Showing 147001 words to 150000 words out of 221707 words
kuka tace “Mamie Yaya yasiyamin mota nine mai motan nan ni Mamie?” Waya Hameed yaciro yana mata video Mamie tace “kece Asmeey” sai kawai Asmeey tahau tsalle tana rike da hannun Mamie itane mai mota Mamie tace “bude motan kishiga dena tsalle” dasauri ta zagaya tabude tana kuka sosai tai bismillah ya shiga Munir yashigo yana nuna mata yanda ake kunnawa ta kunna ta danna uban horn haba sai dariya takalli Munir tace “wai da gaske ni Yaya yasiyama mota yar karama dani?” Yanzu nine mai this fine car?” The way Asmeey was super happy made everyone happy da kyar dasauri tace “ina jakana? Wayata” wayanta Munir yadauko mata number Ya Hamad takira but kaman baya online saita mikamai wayan itama bata cika yin hoto ba amman tace yimin hotuna, posing tadingayi a mota na shirme da yarinta da cuteness da menene Munir ma hotunan harda videos tana shirme a motan da wanda take surutu ni yar karama Yaya zai siyawa mota duka Munir Yama Ya Hamad forwarding anan snap sannan duk aka koma cikin gida Hameed yace “anyi magana da driver Baba tsohone mai hankali zai fara koya miki tuki gobe dan ni mammakeki zan banson shirme” dariya tayi tawuce sama tazauna agado tana murmushi sosai tasake kiransa baya shiga ta kwanta tai shiru jin ana kiran magrib ta tashi tai salla she’s so happy tanaso ta gayama sisters nata ba hali sabida abinda Baba yace tahakura tafada baya tai wanka tazo tai salla.
Wuraren 12 nadare harta fara bacci wayanta yahau ringing da sauri tabude idanu tasaki pillow data rungume wanda yanzu bata iya bacci bata rungume sa ba takai wayan kunne kafin tai magana calmly Hamad yace “you know you’re the most beautiful girl I’ve ever seen in my life ko” dan murmushi tayi yace “I just finished watching all ur videos I’m glad I made you happy, do you love your car?” Gyadamai kai tayi da sauri cikin muryan bacci tace “yes! I love it sosai, I love the color, thank you so much Yaya, Allah yamaka albarka!! Allah yakara budi, Allah ya linkamaka dubunsu” Shiru yayi yana sauraronta kaman addu’an tamai dadi asanyaye yace “I can give you the world inhar it will make u this happy that u were today harda tsalle zaki karyamin Mamie” murmushi tayi sosai there’s something tun ranan daya tafi takeson yamata maganan letters datamai but baiyiba that means bai bude ba, ahankali yace “wat i want from you is to be happy, just like today, idan aka kawo miki laptop dinki start writing, get busy before you know it lokaci yatafi har na dawo kokizo okay”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “promise me u will not be crying again!” Ahankali tace “I promise” murmushi yamata yace “good girl nima natura miki pictures dina sorry sai yau natura” dasauri ta katse wayan ta duba chat nasa hotonsa ne yawanci wanda aka masa da baima sani ba sai guda daya rak wanda yamata yana zaune adaki dawani polo mai bala’in kyau white looking damn handsome ta tsaya tanata kallon hoton sai kawai taima hoton reply da I love you Yaya!Hamad baitaba tunanin zata iya gayamai haka a chats ba yace “I love you too thank you for being my wife! I love all the letters you wrote me don’t worry babu wacce zan kalla a nan” dasauri tafita daga chats din dan basically abinda tadinga rubutawa a letters din is karka kalli wasu mata karka kula kowa kaji Yaya inasonka😅😅 karka ma yan office dinku mata murmushi kadinga daure fuska daya bude dariya yadingayi.
Haka takoma bacci.
Washegari around 9 akace mai tuki yazo ta shirya hijab tasa suka tafi awa daya ne Hamad yace adinga mata by 10:15 tadawo Hameed yace “sakon ki na daki daga mijinki” daki taji taga jakan MacBook dasauri tabude taga laptop guda biyu daya yarubuta Munir akai, waya ma biyu daya yarubuta Munir sai headphone shima yarubuta Munir akai ta kwalama Munir kira yazo Munir kaman zai haukace suka fito falo Ya Hameed yataya Asmeey setup shi Munir nayi da kansa yace “yanzu sai rubutu ko”? Ta gyadamai kai tana murmushi rannan sunyi waya tamai godiya.
Aranan da night takejin zancen zuwa umaran su saitahau kuka ai zai karar da kudin kuma an gama komi na Umaran zasu tafi on 18th of November daganan Mamie da ita zasu wuce Dubai sayo kayan akwatinsu Mamie taje Dubai couple of times but tun zamanin da lokacin Baba nada kudi, Asmeey was so happy itada matan yayyin harda Baba da Kawu da Abba da Mamie nan aka fara shirye shirye while Munir zai tafi gobe cus school medicine no be beans.
Saida tai kuka da Munir sai tafi yaga shatara na arziki haka yatafi gidan yadawo just iya da Mamie kullum tana fita car lesson tadawo zata danyi rubutu despite everything she misses mijinta sosai wlh, gashi xuwa uamaransu sai approaching yake.
Rannan tayi suka tafi bata taba shiga jirgi ba tarike Mamie daga baya tadawo daidai sabida yanda aketa hira zuwa Umara da Famiky da dadi kwanansu 15 itada Mamie suka wuce Dubai duk abinda tazaba ake saya akwatinta dana Zee iri daya just difference of colors akai komi kwnansu bakwai suka dawo Mamie notice tun wannan period din da Asmeey tayi tun Hamad na nan haryau bata karaba sai kawai tadingajin dadi tana kula da yarinyar sosai akman bata gayama kowa komiba har Baba tabarma cikinta, while gidansu ana renovating Wanda ake ginawa yayi nisa akasa bikinsu January 20th Asmeey was so happy Ya Hameed yakaita aka fara papers nata da komi cus Hamadi yazo biki tarezasu koma family gabaki daya ska shiga shirin bikin Asmeey da Hamad, Hameed da Zainab.
EPISODE 7️⃣6️⃣
BONUS💃
Har yau aiki ake agidan an gama renovation na waje, compound interlock, flower garden, kitchen da falo da staircase, gidan yadawo na yan gayu sosai, an gama dakin Mamie so Abba yadawo nata ana nasa sai nasu Hameed sai hallway din saikuma nasu Asmeey.
Today is 19th of December duka duka satinsu daya da dawowa daga dubai, tayi wani mahaukacin haske, fatanta yayi kyau amman bata iyacin abinci sosai, so kwata kwata batai kibaba sai uban nono dake kara tasowa sunyi shar kaman zasuce tass, Mamie is trying for her, the way take selecting abinci da ita akema haka datagaji but Mamie bata gajiya gashi batason kamshin abinci abinda yasa ma yanzu idan ta sauka kasa taje fita suje driving me which yanzu ta iya ana mata process na license ma kawai Ya Hamad baya taba yarda ta fita anguwa ne tun gidan Zee dataje rannan sai saloon Hameed ke kaita yajirata adawo da ita tarasa mesa baya bari tafita at all at least kodan layinsu ne tafita da motanta but baya bari.
Yau tun safe datai breakfast take bacci sai yanzu around 12 taji cikinta nawani irin juyawa tashi tayi zaune tana kama cikinta doguwan rigane na atampa ajikinta babu hula akanta kitson kanta yayi kyau tadade batai ciwon ciki ba hakan saiyasa ta tuna ai tama dade batai MP ba, tun Ya Hamadi na nan fa tayi har yau, shine zaizo yau yafara mata haka dafa gadon tayi ta yunkura zata tashi taje bayi tana mikewa taji jiri na dibanta hakan yasa ba shiri takama gadonsu tarike ahankali tace “Mamie!” But shiru kulle idanunta tayi tashiga tafiya tana dafa bango tana layi at dsame time cikinta nawani irin ciwo tace “Ma….” Daidai ta buge da kofa dan juya mata dakin yake, kofan tashiga bugawa tana Ma….mi….. tana sulalewa kasa daidai Ya Hameed yaci gayu cikin wata shadda yafito fita zaiyi, jin ana buga kofa kadan kadan yasa yabi kofofin wajen da kallo ganin dakinsu Hamad yasa yayi wajen dasauri daidai Asmeey na Maaa…..tana haki dasauri yataba kofan anatse yace “Asmeey” saikuma yaji shiru dasauri yabude kofan kofanma sai bai budu duka ba sabida tana wajen akwance tarike cikinta idanunta na juyawa dasauri Hameed yace “Mamie! Mamie!”Yatura dakin yashiga da sauri yana dukawa gabanta yana kallon kofa yana kiran Mamie kadan kadan Asmeey ke bude idanunta dake juyawa she could see yanda Hameed ke kallon kofa yana maganan da bataji all she’s seeing is Ya Hamad, duk uban azaban ciwo hannunta tamika ahankali takama hannunsa bakinta na motsin. “Yaayaa” juyowa Hameed yayi dasauri yace “Asmeey” yanda idanunta ke juyawa tarike hannunsa gam yasa sai kawai ya ciccibeta ya dauka daidai Mamie na zuwa tace “meya sameta?” Dasauri yace “Mamie let’s go to the hospital since Yaya baya kasan dauko hijabi” yana maganan yashiga tafiya da Asmeey yana sauka Asmeey na kallonsa sosai da juyayyun idanu tana motsi da baki tana magana da ba’aji har motansa yakaita ya ijiyeta abaya zai taso tarikesa da muryan da baya fita tace “yaushe kadawo Yaya” tsayawa Hameed yayi yana kallonta her lips are still shaking tana kallonsa idanunta ajuye hakanan kawai yaji gabansa yafadi dasauri yazare hannunta daga hannunta daidai Mamie na zuwa yafito Mamie tashiga tazauna tana rikota tace “Asmeey meya sameki” murya kasa kasa tace “Yaya kadawo! Yaya kadawo” jin sambatun datake yasa Mamie ta taba kanta tace “Subhanallahi mugun zazzabine ajikinta, kara gudu Hameed bari nakira Abban ku” kara gudu yayi bini bini yana kallon Asmeey ta madubi har sukakai asibitin su Ya Mustapa ansan Mamie da Hameed aka karbi Asmeey sharp sharp akai admitting Hameed yace “nagayama Hamadi Mamie?” Dasauri Mamie tace “kasansa zai rude yahau kuka awajen bari muji tukunna kira Yayanku” daidai Abba na zuwa ya zauna kusa da Mamie suna jiran Dr, chan saiga Dr yafito yakira su Mama duka suka bisa yayi murmushi yace “to Mama da Abba congratulations za’a sami jika!” Murmushi Abba da Mamie sukayi hakama Hameed aransa yace “dan iska Hamadi ai wlh saina gayama su Ya Faisal” Dr yace “tana dauke da juna biyu na kimanin sati takwas wato wata biyu” Hamad yace “just few days to Hamadi yayi tafiya yamata ciki kai wannan yaro”Dr yace “but tanada malaria sosai and malaria baida kyau ajikin mai ciki zamu riketa anan zuwa gobe haka, dan Allah aka koma gida let her be on bed rest kartai aiki sannan ya zamto tana cikin kwanciyan hankali always saikuma ba hayaniya ko damuwa sannan next week inda hali ku kawota tafara Antinatal” Mamie da Abba suka gyadamai kai sai murmushi suke Dr yace “anjima kadan zaku iya ganinta” tashi Abba sukayi suka godema Dr suka fito Abba na fito daidai number Baba dan kiransa Baba na dauka Abba yace “to barka barka Allah fa ya albarkaci zuri’a Muhammadu Sani, wannan karan Jikan namu ne namu namu”
Maganan Abba yasa Baba yagane Asmeey na dauke da juna biyu yace “ahhh Alhamdulillah Alhamdulilah ubangiji Allah ya dayyaba yasa albarka, Allah ya raya tana ina”? Abba yace “muna asibiti ba lafiya wai tanada malaria za’a rikemu dai zuwa gobe” Baba yace “Toh Allah yakara mata lafiya Allah ya sauketa lpy” Abba yace “Ameen Ameen” sauki sallama Baba was very very happy
Wajajen 9 Asmeey ke bude idanunta ahankali Hameed kadai tagani zaune kan kujera da waya a kunnensa Mamie kuma na salla, alamun motsin mutum yasa yakalli gadon dasauri ganin Asmeey na kokarin tashi zaune yasa yace “I will call u later” ya katse wayan yazo wajen gadon yace “careful Asmeey bari na tada gadon” taba botun yayi katifan yataso tashiga bin dakin da kallo cikin rashin karfi saikuma ta kalli Ya Hameed dake kallonta tace “ina Yaya?” Hameed na kallonta yace “wani Yayan?” Cikin raunin murya tace “Ya Hamad” dan murmushi yayi yace “aiko kinata sumbatu da sunansa dazu to yana chan kasan nan” fashewa da kuka tayi ahankali tace “wlh na gansa” tasowa Mamie data sallame salla tayi tace “kindaiga Hameed dai ko Asmeey” ahankali Asmeey tace “Mamie wlh na gansa shiya daukeni” zama Mamie tayi kusada ita tace “Hameed yajiyoki yazo ya daukeki” dasauri ta kalli Hameed, mugun kallo ya watsamata yawuce abinsa yafita daga dakin, Mamie tace “mezakici?” Fuskanta ta share tace “tea” tea Mami tamata ta karba tana kallon tea brain dinta na kokarin recalling taga Ya Hamad har tana rike hannunsa, ai tasan Ya Hameed baida idanu kaman na Ya Hamad dazu har idanun Ya Hamadi tagani, da kyar tasha tea akazo aka mata wasu allura nan da nan tayi wani bacci koda Hameed yadawo tayi bacci ko kallonta baiyiba yama Mamie sallama yatafi.
Ba’a sanar da Hamad ba anaso sai an koma gida, washe gari aka sallamesu aka bata magunguna.
**
Mom na zaune cikin gidan Fawaz dan yanzu kusan kullum saitazo dudda rabonta dashi tun a kano but coming there is now her new therapy, wayanta ne yahau ringing da sauri ta daga wayan Mama ce wayan takai kunnenta Mom tace “Ya akayi?” Cikeda kwarema a munafinci tace “ya gajiya hala kina kotu ko nakira ne na tambaya ko ke an aiko miki da taki ankon? Gashinan na karbi nawa na iyaye ganasu Nana kyauta ina gayamiki Maman su Aya ko sisin mu babu ciki” Anatse Mom tace “ankon wa?” Dan shiru Mama tayi chan tace “wlh abin nan namin ciwo yanda mutanen nan suke nuna u are nobody, ke gaki mara daraja akan yarki, keya kamata ki turo mana anko fa ke mai y’a amman sai masu danda ke aiko mana” Mom jitayi zuciyanta yafara radadi gane kan zancen, Mama tace “kinsan ance dashi da Asmeey zasu dawo daga kasan waje January, ga anko nan za’a hada bikinsu dana Hameed on 20th ayi, ga anko nan na manya lashe iya leshi da atampa embellish, ina mai tabbata miki Ammi Maman su Ramla itama ta amsa nata dana yaranta kecedai wacce batakaiba, gaki banza kin haifa musu bakisan da auren yarki ba yanzu biki yazo shima baki sani ba” Mom bata tabajin abu ya tsaya mata arai ba irin na yau, Mama cikeda watsa fetur a wuta tace “hmmm na manta fa yanzu Hamadi yasha karfin mu indai kudine, wai kinsan Umara da mijinki yaje da nawa duk Hamad din yabiya kuwa? Rannan Baban su Nana Allah ya matsi bakinsa yake gayamin ke kinga zafafan motocin daya siya musu agidan nan, kinga yanda aka gyara gidan, kinga estate din dasuka gina su yaran, to yanzu haka Mustapa na China kampani zasu gina anan Nigeria kampani iya kampani kaman dangote fa, ai wlh Hamad yasha karfinki Maman Aya! Baki isa kirabasa da matarsa yanzu ba! Yanada kudi da capacity daureki if u try nonsense” Mama tai maganan da gayya dan itama Mom batada mutunci, wani abu Mom taji ya soki kirjinta ta daure tace “hmmm in yasan wata baisan wata ba, ko duka kudin duniya ya mallaka kafin Hamad yasan dukiya ni nake cikinta nakuma dandana nayi wanka ciki!”Mom tai maganan cikeda girman kai tace “Allah dawo dasu zan gwada muku cewa saidai ayi koni ko shi! Dolene dayanmu baya duniya shine za’ayi bikin nan! Sannan y’ata zata cigaba da zama dasu! Barikiji y’ata saina karbeta wallahi! Biki dai saidai ayi na Hameed namiki alkawarin nan inhar nice Salima Mrs Muhammadu Sani Turaki!” Ta buga kirji tana kashe wayan.
SEE YHUU SATURDAY 💃
EPISODE 7️⃣7️⃣
KANO!
She doesn’t really know abinda ke damunta but somehow she understood kaman ciki gareta, Mamie kaman kunya takeji takasa mata maganan cikin, su Ya Hameed ma haka to ai su maza ne, but matan Yayyin dasuka zo gaisheta sai mata Allah sauketa lpy suke, Matar Ya Faisal Anty Nana harda dan kuka dan har yanzu ita batada ciki.
Itakuma duk kunyansu takeji balle ta tambayesu, dakinta taje dan sallan la’asar tai shiru tadauki wayanta ta duba batada any miss call ko chats from Ya Hamad she knows ba’a gayamai tana rashin lafiya ba even last time sabida ansan zai damu same with now ko itama bazata so ya damu ba but kuma she wants him to call her ijiye wayan tayi tashiga bayi tayi salla tana zaune kan dadduma Anty Asiya Matar Ya Musty tabude kofan tace “oya muje an gama girki” juyawa tayi zata wuce dasauri Asmeey tace “Anty”
Dan dakatawa Anty Asiya tayi ganin Asmeey na kokarin mikewa tsaye saita shigo tareda maida kofan tarufe tace “na’am menene Asmeey?” Dan kallonta Asmeey tayi saita rasa yanda zatai maganan saita shiga wasa da yatsunta tarasa mezatace Anty Asiya tace “menene Asmeey wani abu na damun kine?” Gyadamata kai tayi sai kuma ahankali tace “mesa Mamie kaman tanajin kunyana?” Tadanyi shiru Asiya tai wani murmushi Asmeey tace “rashin lafiyan menayi a hospital?” Dariya saida ya kufcema Anty Asiya tace “laaaaaa aini nasan Mamie bazata taba bude baki ta sanar dake ciki gareki ba akwai wannan kunyan bafulatanan tareda Mamie saidai likita ya gayamiki but zata kula dake, nima nan Dr yagayamin nakira su Nana na gayamusu, ciki ne dake Asmeey har wata biyu, su Ya Hamadi an raya sunna” wani irin kunya yakama Asmeey batasan sanda tajuya tarufe fuskanta da hijabi ba Asiya tadinga dariya tace “ahhh kajita aikin gama yagama munsan komi ustazan munafukai keda mijin naki” dukawa Asmeey tayi tana rufe fuska sosai Asiya tace “nidai sauko natafi” tafice abinta kai Asmeey saitaji tanajin kunyan kowa yanzu ciki gareta? She’s going to be a Mom? Ita da Ya Hamadi are going to be parents? Hannunta takai ta taba cikin sai kawai taji wani dadi da sanyi ya lullubeta no wonder Mamie ke nan nan da ita hawa gado tayi ta kwanta tayi shiru tadaga yatsunta tana kallo dama haka ake ciki da wuri sau uku sukayi fa ko? Rannan farko da kaman baiyiba sai da safe ya karasayi, yayi da daddare na biyu daganan aka karbeta takoma wajen Mamie, bai karayiba sai rannan dazaiyi tafiya da daddare sau uku but hartayi ciki? Tai shiru saita sake murmushi tawani rufe fuska yanzu shikenan kowa yasan abinda sukayi the only person dataji tanason gayamawa is Munir dasauri tabude waya taciro numbersa zata kirasa tagaya masa amman sai kunya duk ya kamata, tayaya zata wani gayama Munir tanada ciki she’s very shy, sai kuma ta shafa cikin tadan dage riganta takalli flat tummy tace “Abee will be very happy if he finds out about u” saikuma tasake murmushi takulle fuskanta duk kunya ya isheta wasa wasa haka bacci yayi awon gaba da ita, bacci take yawan yi gaskiya bata taba amai ba sai dai