Showing 150001 words to 153000 words out of 221707 words

Chapter 51 - UWA KO UBA COMLT

Start ads
Middle Ads

rashin son warin abinci, Mamie ta shigo dakin da magrib ta tadata tace “jeki salla bari nakawo miki abinci” tashi tayi ahankali duk sai taji tanajin kunyan Mamie tawuce bayi tai salla taci abinci bada wani yawa ba tana zaune awajen akai knocking.

Mikewa tayi taje kofa Ya Hameed ne kallo daya yamata yace “ya jikin akwai abinda ke damunki?” Girgizamai kai tayi tace “babu” ice cream dinta yanata yace “gashi” murmushi tayi tace “thank you” ywuace ta maida kofan tarufe takoma tazauna tadauki wayanta tana dubawa shiru tana calculating yanzu karfe nawa wajensu tunda Nigeria nagaba dasu da awanni shida and this is 7:30 probably wajensu karfe daya ko sha biyu na rana ne yana wajen aiki, ahankali ta ijiye wayan tashiga shan ice cream din tass ta shanye tawuce tayo alwala tai sallan isha’i sai kawai ta tashi tazauna kan desk dinshi ta kunna MacBook nata tacigaba da rubuta wani write up datake rubutawa datamai suna THE JOURNEY…..
EPISODE 7️⃣8️⃣



Wajejen 11 tafara hamma takoma gado ta kwanta ahankali ta rungume pillow tai shiru saiga hawaye ya gangaro daga idanunta takai bayan hannu ta share, is not like she’s complaining she’s happy here Mamie da Abba da Gwaggo dasu Ya Faisal suna kula da ita wlh sosai but deep down she’s lonely, fita waje ma fa wani Rahama ne, bata zuwa ko’ina ko saloon baya bari taje da kanta saidai yasa akaita, bata fita compound sabida aiki and shi baya kiranta, she miss him, she misses him alot daurewa kawai take nothing is funny. Takai kusan 12 nadare kuka take kafin bacci ya dauketa.

Wuraren 5 ta tashi da tashin zuciya sosai da sauri tai bayi amai tafara yi ba kakkautawa tadaure tayi brush tayo alwala tafito Mamie tashigo takalleta yanda ta kwanta kan dadduma awahale tace “meya sameki”? Tasowa zaune tayi ahankali takalli Mamie abu yamata yawa kawai saita fashe dawani irin kuka bana wasaba, cikeda damuwa Mamie tace “menene Asmeey”? Rasa yanda zatayi Asmeey tayi kai kirjinta zafi yake mata sai kawai tarike hannun Mamie gam tana kuka ba magana, Mamie tai shiru tana kallonta kafin ahankali tace “Hamad yakiraki yau?” Tana kuka ta girgiza mata kai, Mamie tace “jiya fa?” Sake girgiza mata kai Asmeey tayi, Mamie tace “shekaran jiya fa?” Sake girgiza mata kai Asmeey tayi, Mamie don’t even need to ask further from the way she’s crying mijinta baya kiranta yanda yakamata sai Mamie kawai ta rungumeta tana shafa bayanta tace “ya isa komi zai daidaita kiyakuri, rayuwa baka tare da mijinka waje daya ba dadi, Alhamdulillah an fara miki papers naki yana dawowa zaku tafi tare sannu kinji” gyadamata kai tayi Mamie tace dagota tareda sharemata fuska tace “kidena sa damuwa aranki haka Asma’u is not good for you and for your baby kinajina” sauke kanta kasa Asmeey tayi akunyace, Mamie tace “bari na kawo miki shayi” ahankali tace “anjima zanci Mamie amai zanyi yanzu” dasauri Mamie tace “kinyi amai ne?” Gyadamata kai tayi tace “eh shiya tasheni” gyadamata kai Mamie tayi tace “kinyi salla?” Gyadama Mamie kai tayi Mamie tai shiruuu tana kallonta sai kawai yakamata tace “muje gado” gado suka wuce Mamie ta kwantar da ita ta daura kanta a cinyanta tana shafa mata kai da hannu daya Asmeey ta kankame hannun Mamie guda daya tana sauke ijiyan zuciya feeling calm and happy sai kawai Mom tafado mata arai, lumshe idanu dasauri tayi tajason mahaifiyarta she wish ko hannun Mom zata iya rikewa haka amman bakomi she promise she will love kome zata haifa genuinely saida bacci ya kwasheta Mamie ta gyara ta ta lullubeta tai shiruuu tareda jan bargo tarufe ta tafice takoma dakinta su Abba basu dawo daga mosque ba dakinta ta shiga tai dialing number Hamad but baya zuwa sai kawai ta kira Doctor dake China katse wayan yayi shi yakirata back yace “Mamie na ina kwana ya kuke ya Asmeey dajiki” dan ijiyan zuciya ta sauke tace “fine Alhamdulillah ya wajen ya kk” ahankali yace “fine menene Mamie?”Anatse Mamie tace “Dr damuwa nake da Asmeey, yarinyar sai ramewa take wlh, rama sosai fa, babu abinda yarage sai haske bauuu ko Gwaggo saida tace dibanki ake kullum ne cus raman yay yawa kuma damuwa ce zalla aranta sosai” anatse Ya Mustapa yace “meke damunta Mamie”? Dan shiru Mamie tayi kafin ahankali tace “from wat i observe they’re having communication issues!” Mamie tai shiruuu hakama Ya Mustapa, Mamie tace “Doctor ni mace ce I know how we are, duk yanda mukakai ga son Asmeey da nuna mata kulawa can never equal to kulawa da soyayyyan mijinta, banda haka I think Asmeey loves Hamad way tooo much, maybe sama da yanda shi Hamad dinma ke sonta” anatse Ya Mustapa yace “Mamie don’t say that wallahi cus Hamad na son Asma’u beyond yanda duk muke tunani, and this communication issue daman dole saisun fuskanci hakan cus Mamie Hamad baya magana, muna gida daya da Hamad Mamie have u ever seen that boy make call? Yakira wani ko akira sa ko muji yana waya? Saidai mu, muma once in a while mu din ma bata wuce few minutes call” anatse Mamie tace “amman yayi aure Mustapa the same way yacire kunya yayi abinda yakamata ga yarinya nada juna biyu yanzu haka zaiyi abinda yakamata yadinga waya da ita kafin abu ya sameta cike gareta kasan haka sama dani kune likitoci” Ya Mustapa yace “hakane Mamie”yadanyi shiru chan yace “Mamie bawai ina taking side na dan uwana ba but duk wanda ya auri Hamadi should get ready na fighting da dabi’unsa, for once Mamie karkima Asmeey kallon yarinya ita mace ce, mata have plenty ways na chanza maza, tadena zama wani dum dum Mamie u know tadinga kiransa mana ita, tadamesa, tamasa hira, it’s a gradual process it shouldn’t always be Hamadi that is putting on efforts itama ta koyi abubuwa cus both of them sai ahankali, Asmeey lacks exposure gaskiya, akwai wani class danaga Asiya na ciki na wata wai M Shakur Intimacy class zansa Asiya tabiya mata asaka Asmeey, tadan waye cus this shiru shiru can’t work for them before shima yaje yahadu da wata achan this our gender bamu da tabbas especially yanzu da Hamadi yazama hot cake” Mamie tace “nidai kama kaninka magana, zan kira Asiyan asata a class din, Asmeey hakkinsa ce dole yakirata kowani rana yaji yatake, da munce sai yadawo agayaa masa zancen juna biyun amman gaskiya na fasa ka gayamasa koni zan gayamasa dudda inajin nauyi, but tell him sabida he should take his wife seriously! Haba yarinya na nan yasan bata da kowa fa”.
EPISODE 7️⃣9️⃣






Mamie tace “ yan uwanta duk an dauka tana chan dashi babu mai kiranta batada wata kawa, gata ba yar kano ba, ba inda tasani, yarinya ba inda take zuwa ya za’ayi bazata damu ba, Fisabillillahi fa Doctor, the only abinda takeda shi is Hamadi, gaskiya he needs to do better inba hakaba raina zai baci” Ya Mustapa yayi dan murmushi jin Mamie na fada sosai yace “Mamie kiyakuri I will talk to him” ahankali Mamie tace “kaikuma yaushe zaka dawo?” Murmushi yayi yace “kewana kike ne Mamie na” dan shiru tayi idanunta na tattaro hawaye ahankali tace “ina kewanka sosai Mustapa baka ba Hamadi, sai marasa jin nan kuka barmini Oga Hameed da Faisal, dama dama ma Abdullahi” dan dariya yayi yace “awwwn nima ina missing Mamie na sosai, this week zan dawo kinji so don’t cry again, clean those tears” hannu tasa ta goge fuskanta tass tasauke ijiyan zuciya Ya Mustapa yacigaba da hira da ita har tadan warware kafin suyi sallama yana murmushi Mamie na son dukansu Matar akwai big heart

Haka rannan all through Asmeey ta wuni ko abincin kirki bataci rannan ba sabida ciwo bawai zazzabi takeba kawai batajin dadin jikinta zuciyanta kawai tashi yake kome takai baki saita amayar wuraren 10 daga Abba har Mamie sukabar dakin bayan sun dubata sunyi kusan awa daya tareda ita, Suna barın dakin saitaji kaman duk wani ni’ima na dakin sun tafi dashi duniyan yamata zafi wayanta ta dauka ahankali jikinta yayi wani sanyi tai dialing number Hamad yashiga wayan unlike other day yanata nuna mata ringing amman harya gama ringing bai dauka ba sai kawai zuciya taji yakawo mata wuya she can’t hold it any longer kawai ta shiga typing message.
Zaka iya kirga yau kwana na nawa baka kirani ba? Talking to me is a waste of time ko? I’m no longer in your agenda, you have a busy schedule which your wife don’t happens to be among Mr Hamad! Shikenan dagayau bazan kara kiranka ba bazan kara daukan wayanka ba kuma Allah ma yaciremin tunaninka nima nahutama rayuwana dan banga amfanin tunanin wanda shi baya tunani na ba he can go days weeks without talking to me idanma wata kagani kanaso achan kuyi aurenku nina hakura.
Asmeey ta tura message din tana vibrating sosai zuciyanta namata zafi saitaji dakin ma is hot for her all she wants is inda za’a mata surutu sai kawai ta taso ta dauki hijab ta sanya tareda bude kofan ta ahankali tafito tasauko kasa dakin Gwaggo tawuce tabude kofa ahankali Gwaggo na kampatsa uban hamma tana magagin bacci taga mutu dasauri tace “wayyoo” akufule Asmeey tace “nice kekuma” tashi Gwaggo tayi tana chanza wutan dakin zuwa mai haske Asmeey tawuce tazauna bakin gado Gwaggo tace “lafiya? Ubanme kikazo yimini a daki” kallon Gwaggo tayi cikeda masifa tace “kice nafita nafita mana” ganin masifa Asmeey keji yasa Gwaggo ta taso tareda rike baki tace “ke diyar yar boko waya gabaki gayamin gaskiya” banza tama Gwaggo tahau gadon tashige ciki tai kwanciyanta, murmushi Gwaggo tayi saita taso takama hannunta tanamata tausa tace “kece kibini muje unguwa baki zuwa kullum kina gidan nan ai sai cuta ta kasheki bakiga ko ciwon kai banyi ba, ina zan zauna gida babu kananun yara sai randa marasa mutuncin nan suka ga daman kawo mana Areef zasu kawo shima Abdallah haka gashi sai gayu suke sun tsufa basuson su hayayyafa, bari kiji Asmaa kina haiho wannan kafin shekara ta zagayo ki haiho na biyu ba’a bata lokacin yanzu kiyi kigama saikiga kin tsufa da kyanki bakiga Mamie ba yanzu kaman ba ita ta haifi gardawan nan ba” Gwaggo tace “yanzu dai gobe zaki bini muje makota daman za’ayi bikin diyar Hajiyayye sunanta Firdausi kinga yarinyar akwai rashin kunya da tsiwa kaman ke ki shirya muje gobe kinji zakije?” Gyadamata kai Asmeey tayi tace “eh zanje Gwaggo” Gwaggo tawani kwashe da dariya tace “ko kefa inada fura nabaki kisha” tasowa zaune Asmeey tayi tace “bazai sani amai ba? Inata amai yau Gwaggo” Gwaggo tace “gwada sha mugani” yar fridge nata na dakin tabude tacirowa Asmeey guran aiko Asmeey tasha sosai yayi sanyi tabalain jin dadinsa tanasha ta lapke sai bacci Gwaggo ta gyara mata kwanciya tana rufa mata bargo tace “ke bakisan nafi kowa dadin zama ba da kin lapke chan baki zuwa wajena yanzu zaki gane nine nafi kowa dadin zama Allah dai ya saukeki lpy, Allah yamuku albarka keda Hamadi”

Rabon da Asmeey datayi baccin daya mata dadi harta manta sai yau ko harda huran data sha ne haka ta lapke Gwaggo tai juyin duniya Asmeey ta tashi da asuba tai salla takasa wuraren 5:30 arude Mamie tazo dakin Gwaggo ijiyan zuciya ta sauke ganin Asmeey na bacci a dakin Gwaggo ta sallame salla tace “kaman yarnan irin laulayinki ta dauko mai fitina jiya datazo ta tasani agaba harna fara bacci fa saida natashi nabata hura” dan murmushi Gwaggo tayi tace “tafi abinki zan tada ita anjima kadan tai salla, masu ciki nada uzuri dan Allah” juyawa Mamie tayi tafitoo around 6 Asmeey ta tashi mikewa tayi tashiga bayin Gwaggo tayo alwala tazo tasaka hijabi tai salla tana idarwa tai azkar tasake komawa gado sai wajajen goma Gwaggo ta daka mata duka tace “wai bazaki tashi mutafi biki diyar Hajiyayye ba” tashi Asmeey tayi ahankali tana shafa inda Gwaggo ta daketa tace “bari naje nai wanka” tawuce tafito saita wuce kitchen Mamie na magana da mai aiki she woke up good yau kawai saita rungume Mamie tace “Mamie ina kwana, Mamie zanbi Gwaggo muje biki” layinsu ne bikin just 2house tsakaninsu ko itama zata shiga bikin sai zuwa anjima amman hakan yasa Mamie tace “tom kije amman jeki wanka sai kizo kiyi kari” gyadama Mamie kai tayi tasaketa tawuce tafita Mamie tabita da kallo shes not happy with yanda take raman nan sai duwawu datake karayi da nono shikenan da hasken fata, sama Asmeey taje tafada bayi brush tayi wanda saida tai yellow amai ta lallaba tai wanka tafito daga bayin wayanta data bari dakin na ringing wucewa tayi wajen gado ta tsaya tana kallon wayan Hamad ne hararan wayan tayi tawani juya dudda zuciyanta namata tadauka but tayi alkawari zata daure.

Wani lace mai bala’in kyau sky blue taciro ta zaro sky blue gyale ta shirya tsaf tayi makeup sosai tasa dan kunne ta fesa turare tadauki handbag tazo tadauki wayan datake harara ta jefa ciki tadauki car key kuma da motanta zataje tafito Gwaggo da Mamie kallo suka bita da shi Gwaggo tace “yau naga abu Asama bikinki sai ashirin ga watan gobe wannan gayun ai saikifi Fiduh kyau” Mamie tayi dan murmushi tace “zoki kari” zuwa tayi ta zauna Mamie tabata tea sai waina da pepper soup tea tasha tasha pepper soup ko waina daya bata tababa tana gamaci ta mike tace “muje Gwaggo” tashi Gwaggo tayi tace “saikin shigo Hamida” Asmeey tace “Mamie bye bye”dan zuwa is wajen Mamie tayi saita karbi gyalen Asmeey ta yafamata daga saman kai tace “saikin dawo”
Suka wuce suka fita Mamie takoma kitchen ga mamakin Gwaggo wajen motanta Asmeey tayi tace “Gwaggo da mota zani nagaji ban iya tafiya” Gwaggo tace “nan da nan Asama ni zaki kashe bari kiji banda motar Doctor babu motar wanda nake shiga agidan nan hakanan ku kasheni” bude mota Asmeey tayi tace “nidai natafi” Asmeey ta tada motan tana murmushi tai reverse ta juya Gwaggo tasaki baki Asmeey tai gate abinta mai gadi yabude Gwaggo tabita da kafa tana fita waje tamaga gidan bikin danga mutane awajen saita wuce wajen tayi parking a layin motocin wajen tana jiran Gwaggo takaraso ga maza sosai awajen sai bin motanta ake da kallo thank God tinted ne, Gwaggo na zuwa wajen ta tsaya Asmeey tabude kofan ahankali tafito tanama Gwaggo dake hararanta murmushi sunyi wani irin kyau tace “bakene kikaki shiga ba” rufe motan tayi Gwaggo tasa hannu tawani kama hannunta tace “muje ina rike da ke kafin ki bata” sukai gate din ana kallonsu ahankali sukaji ance Gwaggo. Dasauri Gwaggo tajuyo ganin wani matashi sanye da manyan kaya farare masu kyau da zaiyi tsaran Hamad yasa Gwaggo tace “Aliyuuuuuuu! Aliyuuu gizo idanunta ke mini” dan murmushi yayi yace “nine Gwaggo” Asmeey kuma tajuya abinta tana kallo cikin gidan inda yanmata ke rawa DJ nasaka kida, murmushi yayi yana satan kallon Asmeey yace “ina kwana Gwaggo” daidai nan Asmeey ta fizge hannunta daga na Gwaggo tai cikin gidan, Gwaggo tace “kika bace baruwana” Aliyu yabi Asmeey da kallo yace “wacece ita Gwaggo yaushe Mamie ta haifi mace”? Dariya Gwaggo tayi tace “yar wajen Muhammadu Sani ce, yarona na biyu dake Bauchi” Aliyu ya gyadakai yana kallon Asmeey dahar taje ta zauna akan kujera tana kallon Amarya sa masu rawa, Gwaggo tace “kaga bari naje” Gwaggo ta wuce cikin gida tace “ga Gwaggo gaGwaggo” dagudu Fidduh tawani rungume Gwaggo suna rawa zokaga yanda aka zagaye Gwaggo Asmeey tai shiru tana kallonsu tana murmushi dole Gwaggo tadinga gantali sonta ake sosaitazama Gwaggon kowa da kowa, ringing wayanta yashiga yi ba kakkautawa dasauri tabude jakanta taciro wayan Ya Hamad ne ke kiranta, amman taki dauka harya katse yana sake kira taki dagawa harya katse yasake kira na uku saitai wani murmushi dadi na lullubeta ashe yadamu ta duba from jiya zuwa yanzu yamata 23missws calls, ganin he’s still calling and zuciyanta na gayamata bazai hakura ba saita amsa yasa tamike tai waje tana tafiya ahankali tafito tabude motanta tashiga daidai yana sake kiranta this time video call hade fuska tayi tasa hannu ta dauka taki kallon screen dinma dan bataso ta kallesa zuciyanta ya karaya, ijiyan zuciya Hamad ya sauke ahankali yana zaune kan gado dagashi sai wasu fararen pajama masu kyau da farin hulan sanyi akansa, duk yayi wani iri kaman ma baida lafiya, binta yayi da kallo da motan datake ciki da gayun datayi calmly cikin voice dinsa mai bala’in dadi yace “kina ina!”? Ya Allah! Wani irin faduwa gaban Asmeey yayi jin calm sweet voice nasa datai missing for days har lokacin taki kallon screen din wayan kai tsaye cikeda jin haushi da fushi tace “biki!” Saikuma cikeda jin haushi yanda dai mata keyi idan sunaso sukai maza bango tace “biki nazo” shiru Hamad yayi yana kallonta ranshi ya bala’in sosu cus bikin nan ba’a tambayesa ba, baisan da bikin ba, baimasan nawaye ba but takama ta fice and look at yanda taci gayu da gyale on her shoulders ana ganin gashinta ta keya sosai data gaban kan ga kirjinta a bude dan bata rufe chest nata da mayafi ba, danne zuciyarsa yayi yace “kin sanar dani about bikin nan? Bikin waye? Wa kika sani? Waya baki izinin fita Asma’u?” Juyowa Asmeey tayi ta kallesa cikin ido cikeda masifa zatai magana akai knocking motanta dasauri ta juya ganin mutumin dazu yasa aranta tace “ko Gwaggo ta aika anemota ne” da sauri ta birkito hakan yasa wayan hannunta ya karkace shima Hamad was able to see d glass ya hango wani a tsaye Asmeey ta sauke glass kasa da sauri ta kallesa Aliyu dabai lurada wayan ba at all yace “wat are u doing a mota ke kadai Pretty?” Wani iri Asmeey taji kafin tace “wani abu yana mata wani kallo bayama iya boye yakamı yace “Gwaggo ke nemanki but tunda kina mota bari naje nagaya mata ko” gyadamai kai tayi ya juya Asmeey taja glass din sama hakanan kawai saitaji gabanta yafadi tana addu’a Allah sa Ya Hamadi baiji ba tajuyo ta kalli wayan wlh yanda taga fuskansa saida gabanta yayi mummunan faduwa but ta dake takuma ki magana saima sauke

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login