Showing 84001 words to 87000 words out of 142410 words
da shakan isakan dake kadawa a lokacin may hade da kamshi kasa wanda ke nuna dama na son sauka a lokacin.
Ba wani guri mukaje ba sai yawata garin da mukayi kawai ya dawo dani hostel ya aje ba tare da na tsaya ba na shige kai tsaye yaja motar shi ya tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUMommy wayayir mace mai haba haba da jamma irin matan nan ne masu fara,a a fuskan su kuma ita har cikin zuciyar ta haka take da kowa sai dai bata daukan raini.
Abin ta bai rufe mata ido ba tana da ilimi na boko wadattace don duk matan na Abban su Abdulsamad suna da ilimin su ya aure su in ka debe ummi wace iyakarta secondary kadai tayi har hajiya mama mahaifiyar Abdulsamad a gidan shi ta hada karatun ta na NCE wanda dama koyarwa take koda ya aure ta.
Ita anty amarya ma da aikin ta ya auro ta wanda yanzu ta daina duk ya hana matan nasa aiki ya tsaya ga bukatun su kuma.
Mommy ne zaune tare da Abban yana karyawa hajiya mama wadda yaranta ke kira da hajiyan mu ko hajiya mama ta shigo falon.
Akan maganan tafiyan mommy da Abdul din ya bugo yana mata tuni a daren jiya don sun fara tatauna maganan sai Abban bai bada goyon baya akan haka ba.
Yanzu shine ta shigo ayita akaare idan zai yarda shigowan mama yayi daidai da shigowan hajiya ummi da anty Amarya data kira kaffinta shigo.
Sun sami wurin sun zauna tare da fuskantar shi yasa yasan da magana sukazo mai ummi ce ta fara maganan amma sai anty amarya ta dan saka larin kishi a ciki tace ni naga ai ba sai taje ba ya mayar da matar shi mana zaifi sauki.
Ummi da wanan kkaron bata goyi bayan maganan anty amaryan ba tace a a Sadiya tunda har kika ji wanan yaron ya bukaci hakan ai sai mu gode ma Allah da har wanan tunanen yazo mashi a rai.
Ko ba komai ya kamata ace sanin halin ita Nafisa ya kamata wani daga cikin mu yaje ya zauna kamar yadda ya bukata din don ace mai daki shiyasan ida ruwa ke yoyo a dakin.
Nidai kunsan ba lafiya ke gareni ba ba zan iya zuwa ba ita dai suwaiba din ya dace ta tafi don ita dai zainab din ya dace taje ta zauna dasu ta saka ido tunda da iyan bawa zasuyi tafiyan.
Murmushi Abban yayi yace ke nan dai kun gama magana kuna goyon bayan dan ku ko ummi tace ba hakana bane Alhaji.
Ganin dai dacewan hakan mukayi yasa muka goya baya ga maganan shi da kan shi babangidan ya fara tuntubana da wanan zancen da yazo na bashi goyon baya akan haka.
Sai anty amarya ta kalle ta ta rausaya da kanta gefe daya bata kara magana ba har lokacin da Abba ya gama ja ma mommy kunne akan zaman da zatayi a gidan dan nasu.
Suka bar mommy dashi a falon kowa ya kama gaban shi tun wanan ranan mommy ta fara shirin tafiya Abuja gidan Abdulsamad wanda suke kira da babangida kasancewa sunan mahaifin maigidan su ke gare shi.
Abdulsamad bai fada ma Nafisa zuwan mommy ba gidan sai cin karen su ba babbaka suke ita da yan uwanta a gidan banza ta fadi masu kasa gasasa dama haka aladansu yake yar su ta auri mai arziki dangi su kwaso a taru aci arzikin ta.
Mommy bata boye ma Anty Fati zancen tafiyan ta ba inda ta kirata ta fada mata da bakin ta tare da cewa zatayi iya kokarin ta taga ta shirya tsakanin ta da mijin ta kafin ta bar Abuja din.
Allah ya kiyaye hanya Fati tai mata tare da cewa mommy amma fa sai kin hada da hakkuri don kun san Nafisa bata kaunar taga kowa ya rabi yaya Abdulsamad.
Abinda yakai ni shi zanyi idan tayi ba daidai ba dole ne in fada mata gaskiya koda kuwa bata so dariya tayi don sanin halin Nafisa da tayi kamar yunwar cikin ta.
Tsaye yake tsakar falon inda yake umartan masu aikin da ya shigo dasu da su gyara part din Fati yana masu kwatance yadda yake son gyaran.
Nafisa da ke barci a dakin ta Yanyala ta shiga mata da maganar cewa may ke faruwa ne taga ana gyaran dayan part din da tace na uwar gidan ta ne.
Kamar ba cikine a jikin ta ba ta diro saman gadon ta fito inda masu aikin su nan ta hausu da fada wayasa su aiki a gidan ta ba a fada mata ba.
Daga bayan ta ya bata amsa yana saukowa daga sama yace nine nan maigidan na basu aiki suyi in biya su wani irin kallo mai kama da kai asuwa ta aika mashi.
Bai tsaya kulata ba sai kokarin shiga dakin da yake yi tasha gaban shi da sauri ta tsare shi may kake nufi ne samad da wanan gyaran da akeyi ?
Yace abinda kika gani Nafisa shi nake nufi don gida nawa ne ba naki ba kamar yadda kika fadi yanzu.
Nan hankalin ta ya tashi sai ta fara surutu ita may yake nufi da ita da zai mata haka yace don yaga zata haihu zai dawo da fati da yaranta gidan shi.
Tace nasan dama kule kulen da ake shiryama ke nan kake yawan zuwa kaduna akai akai yanzu dama ba so na yan uwanka keyi dani ba .
Shi dai bai mata magana ba don mazan dake gidan suna aiki ya fita batunta basu raba hali a gaban su ba.
Hankali tashe ta kira madam tana fada mata abinda ke faruwa madam tace kika sani ko watace zai dauko ya saka a dakin ba Fati ba ?
Nan hankalin ta ya kara tashi sosai tace Nafisa dam wanan tunanen baizo min ba sai da kika tunatar dani haka yanzu.
Madam tace to zauna nan kina fada akan fati wata tazo ta shige dakin kina gani saboda sakaci irin naki in zaki mike ki mike tun yaushe muka gama da wata fati can.
Wacce hudi daya mukai mata muka fitar da ita a gidan har diyan ta sai tarihin su yanzu har kike tunanen ita zai mayar dakin ta.
Ke kasar ku fa zaki koma aiki kaifi sai Niger nan kusa kafin ma mu dawo aiki ya kankama ko mu huta da ko wacece ma ke son muna kutse haka cikin ruwan sanyi.
Nafisa tace madam kin san ba zuwan ba kuma ba kudin nake jiwa ba don zan iya saida da duk wani kaddara da nake da akan wanan aikin tunda yanzu na rasa gane kan shi.
Matsala daya ne shine mutumin nawa yanzu kin san matsi yake min tun wanan tafiyan da mukayi ondo ya kara burge min a gidan nan baya sake min har yanzu ga kuma lalurar cikin nan dake jikina yanzu.
Madam tace ke dai kawai tawa ki nemi kudi in ma bai barki ba sai ni inje maki manene amfanin zaman mu tare da ba zan iya maki komai ba.
Ai kawai ki daina damun kan ki mu za a gwadawa hanyar boka ko malam kuma ko latsandan ne gaba da lahira indai ana zuwa zamuje shi.
Sai lokacin Nafisa tayi ajiyan zuciya taji dadi a ranta tana ganin aduniya bata da kamar su madam dake tsaye a kan ta yanzu.
Tace uwar dakina Allah dai yaja muna nisan kwana tare ni nasan banda kamar ki a duniyan nan yanzu.
Da wanan shawaran hankalin Nafisa ya kwanta nan ta shiga buga waya gida Niger ko an samu wani bakon boka ko malami mai tashe a kasan.
Sai da ya ga komai ya kankama yadda yake so ya bar gidan bayan ya sallami mutanen da sukai mashi aiki duk da yawan samari yan uwan Nafisa a gidan ba wanda zaiyi bugun gaba dashi yayi mashi aiki alhalin biyansu yake duk wata dasunan aiki suke mai a gida.
Bayan kwana biyu su mommy sun gama shirin su tsab ya tura Yusuf ya dauko su zuwa garin Abujan mommy a gutin hajiya mama ta bar yaran ta tazo ita kadai sai iyan Bawa da suka zo tare da wata yar mai masu shara budurwa don taimaka masu da wani abin.
Mommy sunyi waya da Ya Amina tana sallaman ta tace zata gidan Abdulsamad wanda matar shi watan haihuwan ta ya kama zasu dan kwana biyu acan .
Ya Amina sai sulbul da baka tayi tace mommy ashe zaku hadu da Khadija na ke nan mummy tace banda abinki khadija dake makaranta ina zan ganta ni ?
Sai dai idan sawa zanyi a dauko min ita ko akaini in gano maki lafiyan ta idan na samu lokaci dariya kawai ta Amina tayi don ta san gidan su Abdulsamad basu san komai ba a tsakanin mu dashi.
Tafiyan rana sukayi don haka sai da yamma lis suka shigo garin Abuja din direct gidan shi suka nufa yana gida a lokacin don yana dakon zuwan su.
Nafisa wace ke falo tana shan iska ga yan uwanta a kewaye da ita kowa na shaanin gaban shi sai sallaman su mommy da su iyan bawa suka ji .
Gaban tane ya fadi da ganin su mommy din gidan don bata taba zaton zuwan su ba don a wautan Nafisa ta gama da kowa nashi yanzu babu mai marmarin zuwa inda yake.
Zuwan su mommy ba karamin faduwan gaba yasa ta ba sai take ganin ai zancen auren da take zato ko dawowan Fati gidan gaskiya ne.
Shiya fito daga daki bayan sunyi waya da Yusuf ya sheda mai sun iso ya fito da yar fara, a a fuskan shi yayin da ko kallo su mommy basu ishi Nafisa da yan uwanta dake falon ba .
Shi da kanshiyayi masu iso dakin da zasu sauka din bayan dun gaisa sun mashi yaya gida ya fito tare da Yusuf da ya shigo da kayan su ciki da taimakon wani saurayi.
Falon ya dawo inda suka samu Nafisa da yan uwanta sun juye harshe cikin yaren su na buzanci suna maganan zuwan su.
Fuska a daure ya kalle ta yace Nafisa baki san mommy bane da gwago na iyan bawa da baki tare su da zuwa ba ?
Tace a yatsune na san su mana ba matar mahaifin ka bane ita yace OK cikin wani irin kallo har ya fara tafiya sai ya juyo yace tunda kin san ta kin san kuma matar mahaifina ne baki iya taron su ba nima haka ban son in fita yanzu in dawo in samu wa yan nan yan uwan naki a gidan nan yanzu.
Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya tace wallahi baka isa ba don zuwan su zakace yan uwana su bar maka gidan ka yanzu yace zaki san na isa idan yan sanda dun shigo sun fitar min dasu.
Idan akwai abin da yan Niger sukaki jini shine dan kakin Nigeria don basu yi masu da wasa idan sun farmake su.
Nan Yanyala ta fara magana tace haba Allaji ai bin baikai can ba daga dan wanan magana har zaikai ka kira muna polizawa kawai dai jira muke su huta mu mika masu gaisuwan mu.
Ya fice zuwa nemo ma su mommy abinda zasu ci a gidan don yasan ba zasu iya taba cin abincin da suka dafa ba.
Bai dauki lokaci ba ya dawo dauke da ledoji iri na restaurant dauke abinci dasu ruwa a ciki ya bayar aka shigo masu dashi har dakin.
Mommy ta idar da sallah sai ga yaron shi isyaka yana shigo da kayan ciki tare da gaba tar masu da abincin.
Sunka ce har da dawai niya zuwa sayo abinci kuma nan dai iyan bawa ta kasa hakkuri tace zainabu may kika fahinta ga wanan zaman ?
Murmushi mommy tayi tace ke dai iyan bawa ai ayi shani kawai wai ancuci na kauye wanan matar bata da hali ko kadan.
Kin dai fara ganin makasudin zuwan mu garin nan ke nan don fitar shi kunyan abokan shi nasan halin matar nan tashi dakilace na gani a fada.
Ba zamu sakar mata fuskan da zata kawo muna raini ko wulakanci ba don nasan tun zuwan mu batayi farin ciki da ganin mu ba.
Sunci abinci sun huta sai ga Nafisa ta shigo tayi wanka ta saka sutura a jikin ta yan uwan ta suna mara mata baya suka shigo dakin.
A falo suka samay su nan ta ja ta tsaya bata zauna ba tana fadin kunzo lafiya ya hanya da mutanen gida ?
Mommy tace lafiya duk suna gaida ku yaya nauyi Allah ya rabaku lafiya tace amin sauran suka shiga gaida su da yi masu ya hanya suka fice daga dakin ba wanda ya zauna.
Shiko bayan ya mika sakon wuri na ya nufa kamar yadda ya saba zuwa man koda ya kirani muna tare da maryam da zarah a dakina kiranshi ya shigo min.
Mutumin ki ne halan yazo maryam take tambayana nace cikin tabe baki shine ai kin san bai tashi zuwa min sai wanan lokaci.
Maryam tace ai kuna daidai dashi in kin isa ki fadi a gaban shi yana da amsan baki indai wanan yaya in love din kine.
Kai maryam kina da wuyan sha,ani wallahi na fada maki ba soyayya a tsakani na dashi sai amin taka kawai na damuwa.
Zarah ta dago kai tace min wani guy kuke magana muje in gani idan ya min in saka shi a layi mu shiga sha,ani dashi.
Zarah wai ke baki jin kunyan fadin fitsrane haka tace in banda abinki wake ta wani wasa da so yanzu khadija bari kiyi wasa da daman ki yanzu yan jami,an nan suyi maki wuf dashi.
Idan banda abinki an fada maki kowane yan matan jamia ke iya wuf dashi kai daya zarah wanan ya wuce sanin ki wallahi.
Dariya tayi tace muje inga guy din nan dai da kuke wani zuzutawa haka dai murmushi nayi kawai don ba zan so a ganni da ita ba.
Duk da ba wani shiga na yi ba amma suna ta yaba kyau da nayi wai na hadu zarah na fadin ashe zaki zama yar hannu haka khadija.
Tare muka fito dasu sun zo su gaida shi tunda muka tunkare shi zarah ta tsunke da ganin motar da yazo da ita tana fadin tun ban ga guy din ba wallahi nasan zai hadu ko don motar nan da nagani how lucky you are da kika iya canko wanan zukeken guy haka.
Mun iso yana ta faman ansa call a wayan shi sai da zarah ta kare mai kallo ta dago bayan ya gama wayan suna gaida shi bai wani sake fuska ba ya amsa gaisuwan.
Tare da kawar da kanshi gefe daya zarah tace dama na sani sai irin wanan guy din khadija wanan jan ajin naki yayi yawa wallahi har ta gama ta wuce bai yi magana ba suna shiga maryam ta nufi dakin ta.
Maganar shi ta farko bayan wucewar su shine ina kika samo wanan kawar kuma ?
Nace a inda ka gan mu yanzu yace No ba girman ki bane da mutuncin ki yawo da irin wayan nan nace kawatace fa tare mukazo karatu daga gida.
Na fada maki bana son in kara ganin ki tare da ita please na juyo ina kallon shi ido cikin ido nace tana da aibu ne komay ?
Au ke baki ga aibu ta ba wanan bata da kamun kai ba girman ki bane yawo da ita nace ka taba ganin mu a tare ne ko yanzu ma daurowa tayi ka gan mu da ita.
Har ya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru nima shirun nayi ba wanda yayi magana daga cikin mu.
Can naji yace idan na fada maki wani abu zaki yarda dani ?
Zaki yarda gaskiya nake fadi.
Murmushi nayi nace idan maganar ta kama gaskiya mai zai hana nayarda tunda nasan gaskiya ka fada.
Kin yarda dani khadija ?
Nace na yarda dakai mana yaya Abdul fati da mijin buzuwa ina fadi ina mashi dariyan shakiyanci cikin gatse.
Shima murmishin ya dan yi wanda sai wanda ya sanshi zai iya fahintar hakan daga gare shi yace kin san kamun kan ki yasa muke tare da ke har wanan lokacin.
Kasan ni ne da zaka wani ce ina da kamun kai bayan iyakar mu dan wanan haduwan da muke yi.
Na tsinci muryan shi yana fadin niko na sanki khadija you are classic baby da na taba haduwa da ita a rayuwana.
Katse shi nayi da fadin may ke faruwa daksi haka ne wai ke irin wanan magana yanzu a kai na ko last zuwa da kayi haka ka dinga min wanan maganganun.
Ya girgiza min kai tare da fadin ba komai cikin lumshe idanuwa shi sai kuma ya bude su ya sani gaba yana kallo na.
Shirun motar na kawar da fadin yau ba fita ke nan yace ina kike son muje nace inda ka saba zuwa mana mu zaga