Showing 6001 words to 9000 words out of 221707 words

Chapter 3 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

da wando dan Allah Hamad ciwon ya warke, dagakai sai yan uwanka agidan nan kumama duk aiki suke zuwa kai kadai ke wuni so kafinga bari yanashan iska” gyadama Abba kai yayi Abdallah yace “sannu Hamadi” gyadamai kai yayi duk suna tareda shi ahaka bacci yayi awon gaba da shi sabida alluran Abba yace “yatashi yayi isha’i” Mustapha yace “kada kadamu Abba nan da 3 days ya warke” gyadamai kai Abba yayi yace “kuwuce kuma kutafi gida” bargo Ya Mustapa yasa ya rufamai sannan suka kashe wuta suka fice.
💫MOTHER OR CURSE? 💫


✍🏻M SHAKUR


OYA JOIN GROUP DINA INDA NAKE POSTING UWA KO UKUBA IDAN KINA CIKIN 1-8 DONT JOIN 9 PLEASE
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 3️⃣
Around 10 nadare Hameed yashigo dakin wuta ya kunna yana kallon Hammad dake bacci mai nauyin gaske yawuce bayi ya watso ruwa yafito daure da towel yaje yasa boxer kadai yazo zai kwanta ya tsaya yana kallon Hamad, saiya tashi yakai hannu yasake gyaramai bargon dayake lullube dashi sannan ya kashe wuta yahau gadonshi, ya kwanta daidai wayanshi na ringing ya daga yakai kunne murya chan kasa yace “Zeezee” daga tachan bangaren tace “Ya Hameed baka kirani ba why is your voice so down haka kaman you are not happy wat is it”? Dudda akwai duhu juyowa yayi yakalli gadon Hamad ahankali yace “my brother is sick Zee” dasauri tace “subhanallah your twin? Wanda akama operation last week?”Gyadamata kai yayi yace “yes!” Murya chan kasa tace “ayyahhh so sorry Allah yabashi lpy, Ya Hameed kanason twin brother ka sosai” murmushi kadan yayi kaman bazaiyi magana ba yace “I don’t even love him as much as he loves me! Hamadi na sona sosai fa, he’s not much of a talker but actions nashi speaks love, anytime I’m sick baya bacci he stays all night yana kula dani, before nace kaza or nafurta i want kaza Hamad yamin is as if he reads my mind, kokuma my mind na jikinshi ne I don’t know but kaman magic, saisa anytime he’s sick jinake rayuwana ba dadi, sai narasa ina zansa kaina naji dadi, most times he knows we all get worked up idan baida lafiya saisa baya fada mana, he’s always sick ne yau mura, gobe kai gata kaza, he feels bad yana unnecessary damunmu shi ba sikla ba, even today bansan he was sick ba cus bayaso mu damu, and bansan why I didn’t noticed ba cus I’m always the first to know whenever he’s sick, I’m feeling very bad Zee I don’t give dan uwana dsame kind of love and care he gives to me” Zee tace “don’t say that, kanason brother ka sosai saisa ma har kakejin guilt din nan, anyways shi kadaine ban sani ba agidanku, bantaba ganin twins da ba’a san daya ba sai akanku” dariya Hameed yayi for the first time yace “Hamadi baya hoto, he hates pictures, he hates cameras, bayason mutane, Grandama dinmu tace mutum daya kadai Hamadi keso aduniya” Dasauri Zee tace “waye?” Ahankali yace “Mamie! Idan kinga yadanyi few magana ko hira to da Mamie ne, gashi you will never hear meyake cemata kaman munafuki, Gwaggo always call him makiri takadirin yaro” dukansu sukahau dariya yadan tsagaita yace “don’t worry bari yaji sauki zan jawoshi muzo zance gidanku tare” murmushi tayi tace “okay” ahankali yace “bari ki kwanta we will talk tomorrow agaida Mama bye” bye.
**


Bauchi!
“Wai bazaki tashi ba Asmeey?” Wata doguwar matashiya fara dake tsaye gaban wani gado haka mai kyau 6/7 tahau dukan wacce ke nannade cikin bargo da ba’a ganinta tace “kowa yatashi anyi salla an tafi aji banda ke, bazaki tashi ba sai Baba yashigo gida daga masallaci wai Husna” ko motsi batayiba, baccin ta takeyi lafiyayye, bude kofan dakin akayi hakan yasa wacce ke tsaye gaban gadon ta juyo da sauri, wata hamshakiyan mace ce tsaye gaban dakin mai jiki yar gajera haka dan batada tsayi ga farin glasses a kan idanunta tana sanye da dogon hijabi har kasa mai kyau ga charbi a hannunta, tanada jiki, fuskanta babu alamun wasa, kana ganinta kawai kasan no nonsense mutane ne hakan yasa yarinyar dake tsaye gaban gadon cikin whispering tana kallon wacce ke cikin bargon ta side na idanu tace “ai ga Mom nan” awani mahaukacin zabure yarinyar dake nannade cikin bargon tawani yaye bargo ta taso da mugun gudu akuma firgice tana dirkowa daga gadon har tana neman fadi sabida baccin dake idanunta jikinta ba karfi amman ta dafa gado ta tsaya da kyau tana goge idanunta da gefen bakinta da duk miyan bacci, daga ita sai yar rigan bacci daya tsaya mata a knee fari fari, kanta babu dankwlali gashinta dayake a tsefe baki sidik yayi biji biji ya sauko har gadon bayanta, fara ce sosai like asalin fara dan tafi wacce ke tashinta haske ma, ba siririya bace tanada dan kiba unlike dayan da siririya ce sosai saidai tafi wacce ta tashi daga baccin tsayi da matured face alamun kaman ta girmeta, sannan wacce ta tashi na bala’in kama da matar dake kofa kaman tayi kaki ta tofar, har yanayin rashin tsayin saidai yarinyar da dan tsayinta ba laifi but bawani sosai ba dan akafadan wacce ke tashinta daga bacci tsawonta ya tsaya, strictly matan dake kofan babu wasa kan fuskanta cikin wani thick powerful voice tace “okay ita Ramla bata isa ta tasheki ba kinaji ana tashinki kinyi shiru right”? Baki tabude zatai magana babu wasa kan muryan matan tace “idan kince uppan sainazo wajen nan na daura miki mari stupid girl!” Shiru taja bakinta tayi gabanta na faduwa dum dum dum, matan tace “nabaki 3min do whatever you want to do kifito kiwuce aji kona saba miki” dawani irin sauri tajuya tayi bayin dakinsu matan ta kalli dayan budurwan da kanta ke kasa tace “kekuma me kike jira? Oya bacemin daga sight kiwuce kitafi aji kema” dasauri yarinyar tace “toh Mom” hijab nata dake kan gadon ta dauka tasaka da sauri tawuce gaban dressing mirror su tadauki Al Qur’anin ta tazo wajen sai kuma takasa wucewa, babu wani yaro in this house da baya shakkan Mom kawai ajininta abin yake, she’s so scary cus bata da wasa and batason nonsense even a bit, ganin haka yasa Mom tajuya tawuce tabar wajen itakuma Ramla tafito, Babban gidane sosai tashiga sauka kasa ta sauko falo tabude kofa tafita gidansu is a very biggggg house, ga flats daban daban chan tawajen masallacinsu akwai wani katon class tawuce direct tabude kofa tashiga yaran gidan su ne ciki, 6boys ne awajen akwai dan 20yrs sai sauran duka kanninshi ne sai kuma mata yan 8yrs, da 9yrs sai ita datashigo ta zauna tana sauke ijiyan zuciya ganin Malamin su bai shigo ba yar 9yrs din tace “Ya Ramla ina Ya Asma’u?” Yar 8yrs tace “hmmm Ya Asmeey ai bata tashi ba, Allah yasa Malam yamata dukan latti jiya daman ta dakeni” ballamata harara Ramla tayi tace “zan fasa miki baki fa, wayace ki taba mata hoda ba saisa ta dake ki ba” turo baki tayi tajuya ta cigaba da karatunta daidai nan Malaminsu ya shigo wani Ustaz ne da dingilallen wandonshi yasa hula akai ga dorina akan kafadarshi ko kadan baya ragama anyone cikinsu wanda hakan umarnin Baba ne saisa suke tsoronshi ba wasa duk wacce tai latti ko takasa bada hadda akwai duka although hadda Saturdays and Sundays suke bayarwa, baice komiba yawuce gaban aji ya zauna zauna.
Tana shiga bayi ko brush batayiba tafito tasa hijabi tai salla ko azkar batayi ba ta mike tsaye tadauki daddumanta ta ijiye kan gadonsu tadauki Qur’anin ta tazo kofa tafito gabanta na faduwa sosai ta shiga sauka kasa tafito tawuce class ta window ta leka ganin Malam yana aji haba saita kasa shiga idanunta take sukai ja, masallacinsu ta kalla tasan Baba na ciki but dazaran tawuce zata shiga masallacin Malam zai hangota hakan yasa tajuya takoma flat nasu tabude tawuce kitchen nasu tana bude kofa taga wata mata but bata dazu ba wannan looks exactly like Ramla tareda wasu mata da kana ganinsu kasan yan aiki ne binta da kallo matan tayi hakan yasa arude idanunta sunyi raurau tai wajen matar kaman zatai kuka tace “Ammi” wani kallo matan tamata tace “yauma kin sake latti ko Husna” saiga hawaye kaman jira take tace “Ammi dan Allah kisani kowani aiki zanyi I will even cook abincin lunch din su Yusra saikicema Malam kene kika sani aiki yau su Gambo basajin dadi basu tayamu aiki ba kinji Ammi wlh dukana zaiyi” Ammi na kallonta tace “inaji ana tashinki fa kikai shiru Asma’u? Mesa bakiji kullum kece ke latti eh kinsan idan Baban ki yazo yaganki a kitchen din nan ranki harda nawa saiya baci da safen nan dan haka wuce kitafi kibama Malam hakuri kinji” girgizama Ammi kai tayi kawai tasaki kuka zatai magana cikin kakkausan murya akace “Asma’u” juyowa tayi arude ganin Mom ce saida kirjinta yayi mugun faduwa kawai tafashe da kuka sosai taboye bayan Ammi tace “na shiga uku wayyooo Allah Ammi Mommy zata dakeni mari na zatayi Ammi” dan murmushi Ammi tayi tace “Mommy dan Allah kimata hakuri kada ki tabata yanzu zata tafi kinsan Asmeey akwai tsoron duka” Mom zatai magana duk sukaji muryan Baba. “Meke faruwa awajen nan?” Duk juyawa sukayi daidai Baba na karasowa wajen ya tsaya dab da Mom yana kallo kitchen din yana jiyo kukan Asmeey, yan aiki duka suka gaidashi but baima iya amsawa ba yace “meke faruwa? Meya faru Asma’u ke kuka? Mesa bataje makaranta ba”? Cikin kuka Asmeey tace “Baba Mommy” dan kallon Mom yayi dake kallonta rai abace saikuma yakalli Asmeey dake lekowa daga bayan Ammi yace “zonan” ba musu ta taho ahankali tana goge fuskanta da tasan Baba bazai taba dukanta ba baya dukansu, agabasa ta tsaya kanta akasa yace “mena gayamiki kan zuwa aji latti da asuba” ahankali tace “kace nadena?” Baba yace “so danazo na tadaku kika tashi kika kalleni ina wucewa natafi daman bacci kika koma?” Fuskanta tashiga gogewa takasa magana, Baba dake kallonta yace “kinaso ki gamu da fushina ko”? Girgiza kai tayi tace “Baba bazan karaba kayakuri” shiru yayi yana kallonta saikuma yace “zoki wuce kitafi” bakinta na rawa tace “Baba Malam zai dokeni” saikuma ta rushe da kuka Mom tamata wani kallo dayasa tayi kan Baba zata shige jikinshi Baba ya kalli Mom hakan yasa ta dauke kanta tawuce tashiga kitchen din shikuma yace “wuce muje” ba musu tabishi suka fice tana murmushi, har ajin nasu yayi sallama Malam ya amsa yana tasowa Baba yace “basai ka tasoba Malam kaga Asma’u sai kuka take sabida tasan tayi latti amata afuwa adaga mata kafa nayau gobe tayi latti amata hukunci” murmushi Malam yayi yace “shikenan Alhaji ta shigo” Baba yakalli Asmeey dake gefenshi data share fuskanta da sauri tanamai murmushi mai bala’in kyau yace “da idanunta awajen kaman na mutanen da wuce kishiga” murmushi tayi ta shiga tana ballama kannenta harara dake kallonta barinma su Yusra.
Dan saurayin dake 20yrs yana kama da ita sosai yajuyo yakallota yamata gwalo kirne fuska tayi Malam yadawo ya zauna kowa ya natsu suka cigaba da karatu.
7:00 daidai na safe aka tasosu duk suka fito dayake almost dukansu yaran suna zuwa school Asmeey ne kawai da Ramla basa zuwa su sun gama university Ramla NYSC zata yanzu ita kuma Asmeey law school duk suka wuce cikin gidan, zama all the children sukayi anan babban falo su Gambo da Ammi na bama kowa breakfast, Asmeey tawuce sama da sauri dakinsu tawuce taje tai wanka tai brush tafito tai shafe shafen ta sannan ta dauko wani white shirt mai boturi tasaka sannan tadauki black skirt daidai ita tasaka tadauki black veil tai rolling daya mata kyau ta dauki wani LV bag mai kyau ta hada yan abubuwa da wasu books da jotter ciki ta feffesa turare sannan tafito daga dakinsu, gidansu is big flat da akwai 2more flat ciki, flat din dake left and right sai dakin Baban su at the center sai dakinsu na mata agefe na maza ana dayan gefen babansu, right flat din tawuce da saurinta da dan kunne a hannunta tabude kofan ahankali ta shiga ciki.
Gambo ce kadai a falon tana goge goge ansaka turaren wuta dakin na kamshi sosai, ahankali tace “ina kwana Gambo” murmushi tamata tace “Asmeey an shirya” gyadamata kai tayi da saurinta tawuce bedroom na Mom tai knocking ahankali kusan 1min akace “come in” bude kofan tayi ahankali ta shiga ciki, dakin Mom yahadu iya haduwa komi nata is well organized, ga bango guda da duk books ne acikin shelf, Mom ce zaune kan wani couch mai bala’in kyau taci gayu sosai tasaka wani lace mai kyau hadadde, ga glass akan idanunta tana aiki dawani iPad dinta, harta karaso wajen kanta na kan iPad bata dagoba, dukawa tayi agabanta cikin muryanta mai sanyi and very fresh tace “Mom Good morning” dagowa Mom tayi tabita da kallo daga sama har kasa fuskanta ba walwala, wani irin murmushi mai kyau tama mamanta tace “Mom bazan kara makara ba sorry karki fushi” dan hararanta Mom tayi cikin muryan kasaita da iko tace “kinyi breakfast?” Girgiza mata kai tayi tana mikama Mom dan kunnenta tace “Mom samin” karba Mom tayi tanabin dankunnayen da kallo dasauri Asmeey ta tashi tahau kan kujeran ta daura kanta ajikin Mom tana shakan kamshin da mamanta keyi mai dadi tawani sauke ijiyan zuciya kaman irin yaron dayayi shekara baizo jikin mahaifiyarsa ba, tai lamo ajikinta, dan kallonta Mom tayi for few seconds sannan tasamata dan kunnen, cikin kakkausan murya tace “dagani” dasauri Asmeey ta dago daga jikinta Mom tasake kallon yarinyar saikuma takai hannunta ta daga black veil nata tana kallon gaban white shirt nata tace “banace anytime kikasa white shirt haka ki dinga sa singlet ba aciki can’t u see yanda bra naki ke showing” dan komawa baya kadan tayi da mahaifiyar tata gabanta na faduwa hankali kaman mai tsoron magana tace “Mom duka sunyi datti ne but yau duk zan wanke” wani kallo Mom ta mata hakan yasa tasake matsawa daga kusa da ita dasauri, girgiza kai na takaici tayi tace “be very very careful Husna or you will not like me kikai provoking din kinsanni very well stand up open that drawer ki dauki sabon singlet” tashi tayi dasauri ta tawuce wajen drawer tajawo sabon singlet taciro tabude shi daga leda black ne mai kyau sai kawai ta cire rolling na gyalen tabude shirt nata tadan kalli Mom ganin bata kallonta yasa tacire rigan ta ijiye kan gado zata dauki singlet tasaka authoritatively Mom tace “zonan Husna” dasauri Asmeey tajuyo takalli Mom dataga ta tsareta da idanu saikuma tadan kara singlet din gaban kirjinta cikeda kunya ta taho ahankali har gaban Mom, muryanta har rawa yake tace “g…gani Mom”
Mom irin iyayen nan ne masu lura da yaransu sosai, masu sa ido, ga basu tarbiya, yaranta must do abinda takeso ne dukansu haka ta rainesu har yarage saura biyu gabanta yanzu da Asma’u da Munir, wuyanta Mom takai hannu ta taba tace “yaushe eczema yakamaki?” Zaro idanu Asmeey tayi cus ita bama tasani ba tace “ni Mom an ina”? Wuyanta gabaki daya Mom tashiga dubawa zuwa bayanta saikuma ta juyo da ita hannunta tasa, tashi daya ta karbi singlet datake kare kirjinta dashi ta ijiye a gefe, Asmeey tadan sunnar da kanta kasa, ahankali Mom tabi saman kirjinta da kallo tace “stand up” tashi tayi dasauri agaban Mom, Mom tabi cikinta da kallo sannan da masifa tace “eczema ko’ina a jikinki dame kike wanka? Ina soap naki?” Murya chan kasa gabanta na faduwa tace “yakare” Mom aharzuke tace “tun yaushe”? Gaban Asmeey faduwa yake bana wasaba tace “the 3rd day dakika bani” Mom namata wani kallo tace “mesa baki gayamin ba”? Dasauri tace “Mom ai munada sabulu dayawa a bathroom dinmu anyone nagani sainai wanka dashi” shiru Mom tayi saikuma chan cikin kakkausan murya tace “you’re very stupid, wawiyan yarinya kawai mara wayau, shashasha” sauke kanta kasa Asmeey tayi ahankali hannunta yahau rawa, Mom tace “wani irin stupidity zaisa ki kasa gane cewa you’ve always had a sensitive skin? Waya cemiki u can use just anything kika gani kiyi wanka dashi eh? Why do I waste my money ina saimiki separate abubuwan skincare batare da bari kinyi using sabulan da mayukan da Babanku ke kawo muku ba, If you ever made that kind mistake again saina sabamiki shashasha kawai, bacemin daga gani ki wuce ki maida kayanki kizo kiyi briefing dina on case file dana baki last lemme see idan kinyi wannan” gyadama Mom kai tayi asanyaye duk tayi wani iri tawuce ahankali tasaka singlet din sannan tasaka shirt dinta, bata maida veil dinba tazo wajen tabude jakanta taciro file da Mom tabata jiya tabude tadago kanta takalli Mom kirjinta na dukan uku uku, Mom tace “bani distinction na case din but I prefer persuasive brief, inason statements of facts, then give me substantive issues and procedural issues” gyadama Mom kai tayi hannunta nadan rawa tasake bude jakanta tadauko wani book nata datai jotting komi, tabude zata karanta, Mom tamata wani kallon uku saura kwata tace “kikaje law school haka zaki dingayi? Reading from book? how many days nabaki case din nan nace kiyi reviewing?” Murya chan kasa irin na mara gaskiya tace “7days” Mom tahada fuska tana karkada kafa tace “idan kikamin shirme awajen nan ranki zaiyi masifan baci Asma’u, drop that book I’m listening” gyadama Mom kai tayi saita ijiye book din gently and calmly tafara briefing Mom voice nata narawa, tun tana yi Mom na aikinta harta juyo ta natsu tana kallonta she really tried, saida takai procedural issues ne takakare Mom tamata wani kallo hakan yasa hawaye yafado daga idanunta tace “sorry Mom” Mom tace “okay wat is procedural issues?” Anatse tace “ Procedural issues shine irin wat is the appealing party claiming the lower court did wrong example kaman ruling on evidence, jury instructions, granting of summary judgment, etc” Mom ta gyadakai cikeda gamsuwa tace “okay if you know this then a case file dana baki menene Procedural issues na wajen” shiru tasakeyi cus bata karanta yakai wajen ba, Mom na karkada kafafu tace

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login