Showing 24001 words to 27000 words out of 221707 words
account” shiru Mami tayi tana kallonshi chan ta shafa bayanshi tace “it’s okay but next time kada ka kara kashe kudin aikin ka haka duk sun fika kudi sunada tsayayyan aikin yi mai albashi kaji” gyadamata kai yayi, daidai an bude kofan dasauri yafita daga jikinta dudda haka saida Hameed yagani yawani zaro idanu yace “Mamie dama yaron nan na hugging naki ko gizo idanuna kemin” dawani kalan sauri Hamad yatashi zai wuce bayi Hameed yashigo da gudu yarikeshi yace “so you can hug Mami Hamad amman ni baka taba bari nai hugging naka to wlh sainayi yau” yataho zaiyi hugging nashi da sauri Hamad ya fizge kanshi yace “Mamie” Mamie dake dan dariya tace “mehaka Hameed ka kyaleshi please” dariya Hameed yayi yataho wajen Mamie tamikamai sarkan tace “kalli abinda ya siyamin yasami kudi duka ya kashemana” murmushi sosai Hameed yayi yace “kafito daga bayi ina nawa?” Yakalli Mami yace “ga Gwaggo chan takasa hayowa sama tana jiranku itama ta nunamin gyalenta” Mamie tace “bari naje kuhada kayanku ku kuka rage” yace “toh Mamie” tawuce.
Fitowa Hamad yayi kana gani kasan wanka yayi but he’s still wearing kayan daya saka dazu sabida damuwan Hameed bai bari yadauki wani kaya ba ko kallon Hameed baiyiba yazo wardrobe yadauki jogger da t-shirt yawuce yakoma bayi ya shirya tsaf yafito yajefa kayan daya cire a laundry basket sannan yazo Hameed yace “ina nawa Hamadi” jakan shi yabude yaciro nashi ya bashi yaciro na sauran yayi shi ya ijiye a gefe Hameed was so happy with the perfume sai murmushi yake yace “tashi toh muhada kayanmu” kwanciya kan gado yayi yace “I’m tired” hararanshi Hameed yayi yasauko da box nasu yahada musu kayan tsaf yasama Hamadi kayan zama gida da jallabiya guda biyu da turarukanshi duka ciki da takalman daya saya musu na salla da hula da agogo tsaf da sabulan wanka, yadebi few novels na Hamad ya samai, ka’ida ne duk babban salla a Bauchi sukeyi 7days kuma sukeyi a Bauchi kafin su dawo, gama hadawa yayi yawuce shima yaje yayi wanka.
Around 9 yashigo gidan daga mosque Abba yagani zaune kan carpet ga kwalin agogon daya siyamai ga Gwaggo gefensa akasa ta kishinguda da gyalenta amman bacci ya kwasheta tsaresa da idanu Abba yayi ahankali yace “sannu da dawowa Abba” murmushi Abba yamai yace “zonan Hamad” karasawa wajen Abba yayi ya zauna ahankali, Abba ya kalli agogon saiya kalleshi yace “naga abinda ka siyama kowa harda ni Allah yayi albarka, kaima Allah yasa naka yaran su maka abinda yafi haka sannan Allah ya sanyama hanyar nemanka albarka, Allah yakawo tsayayyen aiki” gyadama Abba kai yayi murya chan kasa yace “Ameen Abba” yatashi yawuce sama Abba yasake binshi da kallo sannan yakalli agogon kafin yakalli Gwaggo dake munshari.
Around 7AM Ya Mustapa yazo gidan da matarsa da yaransa biyu Areef and Arfat, shima Ya Abdallah yazo gidan da matarsa da yarsu Amra tasha lalle ta tafi wajen Mamie da gudu tana nunama Mamie lallinta saiga Ya Faisal shima da matarsa ita har yanzu bata haihuba duk suna falo an gama loda kaya tsaf, Hameed ya sauko yana sanye dawani ash color yadi mai kyau Abba dake wasa da jikokinsa yace “Ina Hamadi? Shikadai ake jira” “gashinan zuwa Abba shiryawa yake” gyadamai kai yayi, Hameed yazo ya zauna abinshi bai gaida kowa ba, kusan 10minutes saiga Hamad yana saukowa yana sanye da ash color yadi exactly irin na Hameed sai kamshi yake, yadin yamai bala’in kyau bambamcinsa da Hameed is just eyes, idanun kwalli garesa and it’s so obvious kansa akasa anatse yake tafiya daidai cikeda kamala da natsuwa kuma, ya shigo cikin falon calmly yazo gaban Ya Mustapa da matarsa ke zaune kusa dashi kanshi akasa yace “ina kwana Anty” murmushi tayi sosai tace “Alhamdulillah Ya Hamadi ya karfin jikin an warware ko” gyadamata kai yayi yatako zuwa gaban ya Abdallah kanshi akasa anutse yace “ina kwana Anty” cikeda so tace “lafiya lau Ya Hamad ya jiki” bai amsaba yadai gyada kai takawa yayi zuwa wajen Ya Faisal yace “ina kwana Anty” kanta tasauke akasa cus Hamadi ya girmeta she’s just 25 amman baida girman kai tace “ina kwana Ya Hamadi” kasa amsawa yayi yawuce gently kusada Mamie duka yayyinshi na binshi da kallo ya zauna, Gwaggo tashigo taci gayu wani bubu da zani da mayafi tasaka na hadari lace tace “mutafi yaufa jajubari akwai go slow” tashi Abba yayi kowa yatashi aka fito Mamie takashe wutan kowani daki ta tofa addu’a duka kulle gidan aka shishiga mota
Abba yaje yana sallama da mai gadi yabashi makullin gida da kudade da motoci hudu sukai tafiyan motan Abba sai motan Ya Mustapa Ya Abdallahi Ya Faisal, motan Abba Hamad ya shiga gaba kusada dreban Abba, Abba da Mami suka shiga baya, shikuma Hameed ya shiga motan ya Faisal, Gwaggo tashiga motan Ya Mustapa suka wuce.
**
Bauchi
Shigowa gidan Munir yayi su Yusra dasu Amina da Ya Ramla duk suna kasan bishiya da aka shimfida babban tabarma ga masu kitso da masu lalle duka ana musu, ga yaran maza da anriga an musu aski sai wasa suke a tsakar gida Ammi sai up and down take itada masu aiki a backyard ana soye soyen su cincin da kuma girki sabida su Kawu da Abba dazasuzo yau everyone looks happy the only person dabai gani ba is Ya Asmeey wucewa yayi ya shiga flat dinsu babu kowa a falo banda tv dake aiki dan duka yaran suna waje staircase yashiga hawa dakinsu Asmeey yawuce yabude kofa bata ciki hakan yasa yarufo kofan yayi jimm cus yasan tana wajen Mom wlh ranan nan dayace he wish Ammi ce mamansu bawai karya yayi ba cus look at yaranta they’re so happy anachan ana musu lalle suna tsalle tsalle a compound haba gobe salla fa at least tabar Asmeey amata kitso da lalle like every other gurl but no itama tafito tayi aiki she’s too big tayi Ammi ke handling komi, kullum Asmeey sai ramewa take duk tayi zuru zuru sabida jaraban Mom he called Ya Aya da Ya Aysha akan suma Mom magana tadan sassautama Asmeey but sun kasa kowa tsoron Mom yake ga Baba baicika zama ba baimasan wat is going on ba sai wanda yagani akan idanunshi, ahankali yawuce side din Mom kofan yabude babu kowa a falo sai tv dake aiki falon na kamshin turaren wuta tafiya yashiga yi yana shiga corridor dazai sadashi da bedroom din Mom yaji muryan Mom na bala’i. “Kin kosan how important this property law practice yake a law school? Are you dumb da kin kasa iyawa so nawa zan koya miki? See Asmeey idan kika fadi bar exam dinki just die kafin kizo ki sanar dani kin fadi, what is so difficult about property law practice when kinada all materials duk abinda za’a muku a law school na zaunar dake ina koyamiki did you know how lucky you are? Wlh kika karamin shirme sai ranki ya baci give me requirement din ina jinki” muryan Asmeey yaji baya fita sosai and it’s even shaking cus bayajin ma abinda take fadi wani irin yaji zuciyansa yamai har wani daci daci yakeji juyawa yayi ahankali zai tafi sai kawai yaji karan saukan mari dakuma buguwan abu Mom tayi ihu tace “idan bazaki iya zama ni ki gajeni ba just die Asma’u dan banga amfaninki a doron kasa ba” wajen kofan Munir yayi da sauri zai bude yakasa sabida tsoro yakafa kanshi jikin kofan yanajin kukan Asmeey kasa kasa sai kawai yajuya da sauri yabude kofa yafita ta nan window sama ya hango motan Baba alamun yadawo hakan yasa yayi hanyar dakin Baba kai tsaye yabude kofan baima tsaya sallama ba babban falo ne sosai mai bala’in kyau Baba na zaune kan kujera ko takalmi bai cireba magana yake awaya yana sanye da faran shadda ganin idanun Munir sunyi ja yasa yace “Yaya saikun iso Allah kiyaye hanya bari na kira Kawu” katse wayan yayi yakalli Munir yace “menene Munir”? Tahowa wajensa Munir yayi yana kokarin magana sai kawai yakasa yafashe da kuka cikeda damuwa Baba yace “Munir what happened meya faru”? Ina Munir yakasa magana, Baba yadagosa yace “Munir menene”? Da kyar ya tsagaita kukan yana wani irin nishi na zuciya in a very childish way yace “Baba banso ace nayi gulman mahaifiyata ko ace nafadi wani abu mara kyau akan Mahaifiyata, Baba just save Asmeey sabida idan wani abu yasameta Baba harkai sai Allah ya tambaya ni shikenan abinda nazo na gayamaka” yana maganan ya fizge jikinshi daga na Baba ya ruga da gudu yafita daga dakin Baba ya tsaya looking confuse ya bisa da kallo yana maimaita kalaman Munir yakai kusan 2min ahaka sai kuma yamike, fitowa yayi daga dakinshi yabude dakin su Asmeey dake next to him but babu kowa adaki sai kawai yashiga sauka daga bene cus his believes Asmeey na waje, su Ammi da Mom na backyard suna girki yana sauka kasa Ammi na fitowa daga kitchen yace “Asmeey na wajen lalle ne?” Da zuciya daya Ammi tace “a’a bata waje ai tun safe datazo gaidani takoma sama ina ganin tana dakin Mamanta” dasauri Baba yace “Salima bata tareda ku wajen girki ne” gyadamai kai Ammi tayi tace “eh tana sama bata sauko ba inaga wani abun suke” Baba ji yayi ranshi yabaci sosai sai kawai yajuya yakoma sama Ammi kuma tawuce tafita falon Mom yabude but bakowa ciki but yana jiyo muryan Mom daga ciki tana banbami, kai tsaye bude kofan dakin yayi dadan sauri Mom tajuyo ko kadan bata dauka yanzu Baba zai dawo ba sai chan anjima chak Baba ya tsaya yana kallon Asmeey dake zaune akasa gaban Mamanta ga uban files da manyan textbooks agabanta gadan jini daya gani gefen lips nata which yana shigowa akan idanunshi yaga tagoge da sauri but bata dago kai ta kalleshi ba, tashi Mom tayi tana sauke littafan dake kan cinyanta tace “Alhaji kadawo” ko kallonta baiyiba idanunshi nakan Asmeeey yace “Husna” dan dago kanta Asmeey tayi takalli Baba tareda kakalo murmushi asanyaye tace “Baba sannu da zuwa” wani irin faduwa gaban Baba yayi ganin idanun yarinyar sunyi jaa gashi kuncinta shaidan hannu dayayi ja abunka da fara lips dinta yadan kumbura Mom takalleta tace “Babanki na kiranki kitashi kin zauna” dasauri tace “toh” kokarin tashi tashugayi kafafunta sunyi sanyi sai Mom tashiga gaban Baba ta kareshi tana murmushi tace “muje falo ta biyomu an kawomin kayan sallan dana maka muje kaga dinkin” ko motsi Baba baiyiba kokarin kallon Asmeey dake kokarin tashi yake Mom tasake kareshi takai hannunta takama nashi tace “muje kagani” fizge hannunshi yayi yamata wani kallo yace “don’t touch me” yawuce gefenta yaje wajen Asmeey data tashi, ahankali yakai hannunshi yakama kuncinta yana kallon wajen strictly Baba yace “meya sami fuskanki yayi ja haka” washema Baba baki tayi tace “faduwa nayi dazu Baba” boyayen ijiyan zuciya Mom ta sauke, Baba yace “to me kikeyi anan bakije kinyi kitso ba zo muje” riketa Baba yayi yasata ajikinshi yashiga tafiya da ita ahankali sukabi ta gefen Mom suka fice dakinshi yawuce da ita kan kujeranshi ya zaunar da ita yawuce fridge dinshi yabude laban yadauko me sanyi yakawo mata yabude yabata ta amsa tana murmushi tace “nagode Baba” takai bakinta tadan kurba, gently Baba yasake kai hannunshi gefen kuncinta anatse yace “tell me the truth Mamanki ne tadakeki haka”? Dasauri ta girgiza kai tace “Baba faduwa nayi dazu Mom bata dakeni ba” shiru Baba yayi yana kallonta ganin haka yasa tashiga shan madaran gabanta na faduwa, saida ta shanye Baba yace “tashi kije waje wajen kitso da lalle kema amiki” tashi tayi tace “toh” tawuce tayi wajen kofa tafice yayi shiru sannan yadauki wayanshi yasa a kunne kai tsaye yace “meet me in my room” ba’a wani jimaba Mom tashigo sai kamshi take dubawa Baba yabita da kallo ranshi abace yace “Salima nina sa aka kira masu lalli har gida da masu kitso sabida ama yarana mata akan wani dalili zaki ijiye Husna adakin ki bazaki barta taje tayi ba” Mom na kallonshi tace “au haka tace maka”? Ran Baba abace yace “babu abinda Husna ta gayamin rannan nan I told you kibimin yara ahankali wai shi karatun nan dole ne? Law school zata iya zuwa aduk sanda taga dama akanme zaki tasamin y’a agaba? This is the last time dazan miki wannan maganan ba dole bane Husna saita gajeki ba! Ni dan kasuwa ne mesa bance Munir dole sai yazama dan kasuwa kaman ni ba? Kibar yara suyu abinda sukeso, the next time zaki takurama yar nan wlh saina dauki mummunan matankin da saiya baki mamaki! Imagine yau baki zanyi mahaifiyata da yan uwana suna hanya keçe babba agidan nan amman bata ayyuka da abincin da zasuci kike ba, I will not say anything ku cigaba da halinki gida biyu maganin gobara kada ki komi ko yaya kikeso kiyi amman yarana kidena takura musu na gaya miki”Mom na kallonshi tace “shine kakemin ihu”? “Wacece ke da baza’amiki ihu ba” yana maganan yawuce ya shiga bedroom dinshi ya barta nan tsaye.
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 9️⃣
Dakinsu ta shiga bayi tashiga tai wanka dan batai wanka ba tun safe fitowa tayi tabude sip taciro wani gown na atampa mai kyau yanada blue floweres shiryawa tsaf tayi tasaka sannan tazo gaban madubi takalli fuskanta har lokacin fuskan yayi ja sai kawai taji har kunya kunya takeji ma tafita mai ta dauka ta shafa a fuskanta sannan tazo dauki kwalli tasaka duk dan tai looking normal hakan saiya rage redness na fuskanta amman saitayi bala’in kyau gashinta ta warware a wanke yake har tsakiyan bayanta gashi baki gwanin kyau batada full gashi sai tsayi but is scanty and silky combing tayi sai kawai ta dauki blue veil ta yafa tadan fesa bodyspray dinta ta tashi ta kalli madubi murmushi tayi saita fito ta sauko kasa babu kowa a falo saita fita tana tafiya ahankali zuwa wajen masu kitso Ramla dahar an gama mata kitso tace “wat happen to fuskanki?” Zama tayi kan tabarma tace “faduwa nayi laaaa lallinki yayi kyau Ya Ramla” tai maganan da sauri dan ta kauda maganan, takalli lallin Yusra tace “Yusri iyyeee Irin naki za’a min” Yusri ta washe baki Amina tace “Ya Asmeey kiyi irin kitsona” dasauri tace “shiko zanyi” Yusra tace “ga Mom tafito” wani kalan faduwa gaban Asmeey yayi da sauri ta sauke kanta kasa Mom tashiga tahowa wajen fuskanta kaman bata taba dariya aduniya ba tana sanye dawani simple gown na Cotten irin na Egypt din nan masu manyan mayafi sai wani mashahiurin kamshi take idanunta akan Asmeey dataga tai wanka harda chanza kaya, Yusra na ganinta tayi murmushi tace “Mom saura ni ana gamama Amina za’amin kitsona asamin beads” Amina tace “Mommy lalle na yayi kyau” dan murmushi kadan tayi tace “yayi sosai” takalli Asmeey da kanta ke kada cikeda authority da isa da iko tace “ayi miki kitso only banda lalle” ba Asmeey kadai ba hatta su Yusra yara da su masu lallen da masu kitson da Ramla saida suka kalli Mom, wani iri Asmeey taji cus tanason lalle duk salla Allah yasani lalli da kitso da saka sabon kaya are the measure things she looks forward too, amman saita gyadama Mom kai ahankali muryanta nadan breaking tace “tt….toh Mom” strictly Mom tace “good! You’re going to law school bayan sallan nan, henna kowani iri is not allowed” sake gyadama Mom kai tayi ahankali kanta akasa, Mom tajuya tawuce abinta batare data kara kallonsu ba tana tafiya kaman itace mai gidan masu lalle da kitso suka bita da kallo asace ana mamakin gadaran matan, duk yanda Asmeey taso ta daure takasa kawai saiga hawaye sharrr dasauri takai bayan hannu ta share kafin wani ya lura dan kanta na kasa, me lallen tace “menene law school Ramla?” Ahankali Ramla tace “makarantan dakake zuwa kazama cikakken lawyer, da gaske ba’a barin lalle” mai lallen tace “amman ai yanzu lalle nan da nan yake gogewa kuma shampo na goge lalle lokacin yayi aisaita goge lallen” Ramla tace “tunda Mom tace kartayi kartayi mubar maganan nidai” Asmeey tai shiru zuciyanta baya mata dadi kawai kitson ma kaman kartayi but tasan Baba zaiyi magana, haka aka gama na Yusra sai akahau mata kitso shiku mai bala’in kyau yan kanana ana cikin mata Kawu ya iso daga Gombe.
Tashi duka yaran sukayi bata tashi ba Ramla tace “tashi muje mu gaida su Kawu” ahankali ta tashi suka wuce wajen motansu, wani magidanci na mai kama da Abba na Kano sosai tareda wata mata da yara mata, Matar tace “ana kitso ne Asmeey ba’a gama ba” dasauri Asmeey tace “eh Mama” ta rungume “Nana da Baby tace “Nana, Babyyyy” suma suka rungumeta Nana is 15, Baby kuma 12 sai sauran yaran Maza ne guda hudu, daidai nan Kawu ya gama magana da masu gadi yazo wajen yaran duka suka gaidasa idanunsa nakan Asmeey yace “meya sameki a fuska Asma’u”kafin tai magana Yusra tace “faduwa tayi Kawu” ahankali yace “sannu bakiji wani ciwon bako” gyadamai kai tayi tayi murmushi still ya tsareta da idanu dan kaman mari daidai Baba na fitowa daga flat, Mom da Ammi kuma suna zuwa daga backyard, wani kallo Mom tama Asmeey hakan yasa tajuya ahankali tawuce takoma wajen kitso, Baba yayi hugging dan uwansa cikeda farin ciki suka shiga gaisawa while masu gadi na kai kayansu side nasu, Asmeey takoma wajen kitso tazauna aka cigaba tana kallon yanda kowa ke murna, su Nana suka taho wajen basuyi lalle ba suma Ramla tace “kuje kuhuta ku chanza kaya kar lallen yabata wannan sai kuzo amuku” wucewa sukayi dan chanza kayan.
Suna chanza kaya suka dawo, suna cikin kitson Munir yazo wajen kaman bacci ma yayi dan idanunsa yayi ja bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey ana mata kitso ba dudda yana ganin fuskanta yasan aikin Mom ne yazo wajen yadan harari Nana dake kallonshi yace “ni tsaran wasankine kike kallona” kallon Ramla Asmeey tayi Ramla ma takalli Asmeey suka wani kwashe da dariya bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey tayi dariya ba, Ramla tace “sannu Ya Munir itakuma Nana jibi yanda tawani sunnar dakai kaman irin Ya Mustapa asalin Babban yayanmu