Showing 21001 words to 24000 words out of 221707 words
yarki mace ba ke kimata dakanki ba, wallahi Allah zai tsayar dake akan yaran nan, amman kiyakuri idan na shiga huruminki” Ammi na maganan ta tashi tawuce kofa tabude tafita, Mom tabita da kallo ranta ya dagule, yau Aya da Aisha duk saida suka kirata kuma tasan Babansu ne yakira ya sanar da su, kafafu ta kada tai dan ijiyan zuciya ta sauke anatse tace “Lami” da sauri yar aikinsu Lami tashigo dakin anatse tace “gani Hajiya” “kiramin Asmeey” Mom tafadi atakaice hakan yasa Lami tafice. Asmeey na zaune kan gado idanunta sunyi jazur Lami tabude kofansu tace “kizo Maman ki na kiranki Asmeey” dasauri Asmeey ta mike tsaye ta gyadamata kai gabanta faduwa yake, tafito tana tafiya ahankali tawuce side na Mom ahankali tabude kofa, babu kowa a falo hakan yasa tawuce bedroom din tai knocking da sallama daga ciki Mom tace “come inside and lock the door” kofan tabude ahankali babu kowa a dakin gadai kofan bayi a bude maida kofan tayi tarufe tasa lock ta tsaya awajen, daga bathroom Mom tace “zonan” wajen bayin Asmeey tayi gabanta na faduwa sosai taje gaban bayin ta tsaya, Mom na tsaye wajen tap ga bucket tana tara ruwa tama Asmeey wani kallo tace “zonan” wani irin nishi Asmeey tafara tana kallon Mom, yanda kirjinta ke motsi zaka dauka fashewa zaiyi sai kawai hannayenta suka fara rawa jikinta ma haka takasa magana, tadan shigo ta gaba gaban bayin sai kuma taji knees nata sun kasa daukanta tadafa bango zatai kneeling bakinta na kokarin furta magana. “M…..Mo….Mom….” Taku daya Mom tayi tazo wajen tasa hannu tawani fizgota cikin bayin Asmeey zata tsala ihu Mom ta bugata da bangon bayin takai hannayenta kan wuyanta ta shaketa da bala’in kyau idanunta na kadawa tace “because of you mutanen da basu kai komi ba, in educational level i think NCE gareta but tanada audacity da zatazo tana gayamin maganan banza ana cewa Allah zai tambayeni sabida ke, kedin banza da wofi, Babanki bai kwana anan ba dudda yana bangarena and still yabiyoni yacimin mutunci akanki this morning, are you showing people ina making naki sad eh? Are you showing mutane I’m hurting you”? Girgixamata kai Asmeey tayi tana tari idanunta sunyi ja kaman zasu fito, Mom nawani irin kallonta tace “nina haifoki and I can kill you babu abinda zai faru, Shegiya wulakantacciya sabida ke anata kirana, wani daraja gareki Asma’u dan Maman ubanki” wani Irin kyarma tafara idanunta na juyawa kaman zata mutu ganin haka yasa Mom tasaketa Asmeey ta zube awajen tana wani irin tari tana bankarewa tana dukan wuyanta, Mom ta tsaya tana kallonta zuciyanta na tafarfasa sai kwai ta juya ta sunkuci bucket na ruwan datake tarawa ta daga ta juye akan Asmeey tai wani irin ihu da baya fitowa sosai Mom tace “Shegiya jaka kawai duk sanda akamin magana akanki sai kinji ajikinki” zata ijiye bucket din sai kuma ta daga bucket din ta shiga bugama Asmeey tana rafka mata duk ta inda ta samu Asmeey na wani irin kuka tana kare fuskanta da hannayenta akasan bayi, Mom ta jefar da bucket din daya fashe tajuya tafita daga bayin tarufe bayin tana huci sosai.
Kaya tawuce ta chanza sannan tafita daga dakin tawuce kitchen dan yauma Baba na side nata.
Kusan 1hr tana akasan bayin ahaka sannan ta dafa bango ta lallaba ta tashi ta zauna ta kankame jikinta, this is the reason jiya she tried to protect Munir cus bataso Mom tafaramai Irin wannan dukan gwara ita ayita mata dan tama fara sabawa, sosai takejin sanyi but unless Mom ce tazo ta budeta bata isa ba tafito da kanta ba, wani irin zama tayi kaman almajira tana kallon window bayin hawaye na fita daga idanunta kadan kadan har wajajen 5:30 na yamma sannan taji an shigo flat din.
Tana wajen akazo aka bude kofan bayin dasauri takalli Mom jikinta na rawa muryanta baya fita sosai tace “I am sorry Mom” wani kallo Mom tamata ta daka mata tsawa tashi kicire kaya, zabura tayi tamike tsaye da kyar tana dafa bango ta shiga cire kayan Mom na kallonta hawaye sake kwararo mata daga idanu sukayi Mom tace “yayyinki basu taba ja da dokana ba and look at them they’re living a very fruitful life, I will say this to you for the last last! The next time zan ce kiyi abu ki kiyi, na hanaki abu kikiyi, konace kiyi abu ki kiyi wlh wlh zam share sunanki daga cikin yaran dana haifa Alhamdulillah bake kadai gareni ba” daidai tacire rigan yarage sauran pant and bra hannayenta duk ciwo sabida yanda tadinga kare fuskanta dasu da Mom na bugamata bucket, Mom ta mata wani mugun kallo tace “ko ina zakikai girman nono oho jaka kawai saina kaiki an ciresu cus suke saki feeling kaman kin girma bakisan zan iya tattakaki ba kokinkai shakera dari, juya nagani” juyawa tayi Mom tabi bayan nata da kallo duk shaida na dukan shekaran jiya juyawa tayi takoma daki chan ta dawo da magani a hannu ta bude tafara shafamata tana fada tace “kunyi waya da Fawaz”? Gyadama Mom kai tayi alamun eh, Mom tadanyi shiru chan cikin kakkausan murya tace “I choosed him for you! Shizaki aura, shi kadai ne namijin dana yarda dashi in your life kuma bance you should get distracted da soyayya ba, tsakani ki dashi biyayya, your top pariority shine ki gama Law school da good grade, sai bayan kin gama law school zan turashi yaga Babanku asa rana ko ayi biki kinakan NYSC ko bayan NYSC so ki saki jiki dashi yarone mai tarbiya i choosed him for you jiya nina kirashi kotu dan yazo ya ganki dudda ya sanki tun kina little gurl, sister shi kawar yayanki Aya ne u remember right?” Gyadama Mom kai tayi jikinta har sannan rawa yake Mom tace “shima I told him banso yayi distracting naki da soyayya focus on your goals am I clear” ahankali tace “yes Mom” Mom tace “all the files dana baki gobe zaki bani summary kowani case I don’t bloody care how u will do it, get out of my bayi” dasauri ta dauki riganta tadan juyama Mom baya tana maida riganta Mom na kallonta kusan Asmeey tafi yayyinta duka nono har Ramla datake gani tanada shi, ina zatakai nono haka God she’s just turned 21 batason hakan ko kadan, wucewa tayi tafita daga bayin tana tafiya kadan kadan tafice gwanin ban tausayi tana fita Munir na shigowa da sauri tayi gefe zata wuceshi yakama hannunta chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yana kallonta yace “why did u cry? Did Mom beat u again? Are your clothes wet? Ruwa ta watsa miki?” Fizge hannunta tayi da sauri ta kakalo murmushi tace “bayi na wanke ma Mom yes I cried but sabida ta hakura, jeka bama Mom hakuri kaima Munir” Dan Jim Munir yayi yana kallonta tausayin Asmeey yakeji sosai hakan yasa ta turashi ganin yana kokarin magana yawuce side na Mom itama tawuce.
ABINDA MOM KEYI TA KYAUTA?????
COMMENT DANAKE GANI TAKO’INA YASA NA KARA MUKU💃💃💃💃💃
💫UWA KO UKUBA💫
✍🏻M SHAKUR
LOOKING FOR INDA ZAKU SAMI TURBAN, HEAD BAND,
HAIR BEAD, AND BABY CLOTHES AND BACK TO SCHOOL ITEMS
FROM GA MOMMY JUNIOR COLLECTION 💃
https://chat.whatsapp.com/DKwIcG6u9OL1LolCjvOmJC
EPISODE 8️⃣
KANO
Two days to salla
Yau tun safe shirye shirye ake agidan, Abba is a very cultured and family man baya wasa da zuwa garinsu babban salla, a kauye suka taso bayan mahaifinsu yayi kudi yadawo dasu cikin birnin Bauchi, so duk salla anan Bauchi sukeyi, rannan salla na biyu kuma sai suje kauye ziyara.
Mamie is very busy da shirye shirye, Gwaggo da sai yau ta zauna agida dan tunda aka mata takwara agidan mai jego take zama rainon takwaranta, itama nata aikin take uban kayan da Gwaggo tahada na tafiya zaka dauka bazata kara dawowa gidan ba, a manya manyan gana masgon tahada komi, Abdallah kawai ake jira yadawo da motoci daga service a jejjera komi gobe da safe zasu shiga hanya.
Gently yashiga saukowa daga staircase yana sanye dawani wando black sai maroon t-shirt daya zauna ajikinsa da kyau, yasaka pcap black akai sai black shade a idanunshi ya goya black bag pack abaya, he looks damn handsome and huge, babu kowa a falon sai kamshin turaren wuta dake tashi, muryan Mamie dayaji a kitchen yasa yatafi wajen baitaba fita bai sanar da mamanshi zai fita ba, a gefen kitchen din ya tsaya cus baimaso yaga matan dake tayata aiki, murya kasa kasa yace “Mamie!” Dasauri Mami tajuyo jin muryan Hamad, ganin bata ganshi ba yasa takalli matan Ya Mustapa dake wajen tace “ina zuwa Ummi” tafito daga kitchen din ganinshi tsaye a gefe ya shirya tsaf kanshi na kasa yayi kyau sosai yasa tadan tako dab dashi tace “ina zaka Hamadi”? Murya chan kasa yanda dagashi sai Mamin shi zasu iyajin meyake fadi yace “zanje na sama wani cafe software ne dasuka sa nai musu rannan salla zasu bude cafe”murmushi Mamie tayi sosai tace “Masha Allah, Alhamdulillah Allah bada sa’a, Allah yacigaba da kawo maka aiki haka, kayi gudu ahankali kasan titi acike yake sabida salla saika dawo” gyadamata kai yayi yajuya yafice Mamie tabishi da kallo harya fice sannan takoma kitchen. Compound dinsu yafito ya goge machine dinsa yahau kai yatada aka budemai gate yafice, cafe da dan nisa but haka yaje, he install it for them ya nunama Ogansu yanda ake amfani dashi sukai test running akai order from site din sannan Ogan yamai godiya yabiyashi payment nashi 250k ya karba yafito lokacin around 12:50, awani masallaci ya tsaya yayi salla sannan yafito yahau machine nashi wani babban plaza yaje yayi parking sannan yashiga cikin mall na wajen he wants to buy something for Mamie, Abba da Ya Mustapa tunda yau yasami kudi, wajen agogon maza yaje wasu agoguna yazabo masu kyau guda biyu 50k each na Micserah, sai yaje bangaren mata ya tsaya turus yarasa mezai sayama Mamin shi, baitaba sayan wani abu na mata ba, idanunshi ne suka sauka kan set na wani sarka da dan kunne da warwaro is 35k dauka yayi sai ga wani red veil babban gaske hakanan Gwaggo kawai tafado ranshi baitaba really siyama family shi wani abu ba cus baya aiki saidai su subashi kudi, kawai dauka yayi yaga 15k gyalen, yabiya kudinsu 150k, yasa kowanne aka packing daban yafito yasa komi ajakan bayanshi yahau machine nashi sai yawuce shagon dayake sayan turare ya saima kanshi da Hameed sai Ya Abdullahi da Ya Faisal saida yakashe 80k ashagon yarage saura 20k kacal a kudin sannan yahau machine yabiya filling station yasai fuel na 5k a machine sannan yawuce hospital din Ya Mustapa yayi parking yaciro wayanshi yayi dialing number sa wayan na gab da katsewa ya daga yace “Hamadi!” Anatse cikeda girmamawa yace “ina waje Yaya” yana maganan ya katse wayan Mustapa yasan Hamad bazai taba shigowa ba he’s even use to it dudda baicemai yazo ba cus bazai taba iya cewa Yaya kazo ba but he knows yana jiransa awaje ne, akwai that respect in Hamad sosai fitowa yayi ya sameshi yana tsaye awajen goye da jaka gawani paper bag a hannunsa na micserah watches yakaraso wajen yace “hope everything is fine with you Hamadi”? Gyadamai kai yayi yadan sauke kansa kasa tareda daga hannu yabashi paper bag din Mustapa yadan kalleshi sannan yasa hannu ya amsa hakan yasa dasauri Hamad yajuya zaihau machine dinsa karaf Ya Mustapa yarikesa yace “ina zaka? Tsaya wat is this? Nawaye?”
Kanshi akasa yace “is urs” dasauri Ya Mustapha yaciro akwatin agogon yabude da sauri yace “for me? You got this for me Hamadi?” Daidai agogon ya bayyana is a minimalist agogo brown mai kyau, shiru yayi yana kallon agogon saikuma yakalli Hamadi da kanshi ke kasa yace “an ina kasami kudi Hamadi?” Very low calm voice yace “I design website for one cafe they paid me” dadan fada Ya Mustapha yace “shine bazaka ijiye kudinka katara ba, why are you wasting money? Nacema I need agogo ne?” Har lokacin kan Hamad akasa baice komiba, Ya Mustapa yayi shiru yana kallon agogon he’s feeling very emotional cus duka kannensa saidai shi yamusu abu, He’s the first one so kwata kwata baitaba tasowa dawani expectation na kannensa sumai abuba, bawai basason juna ba no they’re united kawai dai wai wani cikinsu yasayo specific gift yabashi wlh basu tababa sai yau da Hamad yamai so abun ya mugun tabashi he was even speechless saiya kalli agogon saiya kalli Hamad da kanshi ke kasa, gently Hamad yaji Ya Mustapa ya rungume shi cikeda so yace “thank you Hamadi” wani irin kunya ne yakama Hamad kaman zai nutse awajen yadan shiga komawa baya alamun ya sakeshi abinma sai yabama Ya Mustapha dariya, yasakeshi yakai hannu yadanja kunnenshi yace “even a hug from you big brother kunya ko” kanshi na kasa har lokacin bai magana ba, Ya Mustapa yace “thank you Hamadi, nagode” juyawa yayi da sauri yahau machine ya kunna yabar wajen Ya Mustapa yabishi da kallo harya fita daga gate na hospital na su, yasake kallon agogonshi yayi shiru sannan ya maida ya rufe yasa a jakan yawuce ya koma cikin hospital din.
Wuraren 2 yakai gida a falo yaga Gwaggo tanacin alalen gwangwani da akayi da sunkai guda 6 da manja ga kaji a gefe ga ruwa ga maltina na gwangwani tana ganinshi ta washe baki tace “oyoyooo Hamadi na yadawo, yaka zokaci abinci” ga mamakinta saitaga yataho, yaune rana na farko datake kiranshi yazo Hamadi yazo, ta shiga mikewa da sauri tana wani Irin murna tace “bara na daukoma cokali” tayi hanyar kitchen zama yayi yaciro gyalenta ya ijiye mata yamike, daidai Gwaggo na dawowa taga bashi awajen but ga gyalen awajen data tashi da sauri ta ijiye cokalin tadauki ledan gyalen tashiga warwarewa tace “menake gani haka? Hameeda zo zo zo taho yau danki yayi abun arziki Hameeda” Gwaggo ta shiga warware gyalen Mami na fitowa daga bangaren Abba tazo Gwaggo tace “kinga Hamadi ya sayamin mayafin salla ni Madina oh dama yaron nan nada kirki da hankali haka dubi mayafin nawa fa” sosai Mamie taji dadi tace “Masha Allah akashe lafiya Gwaggo” Gwaggo tace “ni nasan Hamadi yayi kudi na more ba sauran gantalallun da matansu kadai suke kashema kudiba, jibi abinda yaron da baya aiki ya siyamin na salla banda ke dakika bani atampan codivowel, shikuma Abubakar yamin leshi da atampa gwara gwara likita yamin takalmi amman sauran ko hoda basu sayamin ba, kiga wannan gyale kaman wata Amarya da Hamadi ya sayamin ohh Allah, Allah ka karama yaron nan lafiya ka kuma bashi aiki sabida zamu huta, ahhh zamu huta Madina” Mamie murmushi tayi tace “cinye abincin ki toh Gwaggo” dasauri Gwaggo tace “hakane ungo linkemin ki maidamin ita cikin leda zanje namai godiya kinga ya sayamin mayafin amman kunya ya dingaji harya gudu banmai godiyaba” linkemata Mamie tayi tawuce sama abinta takoma bangaren Abba tana hadamai kayansa tsaf ta gama tafito dakinta ta shiga saitaga yar leda kan gadonta dasauri tawuce ta dauka tabude taga sarka mai kyau da dan kunne da warwaro harda zobe, shiru Mamie tayi saikuma tafito kai tsaye tawuce dakinsu tabude kofa yana zaune akan gadonshi yabude system dinshi ya daura kan cinya yana dandannawa jin anbude kofa yasa yadago kanshi ganin Mamie ce ta maida kofan ta rufe tace “who asked you to spend money like this eh Hamadi?” Sauke kanshi kasa yayi, Mamie tace “I’ve seen yanda kai aiki for days on this project yauda kagama shine zakaje ka kashe kudinka kaida yakamata akara maka ma kudin so that you will establish something shine kake kashemana eh” kanshi na kasa har lokacin baice komiba, shiru Mamie tayi tana kallon sarkan saikuma ta tako ahankali tazo wajen gadon ta zauna gefenshi tasake kallon sarkan ta kalleshi sai kawai taji hawaye sun zubo mata da sauri takai hannayenta tadaura saman fuskanta ta share, jikin Hamad yayi sanyi sosai ijiye laptop dinshi yayi a gefe yadan juyo yakalli Mamie dake share hawaye har lokacin fuskanta na nuna wrinkles kawai yau saiyaga Mamie shi tafara tsufa sai zuciyanshi yasake yin wani iri, murya chan kasa mai taushi da sanyi da nuna so yace “You’ve done alot for me Mamie” yadan sakeyin shiru kanshi akasa ahankali yace “I am always troubling you da rashin lafiya” ahankali yace “you’re always constantly worried sabida ni” cikin kuka Mamie tace “shine aka cema ka you have to buy something for me? You have to repay me? I’m your mother Hamad I don’t need gift sabida kullum ina cikin dawainiya dakai, you’re my son Hamadi, it’s my duty to take care of duka yarana” dan juyowa yayi yakalleta saikuma gently yakai hannunshi yadaura saman fuskanta ya share mata hawaye yace “don’t cry Mamie” hannunshi tarike tana kallonshi tace “promise me bazaka dinga kashe kudin daka samu a aiki hakaba save your money kaji, kai kadai ne baka da aiki, babanku karfin hali ne kawai baida jari yanzu, yayyinka nada iyali duk ta yanda zasukai ga kula dakai wata rana zasu gasa barinma idan yara suka fara tasawa, dama inada niyyan bayan salla zan saida gwal dina na baka saika bude cafe tunda ka iya abubuwa da computer” ahankali yace “Mamie don’t sell your gold, just pray for me I can take care of myself and you kinji” gyadamai kai yayi sai kawai sai kawai ta rungumeshi yayi lamoo ajikinta, inhar babu kowa he accept hug din Mamie but da wani zai shigo dakin yanzu zai saki Mamie, sun dade ahaka sannan tadago shi ta kalli sarkan tana goge fuskanta tana murmushi sosai tace “nagode Allah yamaka albarka, Allah yabaka abinda kake nema, Allah yabaka nasara a ayyukanka Hamadi, thank You Hussaini, Allah yamaka albarka” murya chan kasa yace “Ameen” sabida baiso Mami tasani daga baya tamai fada yasa yace “I got wristwatch for Abba and turare for my brothers Mamie” sarai tasan yana fada mata ne sabida kartazo taji daga baya tamai fada, dan shiru tayi chan tace “nawa aka biyaka for aikin dakayi?” Ahankali yace “250k” “nawa yarage yanzu?” Dan shiru yayi chan yace “20k” saikuma dasauri yace “inada wasu kudi a