Showing 63001 words to 66000 words out of 221707 words

Chapter 22 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

konazo namikin tsarkin?” Juyowa Asmeey tayi ta kalli Gwaggo tace “huu’um” Gwaggo ta kwashe da dariya tace “ai shikenan jeki abinki nima daman nayi maganan ne amman ina tunanin warin dazan shaka idan kin hada da kashi” maida kofan tayi dasauri ta rufe tafito da alwala tazo tahau dadduma ahankali take salla da hannun.

Yauma haka aka wuni agidan Hamad baya nan only God yasan ina yake zuwa ansan he will definitely do that so babu wani cikin bothers dinsa daya nemesa.
Yau all through Gwaggo na dakinta hakan yasa Asmeey takasa zuwa wajen Mom but zuciyanta na zuci zucin tunanin Mom, sai bayan Isha’i Gwaggo tasa Mamie takamata ta kaita kasa dantai bacci da asusuba zata tashi tahada kaya tunda Allah baiyi zuwansu kauye ba sabida ciwon yarnan Asama.
Sallama Baba yayi hakan yasa Asmeey tadago kanta ganinsa yasa tashiga kokarin tashi dasauri Baba yakarasa wajen gadon yakai hannunsa yadagata yana saka mata pillow abaya yace “sannu ya jikin”? Ahankali tace “dasauki Baba” zama yayi bakin gadon yana facing nata yakai hannunshi ahankali yadauki hannun nata da aka kulle yana kallo yayi shiru fuskanshi yayi wani iri kasan he’s hurting hakan yasa gently Asmeey tace “Baba bayamin zafi yanzu wlh” dan kallonta yayi har yanzu fuskanta bai dawo daidai ba kana ganinta kasan taci duka wlh, sai yaji kaman Allah zai kamasa for all the pain she went through, Asmeey is the most beautiful daughter dayake dashi mai kyawun hali da hakuri da biyayya she’s going through this pain duk baisani ba and yana gidan, ijiyan zuciya ya sauke yace “mesa baki sanar dani kalan dukan da Mamanki ke miki ba”? Dan zaro idanu tayi tace “Mom bata wani dukana Baba sai once in a while kawai idan na bata mata rai ne”lumshe idanu Baba yayi yabude yace “naga jikinki Husna, i saw duka dukan, i saw hands naki” sauke kanta kasa tayi da sauri lips dinta yashiga rawa chan tace “nike mata laifi Baba” ajiyan zuciya Baba yasauke anatse yace “Asma’u” hakanan taji gabanta yafadi tace “na’am Baba” ahankali Baba yace “jiya da rana bayan sallan azahar na dauramiki aure da cousin dinki, Yayanki Hussain, Hamad!” Wani wawan faduwa gabanta yayi dasauri takalli Baba gabanta na bugawa beyond measure dan har Baba saida yagani yasa hannu yakama hannunta anatse yace “I dont know mesa mahaifiyarki kemiki abinda take miki but ban haifeki dan wani ya kashemin ke ba and Munir ya sanar dani komi dan yajuyo maganan datake gayamiki adaki kan tamiki miji da yanda tazage yan uwana harda kiran mijin naki mara aiki da abinyi”Baba yace “amatsayina na mahaifinki ni da Yayana muka hada aurenki da Hamad” kawai sai hawaye sharrr ya sauko daga idanun Asmeey tasauke kanta kasa tanaji kaman mafarki take Baba yace “sadaki dubu dari nabawa mijin naki yarike miki kudin kukaje kano zai baki, gobe da izninin Allah zaku tafi Kano aduk sanda komi yazama daidai za’a tsara lokacin da za’a kira mutane ayi yinin biki wato walima, dazu nasaka yayarki Aya tahada kayanki tsaf itada Ramla ankai mota” Baba yasauke ijiyan zuciya yana kallon ya da take share hawaye Baba yace “iya abinda nasani shine kin gama university Asma’u, zancen zuciyanki law school lies a tafin hannun mijin naki sabida shine keda iko dake, idan yaga dama yabarki kije idan yaga dama yahana shine mai iko dake yanzu” Baba yasake yin shiru sannan yakai hannunsa yakama hannunta ahankali yasake daura dayan hannunsa saman kanta yace “Asma’u nasan yanda kikeda tarbiya da natsuwa mijinki Hamad for now baida wani tsayayyen aiki, ki zama mata mai tsoron Allah da kaunar mijinta domin Allah, kada ki takuramai da siyan abubuwan kyalekyalen duniya siyamin kaza, siyamin kaza, ki zama mai godiyan Allah kiyakuri da abinda ya iya samu yabaki, kada kice dan kinga matan yayyinsa da kaza sai kema yamiki kaza, wata rana sai labari shi arziki na Allah ne, kuma yana bawa duk wanda yaso, Hamad nada kwazo zai kula dake iya gwargwado, iya karfinsa kuma kinji” gyadamai kai tayi tafashe da kuka maganganun namata wani iri, Baba yace “Hamad baida gida, yanzu kukaje kano a flat din Abba da Mamie zaku zauna kafin agama gina flat dinku, Abba Yayana ne kuma matsayin mahaifina yake bazai taba bari ki cutu ba hakama Mamie, ki kula dasu Asmeey kinga sun soma gajiyawa jiki ya tsufa ki zama mai taimaka musu da abubuwa da dama tundaga kan girki da sauransu kinji Asma’u” Baba yasa hannu yaciro wayanta da Ramla takawo mai dazu yace “ga wayanki nan nacire sim naki nada zan ijiye wajena zuwa nan gaba, nasaka miki wata SIM card danake dashi ki dinga amfani dashi, Asma’u ina sonki nayafe miki duk wani abu dakika tabamin da Wanda na sani da wanda ban sani ba sannan ina neman yafiyanki ina matsayin mahaifinki but i couldn’t protect you kalleki yau Asma’u kiyafema Babanki kinji” dawani sauri Asmeey ta rungume Baba tana kuka murya kasa kasa tace “Baba bakamin komiba baka tabamin komiba dan Allah kadena rokona Baba” tafashe dawani irin kuka, Baba yadagota yakai hannu yashare mata fuska yace “I am sure babu wanda zai kara dukanki agidan Yayana, Mijinki, Yayinki da Abba will shield you Asma’u thank you for being a good daughter to me, me rufama iyayenta asiri, mai hakuri da juriya da kwazo, ina alfaharin zama mahaifinki” kara rungume Baba tayi tana kuka, Baba yayi murmushi yana shafa bayanta yace “go and start a new life kinji”? Dagowa tayi ahankali takalli Baba tace “Baba Mom tas….”? Baba bai barta ta karasa maganan ba yace “mahaifiyarki mahaifiyarki ce har abada Asma’u but kaman yanda banda wani iko akanki yanzu itama batadashi kina karkashin Hamadi yanzu ba muba kinji” gyadama Baba kai tayi gabanta na faduwa ita kadai tasan ya zuciyanta ke mata sai wajejen 11 Baba yabar dakin ta kwanta tai shiru tana kallon sama jitayi bakinta ya bushe dasauri tatashi zaune da kyar takalli side drawer tabi duka dakin da kallo babu bottle water da dane data kira Mamie but hakanna saitaji tanajin nauyinta bamataso su hada ido, ahankali tasauka dagakan gadon tamike tsaye tunda Baba yafita bataji any motsi ba maybe kowa yayi bacci tunda gobe zasuyi tafiya, daya daga cikin gown din Ya Aya tasaka red mai botura agaba ya tsaya mata a gabada guiwa but baikai har kasa ba, babu dan kwali akanta ko hula, rigan short hand garesa, slippers tasaka tabude kofan ahankali tafito tana tafiya, hannunta always feels kaman kaya sabida nauyi ko na daurin da aka matane oho, staircase tahau tasauka a first matakalan da kyar tana shirin sauka na biyu…. “Ina zaki?” Chak Asmeey ta tsaya sabida muryan Ya Hamad dataji da kamshinsa duka at the same time, wani kalan nauyi taji tajuyo balle ta kallesa yau, sai kawai tasauke kanta kasa lips nata yahau rawa kaman yar baby tace “ruwa zanje kitchen na dauka” murya ciki kaman baiso yayi magana yace “go inside, I will bring it for you” gyadamai kai tayi still taki kallonsa ta taka bene dayan data sauka akai tahayo nan falon sama tawuce dakin Mamie, Hamad dake sanye da joggers ash color yana sanye dawani black t-shirt dayamai bala’in kyau yawuce yasauka kasa, kitchen ya shiga yadauko bottle water marasa sanyi guda biyu yahayo sama, kofan dakinsu yakalla sannan yawuce dakin Mamie ahankali yabude kofan batare daya bar door din yayi kara ba ya shiga ciki.
💫UWA KO UKUBA?💫


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣2️⃣



Hakanan gaban Asmeey yawani fadi ganin Ya Hamad yashigo dakin yamaida kofan yarufe kawai yau saitaga Ya Hamad yafi koda yaushe mata girma, saitaga yamafi Ya Mustapa tsayi da cika, maida kanta kasa tayi dasauri ganin zai juyo, juyowa yayi yadan kalleta tana zaune bakin gadon kanta akasa, yatako yafara zuwa sai kawai Asmeey tafara wasa da fingers nata she’s just so nervous and tense jikinta namata wani iri harya karaso gaban gadon ya ijiye gora daya kan side drawer hannunta Asmeey ta mika dakedan rawa zata karbi dayan bottle dake hannunsa sai taji shiru bai bata ba. Dan daga kanta tayi kadan ganin bai bata ruwan ba, budemata goran ruwan yake idanunsa nakan ruwan da fararen hannunsa kumbunansa agyare gwanin ban sha’awa, maida kanta kasa tayi ahankali, bude ruwan Hamadi yayi yakalleta tareda mika mata calmly kaman wanda baisan yanda ake daga murya ba yace “take” hakanan kawai saitaji hannunta na rawa she’s trying to control it takasa tashiga mikamai hannun yana kallon hannun samata bottle din yayi a hannun ta karba tadawo dashi jikinta still hannun rawa yake tadaura kan cinya tarike trying tadan natsu cus she’s shaking too much and she doesn’t know why, kusan 3secs tayi ahaka kafin ahankali takai ruwan baki tasha da dan yawa sannan tacire abakinta tamikamai hannu yakawo zai karba ta dauka ya amsa kawai tasaki, goran yafadi akasa dasauri ta kalla tace “sorry bansan bak….” Ta sauko daga gadon zatai tafiya ruwan yajata zata zamiye tai baya dawani irin sauri Ya Hamad yariketa ta hanyar kama waist nata da kafadanta tadan shigo jikinsa bawani sosai ba yana kallon floor din batare dayama lurada abinda yayi ba kawai tashi tsigan jikinshi yayi sosai dasauri ya kalleta itama Asmesy ta kalleshi gabanta na faduwa asanyaye eyes nawa nawani shinning, her body is so warm da yanajin warmth din a hannunsa dake waist nashi ga idanunwanta tana kallonshi dayaji cikinsa yafara juyawa da sauri yacire hannunsa daga waist nashi dana shoulder nata atare dukansu suka sauke idanunsu Hamad yadan koma baya kadan,
dasauri takoma baya adan daburce tajuya zara wuce, murya kasa kasa yace “ina zaki”? Asanyaye tace “mop zan dauko” juyawa yayi yace “don’t worry” wucewa yayi yabude kofa yafita bai jimaba yadawo da mop, Asmeey tamikamai hannu zata amsa sai kawai yawuceta yashiga gabanta yafara goge ruwan Asmeey ta tsaya tana kallonsa adan sace takasa denawa, he’s so calm! He’s kind, and yanada good heart, gashi da tausayi, and he’s respectful! Dago da kansa yayi suka hada ido dasauri ta sauke kanta kasa kaman wata munafuka, jingina mop din yayi abango ahankali yasa hannunsa yadanja zanin gadon ya gyara yasa hannu yayi dusting dudda babu any dirt agadon sannan yadan matsa gefe batare daya kalleta ba ahankali yace “zoki kwanta” gyadamai kai tayi ta taho ahankali ta shiga kwanciya da kyar yadan tsaya yana kallonta saikuma ya matso gadon dasauri ta kalleshi kallonta shima yayi right in the eyes dawani irin sauri ta lumshe ido, bargon yadauka yana rufa mata saiya sauke gaze nasa kasa yajuya dasauri yadauki mop daya jingina a bango kafin chan kasa kasa yace “good night Husnah!” Wani kalan runtse idanu Asmeey tayi da karfi tanajin wani iri ajikinta, the way he called that name Husnah sai kawai taji no one does it better than him, saitaji tafison ana kiranta Husna than Asmeey ma, bude kofa taji yayi hakan yasa tadan bude idanunta kadan daidai yana fita juyoda kansa yakarayi da gudu ta runtse idanun sai taji yafice ya maido kofan yarufe ahankali. Bude idanunta tayi tana sauke wani irin ijiyan zuciya she’s feeling some wired movement ajikinta especially her tummy kaman butterflies na tashi, murya chan kasa tace “yanzu ni Matar Ya Hamad ce? Matarshi Matarshi?” Sai kawai tawani kankame bargon murmushi takejinyi but saitakiyi, wani dan karamin waje in her heart is happy she’s his wife batamasan mesa hakan ba ko menene dalilin ba, but the rest of her heart is just fear tana mamakin tayaya Mom ta yarda da aurensu da Ya Hamad cus batason mutanen kokuma Mom bata yarda ba Baba yamata auren? Or maybe Mom ta yarda sabida abinda Fawaz yamata? Sai saka take tana warwara ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
*

Itadai Mama ta lurada yanda aketa kuskus barinma wajensu Gwaggo dazu kuma tana flat din taga Ammi da Mamie da Abba da Gwaggo da Aya sun fito daga dakin Gwaggo ana ganinta sai akayi kaman an chanza topic which is so unusual koma meeting ne koda yaushe ana sata aciki abun kuma ya tsaya mata arai har zata kwanta saikuma tace bari taje tama Baban su Nana maganan bude kofan dakinta tayi tafito tawuce dakin Baba dake opposite her daidai zata bude kofan taji yana magana ko waya yake ko menene kawai saita tsaya tareda kare kunnenta Baban Nana yace “tunda kafadama Asmeey komi ai shikenan Alhamdulillah gobe wara haka tana dakin mijinta!” Wani irin rasss gaban Mama yafadi tazaro ido tana kara manna kunnenta dantaji da kyau taji Kawu na dariya yace “Hamadi da kunya Hamadi da kunya toh Alhamdulillah yadawo gidan tunda aka daura auren nadena ganinsa baya wuni agidan” wani kalan komawa baya Mama tayi tana daura hannayenta a kirji tana zaro idanu irin menakeji haka? Hamadi? Asmeey daura aure? Kai? Daura aure? Daurin aure dai? Kai aure aure dai data sani? Juyawa tayi da sauri takoma dakinta hijabi taja tasaka akan rigan baccin dake jikinta tasaka slippers tafito ahankali tasauka tawuce kofa ahankali tabude kofan ta leko tsakar gidan ganin babu kowa yasa ta shiga falla kafafu kaman zata tashi sama burintabkawai taganta dakin Mom.
Tasan yawanci basu kulle doors na flat nasu hakan yasa ta murza kofan ta shiga babu kowa a falo hakan yamata dadi tayi sama da saurinta, tana zuwa bata tsaya knocking ba tabude kofar flat din Mom ta shiga falon babu Mom sai kamshin turare da dakin keyi hanyar bedroom din Mom tayi tana kiranta da murya kasa kasa “Maman Aya, Maman Aya” Mom na kwance kan gadonta da kayan bacci waya take da Fawaz jin ana kiranta yasa tace “Ina zuwa Rayuwata” ta katse wayan dasauri tana mamakin wanda ya isa yafado mata flat ba sallama ba knocking ta taso tana bude kofa taga Maman su Nana dasauri cikeda isa tace “lafiya?” Gefenta Maman Nana tabi tashigo bedroom din Mom tajuyo ta kalleta tana maida kofan tarufe Maman Nana tawani zaro idanu zatai magana saikuma tari da sauri tasa hannu tadauki bottle water data gani tabude da sauri tanasha Mom ta karasa kan couch na dakin ta zauna ta daura kafa daya kan daya cikeda isa da iko tana kallon Maman Aya dake bankan uban ruwa, ijiye goran tayi da sauri sannan tazo wajen Mom dake kallonta cikin wishpering tace “Maman Aya wani mummunan zance naji kuma kin sanni bazaki taba samuna cikin masu cimiki amana ba Billahillazi” kada kafa Mom tashigayi dudda she’s feeling tense already cus she’s sensing bad energy but ta daure batason tai loosing steeze, Maman Aya tace “dazu da rana na shiga flat dinsu Gwaggo inama falo tareda Matar Musty Asiya saiga Gwaggo tafito daga dakinta ba, da Ammi da Mamie, ke harda Aya nakoga goro daga minti a hannuwansu araina nace Gwaggo ce taraba musu Gwaggo tashiga bawa yara minti tana cemusu suce Allah sa albarka sunata fadin haka” Mom ta natsu tana kallon Maman Nana kafin tace “yanzun nan Allah ya jiyardani dalilin meeting din” Maman Nana tasake dafa kirji, Mom tace “get to the point waya nake” Maman Nana takara rage murya tace “kaman fa aure Baba ya daurama Asmeeey da Hamad!” Dummmm! Dummm! DurummmDum! Haka kirjin Mom ke bugawa dan shi kansa kujeran datake kai saida yayi motsi ta zubama Maman Aya wasu kalan idanu da kallo da ita kanta saida ta tsorata tace “kwaran kwatsa abinda naji da kunine kenan yanzu kinga kayan bacci ne ma ajikina haka nasayo hijabi nataho na sanar dake amman kira Aya dan ni da idona naga Aya naga minti naga goro a hannuwanta wallahi tallahi” lumshe idanu Mom tayi trying her best to calm her self down da kyar muryanta har baya fita tsabagen bacin rai tanuna gadonta tace “phone” dasauri Mama tamike tayi gadonta tadauko mata wayan tazo gaban Mom da idanunta suke a runtse tana kallon fuskanta ita kanta ta tsorata tace “ga wayan Maman Aya” mika mata hannu Mom tayi batare data bude idanunta ba Maman Nana ta samata Mom tai shiru ahaka kafin ahankali tabude idanunta sun kada iya kadawa ta fuzar da iska tabude wayan tai dialing number Aya tana tafarfasa aciki cus betrayal din Aya yafi shocking dinta inhar anyi auren nan da gaske and Aya knows bata sanar da ita ba Aya will definitely see a different her entirely, number tai dialing wayan na gab da katsewa Aya ta dauka cikin muryan bacci tace “hello Mom” lumshe idanu Mom tayi cus muryan yarinyar is making her bones to cringe and shake in anger cikin tsananin zafi tace “I give you 10secs get yourself together and call me back Aya!” Kai wato dole yaran matan nan su dinga tsorata Maman su Aya nada zafi kuturun ubanchan heat harwani fita yake ajikinta da ita kanta Mama ta tsorata kaman munafuka tace “to bari naje ni Maman Aya” “ban sallameki ba!” Mom tafada da zafi kaman she owns Mama, Mama saitaji takasa koda motsi saiga kiran Aya Mama ta kara girgiza da lamarin Mom dan wlh 10secs din basu cika ba Mom tasa wayan a speaker dan yanda take fushi bamata so waya na zuwa wajen kunnenta. Cikide zafi dakuma kakkausar dakakkiyan murya tace “I have one single question for you Aya” dasauri Aya da muryanta harya fara rawa danta tsorata tace “toh Mom” Mom tace “banson surutu or long story I want yes or no as an answer am I clear!”? “Y….ye…yes Mom” Aya tayi maganan muryanta na breaking Maman Aya ta gyara zama tana kallon ikon Allah uba me matan nan tama yaranta dake tsoronta haka? Ina su Nana ke tsoronta infact su Nana ma su maidata shashasha idan tana musu fada ma kalli yanda Aya ke shaking and trembling a girl of 27yrs old, a registered nurse dake aiki working class woman me yarinya daya ke tsoron uwarta haka yau tana ganin abu, idan baka mutu ba baka gama ganin kallo ba, runtse idanu Mom tayi cus she wants to stay as calm as possible tace “Aya Babanki ya daurama Asmeey aure da Hamadi ko baiyiba”? Murya na shaking sosai Aya tace “uhnnn” takasa magana Mom tai shiru tana sauraro Aya tasan wacece ita bata repeating tambaya kuma tasan ba’a bata mata lokacin a amsa tambaya, cikeda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login