Showing 123001 words to 126000 words out of 142410 words
gyara mata gida don haka take ba gwanan gyara bace ita amma idan ka ganta a waje sai ka dauka ko agidan ta haka take da tsabta.
Ranan sai magariba muka koma koma gida na samu daddy yana fadan rashin dawowan mu da wuri gida.
Muna shiga ya mayar da fadan da yake wa mama akan mu may yasa na bari nakai wanan lokacin ban dawo gida ba idan na fita kada in kara kai dare haka bamu dawo gida ba .
Kaina yana sunkuye a kasa na amsa da toh daddy daga haka ya fita daga gidan rai bace buta na dauka naje na kewaya na dawo na daura alwala don har an sallamay sallah a lokacin.
Sai da na idar da sallah na gaida mama da gida da take dakin ta zaune saman sallaya tana jan tasbaha.
Tace khadija may yasa kuka kai wanan lokacin a waje haka kika bari har magariba yayi maku a waje haka baki san fita a wanan lokacin baida kyau ba.
Mama kuyi hakkuri ba zan kara kai haka ba tsayawa nayi gyara ma ya hauwa gida shine yasa mukai wanan lokacin a can .
Tsuki tayi tana kawar da kanta tare da fadin ita ke nan malalaciya bata iya gyaran gida kullun sai dai ai mata ina amfanin a ganta a waje fes amma a gidan ta baya kalluwa.
Ban san inda ta dauko wanan hakin nata ba nidai nasan na koyar daku abinda ya dace koda kun kama dakin ku zaku iya kulawa dayi amma sai dai kayya bata dauki wanan tarbiyan dana baku ba ita.
Wanka nashiga don inji dadin kwaciya saboda yau na aikatu a gidan yar uwar tawa bayan na fito na tayar da sallah isha,i mama ta turu yaro wai idan na gama inje in debi abinci nace a koshe nake munci abinci gidan ya hauwa kafin mu dawo gida.
Wani yaro ne ya shigo yana sallama da bazan iya sheda muryan yaron ba yana fadin wai ana sallama da khadija a waje.
Da mamaki daga cikin dakin da nake, nake tambayan yaron ko waye yace shima zai wuce ne ya aiko shi don haka bai san ko waye ba.
Jekace dashi tayi barci yaron ya fita can sai gashi ya dawo yana fadi cikin daga murya wai yace kiyi hakkuri kizo minti biyu .
Na fito daga dakin ina fadin bana ce kace dashi nayi barci bane yaron yace na fada mashi yace indawo in fada maki haka.
Zan sake magana mama tace da yaron ya tafi ganin nan zuwa tace kije giga kowaye kin san damay yazo gurin ki wulakamci bai da kyau ina fada maku.
Hijjab na dauko na aza saman rigar dake jikina na fita tun daga nisa na gane motar mamud ta dazun da ya dauke mu dashi.
Mamakin abinda ya kawo shi nake yi da wanda ya nuna mashi gidan namu yazo yana ganina ya fito daga motar zuwa guri na.
Bayan mun gaisa ne yace kin yi mamakin hani na yanzu ko nace kwarai kuwa yace to kibar mamaki don abin jiya na dawo maki dashi.
Da sauri nace meke nan sai da yayi murmyshi yace khadija ke nan So mana da kaunar ki khadija don tun dazun dana ganki na kasa natsuwa tundazu na kasa control din kaina akan ki abin ya dawo min sabo yanzu a raina.
Mamud ke nan abinda ya wuce ai ya riga da ya tafi don ni kuma sai naji yanzu sam baka kwanta min ba a raina.
Da sauri yace saboda may khadija nace halinka bai mun a yanzu don ba zan kara yarda ka sa min miki a zuciya ba.
Kasan ina son ka da farko mamud sai da ka bari na gama yarda dakai ka gudu ka barni babu bayanin komai daga gare ka Allah ya taimake ni, ni ba mai sa abu ga zuciyana bane .
Khadija ba haka na bane wallahi don koda muke tare dake already ina da mata karawa nake son yi sai kuma naje ma iyayyena da maganan ki amma sukaki banin goyon bayan haka don basu son in auri wace ba yaren mu ba.
Kin ga kuma bazanki maganan iyayye na ba sai naji kunyan komawa gare ki in maki bayanin halin da nake ciki .
Katse shi nayi da fadin basu sona yanzu may kadawo yi wuri na kuma yace ina da daman yanzu in zabi wace nake so tunda ina da yaren mu mutum biyu .
Kai na girgiza tare da fadin mamud kasan tun farko ban kika ba kai da kanka ka guje ni yanzun kuma baka da bakin cewa ka dawo gare ni.
Ko banza na farko ba zan shiga inda ba a sona ba sai na biyu yanzu ni mai zai kaini wurin mai mata biyu in ba daukan magana ba.
Dariya yayi a lokacin tare da fadin khadija ke nan watau kin mayar da laifin a gare ni ni daya to naji na dauka kuma ki kwantar da hankalin ki ba a gida daya zan ajeki dasu ba.
Don haka ai min hakkuri muci gaba kamar yadda muke da don son ki yana son ya min illa a rayuwana.
Mamud gaskiya sai dai kayi hakkuri don ba zan iya ba yanzu gidan ka yafi karfi na da sauri yace what ?
Nace yes I mean it don bazan dauki wanan risk din ba da hankali na ina ji ina gani.
Shiru yadan yi na dan wani lokaci kafin ya dago kai yace is ok naji amma zaki yarda ina kawo maki ziyara lokaci lokaci don ban sani ba koda rabo na ciki.
Dadai kayi hakkurin kamar yadda nace dakai zafi kyau don ban son ka dinga wahal da kan ka yace ke kika dauke shi a wahala.
Ni abinda nake so ne na damu dashi don haka ban hakkura ba ki sani nace wanan kuma matsalar kace ni dai na fada ma gaskiya.
Bai dade ba mukayi sallama ya tafi na shigo gida alwala nayi na gabatar da shafa,i da wuturi na samu wuri na kwanta.
Amma ranan sai barci ya gagari idona saboda tunanen dayayi min yawa a lokacin a raina nace ohh ni khadija haka rayuwa zai kasance kuma sai masu mata ne ke zuwa ne mana ni ban san ko may yakawo haka ba gare ni.
Gashi ni kuma banda sha,awan auren namiji mai mata don ban son yawan fitina daga anayi a gidajen masu mata nasan da laifi nane kin kula samari amma yanzu ban san dalilin rashin samun su ba, da haka har barci ya dauke ni ban sani ba.
Matafiya umurah sun sauka lafiya don haka yan uwa da abokan arziki suke shigowa gaida shi gidan shi wanda ba wasu mutane ke zuwa ba don sanin hslin matar gidan da sukayi sai wa yan da ya zama ma dole sai sun zo ke zuwa gaida shi.
Bata san cewa Fati ta koma dakin ta ba sai a bakin wani abokin shi da yazo yana mashi sherin yaushe zai leka can kaduna yaji ance fati na gidan shi yanzu.
Wani kallon mamaki ta aikawa AA din sai da yasha jinin jikin shi don yasan akwai rikici babba yau a tsakanin su dakewa yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da hira da abokin shi.
Sai dai hankalin shi yana gurin ta duk abinda yake yi din bayan tafiyan mutumin tun a falo ta fara tambayan shi Fati ta dawo gidan ka ne baka fada min ba.
Yace ta dawo suna nan gida yanzu haka shewa tayi tare da mikewa tsaye tana fadin haukan banza ke nan yadda ta dawo haka zata koma inda ta fito.
Wanan kuma maganan ki ne don dama ai ba wanda ya kore ta ita da kanta taga daman fita yanzu kuma ta dawo tace ashe ko zamu zuba daku mugani a gidan nan.
Ke ban fa son haukan naki na bazan Fati bakuwa ce a gare ki ko yanzu ne na fara zama da ita zaman ki na nan Abuja ita kuma yanzu bayan shekaru ta zabi zama kaduna ita da diyan ta.
Don haka ban son jaye jayen wani matsala kima da zai kawo muna tashin hankali ba gaira ba dalili haka,
Yana fadin haka ya mike ya haura sama ya barta a falon cike da mamaki halin irin na Nafisa da bata iya boye kishin ta .
Satin shi biyu abuja yana hutawa ya kama hanyan zuwa kaduna gida don ya hana kowa yazo daga can yace yana nan tafe.
Nafisa bata yarda cewa iyayyen shi zai tafi gani ba ta shirya wai tare zasu tafi ba yadda ya iya dole a tare da ita yayi tafiyan.
Tunda suka shiga garin ta hana komai a tsakanin shi da Fati din bayan gaisuwa bata yarda komai ya kara hada suba don ko abinci da Fati ta gama sai cewa nafisa tayi abincin yayi mai nauyi ba zai ci ba.
Suna zaune da dare ta na kokarin hana shi shiga wurin Fati da kissa da iyayi wayan hajiya mama ya shigo mashi nasiha tayi mai sosai wanda ya kashe mai jiki inda take mai tuni da cewa ya tuna hakkin ko wace yana a kanshi do haka ya daure yana ba kowa hakkin ta.
Bayan sun gama waya ne da mahafiyar shi bai wani dauki lokaci taga ya mike da sauri take tambayan shi ina zai tafi kuma.
Kai tsaye yace mata gun Fati zan tafi bata iya boye bacin ranta ba ko kadan tace bai isa ba don tare suka zo fati ta bari idan bai zo da ita ba sai ta kwana dashi.
Yace a garin ku haka akeyi wanan dokan hakan wai Nafisa may kika dauke ni kamar wace ta haife ni zaki dinga bani umurni kai tsaye.
Ba sake kula ta ba ya shige sashen Fatin kamar yadda yayi tsamani hakan ya samay ta sunyi barci da yaranta a saman gadon dakin ta tana saye da kayan data wuni dashi a jikin ta tunda suka zo,
Ya dade tsaye a kansu bata san ya shigo dakin ba sai da ya dan bubuga mata kafa ta falka ina zan kwanta yace da ita kai tsaye dan watsake idon ta takeyi daga nauyin barcin da ya fara kama idon ta din.
Sai can tace dakin ka fa yace Nafisa na cikin dakin kin sani mikewa tayi tana gyara ma yaran kwanciya tare da gyara dan wurin da ta bar mashi ya kwanta.
Kallon ta yayi daga inda yake tsaye yana tambayan ta wai dakin su fa da kika dawo da kwanan su nan kamar ba zata bashi amsa ba sai can tace ban san anan zaka kwana ba ai tare muke kwana tunda ba kowa a gidan.
Tsuki yayi yana hawowa gadon ya takure kan shi a guri daya kamar may kyankyamin dakin amma kin san hakan ba daidai bane nasha fada maki haka kwana da yara a daki daya.
Banza tayi dashi ba wai banzan bane ya sani halin ta daine nakasa da kyaluwa haka take kindis da ita ko yaushe fuska ba fara, a.
Tunda ya samu barci ya dauke shi bai falka ba sai karfe hudu da rabi na asuba da bugun kofar nafisa ke masu ya tayar dashi a firgice.
Tambaya yayi yana zura riga a jikin shi tace itace ya bude kofan ya bude da mamakon ta a fuskan shi yana tambaya lafiya take cewa dashi.
Banan ce bata da lafiya basuyi barci ba kallon yarinyar dake sabale a kafadan ta yayi tare da fadin ta miko mashi ita.
Sai da tayi mai wani kallo tace ka karasa fitowa daga dakin mana murmushiin gefen fuska ya sauke kafin ya fito din muryam Fatine take tambayan make damun yarinyar ne ?
Kada ki soma ki taba min ya ta yanzu ranki ya baci a gidan nan tana fadi tare da watsa mata harara da saida taja jikin ta ta koma daga bayan shi.
Karban yarinyar yayi ya nufi falon kasa da ita suna biye a bayan shi dukan su ruwa ya fara ba yarinyar tasha sosai tare da ajiyan zuciya ta lafe a jikin shi.
Dakin da bai koma ba ke nan ya zauna nan falo da yarinyar data koma barci a jikin shi tana sauke ajiyan zuciya .
Juyawa fati tayi ta koma dakin ta don ta san kadan ne daga cikin sherin Nafisa ko ba yarinya a tsakanin su haka take masu idan zai kwana a dakin Fati din tace bata da lafiya karshe a dakin ta zai kwana.
Do haka ta juya abinta taje ta kwanta bata kara ganin shi ba har rana breakfast din da ta hada mai baci ba wani aka kawo masu daga gidan Auta amiyar Nafisa din.
Haka fati tayi ta hadiyan bakin ciki da wanan zuwan nasu ita da ganin miji sai dare idan zai kwanta zai lalabo ya dawo dakin ya kwanta da safe ya fice kuma ranan nafisa tace itace zatai girki .
Dole Fati ta kyaleta tayi yadda ranta ke so tunda har mijin ma ya biye mata ita yanzu burin ta shine ta zauna a cikin yaranta kawai su girma a tare da ita.
Nafisa bata shiga gaida sarakkanta ba balle suga yar jikan tasu data haifa da dan su sau daya ta shiga gaidasu ana gobe zata koma bata ba kowa yar ta ba suma basu taya zasu dauka ba.
Sai kuma abin ya bata mata rai don yadda ta shirya bata samu yi ba sai taji haushin basar da ita da sukayi takoma fadin wai yanzu har kiyayyan da suke mata ya shafi yar ta jikan su.
Haka ya sa AA yaji haushin abinda sukai mata a ranshi har ya kira mommy yana fada mata abinda sukaiwa Nafisa da yar shi baiji dadin hakan ba.
Don ba halin ya kira mahaifiyar shi ya fada mata yasan kwanan wasa yanzu za a jisu da ita idan ta fara mai fada yasa shi kiran mommy.
Mommy tace dashi babangida kasan halin matar ka fa ta make yarta a jikin ta bata ba kowa ba mune zamu karba tai muna wullakanci amma munyi kuskure gaba zamu gyara insha Allahu.
Bayan kwana hudu suka nada suka koma abuja tun da suka kama hanya ta washe ranta da ya rasa gane mata da suke a kadunan.
Yanzu ko kamar ba ita ba sai hira take jan shi a motar tana faman dariya tana kuma wasa da yar dake zaune a cinyar baban ta din.
Tunda ya dawo ta samu kansa da kyau sai dai abinda bata sani ba yanzu asiri bai faye tasiri ya dauki lokaci a jikin shi don maganin tsarin da malam na zaria ya bashi.
Kuma abokin shi Yusuf bai zauna ba akan shi yana tsaye da alamarin shi haka ma mahaifan shi suna tsaye da mashi addua sosai yanzu.
Yau tunda na dawo daga islamiya nake kwance ba wai don banda lafiya ba sai dai ina jin jikina ba dadi ne ko aikin gida da nake taya mama ban iya tayata yi ba.
Barci nayi sosai a ranan can zuwa rana yaro ya shigo yana fadin ana sallama dani a waje mama ta shigo ta tadani tana fadin min wai ina da bako a waje.
Mikewa nayi da kyar don barcin dake idona na ban tsaya gyara fuskana ba na fita daga gidan haka na mamud ne zaune a motar shi da yaran shi biyu.
Na iso inda suke ina gaida shi bayan motan na bude inda yaran suke zauna kafa na suna waje ina gaidasu tare da tambaya su yaya makaranta.
Kafin yaran su bani amsa ya jefo min tambaya yaya naga fuskan ki haka kuma ko baki da lafiya ne ya tambaya ?
Nace daga barci na tashi yanzu ba tare dana kalle shi ba hannu na mika wa yar karamar yarinya dake saye a cikin uniform din shekk lemo sai yarinyar ta noke taki zuwa.
Tambayar ta nayi yaya sunan ta yace sadika dayan kuma nasir ina taba kafar yarinyar nace zakici biscut ta daga min kai nace to sai kinzo wurina sai ta kara makewa.
Ina zuwa nace dashi cikina koma na hado masu kayan kwalama na yara wanda na dawo dashi muna ci da kanne na nafito rike da leda a hannuna namikawa yaran.
Da sauri suka karba nan dai muka taba dan hira yace zai maida yaran gida daga islamiya ya dauko su mukai sallama ya tafi.
Bayan sun isa ma sai da ya kirani muka taba hira ya kashe wayan tare da fadin zai zo amsa gudane wurina nace na hutar dakai kada ka wahal da kan ka.
Yace to zamuyi waya nace sai najika aiki gida na taya mama ta koma folo tana kallo sai dana gama zuwa dare na shiga daki na samu wayan mamud har six miscall ya kira ban dauka ba.
Kiran layin shi nayi aka dauka ban tsaya sauraren ba nace ina waje ne ina aiki banga kiran ka ba.
Ban karasa magana na ba naji muryan mace tana fadin ke wacece da zaki kira lamban mijina kin san ko waye mamud kuwa ?
To bari kiji daga yau kada ki sake shiga harkan mijina in ba haka ba zan sa ayi maganin ki a garin nan shiru nayi ina sauraren ta sai da ta gama nace.
Ke kuma wacecd a guri