Showing 27001 words to 30000 words out of 221707 words
namata magana” hararan Ya Ramla yayi yasake tamke fuska sosai shi adole babba sannan yakalli Asmeey yace “Mom is calling you” yajuya abinsa, faduwa gaban Asmeey yayi sosai ta tashi da rabin gashi akitse tawuce Nana tadan saci kallon Munir da tun tana yar karama take sonshi Ramla tace “dalla kidena tsoronshi” murmushi tayi tace “cikamin ido yake Ya Ramla” baki Ramla tabude tace “Munir din ahhh babban magana” shigowa falon sukayi ga Baba da Kawu akan carpet sunashan shayi dake kamshi sosai Baba dake kallon Asmeey tun shigowanta yace “ina zaki da gashi haka ba kallabi” da sauri ta taba kan tace “Mom ke kirana yanzu na manta da kallabin wajen kitso ne” gyadamata kai Baba ta wuce sama afalon Mom taga Mama, Mom na shiri da Mama sosai da Kawu but Mamie kano ne dai basu cika shiri ba dakuma Abba suma bawai fada suke ba kawai dai haka suke sunfi shiri da Ammi su, Mama dakecin samosa tace “Hajiya Salima I trust you dan Allah Asmeey ma ki sama mata gangariyan miji gaskiya dan matar manya ce yarinyar nan ga kyau ga diri dudda naga sai karewa take maybe zullumin zuwa law school ne” akunyace Asmeey tadan sauke fuskanta kasa, Mom tahade fuska tace “zonan” rawa hannayenta suka fara har Mama saida ta lura amman taja baki tai shiru kafin ta shiga black book din Mom, wucewa Asmeey tayi gaban Mamanta wani kallo Mom tamata tace “wuce ki daukomin kayan dana dinkama Maman ki da wanda na dinka miki dasu Nana” wucewa tayi bedroom din Mom, Mama tace “ohh baki gajiya Hajiya Salima! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah kara girma da daraja” kawo kayan Asmeey tayi bakin Mama har kunne Mom nada kudi so manyan exclusive atampopi ne Mama tace “Allah dai yaja zamaninki wlh Babansu Aya shi kanshi yasan yayi dace saisa har yau har gobe kece yar gaban goshi, Aya zatazo namata godiya ko, mijinta ya fitar da zakka dubu dari biyar ta aikamin wlh” murmushi Mom tayi na isa irin abin nan takeso Asmeey ta kalli Mom tace “Mom natafi”? Mom tace “yaron nan has been calling you go and talk to him kafin ki koma” wani iri Asmeey taji, badaman yakira bata dagaba saiya kira Mom, wucewa tayi tafita daga dakin, dakinsu ta wuce ta zauna kan gadonsu tadauki wayan taga 5miss calls nashi, instead of takirashi back sai kawai ta kwanta ahankali kan gadon tarike wayan a hannu within 2mins bacci mai dadi ya kwasheta cus tun asuba data tashi bata koma bacci ba tana wajen Mom, kusan 1hr tana bacci sannan wayanta ya shiga ringing firgigit tabude idanu tana tashi zaune tana mamakin yanda bacci ya saceta haka, daukan wayan tayi takai kunnenta ahankali tace “hello” “Wifey how are you”? Abu taji ya tokare mata wuya she hates d name sosai, da kyar tace “fine” yana murmushi da tana iyaji a muryansa yace “sorry banzo ba har yau ban dawo garin ba sai yau, ya shirye shiryen salla ni da Mommy na zamuzo washegarin salla” gyadamai kai tayi batace komiba cus bama tasan mezata ce ba, matse murya yayi yace “I can’t wait to see you my wife Asma’u” wani iri jikin Asmeey yamata ta runtse idanu, Fawaz yace “kullum sainaga fuskanki a bacci, I don’t know why I love you this much, me kikamin”? Kin magana tayi Fawaz yace “wai yaushe zaki dainajin kunyan mijinki eh? Relax and talk to me babu abinda yakai muryanki dadi arayuwana”? Murya chan kasa mai dari dari tace “kitso akemin zan koma akarasa” dan shiru yayi he feels kaman bata sonshi but he don’t care, ahankali yace “okay kije toh zan kira anjima take care” dasauri ta katse wayan ta ijiye wayan akan gado tanemi another blue veil karamin veil tadaura saman kanta sannan tafito Ammi tagani tana fitowa daga dakinta kaman itama ta hauro tai salla ne ganin kanta bangare daya himm bangare daya a kwance tace “meya faru ba’a gama miki kitso ba har yanzu Asmeey kowa yayi nashi kitson agidan nan?”ahankali tace “Ammi bacci ne ya kwasheni a daki” hararanta Ammi tayi tace “wuce ni kafin in mangareki awajen nan yarinya kaman mage”wucewa tayi tafita sauka kasa Ammi biyeda ita tabude kofa tafice Baba tagani da kanshi yana bude gate murmushi yalwace a fuskanshi, motan su Abba na danno kai dan nasu ne agaba hakanan gaban Asmeey yawani fadi shigowan motan zaro idanu tayi tace “Ammi Gwaggo ta iso”? Daidai nan yaran wajen lalle harda su Ramla da Munir dake wajen dasu Nana suka kwaso da gudu suna ihun. “Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyoooo” Kashe motan akayi Abba ne yafara fitowa yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunsa atare duka yaran gidan sukai kan Abba. “Abba oyoyoooo!” Abba yabude hannunshi dukan uban yaran ya rungumesu, Mamie ma tafito ta zagayo ta dayan bangaren yaran suka saki Abba ta zago ta gaban motan suka rungumeta, Ammi dahar ta wuce tajuyo takalli Asmeey dake tsaye tace “wuce muje kiyi gaisuwa” hakanan kawai saitaji tabajin kunya da nauyi tadajan gyalenta gaba, tawuce wajen Mamie data tsareta da idanu, sai kawai Asmeey taji tanajin kunyan su Mamie suga fuskanta dan jawo gyalenta gaba tayi tadan tsaya gaban Mamie, Mamie dake kallonta tasaki yaran tace “Ma’u kene haka zonan” batai wata wata ba dan tana bala’in son Mamie taje ta rungume Mamie tace “Mamiee” murmushi sosai Mamie tayi tace “Asmeey” Ramla ma tazo aguje dasu Nana suka rungume Mamie, Baba yabudema Gwaggo mota yakamota tafito dan kafafun sunyi tsami tace “Muhammadu Sani wai Bauchin nan kullum kara nisa yake
Ne?” Yaran najin muryan Gwaggo duk suka arto, Gwaggo Gwaggo sun kusa kada Gwaggo, Baba yamusu tsawa. “wai bazaku bi Gwaggo ahankali ba” saukowa kowa yayi su Ya Mustapa da matayensu duk sai gaisawa ake, Mom da Mama suka fito atare sai gaishe gaishe ake everyone looks so happy har lokacin Asmeey na tsaye kusada Mamie, Baba yashiga bin ko’ina da kallo
Abba dake lura da shi yace “me kake nema Muhammad” Baba dake kalle kalle yace “Yaya naga tundaga kan Mustapha har Hassan nagani amman banga Hussaini ba, ina Hamadi”? Kawu yace “ai wannan ka sanshi” girgixakai kawai Abba yayi yace “yana mota” anatse Baba yawuce wajen motan kai tsaye yabude kofan gaba yace “Hussaini har yanzu dai halin nan na nan to sauko, fito” kowa na compound din juyowa yayi jin maganan da Baba yayi, ahankali Asmeey dake tsaye kusada Mamie gaban motan da Baba yabude tajuyo daidai Hamad na fitowa daga motan kanshi akasa cike da bala’in natsuwa sai kawai gently akuma natse yaduka ahankali gaban Baba yace “ina yini Baba!” Dawani irin sauri Baba yataroshi yace “tashi tashi Son ya gajiyan hanya yakuma karfin jiki? Aikin ya warke ko”? Gyadama Baba kai yayi still kanshi na ahaka yace “Kawu ina wuni” Kawu na murmushi yace “Hamadi lpy lau ya karfin jiki Allah dai ya karamana lafiya gabaki daya” dan shafa kanshi yayi kadan saikuma yatako kadan zuwa dan nesa da Mom dake tsaye tareda Ammi da Mama sai kawai ya duka yace “Mommy ina yininku” bayabo ba fallasa Mom tace “barka da zuwa Hamad” Ammi tace “tashi tashi kaida bakada lpy mike” mikewa tsaye yayi sai yadan waiga, Gwaggo dake kallonshi tace “yanzu zai nemi Maman shi” aiko aka kwashe da dariya harda Mamie sai kawai ya sauke kanshi akunyace, Baba yace “kumuje kumuje bismillah”
Yaran suka shiga gaida yayyinsu, Asmeey takalli Hameed tace “ina yini Yaya?” “Wat happen to your face?”Juyowa Mom tayi ta kalli Hameed sannan ta kadakai tai wucewarta Asmeey tace “faduwa nayi” dan hararanta yayi tasauke kai dasauri tajuya zata gaida Ya Hamad yawuce abinshi ko kallon inda take baiyiba instead of yaje flat dinsu Baba sai kawai yawuce flat din dinsu m Ya Mustapa ya kalleshi saikuma ya kyaleshi, dan satan kallonshi Asmeey tayi Ramla taja hannunta tace “muje ciki” suka wuce flat nasu.
Duk zama akayi Baba yakalli kowa na falon ganin babu Hamad yasa yace “ina Hamad”? Ya Faisal yace “yawuce chan side din” hada ido Asmeey tayi da Mom data ℳ𝒶𝓉𝒶𝓇 wani mugun kallo mikewa tayi da sauri zata fice Baba yace “ina zaki?” Ahankali tace “zanje akarasamin kitso ne” Baba yace “je flat din Abban ku ki kiramin Yayanki Hamad kafin kije wajen kitson” gyadama Baba kai tayi tajuya tawuce hakanan taji gabanta ya fadi, duk babban salla anan Bauchi sukeyi every year tana ganinshi sau daya tun tana yarinya amman shi kadai ne cikin yayyinta magana bai taba hadata dashi ba, shine ma wanda ba’a ganinshi, shi kowa ne bayama magana, kullum yana daki saidai ranan da za’a kauye, hartakai gaban flat dinsu gabanta faduwa yake hannu tasa tabude kofan falon babu kowa ciki banda akwati nan su dake nan falon da masu gadi suka kawo.
Gently tace “Assalamu Alaykum” but shiru sai eco na muryanta da flat din yadauka staircase tafara hawa tana wucewa sama daidai nan falon sama ta tsaya ahankali tace “Ya Hamad!” Shiruu kaman babu kowa a side din, dan tafiya tayi zuwa gaban first room dakenan falon saman ahankali tace “Ya Hamad!” Jin shiru yasa ta wuce second door din saitadan taba tareda knocking tace “Ya Hamad!”
Shiru babu amsa hakan yasa tace kodai ba nan ya shigo ba wani flat yaje ko boys quarters, maybe tafita taje boy quarters taduba tana tunanin ta juyo Ya Hamad tagani tsaye abayanta awajen mummunan faduwa gabanta yayi sosai har tana neman kurma ihu tahana kanta da kyar ta daura hannuwanta duka biyun akan kirjinta ta saman gyale tana wani kalan mummunan numfashi sabida tsorata datayi ta jingina da bangon wajen da sauri tana numfashi sosai kaman kirjinta zai fita tana kallonshi fuskanshi da ruwa gashin giranshi yawani kwanta sabida lema, dogayen gashin idanunsa sun tattare sabida ruwa pink lips dinshi sunyi wani pink sosai jikinsu duk lema hakama sajenshi a jike ga hannayenshi daya nannade hannun rigan dake jikinsa zuwa sama tafukan hannayensa ajike da alamu dai he was in the bathroom yana wani irin kallonta, hakanan kasa jure kallonshi tayi sabida yanda taga yanada wani irin kyau barinma yanda kwallin idanunsa yamai kyau, tunda take bata taba tsayawa this close to Ya Hamad ba, idanunshi namata wani iri dasauri ta dauke kanta, kawai bakinta yahau rawa, cikin wata yar kamkanuwan murya da bamatasan tanada kalanta ba dayake so scattered sabida tsoro tace “ahhhmmm…..uhmmm dama daman…..” saikuma ta dafa bango kaman zata suma sabida yanda taji yacika mata gaba and he smells damn good raspberry dawani oud da lavender da sandal wood da vanilla takeji yake mata, softly murya ciki ciki yar karama mai wani irin taushi yace “who slapped you?” Dawani irin sauri tadago idanuwanta ta kalleshi today is the first ever time tunda dai tai girma tayi kuma hankali da Ya Hamad ke mata magana, cus he doesn’t talk to them, yaune rana na farko datakejin muryansa agabanta, kallonsa take kaman yanda yake tsaye shima yana kallonta bazaka iya tantance ya yanayinsa yake ba his eyes looks warm calm serious harsh sexy kai komiba, bala’in kwarjini taji yamata idanu lips dinta rawa suka shigayi sai ta shiga wasa da yatsunta tana kallon yatsun murya chan kasa tace “faduwa nayi akasa” to her biggest suprise saitaga Ya Hamad ya matso gabanta dab da ita da sauri tadago idanunta ta kalleshi bai kalli kwayar idanunta ba duko da kanshi yayi daidai tsayinta yashiga sauko da fuskanshi wajajen fuskanta da mahaukacin sauri Asmeey ta kulle idanunta daidai saitin fuskanta Hamad ya sauke fuskanshi yana kallon wajen dayayi sauka idanunshi sukayi kan kwantaccen gashin sajenta mai kyau zare idanunshi yayi daga wajen ya maida idanunshi kan fuskanta yana kallon yanda ta kulle idanunta lips dinta na rawa tana fidgeting fingers nata sosai hakan yasa yadan koma baya ya tsaya getly yace “who slapped you?” “Mom” ta amsa kai tsaye dawani kalan sauri tabude idanunta cikeda mahaukacin mamaki jin yanda tafadi gaskiya what did he do to her? Dago idanunta tayi suka hada idanu again yai mata wani kallo sai kawai yajuya zai koma first room na wajen data fara zuwa dataga kofan abude dasauri tace “Baba yace nakiraka!” Kaman bada shi tai magana ba dakin ya shiga ya maida kofan yarufe batare daya juyoba tabi kofan da kallo tasake kai hannayenta tadaura kan kirjinta dake bugawa none stop saikuma tasake kallon kofan dakin daya shiga sai kawai tawuce harda dan gudu gudunta tashiga sauka daga staircase din har lokacin kirjinta bai dawo daidai ba tayi kofa daidai zata bude aka rigata budewa Ya Hameed ne chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yace “kin gayamai Baba na kiransa?” Gyadamai kai tayi, Hameed yace “meyace?” Kallonshi tayi tace “baice komiba” sama ya kalla saikuma ya kalleta yace “did u put anything a face dinki?” Girgizamai kai tayi alamun a’a, cikeda kulawa yace “put ice okay” gyadamai kai tayi tace “toh” wucewa abinshi yayi yawuce stairs itakuma takama kofan tafice da sauri tayi wajen mai kitso tazauna aka cigaba da mata kitso har lokacin takasa dawowa daidai she’s just feeling somehow sai taba kirjinta take tana feeling heartbeat nata da har lokacin bai dawo daidai ba tanajin muryanshi a kunnuwanta da bata tabaji ba, for as long as tasan kanta Mom bata taba wani abu ta gayama kowa ba hatta Baba, but wat happened data gayamai Mom ce ta mareta yanzu idan ya sanar da wani akasan Mom ce ta mareta yazatayi? Mom ai saita kusan kasheta, baya magana so ba lallai yafada ba but idan yafada fa? Sai lissafi daban daban take aranta ana mata kitson, kusan 10mins da zamanta awajen hakanan kawai ta dago kai ta kallo gaban flat nasu karaf suka hada idanu yabude kofa yafito daga flat dinsu Ya Hameed biyedashi dasauri ta dauke kanta kasa shima haka baimasan mesa ya kallo wajen bishiyan da baida wani nisa da gaban flat dinsu ba yawuce abinshi, hakanan Asmeey taji takasa daurewa samin kanta tayi da sake juyowa tabishi da kallo tundaga yanda yake tafiya anatse kanshi akasa Ya Hameed kuma na danna waya yana magana dashi, “he’s o quiet” tafadi aranta, saida ya shige flat dinsu sannan tadauke kanta tayi shiruu bamatasan mesa taki dawowa daidai ba in something daya faru within just 1min a flat dinsu, hancinta takai wajen kafadanta sai taji kaman tana kamshin dataji a jikinshi, dasauri tace “Mairo dan Allah kunji ina wani kamshi?” Mai kitson tace “kamshin mene Asmeey?” Tsare mai kitson tayi da idanu dan sun dakatar da kitson saitai shiru wondering why is she even asking this kind of question sai kawai ta dauke kai dasauri tace “uhm ni banmasan mesa nai tambayan ba barshi kinji” dan dariya mai kitson tayi tace “ai ke koda yaushe kina kamshi bantaba zama namiki kitso naji kina wari ha Asmeey kin tuna nataba rokonki turare har kika bani” dan murmushi kadan tayi hakanan sai ta manta she’s sad ma sai tunane tunane kawai take.
YA HAMAD YASAN MARINTA AKAYI??🤩
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
MADAM DA ANTY ABAR GULMA AZO A KOYI YANDA AKE BUGA ODAFARE DA YANDA AKE WAWATSULA AGADO🥳🥳
WACCE TA IYA BALAJA’U A GADO ITACE MAMMALLAKIYAN ZUCIYAN MIJI 🎊🎊🎊
AZO ASHIGA INTIMACY CLASS DA 5k RAK AKOYI HARKA OGA YA ZUZUCE🔥
CHAT ME UP NOW AND JOIN
wa.me/+2347012181461
EPISODE 🔟
Wuraren biyar saura aka gama mata kitson dayayi yayi bala’in kyau, yan kanana aka yaryada mata su, sai fuskanta da goshinta suka fito sosai, ga gashin yayi tsayi, su Nana daman an gama musu lallin nasu da komi itane daman tarage kuma Mom tace bazatai lallen ba, mai lallen tace “Ammi tace idan an gama kizo ki karbo mana abinci” gyadamusu kai tayi ta tashi tareda sa dan gyalen nata ta yafa tarike na sa a hannunta tawuce backyard inda Ammi take tareda Mama dasu Anty Nafisa da Anty Mims da Anty Meena matan su Ya Mustapa Ya Abdullahi da Ya Faisal dakuma matan dake asalin aikatau din da aka dauko, Anty Nafisa tace “an gama kitson Asmeey?” Gyadamata kai tayi tace “eh an gama Anty” Mamie ta kalleta tareda murmushi idanunta suka sauka kan hannayenta da kafafunta dasuke nan farare kal tace “lalle fa? Kowa harmu tsofaffi munsha lalle balle ke yar yarinya” hannunta ta kalla saikuma ta kakalo murmushi batai magana ba, da zuciya daya Anty Mims matan Faisal tace “ko masu lallen basu iyaba ne? But naga wanda akama Nana yayi kyau ko Mama”? Dasauri Mama tace “yayi kyau sosai kam daga jan har bakin ai saisa duk babban salla basu yarda suyi lalli a Gombe saisun iso nan Bauchi” dan dago kanta Asmeey tayi ganin duk kallonta suke yasa cikin innocent voice tace “bayan salla zanje law school saisa banyiba is not allowed a law school” tana maganan saiga hawaye nataruwa a idanunta da sauri tajuya ta goge hawaye saikawai tawuce dasauri muryanta nadan rawa tace “Ammi wai akai musu abinci masu lallen” tabar backyard din all of them knew she was crying so no one bothered to call her back wucewa tayi tafito daga backyard din ganin hawayen yake tsayawa yasa tayi chan parking space nasu dan gidan ko’ina da mutane dukawa tayi gaban daya daga cikin motocin wajen bawai kuka take wiwi ba but hawaye ke fitowa daga idanunta sosai sai sharesu takeyi da bakin gyalenta, she’s feeling sad again wlh, she’s not happy, tasan wani yaganta tana kuka can be a problem especially idan Mom tasani, bude kofar mota akayi hakan yasa tadago rinannun idanunta da sauri dakuma tsoro, Munir tagani yafito daga motan Abban Bauchi, maida kanta tayi ta sauke kasa ganin shine tana goge fuskanta, karasowa wajen yayi cikeda damuwa saiya duka gabanta yace “wat happened Ya Asmeey? Mesa kikazo nan kika boye kina kuka? Mom ta dakeki ne”? Kallonshi tayi yanda yake kallonta cikeda damuwa dakuma so sai kawai yanzu kukan yataso mata tafashe da kuka sosai tana kallon Munir, ja idanunshi yayi cikeda bakin ciki yace “Mom ne ko?” Gyadamai kai tayi cikin kuka tanunamai hannuwanta tace “kowa yayi lalli agidan nan banda ni Munir” har wani daci zuciyan Munir yakeyi, kowa is happy agidan nan banda sister shi, kowace yarinya in this