Showing 210001 words to 213000 words out of 221707 words

Chapter 71 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

Hajiya Ramatu tayi ganin Mom zata mutum musu a falo ya isa security takira security sukazo tanuna musu Mom datai kaman ta mutu tana haki ta jefa mata yan bundle na 500 aka tace “ku dauki akuyar nan kufice da ita kusata a abin hawa akaita gidanta” suka fice da Mom Hajiya Ramatu tayi balbale Fawaz da masifa. “Dan ubanka iskancin ka bai tsaya kan kananun yaran dakake durama ciki ba harna gaji da kashe wuta akanka, har tsofaffi kake ci” cikeda rashin kunya yace “Mommy wat is this? Tabani gindi karnaci Ha’a see me see trouble oo please don’t piss me off Madam” ran Hajiya Ramatu abace tace “ina gujemaka Fawaz karkaje ka kwaso kanjamau tunda kai duk wacce kasamu kaci kama ciki ba protection yaro kwata kwata baka da tarbiya da kama kanka” “shut up” yadakama mahaifiyarsa tsawa tai shiru yawuce dakinsa abinsa ko ajikinsa.

Da kyar Mom tanunama mai keke gidansu tabasa kudi cikin 50k ta sauke da kyar tawuce fuskanta ya kukkumbura dan duka Fawaz yamata na bala’i tashigo gida tazauna compound duk karfin zuciyanta da taurin rai saita fara kuka sosai bana wasaba zuciyanta ba dadi yamata nauyi, Fawaz zai mata haka, she lost everything sabida yaron nan, sabida Fawaz babu abinda batayiba ta musgunawa yarta da bata mata komi, sabida Fawaz ta cusama Baba bakinciki har tazabi saki just to go and bill Fawaz out daga police station, wanki gyaran gida, wanke bayi menene batama Fawaz yanzu in the most darkest moment na rayuwanta zai gujeta? For the first time saitaji babu abinda take kewa sai yaranta, number Aya taciro tai dialing amman baya ma shiga at all, number Aysha takira yayi ringing yagama bata dagaba next kira taji kaman Aysha tamayi blocking nata zuciyan Mom ya katse tayi dialing number Munir bata shiga kwata kwata kaman bata kan network tasake dialing na Aya bata shiga na Aysha busy tai blocking nata kawai saita ijiye wayan tafashe da wani irin kuka tace “I hurt yarana I caused them pain all because of you Fawaz, I tourtured my daughter to dead sabida soyayyan d’a namiji and this is all I get from him! Duka Koran kare! Wlh namiji ba dan goyo bane, bazan taba yafe maka ba Fawaz!”Wani kalan bakin nadama da bakın ciki Mom keji na how she sacrificed everything every important thing na rayuwanta for Fawaz, wanda take tunani bayan mutuwan Asmeey he will focus on her cus he seems to be enjoying her pussy but aure zai karo yar film yar duniya kuma, ga kafa na ciwo ga kowa abandon her yazatayi Yayanta take tunani but tasan takirasa saiyaci mata mutunci yanda yakeda zafi bazaima saurareta ba she knows dole yasan abinda tayi akan Asmeey tayi shiru kawai ta kwanta awajen zazzabi na lullubeta ba kakkautawa.
EPISODE 1️⃣3️⃣8️⃣



Washe gari asibiti taje da ragowan kudin aka duba kafanta Dr yace aiki za’ayi a yanke naman wajen gabaki daya asamata another nama kafin poison din yashiga kashinta, aiki da nama da za’a saya 500k.
Gida Mom tadawo taje takira dillaliya ta saida set na kujerun falo da carpet da dinning da dankararen tv su komi kuma na falon na Baba ne, kayan da normal normal ko tv falo yafi 1m da kyar Mom tahada 1m abanza dillaliyan tasaya washe gari takoma asibiti tabiya akai admitting nata gobe za’ayi surgery tayi undergoing other investigations su xray da sauransu akace takira azauna da ita but batada wanda zata kira she just realized Fawaz yasa tayi feeling nobody is important in her life kawai she just followed him like a fool, washe gari aka shiga aikin aka kwashe naman anan akaga dafi ya shiga kashi fa dole ayanke but bazasu iyaba dole Mom saita farka tabada consent haka aka lullube kafan ba’asa nama ba aka fito da ita, bayan like 5hours allura yasaketa Dr yamata bayani Mom tai shiru tana kallon Doctor is this even real? Ita za’a yankema kafa, bata tabajin tsoro yakamata irin na rannan ba da gaske alhaki nabin mutum dama, no gaskiya zataje wani hospital bazata yarda ayanke mata kafaba ai rayuwanta yakare kennan tace “Dr asamin fatan dana biya nidai bawata yanke kafa zanje Dubai adubani”
Dr yace “gwara ayanke miki yanzu aka saka miki fata kafan ya warke rubewa kafarki zata fara taciki” Mom tace “I reject rubewa pls finish wat I paid for”? Dr yayi yayi Mom taki haka yabarta aka komar da ita aiki aka mata just 1hour yadaukesu aka fito da Mom, kwananta uku a hospital aka sallameta ta tafi gida tasake kirawo dillaliya tv sama da kujeru tasaida da curtains da kujerun flat nasu Abba da Kawu duka kaya dayawa tahada miliyan uku taje tanemi second hand toyota tasaya da kyar hankalinta ya kwanta tazo gida.
Kwananta uku agida kafanta yafara wani irin ciwo dako tafiya da kanta yasoma gagaranta wani hospital taje private nan fa suma suka faracin kudi ana test daban daban before aceme ana neman kusan 1.5 Mom tasake kiran dillaliya funityres na dakin Baba tafitae dana dakin şu Asmeey dana dakin Ammi kaman nata duka ta saida tahada 2M, takoma hospital sai hope suke bata bazasu yanke kafa ba aka bata magunguna masu kyau da allurai tadenajin zafi jikinta yayi kyau tadawo gida again, bayan 4 days saitaga ruwa nafitowa daga aikin takara komawa private hospital din sukace zasu mata aiki su chanza fatar 5m aiki daganan tagama wahala Mom takoma gidan duka wani funityres daya rage na sauran flats din dana dakintama kawai katifa ta ijiyema kanta akasa ta saida tahada 5m takoma akai admitting nata akai aiki bayan 3days tadawo gida tana recovering ba bacci just 2days wani ruwan yauki me wari yafara fitowa daga aikin takoma asibitin sukace ita ke wanka tana bari ruwa yashiga sai an sake chanza skin din 5m again zata kara biya this time komi daya rage na gidan ta sauda harda kayayyakin kitchen da katifan data barma kanta da motan data saya kap tahada 5m da kyar takoma aka sake aiki sunfaga kashin yarube but sunki fada mata sai patch patch suke mata kawai Mom tasake dawowa gida praying wannan ne karshe cus bata da anything left again, rannan takira number Aya wayan ya shiga Aya bata dagaba, ana biyu bata dagaba ana uku Aya tadaga kafin Mom tai magana Aya tace “duk wani relationship dake tsakanin mu da ke mun yanke Mom! Ke kika fara nuna you hate us! You killed our sister and her baby all sabida dadironki Fawaz, u make your choice muma we make ours shine mun barki dashi! Har abada Mom nagama jin tsoronki ko shakkan ki cus kinriga kinyi loosing every respect we have for you! Wlh I wish and wish and wish da bakene mahaifiyata ba! I wish inama Mamie ko Ammi ce mahaifiyata, you don’t deserve to be called my mother! The only reason nake daukan wayanki is because someone has to say it to you, Ayasha da Munir sun fini zafi ko fuskanki basuso su gani dan haka na barki lafiya!” Ya Aya takatse wayan Mom tai wani mutuwan zaune rayuwa kenan! Wato ko duk wanda bai yarda Allah shine above everything and everyone ba yaci baya, is this not Aya da idan tai tsawa saitahau kuka tarude? Yau Aya ce ke gasamata magana haka? Sauran yaran sunmayi blocking nata? Duk tsoron nan da shakka da fargabanta babu shi ko daya aransu ita Mom dake tunkaho tana alfahari da yanda yaranta ke tsoro ta yau yaranta sun nunamata she’s a nobody! Zuciyanta yayi wani iri Asmeey na fado mata arai the only person datasan da ace tana raye zata tausayamata is Asmeey and takashe ta, Asmeey ce kadai yarta dake mata wani kalan mugun so! Ita tasan da ace Asmeey nada rai taganta in this condition she will hugged her cry and tell her Mom I love you! You are the most beautiful Mom….. Mom tawani rushe da kuka wani nadaman abubuwan datama Asmeey na zuwan mata cus Asmeey tafi duka sauran yaranta sonta! Asmey tafisu tausayi! Tafisu soft heart! Tafisu shakuwa da mahaifiyarta! Why did she do all of those things to Asmeey because of a man dagashi nan yau yajuya mata baya? Ita the almighty boss lady Mom ce haka yau? Where is the barristerness? Where’s the connection and her elite contacts yan presidency? She learnt all this elite people datama case sukaci are only using her, idan bakada amfani u are no one to them babu Wanda ya tai maketa and most of them knows she’s sick ta aikama abokan aikinta hotunan kafanta but nobody gave her one kobo not all called sef, she knows Allah is punishing her, tashi daya yasa Fawaz yarabu da ita, yaranta haka, mijinta haka, is time ta nemi gafara, dudda batasan inda Baba yakoma ba ai tasan shagunan sa gobe zataje Allah sa tagansa, zataje gidan Yayanta ta nemi gafaransa shima, zata hada kudi taje Bauchi ta nemi gafaransu, ta nemi yanda zata sami Hamad ta nemi gafaransa takashemai dan ciki da mata.

EPISODE 1️⃣3️⃣9️⃣




Washe gari haka ta shirya hijab tasaka tashiga keke sai rufe hanci yake taje plazan Baba but security suka hanata shiga mutanen da da idan tazo Hajiya Hajiya ake mata ana mata fadanci ana gaidata akace Alhaji yace kar akara bari tashiga da kyar ma ta iya samin Information kan yabar Bauchi yakoma kano one in a while yake zuwa duba shago jikin Mom yayi sanyi daganan ta tafi gidan Yayanta Alhaji Mahmoud, kasa shiga gidan tayi bataso yamata rashin mutunci agaban yaransa haka ta zauna awaje kudaje sai binta suke, around 4 yadawo a babban motansa tundaga nesa yake kallon Mom akofar gida kome sister shi tazama bazai taba iya kasa ganeta ba Salima ta lalace tayi baki, tayi duhu ga kuda sai binta suke, dan farin glasses dinta ya tsufa duk ya koke kaman wata makauniya, budemai gate akayi ya shiga da sauri Mom tashiga tashi tsaye tashiga gidan kashe mota yayi yafito saida yaji wari yakalleta saikuma ya watsar zai wuce ciki da sauri tasha gabansa taduka tahade hannaye looking pathetic tace “Yaya kamin rai! Yarana sun gujeni, mijina haka, duniya ta juyamin baya, kafana tun cizon karya ba lafiya, kamin rai Yaya!” Kafin takara magana yanunata da hannu cikin kakkausan murya yace “nabaki second biyar kitashi kibar gidana! Salima baki isa ki nunamin ni ban isa namiki fada kona gayamiki gaskiya ba sai yanzu da komi ya kwabe miki, Allah ya gwada miki iyakarki zaki nemeni kizo wajen, Wallahi wallahi bazan taimaka miki ba!” Alhaji Mahmoud yafadi azafafe yana kallon Mom yace “babu lallashin duniya daban miki ba ina gayamiki gaskiya amman kin gwammace ki rasa kowa sabida wani dan iskan yaro dakike bi? Harda kashe diyar ki da abin cikinta kaico! Ke bakiga komiba stand up and leave this house, stand up! Yau ina yaran dakike tunkaho kina fafa kina daga kafada cewa sai yanda kikai dasu? When I was telling you a day like this can come da yaran nan dakike gani kin gama dasu zasu juyamiki baya bagashi rannan tazo sooner than I even expected ba? Wacece ke! Ke din banza da wofi! Ke ba komi ba sai girman kai kina feeling kinfi mijinki da kowa nasa ilimi yau ina ilimin? Ina sanayyan manyan mutanen eh hajiyar kotu? Ina kudaden yanzu? Tashi kibarmin gida nace!” Yayi kan Mom kaman zaki takoma baya da gudu, Alhaji Mahmoud yakalli gateman yace “take this smelling woman out of my sight! I do not care kome zai sameki wallahi wallahi I don’t! Bakiga komiba duk wanda baiji bariba zaiji hoho! Go and pay for ur sins alone wallahi ko ajikina! Nayi nawa nayi iyakan kokari na kika maidani jahili baki tubababa Salima, dan da komi zai dawo miki ba chanza wa zakiyi ba, women like u can never change, get out of my sight! Ni ba dam Uwanki bane! Kuma baki bani tausayiba! Abinda kikayi ke binki, ga cin gado ga kisan kai” Mom ta tsorata bata taba sanin her very own blood brother can abandon her in this condition ba well daman ance yara maza basuda tausayi, agaban Yayanta mai gadi yajata yafitar yana jefar bawai beji ciwo aransa bane yaji wlh but yasan Allah ke kamata kuma daman yasa dole a day like this will come, zunubin kisan kai fa? Ga alhakin yarinya hmmm, Mom tayi kuka ahaka daga gidan kawai tawuce tasha around 4something tashiga motan kano sai wari take but tasha ne hakanan aka dauketa wajajen 6 mota tacika sai Kano……


TOM MOM ZATAJE KANO!

ASMEEY NA KANO!

MEZAI FARU?

KUNA GANIN ASMEEY ZATA YAFE MATA TAGA COMDITION NA MOM? CUS ASMEEY NA SON MOM SOSAI?


WAYYOO MOM TABANİ TAUSAYI😭
EPISODE 1️⃣4️⃣0️⃣



Today marks the 3rd week tun dawowansu Kano.
Rannan dasuka sauka washe gari aka fara gyara Asmeey dan wata mai gyaran jiki daga Chad Mamie tabiya tun tana Washington ta iso, ciki da waje ake gyara Asmeey while tana shan su rubutu daga sauransu, kullum rannan duniya suna waya da Ya Hamadi sau biyu ko sau uku, she’s sorrounded cikin yan uwanta su Ramla duk sun gudo wajen Mamie, like gidan Mamie yanzu akwai yara dan gidan Baba is just bayan layinsu, Ya Aysha tazo week dasuka dawo Nigeria, this week ma tazo tareda Ya Aya zasuyi just Saturday Sunday su koma, Asmeey is very happy matsalanta yanzu kadai a rayuwa shine wani jarababben kewan sex datakeyi, ko zama tayi ita kadai sai kawai tafara tuna moments nata da Ya Hamadi, sai kawai taji tajike, she wants to do it again, she wants to kiss him, hug him and do the sex dashi sosai, abinda ba wasa abin har tsoro yake bata ko magungunan datakesha ne oho but feelings takeji sosai.

Yau sunday dukansu suna kitchen din Mamie Ya Aya, Ya Aysha, Ya Ramla, da Asmeey suna aikin, fatan Asmeey sai sheki take tana glowing tayi kiba jikinta yasoma dawowa tana jefa kosai a wuta suna hira while su Mamie da Abba na falo tareda Gwaggo suna hira tareda Ya Mustapa, Ya Abdullahi da Ya Faisal, Hameed ne kawai baizoba, fitowa da kunu Ya Aya tayi Gwaggo tace “ai ina shirin zuwa kitchen din kunu kaman kuna sarrafasa daga farko sabida hira” Abba yace “kyalemin yarana suyi hira abinsu, zo zubamin nawa Aya” murmushi tayi tama Gwaggo gwalo tazo tadauki cup na Abba tasamai saiga Asmeey tafito da kosai a flask mai kyau Mamie tabita da kallo yanda Asmeey ke kara kyau ka kalleta saika kara tafi koda yaushe kyau and she’s very happy ijiye kulan tayi tadauki kosai daya a hannunta tazo kusada Mamie cikeda so takai bakin Mamie tace “Mamie dandana kiji yayi dadi ninayi” Ya Aya tace “kikayi mene?” Turo baki Asmeey tayi takalli Ya Aya Gwaggo ta kwashe da dariya tace “gaskiya tafadi kike tura mata baki” Mamie tabude baki ta gutsura tace “ni nasan y’ata ce tai kosan nan share Aya da Gwaggo kinji uhmmm yayi dadi” dariya Asmeey tayi takai ragowan bakinta ta tashi tawuce kitchen Mamie na binta da kallo hips dinta sun fito sosai magungunan nasa kiba ne koko ciki gareta? But last cikinta raman da ita yayi this one kiba zai sata? This is just sati na uku, ciki zai iya nunawa a 3weeks but she’s really suspecting pregnancy aran Mamie tace “Hamadi ba dama ka kama yarinya saika mata ciki ikon Allah! Yarona is very fertile” tai murmushin manya.
***

Around 1 nadare suka iso kano dan motarsu ta lalace a hanya, sama da kasa Mom ta kalla this middle of night gwara ta kwana atasha wani bench tasamu ta zauna tabuga tagumi tana tunanin rayuwanta duk wanda yazo zai zauna awajen saiya tashi sabida yanda take wari, tayi shiru kawai tana kallon kafan da tagaji bashine agabanta ba haka gari yawaye still tana zaune, fargaban zuwa gidan nan take, tana zaune ahaka har wajajen 8 tamike tanemi ruwa tasami gefe tai salla sannan tashiga tafiya gabaki daya tai butu butu keke ta tare yace zai kaita drop dubu uku ta kalli kudin hannunta sukenan gareta tabasa tashiga har unguwan gabanta sai faduwa yake gabaki daya sun chanza gidan anyi renovating anguwan ma sunsa titi which she’s sure sune sukasa gate din tayi ga security guda biyu awajen takarasa zata wucesu suka tareta. “Yes who are you?” Yadan koma baya sabida warin datake, ahankali Mom tace “masu gidan nake nema” kai tsaya yace “kidawo Friday rannan ake bada taimako not today” shiru M
Mom tayi tana kallonsa araunane tace “dan girman Allah kagaya musu Alhaji Abubakar nake nema ko Gwaggo! Sun sanni” kallonta yayi from head to toe saiya daga waya yana komawa baya Ya Mustapa na zaune a falo wayansa yayi ringing yakalla ganin security ne yasa yadaga kai tsaye yace “a woman is here she wants to see Gwaggo ko Alhaji! She looks like a begger wat do I do?”
Dan shiruuu Ya Mustapa yayi normally normally bazai fitoba but ambato sunan Gwaggo yasa saiyace “I am coming” mikewa yayi Mamie tace “ina zaka baka cinye abinci ba”? Anatse yace “yanzu zan dawo Mamie wata tazo neman taimako lemme give her something” yayi maganan yana ficewa yataba aljihunsa yanada yan 1k yaciro duka yarike a hannu yataho wajen gate din yasa hannu yabude kofa ahankali yakalli security batare dayama lurada Mom dake daga gefe sanye da dogon hijab ba yace “where is sh….” “Mustapaaa!”

EPISODE 1️⃣4️⃣1️⃣



Mom takira sunansa asanyaye dayasa Ya Mustapa yajuyo yakalli Mom to be honest saida yayi kusan 15secs yana kallon Mom kadın yaganeta cus this is not the Salima he use to know, tundaga kasa zuwa sama yabita da kallo yana maida kudaden hannunsa aljihu sannan yajuya zai koma ciki Mom tace “Mustapa kamin rai! Yafiya nazo rokonka, dan girman Allah kuyafemin dan Allah!” Juyowa yayi yama Mom wani kallo sannan kawai yakalli securities yace “don’t let her in” yawuce yakoma ciki ransa abace bude kofa yayi duk aka bisa da kallo cus yanayin fuskansa ya chanza Baba yace “lafiya Mustapa” murmushi ya kakalo yace “fine Baba” saiya kalli Asmeey dake dinning tanashan kunu tana hira da Ramla smiling looking happy yadan kwana biyu bai ganta ba cus yaje China finalizing production na company su sai jiya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login