kaina gefe daga kallon shi.
Ina son in maki godiya amma kin kasa tsaya ki bani daman yin hakan gare ki nace godiya akan may fa ?
Au baki ma san abinda kikayi ba ke nan nace ban sani ba sai ka fada min iska ya dan furzu daga bakin shi yace OK you can go zamuyi waya idan kin isa ki gaida gida na gode kawai nace na fita.
Banji yace dauki kayan ko wani abu ba nikan na shige abina ina fadin dan rainin wayo kawai dama sayayya zan rakashi shine yake min tambayan bazan a hanya.
Har yasa gaba na faduwa ina zan kai wanan uban kayan danaga ya jida a shagon sai yanzu hankalina ya kwanta.
Koda takwas na safe yayi mun gama shirya komai muna zaman jiran su sai na tafi maryam tace zata wuce itama takwas da wani abu ya bugo min yana fafin in fito da kayana ga mota a waje ana jirana.
Fitowa nayi da kayan maryam ce mai karasa min su a wurin motar har aka gama na rufo kofana na saka key din a jakka ta mukai sallama tace za a zo yanzu a dauke ta ta buga waya gida itama.
Driver ya bude min baya na shiga muka dauki hanyan minna shigan wuri zan ma minna wanan karon ba yadda na saba ba da dare nake shiga garin.
Tunda muka kama hanya barci ya dauke don sanyin motar da lafiyar ta sai faman gudu driver ke shararawa dani ina barci na hankali kwance.
Barci nayi sosai driver naji ya tsaya a wani gari na bude ido fita naga yayi zuwa gun masu sai da manja da doya a hanya ya saya aka loda mashi a motar muka kama hanya kuma.
Tun ina duban waya sai na koma barci abina muryan driver ne ya tayar dani yana fadin hajiya wani unguwa zamu je na bude ido ina kallo har mun isa deport din mai zamu shiga cancaga .
Nace a cikin gari kwagila road, zaka kaini yace ban san wurin ba don ni bakon garin ne nace OK mushiga sai in nuna maka.
Miko min envelop yayi yace oga yace idan mun iso in baki wanan sako wai sai kin shiga gida ki bude nace OK
Mun wuto ina mashi kwatance har kofan gidan mu motar ya tsaya duk da rana ne kowa na zirga zirgan gaban shi nai hana masu zama layin namu zama suna ganin motar ya tsaya kofan mu suka sako ido caa suga waye a motar yazo gidan mu.
Driver ya fito ya bude min motar na fito can naji wani classmates dina na primary yana fadin yau Khadija ce a garin namu.
Murmushi nayi mai nace Faisal mun samay ku lafiya ya karaso muna gaisawa dashi na shiga yace bari ya taimaka min da saka kaya a gida.
Da sallama na shiga inda kanne na dake daki suka fito da gudu taro na suna ihu na rungumay su tsayawa nayi ina kallon kayan da su Fesal ke shigowa dashi gidan namu.
Na kasa furta komai mama ma kallon kayan take da mamaki yaran suka fita sai gasu suna shigowa da ba adadi nace wai duk mu muka zo da wanan kayan haka wai ?
Mama tace waya zo dashi in ba ke ba bagashi kin ga ana shigo dasu ba tare da kayan ki ko kina nufin baki san da su bane wai ?
Wallahi mama ban sani ba sai yanzu nima nake ganin su anan kamar kowa yadda ya gansu mama ta katse nu da cewa motar wa kika shigo ne naji yara na fadin kin zo a mota mai kyau.
Shiru nayi na dukar da kaina ba tare da magana ba har suka gama shigo da kayan mama tace ku dauki ruwa kusa a plate kukai ma mai motar kafin ya tafi.
Yaran suka ruga da gudu suka dauki ruwan leda suka sa a plate suka fita dashi waje kamar yadda mama tace dasu ta wuce tabar ni tsaye a gurin.
Dakina na nufa tare da dan hand bag dina dake rike a hannu na rai na babu dadi ko kadan a tare dani ina fadin yaya wanan mutumin zai min haka ya hadani fada da iyayyena su fara zargina.
Anty khadija wai yace a fada maki zai wuce nace ya kice Allah ya kaishi lafiya nace a hasale yaron ya fita da gudu daga dakin zuwa fada mashi.
Daddy ya shigo gida yana fadin ance baby na ta dawo sai kuma yaja ya tsaya yana kallon kayan da mamaki dake zube a tsakar gida.
Mama tace kai nake jira dama kazo ka gani ko zata fada ma inda kaya ya fito haka don wai ita ma bata sani ba tace kuma su sukazo da kayan.
A sanyayye na dago labule dakin na fito ina fadin daddy sannu da dawo wa mun samay ku lafiya ?
Lafiya baby na sai dai wanan kayan kuma fa ina suka fito haka nace wallahi daddy ban san da su ba sai da muka iso na gansu.
Kamar yaya bakin san dasu ba bake kika zo dasu ba sai nayi kasa da kaina ban yi magana ba kuma kayan yake bi da kallo tiryan tiryan yace ikon Allah.
Shiga ciki ki huta zamuyi magana anji yanzu zan tafi inyi sallah ne ya wuce gurin da buta yake yana dauka ni kuma na sake labule na koma ciki jiki a sanyayye.
Na fada saman gadon dakin duk da kuran da yake ciki don ba gyara ake ba a kai akai tunda ba kowa a cikin sa ina zaune kamal kanina ya dawo shiya fara shigo min da kaya yana min sannu da zuwa.
A dadafe na amsa mai ina kallon akwatinan daya shigo min dasu akwatunan da muka sayo a daren jiya ne dashi inba idona ke min gizo ba.
Watau kayan de na yan gidan mu ne kenan ba wasu ya saya wa ba mikewa nayi don in yo alwala ina shiga banda ki sai na samu ai period dina yazo min ba daman inyi sallah ke nan haka na fito jiki a sabule na aje butan.
Sai mama ta aiko da abinci a kawo min ban kali abincin ba nace kaunata ta aje min a nan kawai ina jiran dawowan daddy daga wurin sallah.
Envelop din da driver yaban na tuna dashi na dauko a cikin jakata na bude a hankali kudine a ciki sabbi ful din su anyi rubutu kamar haka a wrafer farko daddy sai na biyun mama.
Na ukun ne bai rubuta komai ba na shiga uku nace tare da yin nadama da haduwa da shi karo na farko a rayuwana don ban san yadda daddy da mama zasu fahince ni ba.
Nayi dana sanin tsaya jiran shi da yace inyi har na tsaya din sam ban kawo komai a raina ba irin haka don ban taba zaton hakan ba dayayi min.
Muryan daddy daya shigo naji ana gaida shi yasa ni kaduwa bai min magana ba har yaci abincin shi ya fita haka na tashi na gyara dakin tsab na fita da na wankewa na wanke a ranan.
Na dawo na sa kamshi a dakin tare da gyara komai a yadda nake bukatan shi a dakin na koma na zauna wayan maryam ne ya shigo tana tambayana yaya muka isa ?
Nace wai kin san abinda mutumin nan yayi mun kuwa maryam nan dai na koro mata labarin abinda ya faru bayan isowar mu gida da driver.
Tace ikon Allah sakayyan da yai maki ke nan ashe kai lallai mutumin nan yaci sunan sa dan Baiwa ne shi din.
Nace ke maryam har kin samu bakin yabashi ko may may kike son in fada ma iyayyena yanzu don Allah wa zance yake gare ni da yai min wanan kyauta haka.
Tace ki fada masu gaskiya taimakon shi kikayi ya saka maki da alheri haka nace ban sin su san ko shi waye tundai Ya Amina .
Dariya tayi tace komai dadewa ai zata sani ne nace amma fa ba yanzu ba koda zata sani din don ban son ta fasara ni da wata manufa.
Har dai dare banji daddy yayi min magana ba haka yasa na dan sake jiki naji shigowan daddy gidan sai na sha jini jikina a daki ban fito yadda na saba muyi hira ba dashi.
Ina nan kwance wayana yayi kara na dauka kamar yadda na rubuta a sunan shi dan Baiwa shi ya baiyana a wayan.
Kamar ba zan dauka ba dai na daga maimakon inyi magana sai na kama kuka nace may yasa zakai min haka don Allah ?
May kake son in fada ma iyayyena yanzu a kan kayan nan yace daddy na gida nace yana nan yace dama shina ke son magana dashi na kira ki yanzu.
Da sauri nace may zaka fada ma daddy din yace gaisawa nake son muyi dasu in masu bayanin kayan ba shike nan ba.
Yasir na kira nace ya kaiwa daddy waya ana magana dashi ban san yadda sukayi ba a wayan har mama naji suna gaisawa da ita.
Washegari da safe ban tashi da wuri ba don fashin sallah da nakeyi sai da naji motsin daddy ya dawo na fito don in gaida su har lokacin a cikin damuwa nake.
Daddy yana zaune a cikin dan karamin falon mu ga abin karyawa a gaban shi mama tana gefen shi ta motsa mashi kunun da ta aje mai a gaban shi sai kamshi kosai ke tashi a falon.
Daga kofa na tsuguna ina gaida su daddy yace a a baby na shigo mana daga ciki na tashi na karasa shigowa cikin falo har lokacin na kasa sakin jiki dasu kamar kullun.
Daddy yace ya karatu nace daddy Alhamdullah yace babu matsalan komai ko nace daddy ba matsalan komai na fada tare da sunkuyar da kaina kasa.
Ina kokarin mai da hawayen da ya ke shirin silalowa a idona nace daddy sai dai wanan mutumin da ya hado ni da kayan nan wallahi ban san ya sakasu a mota ba sai da muka zo nan taimakon shi nayi shine ya saka min da haka.
Ido duk kan su suka tsura min da nake masu bayanin daddy yana kallona yana yaba hankalina don yasan ba zan boye masu komai dake faruwa ba.
Saboda karya ba halina bane kai tsaye nake fadin gaskiya ga mutum yace dakata khadija kin mashi alheri kin shirya shi da iyayyen shi.
Shi kuma yaji dadin hakan ya saka maki da alheri ko kamar yadda yace na gyada kai nace hakane daddy.
Mama tace ina kika hadu dashi haka khadija nace mama a wurin da aka tura mu aiki ne na hadu dashi ya samu matsala da iyayyen shi da yan uwanshi.
Shine na basu shawara ya nemi shiri da yan uwanshi da mahaifar shi ta hanyar aikata masu alheri daya jaraba hakan sai suka shirya dashi.
Shine yazo yace zai saka min da alheri akan abinda nayi mashi tace khadija shine ya kashe maki wanan uban kudin daga taimako kawai irin haka ?
Nace mama wallahi ni ban san haka zai min ba daga ta Hussai yace ma mama kin san ni ya kamata in dauki zafi akan maganan nan fiye da kowa.
Amma sanin halin ya ta danayi yasa na yarda da bayanin mutumin nan tunda ya rantse min da bata roke shi ba kuma ba da wani manufa yayi mata haka ba.
Yai min bayanin da hankalina ya sa na yarda dashi da ita sai dai yanzu ba yadda muka iya tunda kayan nan sun riga sun shigo gidan nan.
Kiga ba komawa zasu yi ba tunda dai ba rokon shi tayi ba sai dai khadija a gaskiya nayi mamaki da wanan abin don ba karamin kudi ya kashe ba ga kayan abincin nan.
Da sauri nace daddy ba kayan abinci bane kawai har da na sakawa da kudi sune a cikin wanan akwatin da ga gani jiya.
Ido maman mu ta fitar waje tace khadija anya ba dan yankan kai bane kika hadu dashi kada fa watarana ya gama zolayar ki da abinduniya mu nemiki mu rasa.
Dariya maganan ta yaso bani sai na dake nace mama ba dan yankar kai bane don nasan kowa nasa na kuma san matar shi.
Share kawai duk wanan tunanen nayi shi a daren jiya har nafila sai da nayi akai banga wani abin cuta ba daga gare shi sai tarin alheri da na hango ga wanan alamarin.
Shiyasa kika ga ban wani damu ba da hakan sai da ita din ta kula da kanta da mutuncin ta da irin tarbiyar da mukai mata zan sake yin yau na gani don ni kaina abin ya daure min kai sosai.
Mikewa nayi na dauko kudin da kayan na turo zuwa dakin nan na fara fitarwa ina masu bayani yadda kayan suke nima mamakin yawan kayan nake yi a cikin macewa jiki.
Daddy yace aje kayan zamuyi sai na nemi yar uwarki a waya naji shawaranta akai da yadda za ayi da kayan.
Zan dage da rokon Allah don ina jiba jikina kamar akwai alheri ga haduwan khadija da wanan mutumin sai dai mu bar ma Allah sanin shi.
Koda yakira ya Amina yayi mata bayanin abinda na dawo dashi wanan karon tare da fadin ta sake binkice na tsakani na da wanan mutumin don a gono gaskiyar maganan.
Ta kira ni lokacin ina kwance mara na yana damu na da ciwo na dauki wayan ina gaida ita bata tsaya amsawa ba sai cewa tayi Deeda make faruwa ne daddy ya kirani yana fada min wani magana da safen nan.
Shiru nayi sai da ta kara maimaita maganan ta nace cikin kuka wallahi ya Amina ba halina da kuka sani da na canza yanzu.
Nima ban san da kayan nan ba sai da muka shigo garin nan

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login