Showing 18001 words to 21000 words out of 221707 words
nuna tamaji tunda ba agabanta yafadi maganan ba but still Baba saiya shiga mai fada calmly yace “har na girma Gwaggo na dukana sabida tana kano ne gidan Baffan ku zasuzo next week salla zaka gani, amman bantabaji dama ba itane mahaifiyata ba, I know your Mom is hot tempered but she wants the best for you saisa take damunka she wants you to become one of the best doctor kaman Yayanku Mustapha eh? Danta mare ka gaban kannenka sai mene ba kanninka bane? Suma ai idan ya kama zata chasasu agabanka kasan mamanka tanada fushi da zafi but she’s very sweet she can give you anything you want don’t ever make that mistake kaji?” Gyadamai kai yayi Baba yace “first thing tommorow morning go and apologize okay” gyadamai kai yayi Baba yace “kwanta anjima katashi saikai salla kahuta yanzu” yazauna kusada shi yana shafa kanshi yaron sai sauke ijiyan zuciya yake bacci yayi gaba dashi.
Saida Ammi tasata ta chanza kaya ta kwanta kan gado sannan takashe musu wuta tafita, shiruuu Asmeey tayi gabanta sai fadi kawai yake yau ta batama Mom rai tarasa inda zatasa kanta har 1 nadare takasa bacci tanajin munsharin kowa tashi zaune tayi ahankali saikuma ta mike tana tafiya ahankali tayi wajen kofa tabude tafita da kyar take tafiya har zuwa kofan dakin Mom tabude tashiga babu kowa a falon gabanta sai fadi yake har zuwa gaban bedroom na Mom dayake arufe tai knocking tama kasa sallama jikinta yafara rawa strictly Mom tace “who is there?” Kasa fadin itane cus tasan Mom zata koreta sai kawai tabude kofan Mom na zaune kan dadduma da hijabi a jikinta da charbi tazuba mata idanunta da babu glass acikinsu sabida dare gaban Asmeey yafadi sosai tasa kafa zata shigo dakin Mom tace “kada ki kuskura ki shigo dakin nan da kafafunki” sai kawai Asmeey ta zube awajen kofan tai kneeling ta rushe da kuka sosai bana wasaba tace “Mom I’m sorry” wani kallo Mom tamata tace “kada ki kuskura ki sake kirana Mom call me Salima na is far better for me you challenged me today? You challenged my authority? Were you trying to tell me kin fini son Munir? Ke gaki big sister? I keep telling you ki tashi daga gabana ki kaki? Waye ke Husna? Guda nawa kike? Yaushe nadena miki wanka? Yaushe kika fara nono dahar zaki challenging dina? Okay now u have everything danake dashi kema kin isa kija dani right”?Girgiza kai Asmeey kawai take tana kuka, asanyaye tace “kiyakuri Mom wlh bazan karaba I will never challenge you, kene mamana I will always do as u told me, banso ki daki Munir ne saisa nakareshi, I will never challenge you duk randa zanyi ma Allah ya kasheni” wani murmushi Mom tayi irin wanda kesa yaro zawo tace “Asmeey kenan Alhamdulillah I have other children masumin biyayya dajin maganata dan ke da Munir kun kini babu komi ai dama bahaushe yace haihuwa da yawa nada rana, kuje dake dashi na barwa kishiyata ku daman ai ita kukeso? Baki taba fita bakije kin mata sallama ba, most of the time she knows your need kafin ni uwarki na sani so tashi kije na yafeki na yafe dan uwanki ma nabarmata ku tahada tarike” wani irin kuka Asmeey take kaman tagama kadewa a duniya zatai magana cikin kuka Mom tace “ke!” Hadiye maganan tayi, Mom tanuna kanta tana buga kirjinta tace “ban haifi d’a ko yarda zataja dani ba, my relationship da abin da cikina ya haifa is nace kiyi kiyi ko kinaso ko bakiso, nace karkiyi karkiyi ko kinaso ko bakiso! You couldn’t maitain that kinmin girman kai kinmin gardama dan haka kije na yafeki” yanda Asmeey ke kuka idan wani na wajen zai iya tayata sabida ban tausayi Mom tace “kin bashi listening ear sabida kema ina forcing naki kiyi karatu, kin bashi listening ear sabida indirectly he’s saying everything dake zuciyanki, na tsaya akanki kinyi school nasa kinyi law, nai making sure kinyi graduating da first class yanzu kuma I’m grooming you towards law school dazaki tafi so kema na takura miki ko?” Girgixakai Asmeey tayi takasa magana sabida kuka Mom tace “no no no speak up ai yanzu dukanku kun sami freedom kuna iya gayamin kome kukeso, tell me Mom banso na gajeki, tell me I’m forcing you! Tell me Mom I never wanted to become a lawyer tursasani kawai kike” baki Asmeey tabude zatai magana Mom tace nunata da yatsa tace “kul!” Cikin kausassan murya tace “stand up and leave wajen nan dagayau karna kara ganinki ko da a parlor na ne, kada ki kara shigomin side dina, kije wajen uwar dakuke craving tazama taku na barmuku ita” cikin wani irin kuka Asmeey tabude baki zatai magana Mom ta daka mata tsawa tace “barmin side dina kafin ranki yabaci, ke din banza! Kaskantacciya irinki wacece ke Asma’u dazaki gwadamin kinfinison Munir get out of my site” dasauri ta tashi hartana neman fadi tabar wajen tawuce tafita takoma dakinsu ta kwanta agado sai kuka.
Da asuba da Ramla ta farka a zaune taganta idanunta sun suntum dasauri tace “Asmeey you’ve been crying ko?” Girgiza mata kai tayi, Ramla tace “dalla ya isa stop crying Mom zata sauko keda bada ke ake fadaba ke kikaficin duka” sai kawai tawuce tafita but har cikin ranta batason yanda Mom kema yaranta wlh.
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 7️⃣
Baba na falo dukansu suka shiga gaidashi yakalli Asmeey yace “meke miki ciwo yanzu?” Ahankali tace “bakomi” yakalli Munir yace “kaifa”? Shima ahankali yace “bakomi Baba” Baba yace “okay kuje ku gaida Maman ku tana ciki” dukansu gaba daya suka wuce kitchen Mom na tsaye cikin kitchen din tana directing yan aiki duka suka shigo suna gaidata she answered dukansu banda Asmeey da Munir, tace “Ramla bring crete na egg from the store” Ramla tace “to Mom” tawuce store, ahankali Hamda tace “mezanyi Mom” kaman bada ita ake magana ba Mom tace “Hannatu sa ruwa a doyan nan wannan yayi kadan” ahankali Munir yace “Mom kiyakuri” kaman bada ita sukai magana ba Mom tace “yauwa ruwan yayi hakanan hannatu daura akan wuta amma yaran nan tea kuma su Yusra” Ramla tafito ta ijiye egg din Mom tace “zaki iya tafiya” tawuce ta tafi su suna tsaye Mom tacigaba da abinda ke gabanta kaman bata gansu ba kusan 10min suna tsaye awajen Baba daga falo yace “Asmeey Munir kuzo nan” juyawa sukayi suka fito daga dakin sukazo falo Baba yakalli Asmeey yace “jekisa kaya I will take u to hospital kafin naje aiki”gyadamai kai tayi tawuce Baba yamike yawuce sama, Mom na tsaye a kitchen din wayanta yayi kara takalla “Ki sameni a side naki” takaranta sakon Baba.
Anatse takalli Hannatu tace “cigaba ina zuwa” tawuce sama falonta tashiga dakinta Baba baya ciki hakan yasa tawuce dakinshi dake side nata tabude kofan yana zaune akan gadonshi tamaida kofa tarufe ahankali tace “ina kwana Alhaji” ranshi a masifan bace yanunata da hannu yace “Salima akan yaranan nan ni da ke wlh wlh zamu samu matsala zan sabamiki sosai! Yarana sune rayuwana you know that! You know how much I love yarana! Why? Akanme zaki dinga azabtar dasu? Munir namijine yanada those manly features in him Is not proper ki dinga dukansa agaban kanninsa, he’s not a child he’s 20yrs, akwai other ways na hukunta yara not by beating! Mesa kin cika saurin hannu? Kinga tabon da kikama Asmeey a jiki? Wat is wrong with you Salima? Mesa kin cika zafi? For God sake Asmeey is a gurl aure zatayi gidan wani zata haka kikeso aganta da tabo abaya? Me amfani kalan wannan zuciya taki?Kowa yasanki da masifa yaran gidan nan babu wanda baya tsoronki! Ki kiyayen mini yara! Ki kiyayesu! Wlh wlh duk randa kika kara daga hannu kika daki ko Asmeey ko Munir Allah sai kinga tsananin bacin rai na wlh kuwa, idan sun miki laifi give them punishment Munir zaki iya sashi share compound ya wanke all cars na gidan nan I will not talk, Asmeey ma you can give her any punishment, duk randa kika kara tabasu san zabamiki Salima” Baba yayi maganan da karfi, kallonshi Mom tayi dudda ranta abace amman sai ahankali tace “hmmmm Alhaji kenan! Stay out of this please, ba ruwanka da yanda zan hukunta yarana, kuma wlh sai sunji ajikinsu especially Asmeey dataja da authority dina” Baba na mata wani kallo yace “I can lay down my life for yarana especially Asmeey! Kiyi kuskuren kara tabamin yara kiga”yajuya yafice fuuu dan ranshi yabaci jiyama sabida kar yayi abinda zaiyi nadama daga bayane yasa baizoba Mom tabishi da kallo yana fitowa afalo yaga yaran yawuce, fuskanshi ahade ya shiga mota driver ya jasu ko 1hr basu bataba suka dawo gida yace “Munir shirya katafi school” gyadama Baba kai yayi yawuce dakinshi Baba yakalli Asmeey datagama zuru zuru yace “jeki kwanta kihuta” gyadamai kai tayi ta tashi tawuce saida yajira Munir yafito sannan suka fice tare, Asmeey na shiga daki kawai tasami gefen gado ta kwanta Ramla ta kalleta duk jikinta yayi wani iri tace “nakawo miki abinci?” Girgiza mata kai Asmeey tayi, Ramla tai shiru tana kallonta bata taba furta maganan nan a fili ba sabida tsoro but anya Mom ce ta haifi yaran nan especially Asmeey, Mom treats the girl kaman wata abokiyar fadanta yar adawanta, Asmeey na tsoro mamanta har cikin kayan cikinta, she just wants to understand something why is Mom like this? Menene abinso a yarka tadinga tsoronka kaman taga mala’ika? She’s too small to understand ne ko akwai wani abune why do Mom hates Asmeey? Wlh da itane Ammi kemata abinda Mom kema Asmeey da tuni ta gudu tabar gidan nan, dan ijiyan zuciya kawai ta fuzar saita zauna ahankali gefen Asmeey, hannunta takai ta dafa kafadanta murya chan kasa tace “Asmeey” dago kanta Asmeey tayi ta kalli Ramla sai kawai ta fashe da kuka ta kifa kanta a kirjin Ramla tace “Ya Ramla I’m a bad daughter I hurt my Mom, bai kamata na tsaya inata sauraron abinda Munir yaketa fada gama da Mom ba, a good daughter bai kamata ta tsaya and listen to any magana ko kalamai marasa kyau akan mahaifiyarta ba, and nadinga tarema Munir da zata dakeshi i didn’t even know why I did it kawai yabani tausayine, banso ta dake shine, da Mom ta daki Munir gwara ta dakeni, he said all he said out of anger but ai Munir is a good boy, he always care for me he shares everything he has with me” ahankali Ramla tace “konine bazanso adaki Munir ba, stop crying hakanan, Mom zata hakura ya isa, you are hurting yourself Asmeey” ijiyan zuciya kawai take ita kadai tasan yanda takeji a zuciyanta, maganganun Mom sun zauna aranta waye ita zataja da authority Mamanta? Was she trying to show Mom tafita son Munir bayan Mom ne ta haifeta? She is feeling so bad and guilty, ahaka baccin da batayi last night ba ya kwasheta ajikin Ramla, Ramla ta kwantar da ita she’s feeling very bad even though sunada different mothers but sunason junansu regardless saisa ma Baba ke hada yaransa waje daya su kwana kuma kusada dakinshi. Tashi tayi ahankali tafito daga dakin tawuce dakin Ammi tabude kofa, Ammi na zaune a falonta wani wa’azi takebi a Sunna tv Ramla ta shigo hakan yasa ta kalleta dasauri ta maida kofan tawuce wajen Ammi ta zauna kusada ita dab sai kuma tayi shiru Ammi tace “menene? Meya faru?” Kaman bazatai maganan ba takasa rikewa murya chan kasa tace “Ammi mesa Mom batason yaranta especially Asmeey kaman yanda ke kike sona?” Tsareta Ammi tayi da idanu tace “idan gulma yakawoki tashi kibarmin daki” kaman zatai kuka tace “wlh Ammi Asmeey tausayi take bani sosai, Ammi kinga ke baki dakinmu baki kwana tareda mu, I use to see wat she’s going through kullum, Ammi idan Mom tabata manya manyan files din nan nasu na kotu idan yarinyar tazo bata iyaba ko bata gama abinda Mom tasata ba kaman zata zare kaman zata haukace wani zubin har zawo takeyi wlh kaman zatai hauka, Ammi all of us zamuyi bacci banda ita sabida she’s trying to read duka abinda mamanta tasata, saisa most of the time saina tashi nabar dakin cus idan ina kallonta zuciyana breaking yake wat kind of mother is Mom Ammi? Why is she making her daughter go through so much pain? And Asmeey can’t react sabida she feels abinda Mom kemata is okay and is normal, Ammi batada lokacin kanta sabida Mom kanta ba kitso sabida Mom, time din dazata zauna ta kula da kanta takasa sabida tunanin files din Mom, what kind of mother is Mom eh Ammi?” Murmushi Ammi tayi tace “the best mother but mai worst approach, Allah ya kyauta ke banson maganan baruwanki kicire idanunki akansu yanda nakeyi dake dasu Yusra ba dole ne sai Mom tayi haka da nata yaran ba so mind your business” hawaye ne yataru a idanun Ramla ahankali tace “Ammi please ki gayama Baba azaban da Asmeey is going through cus bai sani ba, Ammi the worst part is Asmeey can not even show cewa she’s sad! Wlh bantaba ganin sad young girl kaman Asmeey ba, waya babu any social media sai watsapp, waya babu any contact saina sisters nata da yan gidanmu, friend kwara daya Mom tahana, ba saurayi, school Mom takasa ta tsare ita ke kai yarinya tadawo da ita, Ammi wlh I hate Mo….” Wani kallo da Ammi tamata yasa takasa karasa maganan, strictly Ammi tace “tashi kifita daga dakina” ahankali ta mike tawuce tafita daga dakin.
Around 11 Asmeey ta farka gently ta tashi zaune har zazzabi zazzabi takeji bathroom nasu ta wuce tahada ruwan zafi sosai tai wanka tajuya tana kallon bayanta ta madubi da sheda tako’ina sunyi ja abunka da faran fata, ijiyan zuciya ta sauke sannan tafito tazauna gaban madubi tadauki mai tafara shafawa tana cikin shafa man taji wayanta na ringing har mantawa take tanada waya, da sauri ta juyo akan gadon taga wayan hakan yasa ta tashi ahankali tasa hannu ta dauki wayan tana kallon number which is new, ganin sabon number ne saitaki dauka anata kiranta chan wayan yasake ringing tana dagawa taga Mom dasauri ta dauka kirjinta na bugawa sosai ahankali tace “Mom” Strictly Mom tace “when did you become deaf and dumb? Are you blind da bakiga anata kiranki awaya ba? Fawaz ne call him back kuyi magana” gyadama Mom kai tayi kaman tana gabanta tace “t…toh” Mom ta katse wayan dailing number tayi back harya katse ba’a dagaba sai number yakirata back ahankali tadaga tace “Hello Mom tace nakiraka” shiru akayi kaman ba mutum adayan bangaren hakan yasa Asmeey tace “hello” cikin wani husky voice yace “da Mom batace ki kiraba da bazaki kiraba?” Ahankali tace “eh” anatse yace “why?” Ahankali tace “sabida Mom forbid me from talking to kowa banda my family” dan murmushi Fawaz yayi muryanta bala’in dadi, yadan murmusa yace “ai nima yanzu I’m part of the family since I’m going to be your husband!” Hakanan Asmeey taji gabanta yafadi dumm! Takasa magana kawai tunaninta ya tsaya chak, Fawaz yace “Mom choose me to take care of her last baby gurl, I’m your husband to be Asma’u” abu taji ya tsaya mata awuya sai taji kaman kuka takeji saikuma takasa, murya chan ciki yace “I love you Asmeey” sauke kanta kasa tayi this is the first time wani ke gayamata yana sonta, anatse Fawaz yace “zan dinga kiranki wifey daga yanzu” shiru still tayi ahankali yace “I will be going to London gobe it’s a 2days trip idan nadawo I will come and see you okay Wifey” shiru tayi jin batayi magana ba yasa yace “are you there” rasa abinda zatace yasa tace “wayana zai mutu my battery is low zansa charge” dasauri tacire wayan daga kunnenta ta katse ta yarda wayan tareda kifa kanta agado tana sauke ijiyan zuciya. Kusan 3mins tayi ahaka sannan ta tashi tawuce wajen wardrobe nasu tabude wani atampa taciro gown tasaka green yamata so simple a jiki tasaka hijab sai kawai tahau kan dadduma.
Around 3 Mom ta shigo gidan kashe motanta tayi ta shigo falo Ramla tace “Mom sannu da zuwa” ko kallonta Mom batayiba tawuce daki abinta Ammi tafito daga dakinta takalli Asmeey datagani gaban dakinsu tana kallon bangaren Mom sai kawai tazo tawuceta ta tafi dakin Mom kai tsaye tasa hannu tabude kofan da sallama Mom na zaune tana kokarin ciro iPad mata daga cikin jakanta ganin Ammi saita tsaya tana kallonta Ammi ta maida kofan tarufe tazo ta zauna kan kujeran dake facing na Mom anatse tace “Maman Aya nasan maganan dazan miki ba lallai ta miki dadi ba, sannan ba hurumina bane but all I know shine d’a na kowa ne! Asmeey da Ramla da Munir duk daya suke awajena” Ammi ta danyi shiru sannan ta kalleta ido cikin ido tace “Salima yaran nan mune muka haifosu amman kisani amana ne su agaremu wanda Allah yabamu rannan gobe kiyama Allah zai tambayemugame dasu, hakkinsu na kanmu, idan muka cutar dasu Allah zai saka musu sannan zai hukuntamu! Kene mahaifiyar yaran nan kinsan me kike musu kinsan ya fushinki yake aransu, nasan sun miki laifi but yanda kika sharesu is torchuring them, tun jiya they couldn’t eat sabida ke! They couldn’t sleep sabida ke, Asmeey tun jiya takasa saka lafiyayyen abinci abakinta same with Munir dudda Babansu yatasashi agaba yatafi school tun safe, I’m sure ba lallai yama gane abinda ake koyarda su a makaranta ba! Gabaki daya yaran kin barsu agantale duk sun zama wani iri, idan ciwon zuciya ya samesu ko hawan jini I’m sure you will not forgive yourself Salima! It’s okay for us mothers to be angry but kinfi kowa sanin mai fushinki yakema yaran nan I don’t even know wat I’m doing her but seeing them is breaking my heart, what is so big dazakima Asma’u kalan tabon da hala yaran dazata haifa nan gaba zasu gani a jikinta? Aganina me wacce zatai fada ne da duk wanda zaiyi inflicting such pain ajikin