Showing 105001 words to 108000 words out of 142410 words

Chapter 36 - MIJIN BUZUWA COMPLETE

Start ads

08 Aug 2025

54

Middle Ads

Nace ai in ma kunyi niya zaku iya hakan don iya yaudaran ku dariya sosai Yusuf yayi yace munyi kama da mayau dara ke nan khadija.
Kasan ta iya shirme wani lokaci mu sace ki muyi may dake ai ba irin ki zamu sata ba har in muna satan yan mata.
Yusuf yace nikan irin su zan sata don yanzu suna danyun su shar ai kaga daidai sata ke nan nace ai dama nasan zaku iya haka ba sai kun fada ba.
Yace Yusuf ya tsaya a wani guri da ake sai da kaji ya mika mai kudi ya sayo muna da abinsha mai sanyi Yusuf ya fita ya barmu a motan tare dashi.
Naji dadi da maryam ke cikin motar a lokacin ba a barmu mu biyu ba ko kallo gefen da yake ban yi ba maryam ne ta dan zugure ni wai in yi mai magana.
Na kawar da kai kamar ban gane abinda take nufi ba tunane nake ta yadda zan fita motar nasu a lokacin Yusuf ne ya dawo dauke da ledoji a hannun shi ya shigo motan yana aje kayan a gefen shi ya ta da motar muka tafi.
Ban akara ba sai gamu bakin hostel din mu da sauri nayi niyar fita daga motar amma motar tana rufe har lokacin ga sanyin A C motar daya damay ni.
Suna zaune ba wanda yai magana a cikin su har dan wani lokaci can naji Yusuf yace daidai lokacin da nake fadin ka bude mu fita mana.
Shikuma yana fadin gaskiya khadija ba a kyauta maki ba a kyauta maki ba da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf din dake magana.
Yusuf fitar masu da tsaraban sunan su su sauka don Allah zaka tsaya wani magana kuma yace ya zama dole mu bata hakkuri don bamu kyauta mata ba.
Da akai mata may kuma ya tambayi Yusuf din cikin tsare shi da ido yace ai kaine mai lafin yaya zaka saka ta saba da kai daga baya kuma kazo ka share ta haka ba dadi wallahi irin haka kaima ka sani.
Please ka fitar masu dashi mu tafi don ina da abinda nafito yi yanzu ba wanan ne a gabana ba zaiyi magana yace fito masu dashi nace please.
Ai da ka barshi zuwa kawai mukayi in gaida mommy da su anty Fauziya da suka zo ya sake fafin don Allah ciro mata mu tafi ya sake maimaitawa.
Fita Yusuf yayi daga motar ya bude bayan motar yana fitar da kayan da aka saka a bayan motar sai da nayi mamakin ganin yawan kayan da aka debo muna mu kadai.
Haka na dake fuska daure na fita daga motan ban koyi masu godiya ba na fice fuuu a motar Yusuf ne ya tsayar dani yana fadin haba yar mama ki sasauta wanan fushin naki ku fahinci juna da mutumin ki.
Dan Allah yaya Yusuf ka daina hadani da wanan mutumin don ba ajina bane shi mutumin da yake under control din mace macen ma yar haure ba jinsin nahiyar mu ba.
To waima may kake son in kula shi aka in kula shi ya bata min lokaci ya hana mutanen arziki zuwa gurina ko may ?
Subbahanalahi ina wanan maganan ya fito haka a bakin ki baki taba tunanen Abdulsamad son ki yake bane ko may ?
Da sauri nace so so fa kace na girgiza kaina nace a,a dama kace kawai yana amfani dani ne wurin cin ma wani manufa nashi da zan yada da hakan amma ba wanan kalamin naka na so ba.
Sam na sake girgiza kaina karo na biyu tare da fadin wanan wani sallon yaudarane kuma ka dauko yanzu.
Yace to ko ki yarda ko kada ki yarda ni yau na fada maki son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi wallahi bai dai iya fitowa fili na ya fada maki ko ya nuna maki hakan.
Wani irin kallo nayi mashi tare da girgiza kaina na juya na fara tafiya ina jin wani bacin rai a zuciya har na shige ba tare da na dauki komai nasu ba da suka aje muna.
Kwanciya nayi ina tunane a raina maryam da wata suna shigo da kayan daki har suka gama ta debar masu ta basu daga ciki.
Ta dawo ta zauna tana ta faman cicire kayan guda guda tace kai khadija akwai wanda ya samu abinda muka samu kuwa a wurin nan jifa wanan uban kayan da aka loda muna wai duk namu ne mu kadai ina zamu da wanan kayan haka ?
Sai lokacin na dago kaina ina duban kayan data tara a gaban ta na maida kaina saman filo na kwanta magana Yusuf ne ke ta min yawo a zuciyana har wanan lokaci.
Maryam ne naji tace wallahi khadija na yarda da Yusuf daya ce son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi ba karya ya fadi ba don ni na dade da sanin haka tun tuni.
Ina jinta saidai ban yi mata magana ba har ta gama fadin abinda zata nace ke idan nace zan bata lokaci ga wanan mutumin ba zaki min fada ba maryam.
May ke cikin gidan irin su Abdulsamad banda tarin rikici da tashin hankali kulun ni kwadayi bai kai idona ya rufe ga abin hannun shi ba wallahi.
Salama nike nemawa rayuwana ko yaushe ba zan tsaya in yaudari kaina ga abin da nasan yafi karfi na tun yanzu akan matar shine fa ya daina kulani ke ma kin san da hakan.
Tace da sauri Kin san uzurin shine da zaki yanke mai wanan hukucin haka khadaji idan yana son ki ko Allah ya kaddara akwai aure a tsakanin ku matar shi ta isa ta hana ne ko tayi kamar Allah ne.
Sai dai in kece zaki bata kafan da zata hana din ta dauki kanta inda Allah bai kai ta ba kinatsu khadija ki san may son ki da zuciya daya.
Ni na fahinci A,A irin mazan nan ne da furta kalman so ke wahala a bakin su sai dai suyi ta nuna ma mace alama amma basu iya furta mata da baki.
Nace shine kike son in tsaya wahal da kaina gare shi ko may ni koda ya furta bai mun ba don ba zan so shi ba ma ban ra,ayin mijin tace a rayuwa na.
Ban yarda ba wallahi ke ma kina son shi kishine dai ke damun ki ke ma kina ganin kamar ya mutu akan matar shi ya daina kulaki don ta.
Haka zuciyar ki ta fada maki ashe nace mata bata ko fada maki daidai ba ke nan idan tace maki nima ina son shi.
Tace idan baki son shi may yasa yanzu kika rage mashi tsiwa irin da don da dane da yanzu kunyi fada a motan nan yafi a kirga.
Nace amma kin san wulakanci bai da kyau ko saboda haka ne na kyale shi badon komai ba yanzu dai ai kanku ake ji ku karaci gulman ku ku dawo hanya dai.
Indai har kin san kina son shi ya kamata ku daina wanan shirmay tun wuri tun bazuwa bata kara kwace maki shi ba kuma.
Ta kwace shi mana shi ya shafa bani ba nace mata cikin kunan rai tace dukkan ku dai ya shafa khadija bashi daya ba kin dai san so yanzu koda kike kirarin baki taba so ba a rayuwan ki.
Washegari a wurina su Binta da zainab suka wuni don ba shiga school Friday ne yau sai sunday zasu koma kd.
Don haka da yamma muka shiga gari dasu yawo sunyi mamakin sanin garin da nayi don sanin da sukayi min ba mai rigima bace ni.
Munsha yawo sosai rana sai dare muka dawo hostel dasu bamu dade da dawowa ba wayan Binta yai kara ta dauko da sauri tana dubawa take fadin nashiga uku yayane fa ke kirana zainab.
Zainab tace dauka mana kiji may yake kiran mu nasan dai sunga dare yayi ne bamu dawo ba suke neman mu ta dauka tana fadin hello yaya A,A yace kuna ina ne har wanan lokacin hankali mutane ya tashi.
Tace gamu nan wurin khadija tun dazu ita ce zata rako mu mu dawo yanzu yace tana da motane tace a a yaya karatu fa take yi ina zata samu mota kuma ?
Yace ganinan zuwa in dauke ku yanzu ku jirani in zo yace ya kashe wayan kallon ta mukayi nace yanzu ba zai bari ku kwana nan ba ke nan ?
Tace tunda kika ga yakiramu ai haka yake nufi damu nace bari yazo ni zan fita nagan shi da sauri tace ke baki san halin shi bane bari kawai yazo din mu tafi gobe sai mu dawo muyi sallama ba shike nan ba.
Zainab tace ni nafi sakewa a nan wallahi amma can gidan duk a tukure muke wallahi shegiyar matar nan tashi bata bari mutum ya wala a gidan.
Dariya nayi mata sosai da take fadin haka ba a jima ba sai gashi ya kirats yana fadin su fito nace barin je in gashi tace bari dai mu tafi ban son fadan nan nasa wallahi.
Maryam tace ku bari ta fita ta gan shi mana ai zai yarda ku kwana nan idan ta roke shi baku san ko waye bane yaya AA kawai.
Mikewa nayi na fita batare da na kula da kayan dake jikina ba a lokacin yana zaune a cikin motar shi ya fitar da kafa daya waje yana shakan iskan dake kadawa a lokacin .
Na iso gurin sallama nayi mai ya dago kai da sauri yayi min wani irin kallo ya kawar da kan shi kuma kallon da ada in yayi min nasan na bata mashi rai ke nan.
Sai dai yau ban san may yake nufi da hakan ba da yayi min shi nace don Allah ka barsu su kwana guna tunda gobe ne kawai haduwan zasu koma gida jibi.
Ya sake kallo na a karo na biyu yace su ke son kwana nan din sukace maki nace suke son hakan bani ba yace to shike nan indai zaki basu kulawan da ya dace may zai hana nace mai sai yadago ya dube nayi saurin kawar da kaina gefe daya nima.
Nace na gode na juya zan tafi naji yace khadija nayi saurin juyowa sai naga ya kada kai kawai sai kuma yace may yasa kika fito waje haka da wanan kayan ?
Don Allah ki bar fitowa haka na roke ki please kallon kayan dake jikin nawa nayi sai lokacin na ga kayan don na cire abayan da na dora sama da muka dawo daki.
Ki kula daga yau ban son ganin mace a waje haka gara idan mace tana cikin gidan ta zata iya amfani dashi haka ko ga mijin ta.
Kai na rausaya cikin wani irin jan aji da ban san nayi ba nace ga matar da bata da miji fa itama sai a hanatayin yadda take so ko may.
Yayi tsuki yace na dai fada maki ban so ki kula daga yau kada in sake ganin ki haka a waje daga yau.
Jikina ne yayi sanyi na kasa yin wani magana kuma ya kawar da kan shi gefe bai sake magana ba sai ya mayar da kafan shi daya dake waje tare da jan kofar motar yana fadin ni na tafi sai da safen ku.
Kin dai ji abinda nace dake ki kiyaye duk abinda nace dake ban so ban so ne ya rufe motar yai mata key gurin nake tsaye kamar wace aka kafe har ya bace ma gani na naja kafata na koma ciki.
Ina shiga na samay su har sun shirya suna jiran shigowa na dakin nace dasu yadda na gansu a takure yace ku fito bai yarda ba wai.
Zainab tace ai dama na sani don kada kice mun hana ki ne do ba mu son kwana din amma ninasan ba zai yarda ba ta fada a sanyaye.
Tare da fadin tashi muje Binta binta din taja wani tsuki tana shirin mikewa nace ya tafi fa tace don Allah ki bari nace wallahi ya tafi tun dazu na tsaya magana ne a waje.
Wai da gaske kikeyi khadija nace wallahi ya tafi yace sai da safen ku tunda anan kuke son kwana indai kula daku naso ce mashi mudake nan wake kula damu ?
Da sauri tace da kin muna tsiya wallahi nan dai muka sake muna ta hiran mu kayan bukin da muka dawo dashi a tare dasu mukai amfani dashi.
Sai hiran buzuwa da Binta ke ta bamu a dakin wanda inda tasan yadda raina yake baci da ta daina bamu labarin abin haushi haka.
Washe gari ma kusan tare dasu muka wuni a hostel din mu sai da yamma muka je gidan tare dasu yiwa sauran yan uwa sallama.
Mommy tace khadija kice bakin naki ne dai wanan irin fresh da sukayo haka wurin ki dan kwana daya da rabi injin dai ba dan abincin naku suka cinye ba.
Shine ya shigo nan ya gan mu kallo daya yai muna ya kawar da kanshi gare mu gaishe shi suke yi yace da alama kunji dadin zama a inda kukaje din ke nan.
Mun dan jima tare dasu mukai masu sallama suka rako mu zamu tafi sai ga driver yace ance ida zamu koma a sauke mu .

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[28/10, 7:12 am] +234 706 638 5450: Tun wanan ranan ban sake ji daga gare shi ba ban kuma koma ta kan su ba ina karatuna hankali kwance don komai ina dashi a tare da ni.
Ashe suna da kwana biyu bayan tafiyan bakin shi tafiya ya kama shi nan Nafisa ta tubure akan may zaiyi tafiya yanzu bayan yan buki basu gama tafiya ba.
Idan na zauna may zan maki a gidan ina kudi kika sani na kashe maki wanda ni kai na ban san iyakar shi ba.
Yan uwana sun tafi da takaicin abinda kikai masu a gidan nan bayan sun san da komai nayawa kike kadagi a gidan nan amma kika rufe ido kika hana masu komai da na kawo gidan .
Haka suka tafi da bacin rai a tare dasu don ma mommy mace ce mai tunane da sanin ya kamata ta sa na samo masu abinda zasu koma gida dashi.
Don baki da kunya yanzu zakice ba zan tafi neman kudi ba idan ban fita ina samo kudin nan a zaune kudin da kike kashewa zasu samay mu ko may ?
Tunda ya fara magana bata katse shi ba sai da yakai karshen maganan shi tace ina da sunana kasai abin bukin ?
Baka ce da wasu yan uwa naka zamu raba shi ba idan bakayi ba wa kake son yayi min da ?
Tafiya kuma kana nufin ni kadai zaka bari da wahalan dubar yar ka ko may tare muka samay ta don haka tare dakai zamu rene ta babu inda zaka a yanzu kaji na fada maka.
Yace tunda ke kika ajeni sai ki hanani zuwa mugani idan zaman ki nake yi ba ke ke zama na ba a gidan nan Nafisa kin dauki kanki ki kai inda Allah bai kaiki ba fa.
A da ana fadin ina ganin don ba a kaunar ki cikin mu ne yasa ake maki haka ashe halin ki ne hakan ban sani ba ina jiye maki ranan da reshen ki zai juye maki a gidan nan idan har baki nemi shiri da yan uwana ba.
Tace wanan tunane kake a ranka dama akwai wani rana da zaizo min ba daidai ba gidan nan har in neme shiri da yan uwan ka to kasani babu wanan ranan a rayuwana da zan shirya da yan uwanka.
Tunda tun farko sun iya nuna min rashin kaunar su gare ni yanzu may zai sa in dawo ina shiri da mutanen da basu so na ko kadan.
Yace aike baki da kunyan fadin magana wani irin sone basu nuna maki ba da kika zo gidan nan musanman ma mommy amma kikai fatali da kowa don ke kan ki kawai kika sani .
Ya ture ta gefe ya fita rai bace zuwa inda ake neman su dan bayanin tafiyan su ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki.
Don dai malamin ta yace da ita yanzu AA a tafin hannun ta yake saboda sun gama daure mata shi yadda take so kuma ba karamin kudi ta tura wurin yin wanan aikin ba.
Shiko bayan ya fita daga gidan rai bace bai tsaya ko ina ba sai inda club din millonear in the world yake ya cika komai da zai cika na tafiyan shi kasan.
Take a nan wurin suka maida mashi da amsa sakon shi ya karbu sai kudin da zaiyi tafiya da na komai suka turo mai yana barin haraban wurin ya wuce wurin Yusuf kai tsaye.
Ya samu Yusuf wajen gidan yana shan iska taee da waya a hannun shi yana yi wuri ya samu ya zauna daga gefen shi ya tsiyaya lemon da yagani wajen yana sha.
Yayi mamaki daya fahinci Yusuf da mace yake wayan yana kashe murya tare da zuba soyayya baki ya tabe ya kawar da kan shi gefe yana jiran ya gama wayan.
Ya gama yana kallon shi fuskan shi dauke da murmushi yace ya dai ina ka fito yanzu haka sai da ya dauki cup din juice

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login