Showing 12001 words to 15000 words out of 142410 words

Chapter 5 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

19

Middle Ads

fito cikin mamakin ganin yan uwan shi da na Fati wanda bata zaci haka ba yasata daure fuska atake ta nuna kinshin ta karara a wurin.
Gashi kuma har ya iso gida a lokacin nan su mommy suka ja Fatin zuwa taron shi daidai kofan shigowa falon gidan mai dan karen girma da tsaruwa.
Duk abinda su mommy suka ce tayi shi tayi a wurin aka dauki ihu da tafin yan uwa itama tazo da nata tawagan sukayi iskancin su da sowace sowace irin na yan duniyan mata shiko yana wani washe baki yana runguman matan nashi.
Ranan dai naga kishi kara don buzuwa a gaban kowa ta kwace hannun mijin su daga gefen Fati din ta rungumay shi ita kadai.
Juyawa nayi wurin zainab nace wanan tsohuwar may take nufi ne haka wai tsuhuwar da nace yaba sauran yan matan da muke tare dariya duk aka kwashe da dariya.
Ido rufe ta kallo mu tana rugumay dashi a jikin ta kamar wani soko sai lumshe ido yake yi tace kada ku kawo min iskaci a gida na don ban gaiyace ku ba.
Ai ba gaiyyan ki muka zo ba mu wane mu da gaiyan ki kin ga mun yi maki kama da mutanen banza ne duk wurin akayi tsit ana kallon mu .
Wai wanan yarinyar yar gidan uban waye a garin nan nace yar gidan ubanki ne a garin nan tsaye kowa yayi yana kallon mu ta fara fisge fisge wai zata zo ta dake ni a wurin .
Ko dar banji ba na ce da turanci too hell with you wallahi don ba don ki muka zo gida idan kikayi gigin tabani yau sai kin raina kanki wallahi .
Anty Fauziya tazo ta jani da mommy suka hau sama dani shi kuma sai cewa yake ta bari bai son fitina ita fa ta tara mutane tace ba gaiyyaci kowa naka ba don nasan halin su ba sona sukeyi ba.
Saman yabi da kallon mamaki yadda karama dani na iya tsayawa a gaban su nayi wa yar lalai matar shi tas na barta nan tana hargowa.
Anty na duk ta tsure sai fadi take ku bari mu tafi gida khady dama nasan halin ta bata daukan wulakanci tun tana karama.
Kowa a wurin fadin albarkacin baki shi yake yi mun dade a dakin kagin mu fito zuwa gida muka bar wasu anan sai da su Binta sun fito tare damu sai nuna ni abokanta sukeyi da muka fito.
Niko ko a jikina don ban damu ba ban biya gidan su ba gida muka wuce mommy taba anty wani leda dake da kaya a ciki ni har nayi gaba a lokacin har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu.
Sai bayan mun yi sallah magariba da ishai muka fito falon har lokacin ban sake ba raina a bace yake da abinda ya faru dani.
Zaman mu shigowan su zainab da Binta da Amira suna shigowa suka saka dariya gaba dayan su anty tace dasu yau ai ni naga abin mamaki gun khady mata da gidan ta ki ce zaki fadan karfin hali.
Nace anty wallahi ko ba yau ba wanan matar tai min ramawa zan yi haka kawai zan tsaya tana zagina akan may wata tafi asali.
Ni dai don Allah ki rufa min asiri a garin mutane khady ki koma gida lafiya wanan abin da may yayi kama Binta tace anty mu ai tayi muna daidai wallahi.
Baba ma da yaji cewa yayi wai waye khadija din nan har cewa yayi a kiraki mukace kin tafi gida.
Anty tace kinji ko wallahi khadija ki rage wanan girman kan naki don ba zai kaiki ko ina ba wallahi tace ai bayan dawowan mu ayin fitina sosai a gidan dasu anty Fauziya da suka tsaya suma sai da akai rashin mutunci dasu yau.
Wuri ta samu mana shiyasa takewa mutane rashin mutunci son ranta inji zainab ai yau naji mamaki da bai biye mata ba da dane ai rama mata zaiyi.
Sai lokacin nayi magana nace ashe na manajo ne yayan naku cabdi dako yau yaji magana wallahi binta tace da zaki iya ramawa nace mai zai hana iyaka dai yasa a kama ni ko zainab tace wane shi.
SEENABUA raina sai mamaki nake wai wanan matashin da nagani wanda bai wuce ace yanzu zaiyi auren farko ba ke da mata har biyu haka.
Buzuwan nan dai da za a zauna a fadi gaskiya tana iya girmay mashi daga shi har matar shi sai idan ance yanayin jikin su kawai da ba a gane hakan.
Ita kuma Fatin baka ce sai dai da zata zauna ta gyara jikin ta banga abinda buzuwan nan zata gwada mata ba sai dai kasshh yanayi irin namu na matan hausawa yana cin rayuwan ta da haka nake hango buzuwa ta kwace mata miji .
Yau da gobe sai Allah dama sati uku zanyi don hutun ba yawa shiyasa ban so zuwa kaduna ba a wanan lokacin amma anty na ta dage sai nazo ita kadai ne a gida mijin ta yayi tafiya.
Ashe kuma da rabon mu kwasa da matar mulki ne a garin ya kawoni don haka shiri nake inda ba komai nake shiryawa sai kayana don ban daukan provition da ga gida sai na tafi can nake saya.
School zan wuce direct sai nakwana biyu zan shigo mina in masu weekend in kwashi abinda na samu in koma bayan kwana biyu don haka nake ta shirin komawa makaranta a lokacin.
Kwatsan da safe muna karyawa saura kwana biyu tafiyana sai ga wayan mommy ta bugo ma anty wai Fati ta dawo gida yanzu haka tana nan gidan su naji anty na fadin o o Allah yanzu matan nan da karfi da yaji sai ta raba wanan auren take nufi.
Banji may mommy ta fada mata ba nadaiji tana fadin gaskiya haka nane idan abu yaki sai ayi hakkuri kada zumunci ya baci idan abin ya sake shi inda rabon komawan ta gidan sai ta koma.
Bayan ta kashe waya tace mummy tace ki shiga kafin ki wuce kada ki tafi baki sallamay su ba nace haba anty may yasa kika fada mata zan wuce ai sai yazama kamar roko idan naje sallaman su.
Kai ta girgiza min tace ba haka halin su yake ba dauka na sukeyi kamar wata ta gida a gurin du duk zuwa kikayi kika wuce sai sunyi min korafin hakan.
Shiru nayi sai tace o Allah sarki wanan buzuwan dai ta hana Fati zama gidan mijin wai yanzu kuma ta kara fitowa tace bazata koma ba.
Dudufa baifi wata da ta koma gidan na yanzun kuma ta kara fitowa jiya wai sai dai na shiga inji may kuma ya hadasu fada yanzu.
Takaici bai barni nayi magana ba sai dai a zuciyana nake bankawa mijin zagi da rana su binta suka shigo gidan mu anan muke jin labari wai tunda ya dawo buzuwa taki bari ya ke be da fati hakan bai isheta taja Fatin da fada har tana fadin sai ta kashe ta.
Shiya ba Fati tsoro tace barin gidan yafi mata nace shike nan ta samu galabanta ai ta kashe ta din idan ta isa mana.
Gaskiya matan nan ta samu wuri da yawa wallahi nace shiko sokon yayan naku fa may yayi a kai tace jiya baban mu ya kirashi sai cewa yayi shi yagaji da halin fati tana bata mashi suna.
Ai wallahi idan da nice tace sai ta kashe ni da na nuna mata hauka ke matsorata ne fa iskancin abaki yake masu kawai Fatin dai ne wallahi she is to slow .
Anty tace khadija baki san aure ba fa shi wanda ake abin a kansa bai nuna wani feeling din shi akan ta gara dai da ta hakkura ta basu wuri.
Zata tafi nace barin bisu daganan in masu mommy sallama tun ranan da mukai fada da buzuwa ban sake shiga sai yau da zan tafi sallaman su da anty ta matsa min.
Tsab na shirya na fito cikin wani dogon riga mai hannu shara shara shara da gyalen shi na yafa akaina sai turaren da na fesa a jikina.
Mun shiga gida inda na fara zuwa dakin mama na gaida ita sai na fito naga anty amarya a waje anan na gaida ita har zan wuce tace khadija ashe haka kike ina ganin ki shuru shiru dake ashe ke ma jaruma ce ban sani ba.
Dan guntun murmushi nayi nayi kasa da kaina kawai dakin mama na nufa ina jin suna maganan a waje da mai masu aiki na shige wurin mama in gaida ita.
Tana zaune a falon ta tana waya haka yasa na samu wuri a kasa gefeta na zauna ta gama wayan ta dago kai cikin fara a tana fadin yau khadija ne gidan nace mama ina kwana.
Ta amsa min fuska a sake nace mama nazo in sallamay ku gobe zan koma school tace a a har hutun ya kare wanan karon nace eh mama.
Ta sake cewa gida zaki ko Abujan zaki wuce aa zan wuce school ne daga nan tace barin baki tsaraban yan makaranta ko nace mama da ki barshi ai ba zan dauki kaya daga nan ba sai naje can saya.
Tace a a wanan kan zaki so dambu ne da akai ma yayan zai tafi dashi kin san yana son dambun nama sosai shine na aikai mashi shima gobe zasu tafi.
Ta mike ta shiga daga ciki sai gata da roba dan madaidaici ta fito da kudi a hannun ta ta miko min nayi godiya namike zan fita ko ba a fada ba yanzu na sheda wanan kamshi ba kowa bane sai dan ta Abdulsamad mijin buzuwa.
Zai shigo ni kuma zan fita ban yi tunanen in kauce mashi ba a lokacin dole suka jaye a hanyan na fita ashe da buzuwa suke tana bayan shi.
Mama ce naji ta kwala min kira sai na dawo wanan karon sai da na bari sun gama shiga na shiga dakin nima na karasa wurin ta gwiwa na biyu a kasa na zube ina fadin mama gani.
Buzuwa ke gaida ita ta tsaya amsawa ta dago tana cewa dan ta gobe ne zaku tafi din ko yace insha Allahu mama yanzu ma mun zo mu sallama ku ne don goben sakko muke son yi dan zan shiga office.
Ta juya gare ni tana fadin gobe sai ki shirya su tafi dake indan zasu wuce gaba na ya ba da damm da sauri nace a a mama ba tafiyan safe zanyi ba ni.
Khadija yayan ku ne fa ki shirya ki bishi yafi shiga motar kasuwa su wuce da ke shidai baiyi magana ba ya rike goshin shin da hannu guda .
Sai buzuwa ne tace motar tamu ai a cike take dayan ni dashi ne sai driver dayan kuma na masu aiki mun ne su larba sai na security din mu .
Naku zata shiga don ita din ba bare bace yar gida ne kaji na fada maka tau mama yace ta shirya da safe din kada ta makara sukuku na mike tare da fadin mama na gode.
Fitana dakin mommy na tafi ina nuna mata abinda hajiya mama ta bani tace ai yaya tafi danan ban fada mata zancen bin mijin buzuwa da tace in yi ba a lokacin itama daki ta shiga sai gata ta fito min da wani bakin dogon riga da takalma cikin na sayarwanta tace ga wanan a samu na sakawa.
Binta ce ta shigo dakin tana dariya mommy tace maynene kuma tace khady nakewa dariya mommy mama tace da yaya gobe su tafi da ita.
Ga buzuwa can tana fada bayan fitar mama daki wai bata yarda ba bata san mama ta jita ba shine mama ta fito tana fadin har ta isa tace ga abinda take so tace ita bata yarda ba yaya ce shi baice ba zata bisu ba ai.
Juyowa mommy tayi ta kalle ni nace nifa ban iya bin su gaskiya don idan tayi min wallahi nima yi mata zanyi gara ko kada in bisu din.
Dariya take min mommy tace akan may kin samu sauki bazaki bisu ba ai shi Abdulsamad baida hakana tunda har yaya tayi mai magana da bai daukan ki tun a nan zaiyi magana balle yanzu da yasan yaya tana hake dashi ai ba zai so ya bata mata rai ba kuma.
Daga cikin dakin mommy anty Fatine ta fito tana saye da wani hijjab har kasa fuskan ta duk ya kode alaman tasha kuka har ta gaji.
Gaida ita nayi ta amsa kasa kasa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon mommy tace kin tashi tace eh mommy tace ga mutanen ki can sun shigo sallaman mu zasu koma gobe wai.
Shiru tayi batayi magana ba sai mommy ta kara cewa kin san yaya da son jan magana wai cewa tayi gobe su wuce da khadija da zata koma makaranta goben.
Wai ai ba zata bari ba wallahi bata son kowa ya rabe shi balle wanan da take gani mace haka maikyau kuma gasu da wata a kasa daman.
Aiko banyi niyan binsu ba da amma yanzu sai na bisu tunda abin haka inga yadda zatayi a motan dani idan na shiga.
Murmshi mommy tayi tace ki shirya da wuri don shi da wuri yake tafiyan shi idan zai tafi tashi nayi nayiwa mommy sallama muka fita da binta ta rakani.
Naje gida na nuna ma ya Amina tsaraban da suka bani don da zanfito anty amarya taji zan wuce ta dauko min wani set din turare mai kamshi ummi ce bata ban komai ba a cikin su.
Sai can muna hira nace ya Amina kinsan wai mama cewa tayi in shirya gobe in bi mijin buzuwa da buzuwa idan zasu koma.
Da sauri tace may ne ?
Nace wallahi da banyi niyan binsu ba amma tunda ta nuna bata son haka zan bisu din inga yadda zatayi dani a hanya .
Nidai wanan zuwan wai damay yazo muna haka ne da tarihin buzuwa ko damay yanzu ke binsu din zakiyi, ba zaki hakkura kibi motar kasuwa ba.
Don mama ne kawai zan bisu kada in bata kunya tunda tana sin gwada masu ikon ta ne a kan su da kuma ita buzuwan zantafi.
Da yamma sosai na fito zan shiga gari in karbo dinkina da nakai ina fitowa bakin get sai ga motan shi tundaga nisa na kawar da kaina don ban san wanda ke cikin motar ba sun kawo kusa dani na gane su ne na watsa mai harara na kawar dakai.
Yusuf wacece wanan yarinyar wai da nake gani a gurin mama yarinyar bata da kunya ko yanzu baka ga wanj harara da ta watsa muna ba kullun shi take min fa har a falon mama da muke haduwa.
Dariya Yusuf din yayi yace amma kuma tana da kyau gaskiya koda yake kai yanzu baka ganin kyaun mace gaka da buzuwa a gidan ka.
Wai Yusuf may ya kawo wanan magana haka daga tambayan ka yarinya idan baka santaba kace kawai baka santa ba period.
Dariya Yusuf din yayi yace kai ke nan da anga mace mai kyau kace kada ayi magana wallahi yarinyar ta hadu sosai shiya take da jan aji da yawa.
Nafisa fa tayiwa rashin kunya a gida na ka sani kuma kake wanan magana yace a a suka dai yiwa juna ta zage ta ta rama don uba baifi uba ba.
Matsalan Nafisa tace kowa zata juya don tana takama mijin ta na da kudi kaji dai abinda yarinyar tace mata ai batazo roko wurin ku ba zumunci ya kawo ta.
So tayi ka kama mata kuyi wa yar mutane cin mutunci a banza.
Yace ai don na ganta a wurin mama ne yasa na kyale ta amma da ba zan yarda ta shigo min gida tayi min tujara ba for what ?
Matar ka ce yar cin mutunci ai ya furzo iska daga bakin shi yace matsalan ta ke nan wallahi cikin ina tsawata mata ta bari ke nan ma.
Yanzu dai kun kori Fati kun huta tabar maku gidan yace ta dai kori kanta amma ni ban kore ta ba ai ban san irin Fati ba wallahi .
Bandai san irin ka ba malam buzuwa ta hanaka ka ba Fati da yara hakkin su kai kuma ka biye mata ranan fa a gaban kowa ta banbare hannun Fati a jikin ka kuma ka yarda.
Wallahi idan zakai ma kan ka fada kayi tun baka makara ba kana ganin su Affan idan suka girma sukaga kanawa uwar su haka zakaji dadin su ne.
Kai wa kan ka fada wallahi akan buzuwan nan kada ka tashi ranan lahira da bari shayaye .
Bugu yakai ma abokin nashi yace Allah man abinda akace yana samun masu karkata gin mace daya ke nan na fada ma tun farko ban yarda da ita ba yanzu kaji abinda hajiya ta fada muna ranan.
Nisawa yayi yace ai Fati ta riga da ta hadani dasu har baba fushi yake dani a gidan da sauran yan uwa.
Yusuf yace buzuwan ka kuma tana jin dadi ba ta kori yar

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login