Showing 156001 words to 159000 words out of 221707 words

Chapter 53 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

abinda nake cewa shine sabida bikinta bazan fasa zuwa aiki na ba, ni da zan karbi sabon appointment zanyi tafiyana gobe, gaskiya!” Shiru Baba yayi tunda dai tace takura batai hayaniya ba is the most important thing to him, anatse yace “shikenan zan kaiki airport dakaina gobe, zan baki miliyan biyar wannan kaman na sauke nauyi ne na abinda na miki amatsayinki na mahaifiyar Asmeey ga kudin bikinta kema” murmushi Mom tayi tana hadiye komi tace “to nagode” wayansa ya dauka yamata transfer 5M tai murmushi tace “nagode” rungumeta yayi yace “komi yawuce matana” haka ya kara komawa second round da third round da 4th round sai wajajen 1 yafito daga bangaren Mom din, shima zaije kano but sai ana gobe biki dole yaje daurin auren dansa Hameed, Ammi ma zataje gobe sabida kai akwatin Hameed but zatabar Ramla ta zauna da yaran da yan aiki sabida school, Ramla taci kuka cus taso taje saida Baba yasa baki yace bayan sun dawo zataje tamusu kwana biyu sannan tahakura Munir ma school bazai barsa yaje ba.

Washe gari Mom tahada kaya a LV bag Baba da kansa yakaita airport yarakata har ciki yawuce yatafi yana tafita tashiga line na jirgin kano not Abuja tai kwafa tace “da ni daku za’aga wanda zaici wasan nan! I’m going to carry my daughter! Karshen auren nan yazo! Idan ko bahaka ba cikin ni ko Hamad dole zakuga gawan daya!”
**

Kano!
Mamie kwata kwata bata bama Asmeey kayan mata ba inama zata iyasha cikinta ya shiga wata na uku yanzu ne take asalin laulayi, kaniyanta takeci sosai, mugun laulayi take, batason kamshi batason wani batason any kind na smell, sau daya aka mata gyaran jiki na fata ba’a kare lafiya ba, warin abubuwa yasa tadinga amai sai zazzabi saida ta jera kwana uku skin dinta irritating nata yakeyi sabida warin abun. Kowa na gidan tausayinta yake har Abba, har yayin Hamad dan Asmeey najin jiki, tuni ta ijiye kunya gefe daya dan idan tafara wani zazzabin tarasa meke mata dadi, ko’ina zaka iya zuwa kaganta agidan a kwance, kwadayiko har kasa taso tafara ci Ya Mustapa yahana sabida yawu, yayyin basu taba zuwa hannu banza basu kawo mata wani abuba, kowa naji da ita kaman kwai kaman ita tafara ciki, kawai duk tausayinta suke, ga ciki ga ba miji, gata yarinya, ga babu mahaifiya tsaye akanta, yayyi sun dauka tana kasan waje, so they’re taking care of her like an egg wlh, matansu ma girke girke suke suna aiko mata dashi cus cn abinci is hassle, har Zee takan mata su iloka ta aiko mata dashi, kai Asmeey na jin jiki, dudda Mamie na cikin hayaniyan biki but she’s taking care of the girl very well, bama ta fita, wani sabon kaunar Asmeey take ba kadan ba, hakama Abba zai iya kira sau biyar daga kasuwa yana tambayan jikinta koyace yaga kaza ya siyamata Mamie ta tambayeta tace eh aba yaran shago su kawo gida.
Gobe za’akai akwatin Zee na Asmeey na gidan adakin Abba, but sai Ammi ta iso Mama ma haka duk yau zasuzo, Hamad na kula da ita sosai shima, yanda yakejin sonta da cikin nan abin yabaci kaman zai zare, shima yaune flight nasa 18th to da daddare zai iso.

Tana kwance a falo babu dankwali akanta da aka mata kitso kanana jiya masu kyau fuskan nata yayi kyau tarame but tayi wani irin kyau bana wasaba hannunta rikeda cube din sugar guda biyu wanda yanzu shine abinda take masifan so yana hanata tara miyau abaki ga cartoon tana kallo a Tv Ya Mustapa yashigo gidan tareda Faisal yunkurawa tayi da kyar zata tashi zaune Ya Faisal yace “yi kwanciyarki Asmeey” dudda haka tashi tayi zaune taja dankwalin atampanta tasa asaman kai shi kansa Ya Mustapa is not happy da ramanta but he knows harda ciki da kewan miji she will change, zatai kiba cikinta yasoma fitowa, ahankali tace “Yaya ina yininku” atare suka amsa, Ya Mustapa yace “ya jiki meke miki ciwo yanzu?” Girgiza kai tayi tace “bakomi yau” Ya Faisal yace “ba dole Babynki na hanya zai dawo” akunyace tarufe fuskanta da dan kwali Ya Mustapa ya ijiye mata keda kusada ita dasauri ta ijiye two sugars na hannunta duk suna kallonta ta shiga bude ledan tace “thank you Yaya” aya mai sugar ne, da gyara mai gishiri na leda da kantin gana, da tsami gaye, wani murmushi tayi sosai tace “thank you Yaya” Ya Faisal yace “laaaa kaga she likes it Ya Dr daman kace masu zuwa Anti nanta a asibitin ku rushing abin nan sukeyi, wai Yaya haka zanta fama idan Nana tai ciki”? Tashi Asmeey tayi akunyace zata tafi Ya Musty yace “yi zaman ki ba kallo kikeba wajen Mamie zamu” Ya musty yayi sama Faisal na binsa abaya waya ta dauka tai snapping abubuwan ta turama Ya Hamad ta Snapchat tace “Ya Doctor yakawo min”
Around 1 Ya Hameed yakawo Ammi daya dauko daga airport Mama ita jirgin yamma ne Asmeey na kasa Ammi ta shigo dawani gudu ta tashi ta rungume Ammi, Ammi tariketa tace “Asmeey yaushe kuka shigo garin? Amarya wow” Mamie tazo wajen suna murmushi Asmeey tasaki Ammi dake kallonta sosai aka shiga gaisawa duk aka tafi falo Asmeey da kanta taje kitchen takawo ruwa Mamie tace “neman amai kike saisa kiketa shiga kitchen ko” akunyace tai murmushi, tazo ta zauna tanacin ayanta Ammi na kallonta danhar ta gane ciki ne da Asmeey ohh Allah kenan yarinya har tayi ciki abinta.
Around 6 Mama itama ta iso itama batazo da yara ba sabida school Asmeey bata wani rungumeta ba kaman yanda tama Ammi ba bawai she hates Mama bane kawai tasan Mama yar fadan Mom ce so she’s kind of scared of Mama sabida Mom, Gwaggo tace “saura nafara jin zancen gidan nan awani waje sa’idawa an diro, Mama tai banza da Gwaggo tanabin gidan da kallo tace “gida ya chanza gabaki daya kaman kasan waje na kirga motoci sunfi akirga sababbi a tsakar gidan” Mamie tace “an gode Allah” sulalewa Asmeey tayi ta kwashe abubuwanta tawuce sama mijinta by 9 zai sauka akano na dare around 7 zata sauko tamasa girki, da magrib taje tai salla sannan tafito tashiga saukowa kasa a dinning taga Mamie na magana da Mama tazo wajen tadan tsaya Mamie ta kalleta tace “Yaya akayi Asma’u?” Kin magana Asmeey tayi Mama tace “uhnn nidai na wuce” takoma kitchen da sauri Asmeey tazo kusada Mamie kanta akasa tashiga wasa da hannunta Mamie tace “ina jinki” ahankali Asmeey tace “uhmmm…..Mamie….d….dama so nake nai girki” sarai Mamie tagane sotake tama mijinta girki dudda Mamie tama Hamadi abinci da dama yanzu hakama akwai some a wuta amman sai anatse tace “zaki iya?” Gyadama Mamie kai tayi Mamie tace “tom muje kiyi sai atayaki rage ayyuka me zaki dafamai?” Ahankali tace “taliya” Mamie tace “okay” shiga kitchen din sukayi Mama na soya kifi a pan, kifin Asmeey takalla ga kamshin na dukan hancinta kawia taji cikinta ya hatsine, tun aman brush na safe yau batai wani ba she was very happy hartana cewa ta warke sai yanzu hannunta tadaura abaki tai wani kakarin amai da sauri daga Mamie har Mama suka kalleta Mamie tace “you see ba” tashiga bude mata kofan backyard dasauri tafita kafin takai wajen grass ma tafara amai ba kakkautawa duka abincin da Asmeey taci yau taketa murna ya zauna saida ta amayar, Mama takashe gas tafito tana kallon ikon Allah itama tana mata sannu Mamie na bubbuga mata baya tace “sannu, yau baki amai ba inata murna amman kalli yanzu” fitowa Gwaggo tayi dan ta window tajisu cikeda fada yace “mema yakaita kitchen din iyye? Ke wai bazaki rufama kanki asiri ki lallaba wannan cikin naki me mugun laulayi ba!”Faduwa gaban Mama yayi cikinta har wani kyarma yake no wonder taga yarinya tai fara kal kaman zata koma zabiya tayi kyau jikina ne dai babu ashe ciki ne da ita, wankewa mata fuska Mamie tayi Asmeey ta kuskure baki ta mike tace “bari na wanke aman chan” Mamie tace “nasaki? Oya zagaya ki koma compound ki shiga ciki kiwuce sama” Gwaggo tace “barta sotake ta fiffige kamin Hamadi ya iso” Ammi data fito tace “ba shuwaka ne idan zuciyanta na tashi taci yanamin aiki lokacin” Mamie tace “banda shuwaka shine kawai abinda ban shuka agarden ba nama manta, Ammi ko zaki dan tayani kaita daki ba karfi jikin nata” dasauri Ammi takama Asmeey suka zagaya suka shigo sukai sama har dakinsu Ammi ta kaita ta kwantar da ita ta zauna gefen gadon tace “sannu kinji haka ciki yake Allah saukeki lpy, the journey is not easy”hawaye ne yataru a idanunta ahankali tace “Ammi nagaji da wahala, inaso nayi girki amman koyaya naji kamshi sai cikina ya rikice” dariya Ammi tayi tace “hakanan zaki saba kuma yanzu kika fara kuwa zaki saba ne sabida na farko ne saisa kikejin wani iri” ahankali Asmeey tace “Ammi ina Mom?” Dan shiru Ammi tayi tana kallonta Allahu Akbar she just pity this girl yabda takeson mahaifiyarta, murmushi tayi tace “tana Abuja za’a maidata Chief Judge na Bauchi taje tai paper work” murmushi Asmeey tayi cikeda jin dadi tace “finally! Mom tadade tanason that position I am so happy wlh Allah sa albarka” ahankali Ammi tace “Ameen bari naje” ta tashi tafito gama soya kifin Mama tayi jikinta har kyarma yake daidai wayanta na ringing Ammi ce kadai a kitchen din tace “bari nai waya da yaran nan suke kirana” Ammi tace “agaidasu” ficewa Mama tayi ta kofar baya tai backyard din tama bar wajen duka tana rejecting call na Nana tashiga kiran Mom ta zaga chan hanyan dazai bullo dakai asalin compound yanda babu wanda zai ganta tashiga kiran Mom, is as if Mom has been waiting for her call yana ringing ta daga tace “ke Maman Aya kinsan meke faruwa kuwa? Da zafi zafinsa nakira na baki update” dan ijiyan zuciya Mom tasauke cikeda gadara tace “ina jinki” dan juyawa Mama tayi tai kalle kalle dan kara tabbatarwa babu wanda yabiyota tace “kin kosan Asmeey nada ciki!”? Wani durum news din yadaki kan Mom, wallahi wallahi to some extend bata tabajin dar na yaron nan zai kwanta mata da diyaba sabida she believe abubuwan data gayama yarinyar nan ko Asmeey na hauka bazata yarda tabudema mahaukacin nan kafafu ba, yanzu Asmeey ta tsallake tsinuwanta ta aminta da mahaukacin nan kutumar uba, Asmeey bata tsoronta kuma? Kasa yarda Mom tayi tasan Baba forced the girl a aure she can stay ba yanda zatayi but budema yaron kafa after everything she told her is very impossible, no she don’t think ciki Asmeey ke dashi, tace “anya Maman Nana!? Anya Asmeey nada ciki”? Dasauri Maman Nana tace “na rantse miki da girman Allah ciki ne da Asmeey kumama irin cikin nan dakaman tana shigowa ta sameshi ayanda take laulayi da kyarne idan bata cikin wata na uku to duka duka bikin nasu ai wata uku ne da yan kwanaki yanzu, that means ana musu auren basu wani bata lokaci ba sukai tarayya!”.
EPISODE 8️⃣3️⃣




Jikin Mom harwani kyarma da zabura yake sabida bacinrai tama kasa magana ita Asmeey zata watsama kasa a idanu? Ita Asmeey zara yarda ta amincewa mahaukacin nan bayan duk abubuwan data gayamata? Asmeey dares sleep with that imbecile? Mama cikin exaggerating abu tace “ciki dai dakika sani shi Asmeey ke da shi sai uban laulayi ta……..” katse wayan tayi da sauri jin sahun tafiya tajuyo afirgice, Mamie tagani Mamie tahada rai sosai, murmushi Mama tayi tace “Mamie kece wlh nida su Nana ne kinsan yara” ba kunya ko shakka dan enough is enough strictly Mamie tace “idan gulman yarana kikazo yi Maimuna ki tattara inaki inaki yanzun nan nasaka amaidake airport kinemi jirgin Gombe kitafi” dasauri Mama tace “laaa Mamie? Meya faru? Wannan maganan fa maiya kawota?”Cikin tsananin bacin rai Mamie tace “kul Maimuna karki rainamin wayau ni ba tsaran wasanki bane, danayi aure dawuri zan iya haihuwarki wlh da kadan kika darama Mustapa na ashekaru! Nasan dawa kikai waya, I know duka abubuwan dakikayi tun a Bauchi nasan ke kika sanar da ita zancen auren in the first place, daga zuwanki harkin kirata kina sanar da ita zancen cikin Asma’u, cikin shege tayi dakika kai gulma? Koko an gayamiki cikin baida uba ne? Ke uwace kin haifa yara mata bazaki daina wannan halin haddasana ba? Da ace dan alkhairi kika bada sanarwan cikin nan bazanji haushi ba amman kinfi kowa sanin waye Salima wani fitinan kikazo shiryamin agida? Ko ko so kike kada ayi bikin yarana lafiya iyye?” Sunnar da kanta kasa Mama tayi kunyan duniya yagama lullubeta, Mamie tace “Allah yakaimu gobe da safe ki tattara kibarmin gida nagaji da halinki zumunci ba dole bane inhar abin yakai ga haddasa bala’i da fitina, daga zuwanki kin farakai gulman yarana har kina lissafin sanda yarinya tai ciki, yar cikinki fa shame on you Maimuna! Shame on you!” Mamie tajuya zata tafi dasauri Mama tariketa tace “dan Allah ki yakuri Mamie, wallahi na rantse miki da Allah badan haddasa bala’i kowani abun na gayamata ba” cikin fushi Mamie tace “amman kinsan waye Salima? Baki tausayin yar yarinyar nan dake fama da laulayi tarasa inda zatasa kanta taji dadi? Haba Maimuna ke mace ce kin haifa fa kinada yara mata, kema u were once in Asmeey’s shoe kowa yasan ya cikin farko yake, banda haka shi d’a nakowa ne, baki tausayin Asma’u? Idan matar nan tazo tamata jina jina fa? Mezakice? Kinada alhaki da kamasho a zunubin, U are a mother u should protect Asmeey at all cost not expose her to mutum kaman Salima, kibarmin gida I am very serious nagaji da munafuncinki Maimuna nagaji, bikin nayafe miki kitafi, ban bukatar ki wlh har abada”ran Mamie yayi tsananin baci is not like ta tsani Mom but kawai tasan matan ta tsani yarta taji zancen cikin nan she can do the unthinkable, saita iya kashe yarinyar nan, tunda har tabata maganin bera she can kill Asmeey har lahira tsaf, Allah kadai yasan mata dalilin dayasa ta tsani yarta and now look at wat this witch munafukar is doing, sumazo ayi bikin Alhamdulillah an gama komi na Asmeey tare zasu koma DC yanzu, Mama na bata hakuri tawuce tashiga kitchen Ammi tabi Mamie da kallo da ranta yake a bace danta jisu ita daman tasan tunda har Mama tafita munafinci zatayi.
Sanda Mamie ta shigo kitchen ta tambaya ina Mama cemata tayi tafita tayi waya da yara taga Mamie tabita abaya cus Mamie tasan hali.
Chan saiga Mama tashigo duk hankalinta tashe takalli Ammi dan yanzu harga Allah tafi damuwa da fushin su Mamie cus yanzu sune masu kudi ga Hamadi bai riga yabasu komi ba su har yanzu yaron nan zai iya yabasu miliyan goma goma fa itada Ammi kuma yabasu kujeran makka dasauri tace “wlh Ammi ba gulma bace kawai hira ne ina shiri da Salima kowa yasani tace na barmata gidanta so take ta bata zumunci” Ammi tace “zumunci or not ba huruminki bane ki sanar da Salima zancen cikin Asmeey ba kibar diyarta ta sanar da ita ko mijin diyarta ko ita Mamie ko Abba ko Baba koni banda hurumin gaya mata balle ke mesa kike haka ne? Daga zuwanki da yamman nan harkin fara halin, idan an girma asan an girma”.
Cikeda rashin jin dadi Mama tace “dan Allah kiyakuri hakan bazai kara faruwa ba” Ammi kawai tawuce abinta.

Duka yayyins tundaga kan Ya Mustapa down to Hameed dukansu na airport sunzo daukan Hamad tun 8:30 dan 9 jirginsu zai sauka but andan sami delay sai 10 suka sauka kafin yafito 10:35 sabida immagration.
Ahankali yake tafiya yana sanye dawani long pant black mai bala’in kyau, ya sanya wata Rapl Lauren polo shirt fara sai kuma wani jacket na sanyi haka leather black asama dayake a bude yana goye da bagpack dinsa abaya na laptop sai LV box nasa guda daya tak yana gungurawa yana tafiya anatse dayake darene ba glasses a idanunsa yawani kara kyau fatarsa na kyalli sosai, yana sheki gashin kansa da gemunsa sun kara yawa cus all this while baitaba aski agarin ba, sai yawani kara girma wlh looking damn matured sama da Hameed ma and looking very rich yana sanye dawani Rolex wristwatch a hannunsa, kagansa saika kara kallonsa sabida yanda yayi kyau dukansu kallonsa suke babu motsi, shi baima lurada su ba kaman ba Hamad ba, Faisal yace “Hamad ne yawani kara balaga haka?” Hameed yace “yafini girma yanzu Innalillahi yaci abincin turawa” Ya Abdullahi yace “kai my brother is looking very expensive wallahi Tubarkallah” Hameed yakasa daurewa kaman wani mace yayi ihu Hamadi dasauri Hamad ya tsaya ya waigo ya gansu Hameed yataho da gudu baiyi wata wataba yawani rungume dan uwansa Awani irin kunyace Hamad ya sauke kansa duk yaji kunya su Faisal suka taho suka rungumesa duka yace “Welldone da dirkama Yar Mutane ciki ka gudu kasan waje ka barmu da raino ciki kaman zai kasheta koma me kasamata acikin nan akwai fitina kaman kai” Ya Abdullahi yace “Hamadi when did you even sleep with that girl harka mata ciki ni dannan”?.
EPISODE 8️⃣4️⃣




Turesu Hamad yashigayi sukaki sakinsa kaman zaiyi kuka yadago kansa looking for who to rescue him daga hannunsu akunyace yace “Yayaaa” ahankali Ya Mustapa yashiga zuwa anatse, Ya Abdullahi yace “wlh Ya Doctor karka shiga maganan nan, yanda maganan nan ya tsayamin a wuya, he must explain o” Faisal yace “munafukin yaro yadinga buga coitus yana tumurmusan yar mutane babu wanda yasani saidai ya tafi ya barmana result of good knacking! Sannu sharp shooter Hamadi” fizge kansa Hamad yayi da sauri yawani fada jikin Ya Mustapa ya rungumesa asanyaye kunya kaman zai kashesa, ahankali yace “ina yini Yaya” biyosa zasuyi, Ya Mustapa ya daka musu tsawa yace “leave this boy alone me haka kukeyi an airport? Zanci muku mutunci fa” Kyalesa duk sukayi kowa na kwafa, Hameed yaja jakansa Ya Mustapa yace “let’s go” dagowa Hamadi yayi suka shiga tafiya yana gefen Ya Mustapa yaki yarda ya kalli any one of them kunya kaman zai kashesa wlh shi yasan daman ya shiga uku yadawo yanda sukasan Asmeey is pregnant dinnan, kowa yasan meyayi yanzu, suna zuwa waje motan Ya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login