Showing 81001 words to 84000 words out of 221707 words

Chapter 28 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

yawuce bayi dasauri ta tashi, ijiye wayan tayi akan gado sai kawai tabude kofa tafito tasauka kasa saita wuce kitchen, Mamie na ciki tace "Asmeey zakici jellof rice ko?" Ahankali tace "indomie Marie" dan dariya Mamie tayi tace "bari na kira akawo indomie cus bama cefanensa agidan nan babu mai ci, meya sameki kikai kuka"? Share idanunta tayi da sauri tace "abu ne ya shiga mini idanu" saikuma dasauri tace "Mamie mezanyi?" Mamie tace "zauna ga kujera babu abinda zakiyi ko Uwani"? Yar aikinsu tace "eh angama komi Amarya" akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa tana wajen Ya Hamadi yazo kamshinsa kawai taji ta sauke kanta kasa murya chan kasa yana daga gefe yace "Mamie" dasauri-Mamie tafito daga kitchen din tagansa tsaye a gefe yayi kyau yana sanye da manyan kaya ash color yamai kyau tace "zaka fita"? Gyadamata kai yayi yace "zanje masallaci daganan zan fita" Mamie tace "toh adawo lpy banda gudu" harya juya Mamie tace "ka gayama matarka zata fita"? Tsayawa yayi chak sai bai wuce ba saikuma bai juyoba ya bama Mamie amsaba, komawa kitchen din Mamie tayi takalli Asmeey da kanta ke kasa tace "tashi je mijinki na magana" gyadama Mamie kai tayi tamike tsaye ahankali tafito, tsaye tagansa inda Mamie ta barshi ya tsareta da ido yayi mata wani kyau a ido sosai sai kawai gabanta yafadi da sauri ta sauke kanta kasa tace "gani" shiru yadanyi kafin ahankali yanda ko na kitchen bai isa yajiyosu ba yace "I am going out" da sauri Asmeey ta kalleshi saitaji wani iri azuciyanta, saitaji kawai bataso yafita, sai kawai taji she's not happy, sai idanunta suka tsatso da kwalla kaman irin shi kadai tasani agidan nan kuma zai fita yabarta, lumshe idanu Hamadi yayi yabude su kadan softly yace "I will be back soon!" Gyadamai kai tayi wlh she's not just happy zai fita da gasken gaske saitaji duk matsalolinta sun dawo mata fresh a zuciya sai kawai hawaye yazubo mata dasauri tasa bayan hannu ta goge, ahankali Hamad ya matso dab da ita kaman mai whispering yace "why are you crying now"?
Shiru tayi sai goge kwallan take batare data kalleshi ba batare datai magana ba, murya chan kasa yace
"bakiso na fita?" Gyadamai kai tayi ahankali, awani irin hankali yakai hannusa yakama hannunta dasauri ta kalleshi wani kalan shock taji sai lips nata yahau rawa sosai ahankali tace "Allah bada sa'a, saika dawo" gyadamata kai yayi yace "stay inside, akwai men a compound working" gyadamai kai yayi yadan tsaya yana sake kallonta batare daya saki hannunta ba.har lokacin saikuma ahankali yace "Husnahh!" Ahankali ta kalleshi kirjinta na bugawa, murya chan kasa yace
"byee" daidai lokacin an bude kofan falo dawani irin sauri yasaki hannunta yadan koma baya itama haka but dudda haka saida Hameed yagani, Hamad yajuya dasauri yahade fuska batare daya kalli Hameed ba yawuce sa yabude kofa yafice Hameed yabisa da kallo saikuma ya kalli Asmeey data juya da sauri tana share fuskanta tace "good morning ya Hameed" ta shige kitchen, Hameed yazauna yace "kai! Bura'uba!
Yau naga munafukai, where they lovers before?
Hannunta dan Allah naga Hamadi yarike ko idanuna ne? Kai! Kai! Good morning fa tace da ranan Allahn nan" Hameed yahau exclaiming yana murmushi.
Ganinta yasa Mamie tace "tashi kije kiyi salla" gyadama Mamie kai tayi ta mike tawuce tafito Hameed shikuma ya ijiye laptop dinshi nan falo shima yafita salla takoma sama bayinsu tabude ganin pant dinta da bra dinta a wanke a rope dataga Ya Hamad dashi dazu a falo yada da sauri takalli lundry basket dake hanyan bayin but babu any clothes ciki wani kalan kunya taji yakamata at the same time kawai saitaji wani dadi kuma, Ya Hamad yawani kara burgeta yashiga ranta sosai he washed her clothes but she is still shy idan bra dinta na wari fa? Ko pant shikenan yaji? Wih duk sai taji wani nauyi yakamata da kunya kaman tacire pant din da bra daga igiyan taje taboye but saitaji takasa besides zaiyi wari alwala tayi tafito duk kunya yakamata ta shimfida dadduma tayi salla abinta.
💫UWA KO UKUBA?💫



✍🏻M SHAKUR



EPISODE 3️⃣0️⃣

Hameed dazu yasa kawai sai yanzu tafito sanye da hijabi Mamie tasa mata abinci kadan taci Ya Musty yashigo gidan sanye da lab coat yace "Asmeey" akunyace tace "ina yini Yaya" waje yasamu yana zama yace "ya hannun lemme take a look" hannun ya karba ya dudduba yace "kina healing fast gaskiya kinashan maganinki"? Ahankali tace "yau ban sha ba ban gansa ba" Yaya yace "maybe a manta dashi a
Bauchi ina mijinki"? Akunyace ta sunnar dakai tace
"bayanan" sai ta juya zata koma sama Ya Mustapa yace "zauna kici abincin ki Mamie hala taje salla ko?"
Gyadamai kai tayi yace "Gwaggo kuma ya tafi gidan mutane ko" gyadamai kai tayi tacd "this old woman
I know by now those people are regretting abinda yasa suka bama yarsu sunan Gwaggo" "Nakawo maka abinci Yaya"? Girgiza mata kai yayi yana bata ledan hannunsa da surutu yasa ya manta yace "this is for u" bude ledan tayi taga ice cream ne na cold stone murmushi tayi tace "thank you Yaya" Ya Mustapa yace "nazo naga Mamie ne yanzu zan koma hospital zanyi har night yau saisa nazo na ganta kafin tace bata ganni yau gabaki daya ba" daidai nan Mamie tazo shima Hameed yashigo rikeda wara a hannu yamikama Asmeey yace "take Zee loves it maybe kema haka shine nasayo miki" dan murmushi tayi akunyace tace "thank you Yaya" bakaramin dadin hakan Mamie taji ba yanda suke sonta, Asmeey ta tashi saita shiga kitchen freezer su tabude tasaka ice cream din waran kuma tadauki wani small kula tasa aciki Mamie tace "me kikeyi a kitchen" fitowa tayi Mamie tace "ina abun naki bazakici ba?" Da zuciya daya tace "sai Ya Hamadi yadawo na nunamai tukunna" ba Mamie kadai ba har Ya Mustapa da Hameed saida suka kalleta wih sai sukaji ta burgesu sosai, Ya Mustapa was seriously impress but duk sai basu nuna komi ba kartaji kunya, Mamie tace "a fridge kikasa ice cream din"? Gyadamai Mamie kai tayi tace "eh, warana kuma a kula" dan murmushi Mamie tayi tace "yayi kyau" suka cigaba da hira, Mamie last last saida tasa Ya Mustapa cin abinci da Hameed sai kallonsu Asmeey take Mamie na son yaranta sosai sosai, hira suke Ya Mustapa na bata labari kafin around 3 yace "bari naje naga masu aikin nan na haka foundation sunce yau zasusa, Hameed gobe sai office ko?" Gyadamai kai yayi yace "yes Yaya hutu ya kare" Ya Mustapa yace "okay sai anjiman ku" yatafi shikuma Ya Hameed yakira Zee wayan yabama Asmeey yace "ga Zee" ahankali ta amsa Zee tace
"Asmeey" dan zaro idanu Asmeey tayi akunyace tace "na'am ina wuni" Mamie ta harari Hameed dake wani murmushi tawuce kitchen abinta, Zee tace
"congratulations on your wedding Allah sanya alheri" sunnar dakai Asmeey tayi takasa amsawa, Zee tace
"in sha Allah zamu hadu soon nace ma Ya Hameed yabani number ki" ahankali Asmeey tace "nima zan karbi number ki" Zee tace "shikenan sai munyi waya bye" mikama Hameed wayan Asmeey tayi yatashi daga dinning din yawuce sama Mamie tazo suka zauna Mamie na bata labari daban daban.
Har akai la asar taje tayi tasake dawowa falon suna hira da Mamie karan bude gate taji dasauri takalli window Mamie ta tsare yarinyar da idanu Asmeey na son Hamad fa, takosa yadawo, tashi Mamie tayi tace
"bari na dauko wayana na barsa a kitchen" Mamie na wucewa kitchen dasauri Asmeey ta tashi tayi wajen window ta leka, Ya Hamad ta hango kan machine yana parking ga kwalin indomie ta gabansa dawani leda, wani cute smile tasaki tana kallon yanda yasa black shade a idanunshi, tuntuni Mamie ke kallonta but kawai saitadanyi motsi dayasa takoma kujera da sauri ta zauna kaman bata taba tashi ba Mamie kuma tafito rike da wayan tana dannawa daidai an taba door din da sallama Hamad yashigo rike da kwalin indomie dawata yar leda a hannunsa ganin Mamie afalo sai yaji wani irin kunya but ya daure da kyar yakarasa falon wajen Mamie ahankali yace "Mamie" sai ya ijiye ledan da kwalin kusada ita yace "take" zai wuce da sauri Mamie tace "kabama matarka mana Hamadi gidan nan babu mai cin indomie sai ita ai ko Asmeey" akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa shikuma Hamad yayi sama yaki juyowa Mamie tace "yau naga munafukan yara" takalli Asmeey tace "dau abubuwan ki kiduba" akunyace Asmeey tadauki ledan ta duba kwalin conflex ne, sai roban eclairs sweet, sai short bread biscuits guda 5, da chocolate guda biyu, Mamie tace "I said it naki ne yake wani bani" akunyace Asmeey ta sauke kanta kasa Hameed ya sauko yana zuwa wajen yace
"waye mai abun dadi haka"? Yakai hannu zai dauki chocholate Mamie ta bugi hannunsa tace "mijinta ya sayo mata abu kadauka" dasauri yace "Hamadi yadawo ne Mamie?" Eh Mamie tafadi tace "tayata kai kwalin indomie nan store Hameed" dauka yayi yana mamakin Hamadi aranshi yawuce kitchen, Mamie takalleta tace "kekuma kwashe abubuwan ki kitafi daki mijinki yadawo" gyadama Mamie kai tayi ta. maida komi jakan, Hameed yafito daga kitchen yafita itakuma tauce kitchen ice cream dinta ta dauko da kulan wata tarike duka tawuce sama Mamie na kallonta ahankali tace "Alhamdulillah Alhamdulilah Ya Allah" ahankali tabude kofans dago kansa Hamadi yayi yakalleta maida kofan tayi tarufe ya kalleta da abubuwan data kwaso tana support da karyayyen hannunta ahankali kaman mai tsoro tadanzo kusa dashi murya kan kasa tace "thank you Ya Hamadi" dauke Kai yayi daga kallonta sabida cute smile din datayi komawa gado tayi ta ijiye ledan ta sai tadawo wajen yasake juyowa ya kalleta ice cream din ta jiye agabansa da kulan waran tabude tanuna waran murya kasa kasa tace "Ya Hameed yabani wara dazu, Ya Doctor ya kawomin Ice cream" kallon komi yayi saikuma ya kalleta idanunta na kasa har lokacin ahankali yace "mesa bakici ba"? Ahankali tace "saina nuna maka" shiruu yayi yana kallonta maganan really melt his heart yace "to kije kici" gyadamai kai tayi tace "tom" saita juya saikuma ta tsaya batare data juyoba kaman maijin nauyin magana tace "zakasha ice cream?"Ahankali yace "I don't take ice cream" murya kasa kasa tace "wara fa?" "I don't like it" gyadamai kai tayi tawuce ta zauna akan gado tabude waran da ice cream dakuma chocolate tashiga kakkarya chocolates din tasa a ice cream din Hamad yadan juyo ya kalleta she was eating it and smiling tana kara kallon ledan chocolate din daya mata dadi, she looks so happy da he got carried away looking at her, bata iya cinye waran ba but ice cream din ta shanye ta tashi taja drawer gefen gadon tazuba komi awajen ta ijiye conflex tadauki ledan da roban ice cream zatai kofa yace "Husnah" dasauri tajuyo zauna" ahankali ta ijiye komi saitaje ta zauna saikuma tayi shiru saita kwanta kawai tanata kallonshi he's always working desktop computer kome yakeyi oho, tashi yayi dasauri tadauke idanunta daga kallonsa daukan abubuwan yayi yafita dasu Hameed yagani afalo yahade fuska Hameed yace "indomie and chocolate buyer" kitchen yawuce baicemai komi ba yana fitowa yaga Hameed tsaye yarike waist, Hameed yace "na shigo naga kanata murzama yar mutane hannu Hamad" juyawa Hamad yayi yakoma kitchen dayake Mamie kadaine yace "Mamieee Hameed" Juyowa Marie tayi taga Hameed dake jiran Hamad gaban kitchen tace "wlh Hameed zankira Abban ku nakai karanka ha'a" dariya Hameed yayi yace
"shikenan nayi shiru Mamie" Mamie tace "tafi abinka wucewa Hamad yayi Hameed kaman zaiyi kuka yace "Mamie dan Allah nima kumin aure wih kaman inta ihu nakeji, yanzu danaga yanda Hamadi keji da matarsa kaman inta kuka, i am missing Mamieeeeee, aure Rahama ne just one day but my brother is glowingggg!" Mamie ta girgiza kai tace "Allah ya shirya kai Hameed!"
💫UWA KO UKUBA?💫



✍🏻M SHAKUR



EPISODE 3️⃣1️⃣

Kayansu yaso yaje ya dauka but Hameed dake falo yasa bai iya zuwa ba yakoma sama dakinsu yabude yashiga ahankali da sallama Asmeey na zaune kan gado takallesa saikuma ta dauke kanta dasauri tana murmushi without reason Hamad yaje yazauna, kaman bazatai magana ba sai kuma ahankali tace
"bakaci abinci ba Yaya" ahankali yana aiki yace "I will eat later" gyadamai kai tayi sai kuma ta kwanta a gadon tana kallonsa bacci na neman fizganta tana lumlumshe idanu, kaman daga sama yace "don't sleep ice cream and wara Babe" bude idanu tayi suka hada ido ganin yajuyo gabaki daya yana kallonta kaman wata laptop dinshi sai kawai taji kunya yakamata dasauri ta rufe fuskanta da hannayenta biyu jin sunan daya kirata dashi wai Ice cream and wara Babe, Babe fa Ya Hamadi yace.
Tashi yayi daga kujeran yabude kofa yafice, sauka kasa yayi daidai Gwaggo na shigowa gidan yawani balla mata harara baitaba ganin tsohuwa mai shegen yawo irin Gwaggo ba wuni take gidan mutane sabida an mata takwara, tana tahowa tace "bansan kanayi bai naga kwayan idanunka akasa makiri, ni zakasa Asmeey taki bina? Toh wih muzuba ni da ku agidan nan za'aga wazaici wannan fadan" wucewa yayi backyard kafin tazo wajen ma, kayansu ya kwaso yasa na Asmeey a tsakiyan nasa yanda babu wanda zaimasan da nata yadawo yashigo flat din Gwaggo yagani da Mamie tana ganin Hamad tace "cimini mutumci yayi banda yahana Asama bina, nadawo bakiga kallon banzan dayakemin ba" wucesu yayi abinsa Mamie tace "bari Baban su ya shigo Gwaggo saiki gayamai" dakinsu yabude yashiga ahankali * Asmeey na kwance but idanunta biyu daga fitansa taji she's bored, wajen gadon yazo yazuba kayan dasauri ta tashi ganin nata zatakai hannunta yamata wani kallo dayasa ahankali ta maida hannunta kayan yashiga dauka yana folding zai goge gobe idan yasami time kayanta ya dauka yashiga folding
Asmeey tadan saci kallonsa saikuma tamaida kanta kasa zuciyanta duk yayi melting, kwashe komi yayi zuwa wardrobe nasu Asmeey tasake binshi da kallo bangarensa taga yabude ya ijiye komi a side daya kawai zuciyanta yabata gogesu zaiyi yajuyo suka hada ido dasauri ta maida kanta kasa murya chan kasa tace "thank you Yaya" juyawa yayi zaiyi kofa yace "I am going to the mosque sai after ishai zan dawo" ahankali tadago kanta ta kalleshi, haryasa hannu a handle din saikuma gently yace "we have karatu a mosque" gyadamai kai tayi yabude kofan yafice itakuma tai shiru tana zaune awajen taji Mamie na kiranta.
"Asmeey" dasauri tace "na'am" saita taso tafito
Mamie tagani anan falon sama rike da kaskon wuta tasa turare aciki Asmeey tayi wajenta Mamie tace
"kullum ko bana nan safe da yamma ki dinga sa turare a daki saiki kara tsaftace dakin sannan kiyi wanka kinji" gyadama Mamie kai tayi ta karba tajuya Mamie tace "sa kifito ki amsa abincinku ban kara nemanki awaje kuma sai gobe" ahankali tawuce daki ijiye turaren tayi waje daya tafito Mamie rikeda kula mai kyau da tray da plates ke ciki takalleta tace "zama ki iya daukan abubuwan nan" ahankali Asmeey tace "Mamie ki shigo" murmushi Mamie tayi tace "nida shigowa dakinku saikin haihu" akunyace
Asmeey ta sauke kanta kasa Mamie tayi dariya ta ijiye mata komi akasa awajen tace "dinga dauka one bye one kina kaimu ku ciki" Mamie tawuce tasauka kasa Asmeey tashiga daukan komi one one harda ruwansu takai daki tai arranging bangare daya sannan tawuce bayi bayan tacire kayan jikinta zatasa a basket saitaji tana kunyan yamata wanki kuma but ina zatasa kayan dattin? Ahankali tacire tai folding ta ijiye da pant dinta saitaji ta kasa kawai ta dauka tawuce wardrobe tabude side nata ta ijiye kayan bangare daya daban sannan tafada bayi brush tafara yi tayi wanka da shower gel datai amfani dashi da safe na dove mai kamshi tadaura towel tafito daidai wayansa na vibrating dake kan desk. Wucewa tayi wajen ta tsaya ganin number ne is a miss call sai taga watsapp message ya shigo.
"Dan kanada mata is not restriction, I love you wallahi" shiru tayi saitakai wayan ahankali zata ijiye mistakenly ta danna watsapp yabude yakaita direct chat na yarinyar nan all messages data mishi na rannan suna nan almost 50 agabaki daya chat din magana daya Ya Hamad yayi "I'm married, I wish you the best!" Tundaga nan bai kara reply ba amman haushin da Asmeey taji yakamata sai taji kaman zata kama da wuta wayan ta dauka dudda kirjinta na bugawa samin kanta tayi da blocking number on watsapp tai deleting chat din sannan tadawo calls tai blocking number sannan tai deleting tana hararan wayan sannan ta mai wayan ta ijiye tajuya tawuce wardrobe mai ta shafa a gurguje ta fesa bodyspray da turare kayan bacci ta dauko vest da short farare masu kyau vest din v neck garesa da siririn hannu sai short din iya cinya mai kyau is not sexy but it looks damn sexy ajikinta nata wani damuba dan tasan hijab zata saka tai bacci tasa hijabi tazo tai salla tasake dago kai ta kali wayan nasa ta harari wayan ranta sai baci yake saikuma chan Mom tafado mata arai mikewa tsaye tayi ahankali tawuce ta dauki wayanta dake kan table din tadawo ta zauna tana bude wayan gabanta na faduwa contact nata ta shiga but saitaga babu number Mom just na yan gidansu Baba ne ya goge? Tafadi ahankali, tanada number Mom aka saita shiga saka number zatai dailing number saita kasa sai hannunta yahau rawa gabanta na faduwa sosai ijiye wayan tayi tai shiruuu tuna Mom har yasa numfashinta yasoma destabilizing ahaka har aka kira Isha'i ta tashi tayi tai shafa'i da wuturi tana addua hannun nan ya warke tagaji yana hanata yin so many things, tashi tayi tai folding dadduman ta maida wayan ta ijiye kan table sannan ta zauna bakin gado tana jin hayaniya a falo. Shigowa gidan Hamad yayi around 9 duka yayyinsa na falon banda Ya Mustapa duk kallonsa sukayi sunnar da kansa kasa yayi yazo yasami waje kusada Hameed yazauna yace "Abba barka da zuwa" Abba yace "yauwa Hamadi ya iyalin naka kuma?
Ya hannunta?" Murmushi yayinsa sukayi sai wani kallonsa suke sauke kansa kasa yayi yace "fine" Abba yakalli su Ya Abdullahi da Faisal dake zuba uban murmushi suna kallon Hamad yace "gobe Aysha zatazo tareda mijinta sun kirani" gyadamai kai sukayi Mamie tace "nima

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login