Showing 108001 words to 111000 words out of 142410 words
din ya kara korawa yake fada mai inda ya fito.
Yace amma kasan may wai ni yar rainin wayon nan zata raina ma hankali wai bata yarda inyi tafiya yanzu ba.
Nafisa ke nan Yusuf ya fada yace ai kaima ka sani wazaiyi wanan haukan idan ba ita ba yusuf yace wai may matar nan ta dauki kanta ne halan ?
Komay ta dauka zan bata mamaki ai kwanannan kuwa don sai ta rena kanta wallahi yusuf yayi saurin fadin baka iyawa ne ai shiya sa take kawo maka raini haka.
Haka kake gani ko kamar yadda kowa yake dauka na ban iya aiwatar da komai akan nafisa yanzu kaima hakan ka dauko ke nan ?
Yusuf yace ai haka din ne yanzu fa don haihuwa kai mata wanan irin sayayan haka bayan wanda ka din ka mata wanda zata fita dashi ga kuma sayayya kamar na hauka da ka da mata daga baya.
Wanan ba komai bane Yusuf har in zatai amfani dashi ni mutum ne mai son in ga iyalina suna shiga suna fita a gida don haka ban jin kyashin kashe ma iyalina na kudi ko nawa ne.
Kasan wanan halin ne ya hadani da Fati bata sawa bata kuma gyarawa amma mutane basu ganewa ida matsalan mu yake da ita.
Mutum ko yaushe baka gane dadin ran shi kullun ya zauna kamar an mashi wani abu babu marmari ko kadan.
Ita nafisa tana maka yadda kake so ne halan da ita da fatin duk jirgi daya ya kwasosu a gidan banbanci dai kace ita nafisa tana sakewa da kai kawai ne.
Yanzu badon yarinyar nan khadija da ta muka saya ma yara da ita fatin kaya ba a kwanaki ina ban dashi tunda suka tafi har yau bakai tunanen ka kara saya masu komai ba.
Yarinya ta dauko saka ka a hanya tanayi hanyar alheri wanan bakar shu,umar ta shiga ta fita yanzu ta raba ka da ita nasan wurin shige shigenta can aka bata labarin khadija din ta sani.
Khadija khadiji Yusuf ka fasan tafiyan mu ba zai zo daidai da wanan yarinyar da take daukan kanta wani tsiya ba.
Yasuf yace yanzu ka gama fadi da bakin ka mace yar kwalisa da iya gyaran gida da jiki kake so a gidan ka.
Daga cikin wanan wani khadija ta rasa a tare da ita ka fada min ya ja iska yace baka san wani abu ba wallahi ranan naje dauko su Binta da dare wurin ta.
Kasan yarinyar nan sai da taso ta rikitani gaba daya Yusuf ya tambaya yace akan may kuma yace wallahi wani shegen shiga tayi tafito waje dashi sai da na kasa kallon ta.
Ban san lokacin da nayi mata fadan haka na ba don wanan shigan sai ya rikita mutum a banza wallahi.
Dariya sosai Yusuf yayi mashi har sai da yaji haushin shi yace malam na fada ma son yarinyar nan kake yi wallahi ka tsaya kana wani noke noke.
Bari garin kallon ruwa wani ya rigaka jefa fatsan shi kana kallo dama ya samu ka fida zuciyar ka ka tsaya kana wani izza haka.
Shiru yayi mai yace bazan bata lokaci na ba kan wanan da yanzu ma take zama mace bata gama mallakan hankalin ta ba.
Zaka sha mamaki wallahi khadijan ne macen da bata san wani abu ba idan bata san komai ba yanzu akan may take fushi damu.
Badon share tan da mukayi bane kwana biyu ta dauki wanan zafin haka kana tunanen ita ma bata fada tarkkn son ka bane ko may ?
Kallon Yusuf din yake yi yace abinda take ma fushi ke nan dama yace don may baza tayi fushi ba kuwa ?
Kwana biyu da yin maganan su ya shirya ya tafi club din su inda zai buga game a can .
Banda labarin yayi tafiya sai dai ina murna a raina sun gaji sun barni ke nan tunda ban kara jin labarin su ba kuma.
Sai dai tunanen su yana nan a zuciya na inda nayi wani sabon saurayi dan kabilar nufe koshi haduwan mu dashi a wani shago ne yana waya da yaren su na Nufe sai ya yar da dan wallet din shi kasa.
Da yaren Nufanci da nake ji don zaman gari daya da nufawa da nakeyi nace dashi da yare kayar da wallet din ka fa.
Ya juyo ya dauka yana min godiya a cikin yare yana fadin (Nufe wayyo ni )nace dashi a a ke yar ina ce ya tambaya a cikin yare nace ni yar Niger ce yace (kiyyo sunayo) nace dashi khadija.
Sai yace Iam mamud by name yana aiki ne a CBN dake nan cikin garin Abuja shi mutumin garin Bidda ne dan murmushi nayi don kamar naga na gida ne da na ganshi.
Nomber na ya tambaya na nuna bazan bashi ba ya matsa min sai na bashi da na sai turaren da nazo saye sai gashi mun hade wurin biya ya biya min nafito zan wuce sai gashi yace in zo ya sauke ni.
Banyarda na bishi ba ashe ya biyo ni baya muna sauka shima ya tsaya yana dariya ya fito daga motar shi nan muka tsaya dashi yake fadi ashe karatu ya kawo ki, nan ke nan.
Murmushi nayi nace may yasa ka biyo ni har nan kuma yace don in san zahirin ki tunda kin ki yarda in dauko ki ni kuma ba zan yarda ki bace min ba ina ganin nayi babban kamun yar garin mu haka.
Tun daga wanan ranan muka hade dashi saboda nacin shi dole nasaba dashi don mutum ne mai saurin sabo da mutane ga baa da iya magana kamar shiyayi kan shi.
Tun ranan da suka fara haduwa da maryam tace yanzu kan kin samu daidai dake khadija haduwa da mamud yasa na manta zacen wani AA can a rai na.
Shiko yana can yayi nasaran tafiya don shi yazo na daya ga gasan da sukayi na wanan lokacin ya samo makuden daloli a wanan tafiyan.
Tsaraba yayo wa iyalin daga ciki Allah ya ciyar dani ya sako min a wani jakka na daban tun daga can ya ware min nawa.
Yusuf yazo gurina inda ya samu mamud yazo sai da ya jira ya wuce yana zaune cikin motar yana kallon yadda nake kwasan dariya daga inda nake tsaye.
Yana mamaki a ranshi yaushe har na hadu da mamud har mukai nisa haka dashi muna irin wanan hira don yaga na sake jiki sosai da mamud din.
Mamud ya wuce sai lokacin ya kirani yana fadin gashi nan tsaye bakin hostel din mu yana jirana waige na fara yi sai dai ban ganshi ya fara fada min irin kayan dake jikina da yadda nake tsaye ina waige waige.
Har na gano shi na iso gare shi abinda ya fara tambaya na shine waye wancan danaga ya tafi yanzu khadija ?
Mamaki nayi da tambayan shi nace wani abu ne halan sai yace a yanda naga kuna hira dashi yasa na sha jinin jikina khadija kada fa yayiwa abokina yankan baya.
Kai na rausaya nace wani abikin ka kuma ke nan yayana yace haba khadija tun yanzu har kina nufin kin manta damu ne.
Nace haba dai abokin ka ai ba saurayina bane kuma bai taba cewa yana so na ba asalima shiba irin mazan da nake so bane.
What har akwai irin mazan da mace ke so ashe sai yau naji wanan a bakin ki nace kowa da abinda ke masa kasani .
Yace kina Nufin bai maki ba shikenan ko ko sai wanan dan kyamazon ne yayi maki da sauri nace kada muyi haka dakai yayana.
Yace Allah ganin shi nayi kamar dan tsurut a motar bai wani cika motar tashi ba sosai nace akwai dai kishi ga maganan ka ke nan , ?
Dole muyi kishin ki khadija don kin cancanci hakan a gare mu saboda ke mace wance ko wani namiji yake fatan ya mallaka a gidan shi.
Nayi dariya tare da fadin kazo da wata magana ta daban ke nan idan kai nayi ma ai shi abokin naka ban mashi ba.
Ko ya taba cewa dakai son na yake da gaskiya kaga yayana mu bar wanan zancen muyi wanda ya kawo ka yanzu yace maganan tana cikin abinda ya kawo ni ai.
Bashi ya kawo ka ba kadai zo ne don duba kanwar ka na sani kuma gani ka ganni ai na kuma gode kwarai da gaske.
Khadija ya kira sunana wanda ya nuna maganan da zaiyi tana da muhinmaci sosai a lokacin gare ni amsawa nayi da naam yaya na.
Yace don Allah ki natsu kiyi abinda ya kawo ki garin nan ki bar biyewa irin mutanen nan da suke zuwa da karya.
Nace yayana ban yarda na tsaya da mamud ba sai da nasan ko shi waye da sauri yace dani shi waye din kika sani.
Dariya nayi nace yanzu dai mu bar maganan don Allah don naga bazaka fahince ni ba a yanzu gaba mayi idan mun hadu.
Yace to shike nan tunda kin hada ni da Allah yanzu ina maryam ina son ganin ta nace ayyah maryam yau taje gida da yamman nan gurin yayanta.
Kasan ita anan garin take da zama yayan nata ne tayi tafiya ta dawo shine taje mata sannu da zuwa yace ashe idan Abdulsamad ya dawo zaku zo tarun shi ke nan ?
Da sauri nace da zai tafi ya sallamay ni ne da zanje tarun shi yace kece baki bashi dama ba don kina fushi dashi yasa bai sallamay ki ba.
Wanan maganan kane kana kokarin gyara shi a wuri na ne kawai wanda ba zai taba gyaruwa ba kuwa.
Murmushi yayi yace zan gano ko waye wanan dake shirin hure maki kunne haka har kike son yin wa kanki zaben tumun dare.
Haka dai mukai ta zubawa dashi har ya kaimu wani lokaci a wurin karshe dai yayi min sallama ya tafi.
Maryam ta dawo daga gida tana fushi dani wai naki zuwa gidan su in gaida yayanta da dawowa nace ba haka na bane maryam kina dai gani ba fita nakeyi ba amma kullun Daddy fadan da yake min ke nan in natsu.
Kada ki damu watarana zan tafi mu gaisa da ita har ma in kwana ba shike nan ba haka yasa ta sake jiki dani tana bani labarin yayan nata da abinda ta dawo dashi wanan tafiyan.
Ta ciro wani dogon riga tabani tace yayan nata ne ta sayo muna ni da ita don yawan labarina da take bata ko yaushe.
Nayi godiya tare da karban lanbata nace zan kirata inyi mata godiya tace mutumin ki baizo bane yau nace yayi tafiya ai da yanzu kin gashi nan..
Yusuf dai yazo bakya nan ya gan mu tare da mamud yake wani maganan robish a kan sa tace saboda Allah nace wallahi ko.
Ai dama na fada maki ina jiye maki ranan da zasu san mamud ya shigo rayuwan ki gashi wanan mamud din da alama baizo ba kamar sai da ya shirya maki .
Nace kin jjiki da wani magana kuma ba wani shirin da yai min sone kawai wallahi ni kuma ya kwanta min sosai a raina.
Tunda bada wasa yazo min ba ke ma kin sani idan yau zan ba mamud baki ya fito a shirye yake da yafito din.
Allah ya zaba muna abinda yafi zama Alheri a gare nace amin yama zaba min din Allah sa albarka ya rage kice.
Kwana hudu da maganar mu na dawo daga class don yanzu karatun mu ya dau zafi sosai muyi nisa mun zama manya a cikin makarantan.
Kwance nake ina hutawa ban cire kaysn da na dawo dasu ba wata ta shigo tana fadin wai ina da baki a wajen hostel nayi mamakin ko suwaye ?
Sai lokacin na tuna wayana a kashe yake tunda zan shiga class na kashe wayan mikewa nayi daga kwancen ina gyara bujen jikina dakyau.
Dinkin wasu material ne na india da mijin ya Amina ya sawo muna tsaraba nasa takalmana flats shoes na saka don ban faye sa takalma mai hill ba.
Wani dan yalalon gyale na yafa akaina duk rabin jikina yana bude na fito don ganin wanda ke nema a wajen.
Motar AA na hango can nesa kadan sun faka shi da Yusuf sai naji gaba na ya fadi ras don ban san may ya kawo su ba nasan kuma Yusuf ya fada mai zancen mamud yanzu haka ?
In bashi ba may zai sa su zo gurin mutumin da bani a gabasa zai zo wurina yau kuma ?
Haka na daure fuska na karasa inda motar tasu take aje cikin daure fuskana na isa inda suke sallama nayi masu irin na addinin musulunci.
Tare da fadin sannun ku da zuwa Yusuf ne ya amsa min sallaman nawa don shi sai wani kallo yayi min ya kawar da kan shi gefe daya.
Nima yi nayi kamar ban ganshi ba a wurin khadija ya kuke ya karatu nace Alhamdullahi kune tafe yanzu ashe yanzu ko na shigo hostel din ina cikin makaranta tunda safe.
Aike ko alhudahuda ya kauce maki ga karatu yanzu kin zama ina zaki karatu, ina kika fito karatu .
Dariya mukayi dukan mu dashi nace sunan da na samu ke nan kuma yanzu yace sunan ki ke nan ai bakiga mutumin ki ya dawo bane banji kin tare shi ba.
Nace ai bansan yayi tafiya balle in gaida shi da dawowa yace a a fa kada muyi haka dake nace to an dawo lafiya ya hanya ya mutanen can ?
Saida ya sauke wani irin sayayan ajiyan zuciya yace Lafiya kalau suna gaidaku ya karatu fa nace Alhamdullahi lafiya.
Allah bada sa a nace amin yace ya naga kin ramay haka may ke damuwan ki kuma ko duk karatun ne haka ?
Nace kila dai idon kane ke ma gizo amma ni ban ji na ramay ba Yusuf yace yaganine ya fada halan dan banufen ki bai fada maki kin ramay ba.
Daidai lokacin Mamud din daya fito office ya biyo ta gurina ya faka motar shi gurin idon ni da Yusuf muka bi motar dashi.
Bai fito ba nima banje gurin shi ba don wullakanci baida kyau Yusuf yace wanan mutumin ya zama maye ana maganan shi sai gashi.
Rai bace ya juya yana kallon shi yace waye wanan din kuma ?
Cikin dakiya na bashi amsa da fadin wanda zan aura ne in sha Allahu nan bada dadewa ba cikin wani yanayi yace What da mamaki nace barin kirashi ya gaida yayye na ai.
Ban tsaya jiran abinda zasu fada ba na wuce wurin mamud nace mashi ga yayyena sun zo yazo ya gaida su da saurin shi ya fito daga motar yazo gurin su su gaisa.
Sun dawo daga tafiya ne suka zo su duba ni ya mika masu hannu da kyat AA, ya bashi hannu suka gaisa dashi yana masu yaya hanya .
Yace khadija zan tafi sai eight zan dawo tunda kina da baki yanzu ya juya tafi ya barmu nan dasu.
Shiru gurin yayi na dan lokaci yusuf ne ya kawar da shirun da fadin khadija wai kina nufin da gaske wanan mutumin zaki aura ko may ?
Kana mamaki ne da ba auren shi zan yi ba zan gabatar maku dashi ne a matsayin ku na yayyena a gaban ku.
Yusuf don Allah ciro mata tsarabanta ka bata mu tafi kar mu bata lokacin mu anan nace ai da kun barshi ai ko ganin ka dawo lafiya yafi tsaraban da zaku kawo min .
Don Allah ciro mata mu tafi don banda lokacin magana yanzu ban son damuwa akwai gajiya a tare dani ka sani.
Fita Yusuf yayi ya bude bayan motar ya fito da wani jakka mai daukan ido yana miko min tare da fadin ga tsaraban ki nan aboki na ya kawo maki daga Italy.
Nayi mamakin ganin wanan katon jakkan yadda ya dauko shi ba tare da matar shi ta gani ba godiya nayi bayan ya aje min jakka a gaba na.
Ya koma mota ya tayar suka tafi na ja jakkan zuwa ciki ina mamaki a raina guri na samu na aje can kuryan dakina ina jiran shigowan maryam dakin.
Sai da ta dawo tana shigowa da jakkan tayi arba tana fadin wanan kuma fa khadija ?
Nace bari ke dai maryam wai tsaraba ne duk wanan kike gani su Yusuf ne suka zo min dashi A A ya dawo daga italy tace bakaji batun ba maye a ciki.
Ban bude ba ina jiran ki dawo mu bude ne da sauri ta karasa wurin tare da jawo jakkan ta fara budewa tana ciro kayan dake ciki.
Dogayen riguna ne a ciki har kala bakwai sai turare da su man shafi da jakka handa bag da sauran tarkacen mata a ciki .
Zip din jakkan taja sai ga set din sarka da yan kune da awarwaro suma a ciki da sauri ta karasa fidowa waje.
Sai da na gyara zama na alokaci don mamaki sai ta kara fida wani agogon hannu na mata mai ruwan gold mai daukan ido shima.
Nauyi da kunyan kaina naji maryam ta dago kai tana kallona