Showing 66001 words to 69000 words out of 221707 words

Chapter 23 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

tashin hankali Aya tace “….y….y…..e…..s Mom am…….” “Basss!” Mom tabude idanu tana daga mata hannu, Mom ta buga kirji muryanta nawani kalan rikida kaman namiji tsabagen bacin rai tace “Aya ni mahaifiyarki zaki yaudara? Kai! You betray me Aya”? Dasauri Aya tace “wlh wlh wlh Mom nima bansaniba banmasan Baba zaiyi hakaba saida yagama yaz……..” “Keee!” Mom tadaka mata wata uwar tsawa da saida Maman Nana tamatsa baya da gudu itama danta tsorata kawai Aya tafashe da kuka sosai awaya, Maman Nana na kallon ikon Allah, Mom tawani girgiza yatsa da kada kai kaman Aya na gabanta tace “habawaa Aya ke kinyi naki! Kin gwadamin taki wasar, wato kin goyi bayan ubanki ke dari bisa dari ya aurar da kanwarki to that jobless boy mai kama damai matsalan kwakwalwa, which I believe da ace his parents got him check he’s definitely suffering from a mental illness one way or the other, Babanki ya aurar da sister ki to a psycho and you kept Mute kika tattarakika tafi gidanki? Did you for once think of how yaron zai ciyar da kanwarki? How will he clothe her? Asibiti? Rashin lafiya? Tufatarwa? Menene menene ina yaga kudin all of that? Koko kinaso duk sanda Asmeey needs something sai yayyinsa sunyi karo karo an mata? Ni za’a dauki y’ata a aurama those people that are literally my sworn enemies they hated me and hated my existence? Ni zaki gwadama ke diyar ubanki ce?” Aya na kuka sosai tace “wlhy wlhy Mom bah……” “shut up! Ke dabba ce koko ke mahaukaciya ce da zakiji this kind abu bazaki sanar dani ba”? Mom tayi wani dariyan keta tace “now I get it! Kema you just want sister ki tafita daga hannuna at all cost kaman Munir ko?” Mom tawani gyada kai tace “gyara kunne ki kiji Aya na fada miki wani abu dabaki sani ba” Mom takada kafafu tabuga kirjinta tace “kinga Asma’u nina haifi yarnan da cikina and I own her entire life Billahillazi La’ilaha Illahuwa, ba Kano ba idan zasukai yarnan karshen duniya if I want her back she will come to me, babu wani wanda keda iko akan Asma’u sama dani kap duniyan nan, and zan gwada muku dukanku wacece ni muje zuwa the game is called 1 versus All, ni da ku duka, let’s see who will win and who will lose, Aya for now forget kinada wata uwa ko mahaifiya mai suna Salima good night” Mom takatse wayan Aya na kuka sosai trying to talk to her but ina, Aya tacigaba tacigaba da kiran Mom kawai Mom tasa wayanta a DND tana kada kafafu jikinta na kyarma na fushi Maman Nana dake daga nesa tace “kiyakuri and calm down Maman Aya, kema kinsan I will always stand by you duk runtse duk wuya ina sonki Maman Aya kome kikeso ki sanar dani zan miki shi amman dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji Maman Aya, Wallahi Baban su Aya bai kyauta ba Sam Sam kuma nasan duk zugin Yayansa ne Baban su Doctor da Gwaggo, kigafa sabida acimiki mutunci sai aka aurar da ita ga wanda baida ko kwabo wanda har yanzu suke ciyarda shi, Allah natuba bawai inaso bane but amman inama laifin Hameed ai shi yanada dan sana’ansa yana aiki a banki ga yar motarsa yanada shi amman Hamad? Baki karya ba dakikace kaman yanada matsalan kwakwalwa dan wlh haka yake abu kaman mai tabin hankali, bayason mutane baya shiga mutane baya kallon mutane wannan wani irin aure ne su aurama Asmeey mara lafiya gaskiya gaskiya Baban Aya bai kyautaba cin mutunci yayi yawa sai kace shi kadai ya haifi yarinyar ai naga Asma’u yarkuce ku biyu kamata yayi kuyi shawara kafin komi”. Batare da Mom takalli Maman Nana ba tace “zaki iya tafiya” kallon mamaki Maman Nana tamata ganin yanda Mom tai shunning maganganun datayi kaman wata mara daraja saikuma tace “toh mu kwana lpy” tabude kofa tafice daga dakin Mom na zauna awajane tana karkadan kafa tana saka tana warwara tana jinjina abinda Baba yamata irin war gives him the right ya aurar da yarsu without consent nata? Hmm now he started this war on her nobody should blame her for any kind of outcome war dinnan zaiyi yielding suje zuwa, yanzu me zata gayama Fawaz? Mezata gayamai? Idan yarabu da ita fa? She can’t live without him? Idan yaji zancen nan she’s done Goddds wat is this Baban Aya fucked her up big time.
💫UWA KO UKUBA?💫


✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣3️⃣




Tashi tayi tawuce wajen window tadaga labule taga Baba yafito tareda Munir sun wuce masallaci chan saigasu Mustapa sun wuce chan kuma Kawu da Baba da Hameed, chan dan har anje ruku’u saiga Hamad shima yafito, Mom ta tsare Hamad da idanu tana gyara glasses nata tana kara karemai kallo, he walks one step at a time da bala’in natsuwa sai wani sheki yake kaman ma wanka yayi, hulan kwankwasa kaji hadisi ke kansa da faran jallabiya, yayi wani irin kyau yana tafiya, tsayawa taga yayi chak duk Mom na kallonsa to her biggest suprise saitaga Hamad yadago kansa sama ya kallo exactly directly window ta chan saman bene sun hada ido, sauke kansa kasa yayi anatse yacigaba da tafiya, Mom tace “mahaukacin psycho, I said it, yaron nan yanada mental disorder normal people sun wuce no body notice me but he did, this are signs na masu mental kolo kolo brain yawan lura ina chan sama tsaye wajen window but jikinsa ya gaya masa ina nan, my daughter will never join blood with you”.
Saida Hamad ya shiga masallaci Mom tabar window tafada bayi tayi wanka tafito tabude wardobe, wani shadda gzinar taciro royal blue dayaji aiki da duwatsu sannan tayi salla tazo ta shirya tsaf takafa wani dauri mai kama da mafici sabida fadi ta kafa glass din nan tafesa turare takoma tazauna tana kada kafa karyansu tasha karya.

Gabaki daya half half tayi baccin jiya she’s trying to wrap kanta around kalman aure da Baba yace yamata, ga damuwa batasan ko Mom ta yarda ko bata yardaba dan tasan Mom basa shiri da this people gashi tun ranan yawon sallan bata sake ganin Mom ba, then ga Ya Hamad, tunaninshi ya addabi zuciyanta kawai fado mata yake arai nonstop, he’s living rent free in her head, her mind, and her heart so duka duka sai asuban nan tasami bacci. Shigowa dakin Mamie tayi dahar tayi wanka ta shirya dan so suke by 8 zasu wuce wajen gadon tayi tana kallon fuskanta she looks so beautiful while sleeping dudda bata gama warkewa ba har yanzu fuskanta da ragiwan ja Mamie tayi murmushi aranta tace “Hamadi na ya auri kyakkyawan yarinya” azahiri kuma tace “Asmeey Asmeey” bude idanunta Asmeey tayi ahankali Mamie tasa hannu tadagota akunyace Asmeey ta sunnar da kanta kasa kawai yausai taji tanajin kunyan Mamie ita kanta Mamie saida ta lura abin yaso bata dariya tace “ni zaki fara wani jin kunya aiko zan mangareki awajen nan” adan kunyace tai murmushi still taki kallon Mamie, ahankali Mamie ta matso saikuma gently ta rungume Asmeey, Asmeey tawani boye kanta jikin Mamie, patting bayanta Mamie tayi tace “Assalamu Alaykum Daughter na!” Runtse idanunta Asmeey tayi da sauri, Mamie tace “I am so lucky d’ana ya auro mini the most amazing and special yarinya kap duniyan nan Asma’u!” Kaman Asmeey zata nutse akasa Mamie tace “Allah ya sanya albarka a aurenku Asmeey, Hamadi yarone na kwarai dana tabbata wata rana zakiyi alfahari kasancewanki matarsa, tashi kiyi wanka kiyi salla Asmeey yau zakije gidan mijinki”kankame Mamie Asmeey tayi kirjinta na bugawa kawai taji she’s having goosebumps, is she happy she’s married to Ya Hamad? Ta tambayi kanta cus bamata san ko farin ciki takeji ba wlh, but one thing she can say for a fact is ko bakinciki daya bataji na an auramata shi, ko jin haushi not at all, batajin hakan but kuma batasan ko she’s happy bane but then she doesn’t feel sad so she finds the whole of abinda takeji wired and creepy feeling da bata taba experiencing in her life ba”
Ganin taki sakinta yasa Mamie tace “ko muje bayi na miki wankan ne?” Dasauri ta girgizama Mamie kai, Mamie tace “to sakeni” ahankali tana kirjin Mamie cikin whispering tace “kunyanki nakeji Mamie” kwashewa da dariya Mamie tayi sosai and she’s so suprise dabataga any sadness regarding aurenba sai kawai taji alakanta abin da yarinyar tagaji da azaban mahaifiyarta saisa take farin ciki da auren, Mamie tayi murmushi tace “cikani naje bayi nasamiki macleen a brush sai kiyi wanka nakawo miki kari kiyi nasan yanzun nan Gwaggo ma zatazo” ahankali tasaki Mamie tana wani juyar da kanta Mamie ta kadakai tawuce tabude drawer dakin inda Aya ta ijiye ma Asmeey kayan dazata saka yau tabi hanya tace “zan kiramiki Ramla ta tayaki” Mamie ta shiga bayi tasamata toothpaste tafito tace “tashi kije” saukowa daga gadon tayi ahankali Mamie tajuya zata fita ahankali tace “thank you Mamie” tawuce bayi da sauri” da kyar ta iya cire rigan jikinta da kanta da hannu dayan tayi komi da komi tafito Ramla tagani zaune kan gado tana mata murmushi sosai tace “Amaryan Ya Hamadi” cus Munir saida yagaya mata jiya but amana dan he couldn’t contain her joy kaman zatai kuka taturo ma Ramla baki tace “ni ba amaryan kowa bace nidai” Ramla ta tashi tana daukan cream tana zuba mata a hannu itama tana sawa tashiga tayata shiryawa ita ta tayata saka hook na bra abaya sannan tasaka gown na atampa mai kyau free dinki ne bubu sabo a atampa Ami kyau dauke kai tayi da sauri saikuma batace bataso ba ganin haka sai kawai Ramla tafice da sauri taje dakinsu tana mamaki chan tadawo da jakan makeup nata ta zauna kan dadduman taciro kwalli tace “bari mufara sashi” tsaf Asmeey ta tsaya tasamata sannan ta shafamata lip gloss bakinta sai kyalli yake Mamie tashigo da tray na tea da chips dasauri Ramla ta tashi ta amsa tace “Mamie kawo” Mamie takalli Asmeey da taga Ramla na mata kwalliya sai kawai Asmeey ta chanza a idanunta, she looks big and matured bubun atampan data sane ko auren da aka mata ne oho but saita chanza, fita Mamie tayi tabasu wuri bayan tace “tadaure taci” Ramla tace “ci sai mu cigaba” chips tasa hannu ta dauka taci saikuma ta kalli Ramla tace “tayani ci muka gama ki shafamin hoda Ya Ramla” ahankali Ramla tace “Asmeey kinason Ya Hamad ne dama?” Dasauri Asmeey ta kalli Ramla sai tafara kokarin magana takasa batasan mezatace ba lips dinta suka shiga rawa da kyar tace “a….a’a” baki Ramla ta tabe tace “munafuka! Wlh kina sonsa cus u look happy today zakibar gidanmu” tass suka cinye Ramla ko ta shafamata hota da abubuwa da dama Asmeey bata hanata ba harda shafa mata eye shadow, tashafa mata janbaki pink tunda taga tanason amata makeup din, tadauki dankwalin atampan tamata dauri mai bala’in kyau sannan tadauki gyalen ta gold tayafa mata bayan tasaka mata da kunne masu kyau takawo mata takalmi flat shoe ta feffesa mata turare sai kawai ta tsaya Tana kallon Asmeey tace “wlh lalle da karayan hannun nan yayi hindering having that full Amarya look but kinga yanda kikai kyau Asmeey zoki kalli madubi” ahankali Asmeey takalli kanta amadubin kaman ba itaba tama kanta kyau kwalliyan da Ya Ramla tamata kaman wata professional makeup artist faduwa gabanta yayi dasauri tace “Ya Ramla mu gog…” shigowa dakin Munir yayi yana washe baki ganin Asmeey saiya tsaya chak kaman ba Asmeey ba she looks exactly like Matar aure, like Amarya, tayi wani irin kyau looking very very matured, da kyar yarufe kofan yataho wajen baiyi wata wata ba kawai ya rungume Asmeey sai kawai ya fashe da kuka Ya Ramla tace “yasin zanje nakira Nana taganka kana kuka” dasauri yadago kansa daga jikin Asmeey idanunsa sunyi jazur duk ruwa ya harari Ya Ramla datai dariya ta kwanta kan gado tana kallonsu sannan yakalli Asmeey da duk saitai wani iri for the first time tunda ta farka saitaji kuka yazo mata amman tadaure, ahankali takai hannunta saman fuskanshi tana gogemai idanunta na tara hawaye tace “na yafemaka duka kudadena dakaci bashi da wanda na baka ijiya” haba Ramla da Munir sai dariya kyakyakya kaman mahaukata, Asmeey tai kwabe kwabe da fuska tana kallonsu tace “to biyani kudina”.
💫UWA KO UKUBA?💫



✍🏻M SHAKUR



EPISODE 2️⃣4️⃣



LAST FREE PAGE🥳
Munir na tsayar da dariyansa ganin tana shirin kuka yace “Ya Ramla Asmeey tafara hankali tayi aure wai ta yafemin bashi harda sababbin 5k da kika bani rannan” suka sake dariya sai kawai ta tsaya tana kallonsu tanajin wani iri sai taji kawai tana kewansu sai kawai tafashe da kuka, Munir dasauri yace “Ya Asmeey menen….” Rungumeshi Asmeey tayi ahankali tace “you are the best brother in this entire world Munir I don’t want to go kano alone, kadingajin maganan Mom please karka bata mata rai kaji” shiru yayi Asmeey tadago kanta tamikama Ya Ramla hannu ta taso itama idanunta sunyi ja tace “Ya Ramla ki gayama Baba zaki bini banso naje ni kadai kinga bantaba zuwa kano ba ke kinji, Ammi duk taje dake bikinsu Ya Mustapa har Ya Faisal ni kadaice bantaba tafiya ba, please kibini tunda ke Kingama school Munir can not travel sabida school follow me” zaro idanu Ramla tayi tace “zan dai zo nan gaba but not now dena kuka toh kinga makeup dinki duk ya baci” dasauri Munir yace “sake mata gaskiya cus Ya Hamadi ya auri fine Babe see my sister naaa who deyy”
Ramla itama tace “fine girl no pimples, Matar Yaya Hamadi agidan Ya Hamadi” kawai Asmeey tasake fashewa da kuka bude kofan akayi Mamie ce ganin yanda Asmeey ke kuka tace “ohhh kuke sata kuka haka”? Shigowa dakin Abba yayi yace “kuzo kuwuce tunda kuka kuke sata” gyalenta Mamie tayafa mata akai tace “muje” kawai sai Asmeey taji kukan yazo mata da gaske Mamie takamata Munir yakama hannunta mai lafiya yana daurewa but he’s feeling very emotional suka fito.

Around 7:45 na safe Mom tabude kofanta tafito daidai shima Baba na fitowa daga dakinsa ya kalleta ya watsar kaman bai santa ba yawuce stairscase ya sauka, sauka tashigayi tafito falon, tafito tsakar gida, Plastic chair tadauka ta ijiye acikin compound din tai crossing leg like a boss tana jiran fitowan su, Ya Mustapa yafara fitowa rikeda dansa Areef dayasa shadda exactly irin tasa da matarsa abaya Anty Asiya ganin Mom a compound duk sukasha jinin jikinsu Matar tafara cewa “ina kwana Mom” nuna alamun tamaga mutane batayiba Ya Mustapa yacigaba da wasa da Areef yace “morning Mom” yawuce abinsa wajen mota yana kunnawa dudda an riga anyi warming kowace mota, daidai su Faisal da Abdullah da matayensu suma sun fito kowa yaga Mom sai yadanci tura regardless zasu gaidata babu wacce ta amsa cikinsu, Hameed ne yafara fitowa daga flat nasu da box dinsu shida Hamad dan su kadai ne basu hada kaya ba sai this morning yana ganin Mom yadauke kai yace “morning” yayi wucewansa yana loda kayansu a booth.
Tsaf Baba yagano Mom dan daya shigo flat din saida ya kalli window yaga Mom zaune a compound, Mamie na sauko da Asmeey dake kuka nan falo saiya karaso yace “ina kwana Yaya” su Ramla na gaidasa ya amsa ganin yana kallon Asmeey sai Mamie ta saketa tace “bari muje” tawuce Abba yabita, hannayenta Baba yarike Asmeey ta kalli Baba sai kawai tafashe da kuka Baba ya girgiza mata kai yace “ya isa, Ya isa come here” sai kawai ya rungumeta yana shafa bayanta Munir da Ramla na kallo sannan Baba yadagota da kansa yasa hannu yajawo gyalenta yarufa mata fuska yace “kumuje” sai Munir da Ramla suka shiga gaba Baba rikeda ita suna biyedasu, kowa yashiga mota dan da duk basu shiga cikin mota ba, Abba ne kawai da Mamie basu shiga mota ba sai Kawu da Mama wanda gobe ne zasu tafi Gombe suma suna waje sai Ammi da Gwaggo, suna fitowa Munir yaga Mom kirjinsa ya buga Baba yashiga tafiya da Asmeey zuwa wajen motocin sunkai kusan tsakiyan compound din cikin kakkausan murya Mom tace “Asma’u” chak kafafun Asmeey suka tsaya kaman an kafasu Gwaggo dake magana da Ammi tace “ubanme zata miki? Yarinyar nan yau kwana nawa tana akarye baki leko kinzo kin dubata ba sai yanzu kikasanta”? Abba yama Gwaggo wani kallo yace “Gwaggo” Gwaggo tace “dalla kamin shiru Abubakar, nace ubanme zata mata take kiranta, nagadai ba son yar takeba ko, banda haka batada iko kan Asama yanzu dan yarinya tadawo matar Hama……” “Asmeey!”Mom takara kiran Asmeey, a tsorace Asmeey da harwani gigicewa tayi tajuyo dasauri tana jan gyalenta baya ido da ido tayi da Mom dake mata wani kallo da ita kadai tasan meaning dinsa, Gwaggo ta taho da sauri tace “ke dalla chan wuce mutafi me akeyi da wanchan matan” anatse Abba yace “Gwaggo ku cikata taje taga mahaifiyarta” wani kallo Baba yama Abba, Abba ya gyadamai kai, sakin hannun Asmeey Baba wani abu Asmeey tahadiye awuya gabanta na faduwa tana kallon Mom dake kallonta itama ahankali saita fara tafiya hakama Mom saitaga yarinyar ma ta chaxa mata, takara girma tabude kaman yaron yama mata wani abu, tun kafin takai wajen Mom saitaji kafafunta sun kasa daukanta kawai saita duka, Hameed dake motan Ya Faisal yace “now this is wat I was saying jiya, here we go” kasama matsawa kusa da Mom tayi bakinta sai kawai ya shiga rawa tace “i…..ina….kwa….na…..Mo……”
Hannu Mom ta mika mata warmly hakan yasa ta kalli hannun Mom saikuma ta kalli fuskan Mom, murmushi Mom tamata tace “come my baby girl” shiruuu Asmeey tayi tana wani irin kallon Mom kaman tasami tv as long as tundaga time datai hankali tai wayau zuwa yau bata tabajin Mom takirata da My Baby girl ba, and she can’t even remember the last time Mom ta kalleta tayi murmushi, saidai taga Mom nama wasu murmushi ba itaba, ganin takasa motsi yasa Mom tace “nazama dodo ne? I’m calling you, zonan Ma’u na, come, give me ur hand” Mom tasake mika mata hannu sai kawai Asmeey tashiga ciro

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login