Showing 93001 words to 96000 words out of 142410 words

Chapter 32 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

47

Middle Ads

dani duka kace a kwashe mu.
Bissimila yace idan haka yafi maki yan uwa na daine dole na a yanzu gidan nan na kuma gwada maki haka kina iya binsu ga hanya nan a bude ya juya gurin police din yace ku tafi dasu duka.
Samad ni zakai wa haka ni zaka fada a kwashe mu a tafi damu babu ko nauyin haka a bakin ka kake fada.
Ke uwata ce ko may ko ajeni kika yi a gidan mara mutunci kawai ya juya zai fara tafiya da sauri tasha gaban shi tana fadin kuskure ne nasan nayi ba daidai ba don Allah kayi hakkuri.
Madam tace tun farko da haka kikayi da abin baikai haka ba ya nuna su mommy yace su zaki ba hakkuri bani ba ai.
Mommy kiyi hakkuri kisa baki a maganan nan don Allah mommy tace naji zan bashi hakkuri amma haka ya zama ishara a gare ki gaba.
Nan Abdul din ya dage sai idan ta basu hakkuri zai jaye maganan tace cikin dukawa mommy kuyi hakkuri nayi kuskure don Allah.
Iyan bawa tace amma ke kan anyi mutumiyar banza a nan yanzu baki ji kunya ba don Allah ga yan uwan ki ko ina a gidan baki bakin ciki da cin su ba sai mu da mukazo zama daku na dan lokaci.
Dan mune fa mai dukiyan da kike kadagi dashi din har kike ganin kowa ba kowa bane a gurin shi sai ke da yan uwan ki keda iko komai dashi.
Nan suka kaita fada mata abinda suke so a cikin nasiha tace ayi hakkuri zata gyara yusuf ne ya sallami yan sanda suka wuce.
Ranan dai anyi ta ba dadi a gidan tayi nadama tayi bakin ciki abinda Abdulsamad din yayi mata a gaban kowa ya nuna bata da wani power a gare shi yanzu ga madam ma tayi fushi da ita ta tafi tana fadin ta bashe su a idon duniya.
Ta kula wanan ta kwance wancan haka na ta wuni da sake sake a ranta a kan sai ta rama abinda yayi mata akan su mommy din da suka zo gidan don ganin bayan ta.
Ita sam bata dauka don dan su da taimakon ta suka zo ba har yanzu don idon ta ya rufe da son bata kaunar taga wani wanda ba nata ba ya rabe shi saboda tsananin kishi da take dashi irin na buzaye.
Ta kira madam ta bata hakkuri har suka shirya take anan kuma suka fara sabon shirin da zasu aiwatar a kan kowa ma daga bangaren shi.
Shiko a bangare shi ranan daki ya shige bai son yawan hayaniya da kowa don haka ya ke be kan shi a daki ba abinda yake sai tunanen hanyar da zai samu mafita ga alamarin Nafisa.
Saboda yasan ba canza halin ta zatayi ba kwanto kawai tayi a yanzu tana nazarin ta idan zata biyo mashi ne.
Allah ya gani yana son ya kara aure kamar yadda Yusuf yasha fada mai shine kawai mafita gare shi akan Nafisa to amma wa zai aure din da zasuyi daidai da Nafisa a zauna lafiya.
Khadija ina khadija karama ne sosai ga Nafisa da halinta ba zai dauko yar mutane ya jefa a matsala ba ya cuta mata don yanzu yana jin yarinyar a wani bangare na rayuwan shi .
Don haka ba zai cuta mata ba ta wanan hanya na hada aure a tsakanin su wani abu yazo ya samu yar mutane a hannun shi.
Ga mahaifin ta ko yaushe sukai waya yana mashi godiya akan kyautatawan da yake ba yarsu wace kamar kauna take a gareshi.
To amma kuma ga shakuwan da sukayi taya zai iya rabuwa da khadija a yanzu nan tunanen irin rayuwan da suke yi da khadija din ya fado mashi a rai abinda ya sa shi dan murmushi ke nan kadan ya gyara kwaciya yana lumshe idanuwan shi.
Wayan shi ne ya yi tsuwa alaman kira na shigo mai ya dan juya ya daga wayan Queen of matsala ya gani da sauri ya daga kiran nawa.
Tambayan shi nayi lafiya kake kuwa yau ?
May kika gani ya bani amsa dashi sai na rasa abinda zan fada mashi karya na samu kaina da yi nace kawai dai sai nake tunanen hakan .
Fada min kewa na kikayi ko may kika kirani a cikin wanan daren haka baki san ina da mata bane ni Family man ne idan kika hadani fada da mata na fa ?
Wayan na kashe ina ci gaba da tunanen mafalkin da nayi dashi a yanzu daga dan barci ya dauke ni sai wanan mafalkin yazo min gaba daya na saka waya na a off na gyara kwanciya cike da zullumi ina tunanen mafalkin.
Can dai barci ya dauke ni na manta da zancen mafalkin koda na tashi naci gaba da alamura na shima kuma bai kira ba don haka na kara share shi.
Nafisa ko hankalinta bai kwanta ba gida Niger ta kira mai mata aike a can da kukan ta wiwi matar tace may ke faruwa Nafisa ko sakin ki mijin ki yayi ?
Tace bai sake ni ba serah sai dai gaba daya ya canza min yanzu nan dai ta koro mata bayanin abinda ke faruwa cikin kuka.
Serah tace share hawayen ki Nafy murde dan iska zamuyi ya koma sai yadda kika ce a gidan ki bai isa ba wallahi yanzu dai ki daure kibi yan iska yan da suke so daga yau zan shiga in fita zaki gannin nan da kwana uku kedai turo min da kudi kiga aiki da cikawa.
Tace serah har kin kwantar min da hankali na wallahi don yanzu ni damuwa na bai wuce cikin nan dake jikina ba don cewa ake wai idan mace nada ciki ko jinin haihuwa wai komai nata baici.
Serah ta katse ta da fadin da ke nan wanan zancen yanzu may ye kudi baiyi Nafy ina nan shigowa nan da kwana uku kada kiji komai.
Bayan sun gama wayan ta zauna ta zabga ta gumi ta rasa ta ina zata fara da shi zata fara ko da iyayyen ko wanan mugun abokin nasa da ta tsana.
Zaman gidan yanzu haka ake yin shi ba ruwan wani da wani sai gaisuwa a tsakanin su dasu mommy kowa na harkan gaban shi.
Shiko yana tsananin basu mommy girma da kulawan da ya dace a gidan wanda hakan keyi wa Nafisa ciwo matuka ta rasa yadda zatayi dasu a gidan.
Kunci cikin zuciyar ta ba a maganan shi har yakai bata iya boyewa hakan yasa ma ta daina yawan saukowa kasa inda zata gan su ko wani abinda sukeyi shiko sam bai kula da halin da ta jefa kanta a ciki ba yanzu.
Kamar yadda serah tayi alkawari haka ya faru tazo da kule kule da sihiri kala kala tun a ranan suka fara aiwatar da komai kamar yadda suke so ya tafi.
Nafisa sai gani take har aiki ya fara ci saboda yarda da tayi da maganin don irin labarin da Serah ta bata yadda ta shiga kungurumin dajin kasan su wurin samo mata wanan asirin mai amfani da ci da sauri ga wanda akaiwa.
Haka kawai yake ji kwana biyu yana jin haushin kowa a gidan inbanda Nafisa da yanzu yake jin wani irin so da kaunar ta yana shigan shi.
Mommy dake da kaifin basira ta fahinci abubuwa suna sauyawa a gidan don haka ta fara tuntubar Iyan bawa akan abinda da ta fara hangowa ga dan nasu don tun zuwan Serah mommy tasha jinin jikin ta da ita don tsarin ta da zubin ta yafi kama dana yan duniya ta irin mutanen su.
Batai kasa a gwiwa ba ta sanar da mahaifiyar shi hasashen ta amma tace kada ta bari kowa ya fahinci abinda ta fada mata ta dai taimaka mashi da addua.
Hajiya mama tayiwa mommy godiya bayan sun gama tataunawa akan zancen sukai wa juna sallama aka aje wayan.
Sosai hankalin hajiya mama ya tashi da maganan mommy haka yasa ta kira yayan ta da suke uwa daya uba daya a zaria tana neman shawaran shi.
Yace ta bari zai ga wani malamin shi a nan cikin garin zaria da zancen don rayuwar Abdulsamad da wanan matar tashi yana bukatan addua sosai.
Haka suka bar zancen akan zai kira ta taji duk yadda sukayi da malamin nashi idan ya dawo daga wurin shi.

Ban san mun shaku da shi ba sai wanan karon ga jerabawa ya na gaba to muna ga zancen zuci dake damuna haka ya dan sani rama kadan.
Karshe nabawa kaina shawaran abinda ka fisheni na watsar da komai na rugumi karatu na gadangadan ina yi tare da share zancen su gaba daya a raina.
Ranan muna zaune da Maryam a dakin ta tsifar kaina na ke da ya kitso ya tsufa min zan je in wanke kai na wayana yayi tsuwa na duba Yusuf ne a kan layin.
Nayi mamaki kwarai da ganin kiran shi a wanan lokacin na dauka da sallama tare da gaida shi ya amsa yana fadin kanwa ta ina kika shige haka ?
Kai yaya Yusuf ina nan inda nafi karfi mana na bashi amsa yace ko dai mutumin nawa ya boye muna ke ne ban sani ba ?
Wa ke nan kake magana nima na tambayeshi yace abokina mana kuma ogana a wurin aiki nace wai mijin buzuwa kake magana ?
Dariya ya kyalkyale dashi yace kai khadija baki da dama wallahi har yanzu dai mijin buzuwa aiko zaku kwasa dashi idan ya jiki.
Nace ina ruwa na dashi balle balle ya jini .
Yace ke ko keda ruwa dashi khadija yar mama amma dai baki da kirki Abdul din ne zaki ce yau ina ruwan ki dashi da bakin ki kike fadin haka .
Tsuki naja na tabe baki kamar yana gani na a lokacin nace ni na fita batun shi yanzu banda lokacin shi.
Yace subbahanallahi may yai zafi haka ne a tsakanin ku kuma keda mutumin naki khadija ?
Mutumi na ko naka yaya na kai nifa ko wancan lokacin da nake kula shi albarkacin ku ya samu a gare ni har na biye mashi amma ba don shi ba.
Kai haba yar mama bai dace ki fadi haka ba tsakanin ki dashi yanzu ai kunyi nisa sosai bai kamata aji wanan maganan ba a bakin ki.
Taimako fa kikace zakiyi sai da abu ya kusa kai karshe zaki ce ba ruwan ki dashi yanzu ai ko kece mai ruwa har da tsaki akan shi yanzu.
Mu dai bar wanan zancen nace dashi da sauri yace akan may zamu bari idan na tambaye ki zaki fada min gaskiya ?
Nace akan may ke nan yace akan mutumin naki mana nace idan na sani may zai sa na boye maka kuma ?
Yace Yaushe rabon da yazo gurin ki ko kuyi waya dashi when last kukayi koda waya ne please kada ki boye min komai just feel free with me khadija?
Dan jin nayi sai can nace gaskiya mun kwana biyu dashi don ba zan iya tuna zuwan shi gurina ba na karshe ko wayan shi a yanzu.
Yace abinda nake son ji ke nan daga bakin ki sai dai zan ari bakin aboki na inci mashi albasa Abdulsamad yayi tafiya two weeks ago amma dai yanzu ya dawo.
Sai dai ko a yanzu da bukata nazo maki a kan shi don gaba daya khadija ba zan boye maki ba Abdulsamad ya canza ga komai cikin yan kwana kin nan.
Gashi matar shi na shirin haihuwa watan ta ya tsaya tun last month sai dai har yanzu bata haihu ba yana gida ko wani lokaci tunda ya dawo like da ita.
Katse shi nayi da fadin ni may ye nawa a cikin zancen nan kuma can su karata shi da ita tunda shi ba tsayayyen namiji bane ko yaushe.
Namiji ne mana khadija ai shiyasa na kiraki don ki sheda mai cikin wanan wasan da kuke yi don ya farga ga abinda yake yi din.
Ni tsoro na shine kada su mommy daya dauko gidan shi su fahinci susucewar shi a kan wanan shuumar matar tashi sugane gazawan shi a gaban kowa.
Shiya sani mana tunda shi ke ji a jikin shi ba wani ba yayi saurin fadin a a khadija ba haka zamu yi ba daurewa zakiyi mu fitar dashi daga wanan kangin don Allah.
Ni haba yaya Yusuf ni may zan mai kuma shiya sani don Allah khadija dakata ki saurare ni don Allah nace ina jin ka ai.
Zaki iya hakkuri ki daure ki kirashi a waya ki fada mai magana daya wanda zai shi ya natsu ya dawo cikin hankalin shi yanzu don ke ce kawai mafitar da nake dashi bayan Allah.
Ni kuma why sai nice mafita akan haka yace saboda ban taba ganin wani ko wata dake fada mai magana yadda kike fada ba azauna lafiya kuma yai amfani da abin da kika da mai a zauna lafiya.
Dan jin nayi ina tunane yace kada ki karaya khadija don nasan zaki iya ki taimaka muna please wanan taimako ne indan kin yarda.
Yaya Yusuf wanan ya zama na karshe da zan ma wani alfarma akan wanan mutumin don gaskiya baida niyar canza halin shi nake gani .
Khadija ba laifin shi bane shu,umar mace ya hadu da ita take juya shi yadda take so nace har da halin shi a haka.
Kin yarda zaki taimaka muna ke nan nace naji zan gwada don Allah don kai amma da ba haka ba babu abinda zai kara damuna da rayuwan shi.
Nagode kwarai da hakan da zaki min don wanan ne kadai hope din da nake dashi yanzu akan wanan matar tashi.
Ina aje wayan maryam dake zaune ta kura min ido tana sauraren maganan da muke yi din tace kai wasu maza suna haduwa da shu,uman mata wallahi.
Koda yake ba abin mamaki bane ga wanda yasan mazajen da ke auren irin yan yaren buzaye zai san mazan ne a kasa matan suna sama.
Sai abinda sukace komai su mamaye na miji yazama nasu su raba shi kuma da kowa nasa sai su da yan uwan su zasu dinga bushasha da shi da dukiyan shi.
Sai dai kima sam basu son auren mazan yaren su don irin bakar wahalan da suke sha wurin su amma namu mazajen su ke kwadayin matan buzaye saboda bakar jaraban da suka iya.
Yanzu dai kira shi muji yadda zaku kwashe a tsakanin ku don nasan akwai drama nace ni wanan daure ni suke son yi maryam.
Ban san may yasa suke cewa wai sai nice zan iya masu haka ba bayan yana da kanne mata da yan uwa da zasu iya.
Su iya may khadija ai abin sai da hikima ke fa ba yar uwan su bace kin ga yadda kuke moved dashi kamar saurayi da budurwa ne.
Ke komai zaki iya fada mashi a zauna lafiya wani dan uwa idan yafa da sai inda karfin shi ya kare ke ko sai ki fada mai a wasa bai dauki abin da zafi ba.
Wayan ta na karba ta hanyan yi mata karya wayana ba kudi a ciki tace ai bai san layi na ba don haka ba lale bane ya dauki kiran .
Bari dai mu gwada mu gani idan bai dauka kiran har ya kusa karewa ya daga tare da fadin hello nace dole zama da yan haure ya kowa ma wani akidar banza.
Wake magana please ya tambaya nace wata buzuwa ce ko kana son kari su zama biyu a gidan ka murmushi yayi yace khadija nace ba ita bace.
Kina zaton muryan ki nan zai bace min ne nace marya na yana kama da na buzaye ne ?
Yace ai kamar ma ta baci baki ganin zubin ku daya dasu sai dai yaren da baki ji nasu kai malam ni kiran ka nayi naji ko mommy ta koma ne?
Don nasan ba lale bane buzuwan gidan ka ta barsu su dade a gidan yace idan kina son sani kije gidan ki duba mana.
Ban tashi ba ne da zanje yace ya kike nace ina nan yarda ka sanin a baya ke ba a maganar girma da arziki dake ne ?
Nace banson don ba gaisuwa na kira ka muyi ba ko tambayana yaya ni yace ai kogi ba ki dadi ba ko nace .
Wani kogin ke nan dai wani ko wani ruwa ne ya shige shi in ba nasa bane amansa yake yi don haka ba gaisuwan ka nake nema ba.
Yace becareful nace a nan ko sai kaga mutum har mutum amma a gidan shi sai ka rena mai wayo idan kaga abinda yake yi.
Ta yaya bakin haure har zasu shigo su samu mutum a gidan shi in ba samun wuri ba suce sai abinda suke so zasu mai ni wallahi na dade da raina aya don tsakuwar ta.
Yau hausa kike ji ke nan nace daurowa ne hakan adai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login