Showing 102001 words to 105000 words out of 221707 words
kwalama Asmeey kira tace “Asmeey sauko muyi hiranmu tunda mu kadai aka bari agida” dan saita kanta Asmeey tayi ta goge fuskanta, wlh bataso Ya Hamad na fita duk saitaji zuciya bata mata dadi, fitowa tayi ta zauna itada Mamie sukayi breakfast bayan Mamie tabata duka magungunan tasha harda na wajen Aysha tace “je dauko kipiya adakina namiki tsifa yana cikin drawer na, akwai wani saloon a anguwan nan sai muje idan kingama” tashi tayi tawuce sama dakin Mamie tadauko kipiyan tadawo ta kwanta tadaura kanta a cinyan Mamie tana murmushin jin dadi, Mamie tace “na so diya mace aduniya wacce zan dinga mata tsifa na gyara mata kai da sauransu amman kinga Allah bai bani ba, Doctor da AbdallahI kuma sai maza suke haihomin, dake da Matar Faisal Kady nakema addu’a Allah yabaku yara mata abani” akunyace Asmeey ta manna kanta jikin Mamie tana murmushi, Mamie tacigaba da mata hira she just wish this is yanda take da Mom, tuna Mom kawai saitaji gabanta yafadi daidai ana knocking kofarsu tareda budewa duk alokaci daya da Mamie da Asmeey dake kwance jikinta duk suka juyo ganin Mom taci wani lafiyayyen bubu tarike jakan prada ga glasses din nan a idanu tana wani irin kamshi tana kallonsu, ba Asmeey kadai ba har ita Mamie saida gabanta yafadi.
Dawani irin sauri Asmeey ta tashi daga jikin Mamie kawai jikinta yahau rawa lips dinta sukahau rawa ganin Mom take kaman ba itaba, tundaga kan yatsun kafa Mom take kallon Asmeey dataga tai mahaukacin fresh walh, tama kara kiba, tayi haske, fuskanta babu wannan redness dinnan na kuka kona mari skin dinta yayi smooth tana glowing, kawai gabanta yafadi ko yaron nan haryayi amfani da yarta ne idan yayi amfani da ita, mezata gayama Fawaz, saikuma cikin gadara tadauke idanunta dagakan Asmeey tadaurasu kan Mamie dake kallonta tace “kin barni a tsaye Hamida na shigo kokar na shigo? Ba tsiya yakawo ni ba”anatse Mamie tace “Allah ya rabamu da tsiya shigo Salima” shigowa Mom tayi tana rufo kofa sai kawai kafafun Asmeey suka kasa daukanta tashiga dukewa awajen Mamie na kallo kawai Asmeey tayi kneeling tsoro da fargaba yasa takasa bude baki tamayi magana.
EPISODE 4️⃣2️⃣
Mom ta daurama Mamie mugayen idanunta tace “y’ata nazo gani, koko diyar dana haifa ban isa nazo na ganta ba saina tambayeku”? Kallo Mamie tamata sannan takalli Asmeey da jikinta ke rawa tarakube jikin kujera akasa Mamie na mamakin wannan kalan tsoro da yaran nan keji na uwarsu tace “tashi ki daukowa mahaifiyarki lemu da ruwa Asmeey” hannun Mom tadagama Mamie tace “wani lemu? Fanta, coke ko 7up koko Popcola”? Mom tayi wani dariyan keta tace “banashan cheap drinks kuma sune agidan nan” Mamie tawani kalleta Mom ta dauke kai cikeda iko sannan tama Asmeey wani kallo dayasa yarinyar kawai ta dimauce tareda fashewa da kuka murya kasa kasa harwani haki take sabida yanda zuciyanta ya hargitse tace “Mom i…ina kwana! Sannu da zuwa Ya ji…..ki Mom”? Falon Mamie tashigabi da kallo tana neman wayanta da bata ganiba wayanta na sama adakinta, Mom takalli Asmeey tace “tashi muje dakinki I want to talk to you privately!” Mikewa Asmeey tayi tsaye da kyar tana goge kwalla takalli Mamie, cikin tsawa Mom tace “ohh ganin diyata sai kin bani izini Hamidah? Naga kallonki ake”? Dasauri Asmeey tasauke kanta tashiga tafiya, wani kallo Mamie tamata tace “gaki ga ita Salima” wucewa Asmeey tayi sama kafafunta har hardewa suke Mom na biye da ita tana kara kallon yanda yarinyar takara kyau, Asmeey ta chanza mata gabaki daya a idanunta, ahankali Asmeey tabude dakinsu dayake a gyare tsaf yana kamshi turaren wuta Mom tabiyota ciki tanabin dakin da kallo tana tabe baki da yatsine fuska kaman taga kashi tace “look at kurkukun dakike ciki da sunan dakin matan aure wat is this?! This room looks like wani prison room a kuje prison” tanuna dakin da hannu tana daga murya tace “wat kind of cheap paint and curtains ne adakin nan? See gado kaman na almajira, ko Gambo yar aiki na nasiyama yarta dazatai aure gadon dayafi wannan kyau balle ke diyata, carpet din nan ko sadaka aka bani banaso! Wannan dakin shine dakin da aka iyama shi jobless yaron karo karo aka saki ciki? Wait anama baki abinci kuwa? Jibi yanda kika rame kikai duhu? Is that jobless boy feeding you? Are you eating proper balance diet? When was the last time kikaci salad? Good protein kaza ko naman rago? I know it that jobless mahaukacin yaron nan can not feed my daughter? Look at diyata ahaka aka dauketa daga kano? An bawa mahaukaci y’ata da baya ciyar da ita jibi yanda yarinyar ta duk tabi ta lalace” Mamie duk tana jiyo Mom, tasan kuma da ita take sarai, kasa natsuwa tayi ta hayo sama tashiga dakinta taxauna bakin gado tadauki wayanta tai shiru, auren nan means alot to Hameed anything dazaisa takira Abba kowani cikinsu bazasu tsaya inda sukaje ayi komi ba zasu dawo, Hameed can cry for them he will be hurt, hakan yasa takira Hameed ringing na biyu yadaga yace “Mamie na kewana kikeyi ne?” Anatse tace “zaka iya barin abinda kakeyi a bank kazo gida yanzu?” Faduwa gabansa yayi yace “meya faru Mamie? Bakida lafiya ne?” Murmushi tayi tace “lafiya lau just come home now now dan Allah Hameed” kawai tashi hankalinsa yayi yace “okay Mamie, but fadamin menene? Karnaje nai hatsari i am very worried” cikeda damuwa tace “that woman is here” “wace woman Mamie”? “Mahaifiyar Asmeey” cikeda bakin ciki yace “fuck my marriage I am calling Hamad right now I am calling Abba” dasauri Mamie tace “Hameed kabari suyi concentrating wajen neman aurenka” baima tsaya daukan permission ba fitowa yayi wayan na kunnensa yace “Mamie she will hurt our sister again that is idanma bata dauketa tagudu da ita wani waje ba that woman is evil, Mamie gamunan zuwa becareful with her Mamie” ya katse wayan Mamie tafito daga daki falon sama ta zauna.
Gama kushe dakin Mom tayi sannan tayi shiru tana kallon Asmeey dake kneeling agabanta kanta akasa jikinta na rawa uppan bata ceba, jakanta Mom tabude taciro wani abu a black leather tamika mata tace “stand up and take this hide it inda babu wanda zai gani” tashi Asmeey tayi jikinta na rawa ta karba tawuce wajen wardrobe tabude ta boye ledan a karkadhin kayanta sannan tadawo tasake kneeling agaban Mom, Mom takalleta ji take kaman tasa kafafunta ta murje wuyanta ta mutu amman tadaure, yanda takara kyau abin namata ciwo but ta daure da kyar tace “stand up and carry your hijab” mikewa Asmeey tayi tawuce wajen wardrobe tadauko hijabinta gabanta na faduwa, Mom tace “sakashi” sakawa tayi, Mom tanuna mata kofa tace “wuce mutafi auren yakare!” Bugawa kirjin Asmeey yayi sosai dan kallon Mom tayi, dudda gabanta na mahaukacin faduwa amman ta daure ta dake jin Mom nacemata auren yakare tace “ina z……” kwata kwata maganan ya makale mata awuya sabida kallon da Mom ta mata, strictly Mom tace “are you questioning me Asmeey? Koko gezo idanuna ke miki? Koko ciwon kunne yasa naji kaman kin tambayeni ina zaki?” Girgizamata kai tayi tana kuka tace “Y….a yace…..kar…..kar….na…..na……fiii……” Mom tadaga murya tace “ni kike gayama Yaya yace karki fita? Ni Asama’u?” Mamaki yawani kalan cinye Mom ganin Asmeey kaman tarage shakkan ta dan wlh ada Asmeey bata isa tace mata wane kaza ko kaza ba, Mom ta buga kirji tace “nadaukeki acikina! For 9months! Na raineki! Na haifoki! Nature you kawowa this day, Asmeey ni mahaifiyarki kike cema ina zan kaiki? That tababben yaron nan yace karki fita”? Girgizama Mom kai tayi tana kuka wani tsoro na tarwatsa mata zuciya, Mom tace “okay sabida kinyi aure kin zauna awannan wulakantaccen dakin karo karo dawani gantalallan yaro da iyayensa ke ciyarwa har yau! Tufatarwa har yau! Basa makwanci har yau shine kike kike tambayana ina zankaiki kehh! Tufiakwa!” Kasa Asmeey tafarayi tana dukawa cus Mom tafara maganganun nan saitaji rayuwanta na hargitsewa Mom tazo wajen, batai wata wata ba ta daga kafanta da takalminta ke kai mai tudu tawani daki kan Asmeey tace “na kasheki na kashe banza wulakantacciya!” Jikake kummm goshin Asmeey da kanta gabaki daya sun daku da katakon gadosu, gindin tundun takalmin Mom yasa goshinta ya fashe saiga jini wajen na kulu lokaci daya sai kawai Mom ta duko takalleta yanda kan Asmeey ke kasa tana kuka ta rakube da gado kaman marainiya, Mom takai yatsanta takama habanta tadago da fuskanta tace “kalleni nan!” Kallonta Asmeey tayi jikinta na tsuma na kuka tana makyarkyata bamata iya kallon Mom sosai tsabagen tsoranta kaman wata doddanniya haka Asmeey ke ganin Mom, cikin wani irin murya Mom tace “tsakanina dake is biyayya Asma’u sabida ke diyata ce, duk randa kikace bazakini ba bakida ragowan amfani a duniyan nan!” Mom ta nuna mata wardrobe tace “kinga ledan chan maganin bera ne aciki full sachet! Idan you refuse to come with me you choose here kinyi choosing mijinki bakida ragowan amfani aduniya makesure kin dauki maganin chan kin ci inaso naji sanarwan mutuwanki da gaggawa shiyafima rayuwata alkhairi naga kin mutu!”Mom tai maganan batare data daga murya ba Asmeey tawani irin kallonta tana nishi tanaji kaman ma mutuwan na zuwan mata yanzu, Mom tace “since you are torn between Mahaifinki, ni, dakuma mijinki, idan baki bini ba nima na jaye permission na barinki kicigaba da numfashi aduniya your live belongs to me Asmeey! Menace?” Bakın Asmeey nawani kalan bari batama iya maganan da kyau sabida yanda Mom tarike mata habba tace “my life belongs to you Mom!” Wani kalan kallo Mom tamata ido cikin ido tace “na tsaneki Asma’u! Na tsaneki! Ke Allah ya halakaki mutuwan ma banso kiyi ta sauki! Nakawo Fawaz nace shinakeso ki aura ki zabi mahaukaci! Arayuwanki kap ni uwarki niyakamata kibi zabinta not zabin mahaifinki or this jobless boy! I made you Asmeey! You become human in my tummy, and u come to this world through my vagina so kawani yaro mahaifiya ke da iko dashi not uba saisa Annabi ya ambato uwa sau uku kafin uba!” Wani irin ijiyan zuciya Asmeey take tana kallon Mom kallon wat is left again? Rayuwanta yagama yawo? Mom tasaki kumatunta tamike tawuce “tashi mutafi” wlh kasa motsi Asmeey tayi maganganun Mom yasa taji kaman she’s brain dead sai hawaye dake sauka daga idanunta kawai, juyowa Mom tayi ganin Asmeey batai motsi ba mamaki na kashe Mom ganin Asmeey ta chanza tace “badake nake magana ba? Wuce muje someone need to see you!” Ko gezau Asmeey batayiba kaman ma bata hayyacinta, Mom batai wata wata ba tazo wajen ta duko ta daura mata mari dayasa Asmeey taji she’s not just brain dead yanzu she went blind Mom tai ihu da duka gidan ya amsa. “Wuce muje nace kin gama zama da mahaukaci ma kashe auren!” Daidai lokacin aka bude kofan dakin Mamie ta shigo idanunta kan Asmeey dake duke gaban gado tarakube kaman mussa ga jini nabin goshinta dayayi kululu kumatunta yayi jajir hannuwan Mom sun fito radau, dasauri Mom tai wajen Asmeey taduka tanakai hannunwanta tataba goshinta tace “Asmeey! Asmeey! Innalillahi! Asmeey!” Ko motsi Asmeey batayiba, Mom azuciye tace “Hamida tashi kibar wajen nan ko ranki yabaci yanzun nan, zan miki duk abinda yazo raina wallahi, you keep coming between me and my daughter ubanwa yataba coming between ke da yaranki”? Sakin Asmeey Mamie tayi ta taso batai wata wata ba tawani kalan tura Mom Mom ta bugu da kofa azuciye Mamie tace “bar gidan nan! Get out of my house!” Mom tayi wani dariyan keta ta nuna gidan tace “is this wat you call house? This useless 90s house? Yes I am going but da y’ata idan kin isa kihanani” Mamie nawani kalan kallon Mom tace “Salima bantaba ganin wata Uwa dana kalla naji araina cewa she don’t deserve to be a mother arayuwana ba saike! Salima kin dauka abin adone yara sudingajin tsoron iyayensu haka? This is not flex halin nan da dabi’an nan yasa duk na raina iliminki! Your education, qualifications is rubbish is utterly nonsense, kina part of human right activist yet you abuse this poor innocent girl kullum kullum! Koda agidan karuwanci, cikin shege, a turakan karuwai kika haifeta banjin you will be treating this poor child like a goat or jaka hakaba! What is her mistake? What is her sin? Me Asmeey tayi? Look at her! She is just an innocent little girl da all she wants is Mamanta tasota, just look at her face for once arayuwanki with love! Me Asmeey tamiki? What is her crime Salima? Metayi? Metayi? Metayi miki tell me why are you hurting Asmeey na? What did this bright young smart child did to you Salima menene gayamin?” Mamie tafashe da kuka dan yau takasa rike zuciyanta abin namata ciwo, tanunama Mom dake kallonta hannunta dakeda jinin Asmeey na goshinta Mamie nawani kalan kuka tace “look at blood na yarki? Salima wanda ta sanadinki yake zuba! Look at hannunta akarye ta sanadinki! Dubi jikinta duk kene Salima me Asmeey tamiki ehhhhhhh? Menene? Why this much hate for yarki dakika haifa da kanki, why why why do you want Asmeey dead? Sai kinga gawanta zaki huta? What did this poor girl do? Ki gayamin cus azaban yayi yawa, ina gujemiki alhaki fa! Wata rana zaki nadaman abubuwan dakikama yarinyar nan ki rubuta ki ijiye, Salima kiji tsoron Allah” lumshe idanu Mom tayi tabudesu takalli Mamie tace “kinga yanda kika hankadani na bugu da kofa na yafe miki sabida naga kin tsufa jikinki ya gajiya amman kika kara kuskuren tabani saina miki jina jini wallahi tallahi, y’a dai nina haifa ba ke ba ko, ko sokamata wuka nake ba ruwanki! Abarmin kayana! Ninayi wahalanta tun tana yar kunzugu, tashinmini agaba nadauki y’ata mubar gidan nan” tsayuwa Mamie ta gyara tace “idan kin fita da yarnan daga gidan nan saidai idan nafadi anan na mutu Salima!” Ijiye jaka Mom tayi akasa tace “hahaa inaga Asmeey bata gayamuku wacece mahaifiyarta ba, tashi Salima nace” Mamie tace “kome zakimin kimin yanda kika tsani yarnan zan gwada miki akwai wayanda zasu iya basu ranta just to protect her, Salima kasheni shine abinda zaisa ki dauki Asmeey, do your worst” wani irin yunkurowa Asmeey tayi tana layi kanta ya bugu, wani dummm yake mata but tanajin hayaniyan Mom da Mamie hakan yasa ahankali tace “Mamie karki fada da Mom sabida ni Mamie yakuri”maganan da Asmeey takeyi kadan kadan yasa Mamie tajuyo tana kallonta tana kokarin dukawa tama Asmeey magana Mom tawani pushing Mamie mercilessly Mamie tayi mummunan faduwa ta bugu ta desk da chair na Hamad laptop dinsa da desktop suka fado kanta tana kokarin tashi takasa tarufe idanu kaman ta mutu.
EPISODE 4️⃣3️⃣
Asmeey tayi wani ihu tana layi zata tashi tai wajen Mamie Mom tawani ja gaban riganta tadauki jakanta ta finciki Asmeey kaman karya tafito da ita, Asmeey na ihu tana “Mamie, Mamie” amman Mom janta take, yau Sunday masu gini duk basanan mai gadi ma yafita matarsa ce kawai agidan, Mom awaje tai parking motarta, jan Asmeey take sosai akasa Matar mai gadi tafito da gudu but ayanda taga fuskan Mom da yanda Asmeey tai kama da Mom saita sandare takasa magana Mom ta fito da Asmeey waje, daidai Hameed na wani wawan parking motarsa agefe gindansu yafito da gudu, saiga motansu Abba da kawai yakirasu kai tsaye yace komenene su barshi sudawo gida ba lafiya, suna duk sukai parking suka fiffito, Hamad yafito idanunshi sun rikida yashiga takowa a zuciye da saida gaban Mom yafadi ganinsa, dasauri tasaki hannun Asmeey data zube awajen tana kallon Hamad tadan rude takai hannunta tasa ajaka tafito dawani black Nylon dayayi nauyi a hannunta, Hamad yasa gudu dan sundanyi parking nesa da gidan su, kafin ya iso Mom ta jefama Asmeey ledan wani red grinded yaji na zubewa tundaga saman kan Asmeey down to jikinta kawai tabude mota tashige taja motar da mugun gudu tabar wajen.
Asmeey tayi wani irin ihu da tunda aka haifota duniya bata tabajin kalansa ba. “Wayyyyoooooo Allah na namutu! Innalillahi wa Innailaihi raji’un, na shiga uku na lalace, azaba na mutu, wayooooooo azaba” she’s screaming in excruciating pains da top na voice nata tanajin azaban da tace maybe zare ranta akeyi Ya Allah! Hamad baiyi wata wataba kawai yarungume Asmeey batare daya damu da barkonon ba, ina Asmeey bamatasan wake kanta ba sabida kololuwar azaban burkono datakeji, tana wani irin bankarewa daga jikin Hamad dake kokarin daukanta tana kokarin yin tsirara tadaga duka hannayenta tasa asaman kanta kaman wacce tasamu tabin hankali! Ina Hameed jiyayi kaman ya halaka Mom yace “Wlh saina kashe matan nan” yabude mota Faisal da Ya Abdullahi suka bisa sukaja motar Abba yakasa motsi haka ma Gwaggo sunyi mutuwan tsaye, da sauri Ya Mustapa yayi wajen Hamad harya dauketa yashiga gida da ita ganin an fara taruwa awajen, garden ya ijiyeta yadauki pipe na ruwa yawani bude with full force yasamata tundaga saman kan Asmeey zuwa kirjinta da hannayenta idanunta ta runtse su, ya Mustapa yayi wajen motansa yabude yana neme neme Abba yarike Gwaggo dake wani kalan kuka suna shigowa ciki, tass saida Hamad yacire duk wani yajin kawai yasake daukanta Ya Mustapa daya kwaso magunguna yabiyosu da gudu yace “take her to bayi wash her body with soap and cold water with salt bari na dauko salt da ice a kitchen kuje”.
“Zan mutu, zan mutuuuuu na shiga uku wayyooo azaba, Innalillahi wa innailaihi raji’una” dakinsu dayake abude Hamad yayi Mamie yagani akasa tana kokarin motsi takasa idanunta sunyi jajir, wani irin ihu Hamad “Mamie!” Yana ijiye Asmeey yayi kan Mamie Abba da Ya Mustapa na tahowa dakin da gudu, hannu Hamad yakai zai daga Mamie Ya Mustapa yace don’t touch her akwai yaji ajikinka just handle Asmeey”Hamad yawuce da Asmeey bayi Abba yadago Mamie da sauri datake motsi da kyar tace “metama Asmeey take ihu haka? What happen to this poor innocent child”? Abba na shafa fuskanta yace “are you okay”? Gyadamai kai tayi tace “dan bugawa nayi bari naje wajen Asmeey she’s screaming” Abba yatayata ya dagota da kyar take tafiya tana dafa bango, bayın tawuce Hamad dake hada ruwa yana zuba salt