Showing 12001 words to 15000 words out of 221707 words
bashi yayi maganan ba coffee yake kurba abinsa kuma yaki kallonsa, dan tsagaita dariya Hameed yayi yace “jiya I don’t know what got over me I almost kissed her” ijiye mug na coffeee Hamad yayi kawai ya yunkura zai mike da sauri Hameed yarikeshi yace “Hamadi wai I can’t gist with u, if I don’t tell you wats going on in my life wazan gayamawa? Besides ma idan baka koyi all this ba how will you get married? Tayaya zaka raya sunnan ma’aiki da iyalinka”? Fizge hannunshi Hamad yayi dasauri yayi hanyar kofa, Hameed ya kwashe da dariya yace “wlh matarka ba kunya zataci ba atoh banza kawai” bugomai kofan Hamad yayi da karfi, habawa me Hameed zaiyi inba dariya ba abun Hamad is too much shifa Hamad ko kallon mata baya iyayi, you will never see Hamad with any friend aduniya, you will never see Hamad a inda ake maganan banza, ko abu zaiyi on google idan irin advert din banzan nan yayi popping up yahakura kenan wlh, just look at yanzu because of conversation na kiss yagudu yatafi masallaci, Wlh he’s not sure Hamad yamasan yanda ake sex taraya da iyali, he remembers suna yara a fiqhu duk ranan da za’ayi wani baabi na wani abun kunya he will leave the class, Allah yama Hamad kunya da jin nauyin anything raw and bad he just can’t stand it, he just wants to see ranan da Hamad zaiso wata ko ranan aurenshi kai he will love to see matan Hamad da ciki cus yanaso yasan tayaya zaima matanshi ciki ko a ruwa zata sha Hamad fa ko kaya baya iya cirewa gabansa hmm, Allah ya kyauta.
Bayan sallan asuba kowa yadawo banda Hamad daya tsaya muraji’a sai wajejen 9 ya shigo gidan the way yake tafiya ka kalleshi saika kara kallonshi, yana taku cike da izza da natsuwa da haiba da kuma kwarjini, farin jallabiyan jikinsa nawani irin sheki, yau Saturday ko maybe saisa yaga motocin yayyinshi agidan dan yawanci on a Saturday sukanzo suyi breakfast tareda Abba ayi catching up rannan ba aiki.
Gently yayi sallama yashiga falon dukansu suka amsa Abba ne zaune akasa kan lallausan carpet dinsu yana sanye da jallabiya da yar hula akansa ga charbi a hannunsa yana kallon Hamad din, sai Ya Mustapha dake zaune kan kujera kusada Abba, sai Ya Abdullahi shima sanye da jallabiya zaune kan 2 sitter, ya Faisal na zaune kusada shi, sai Hameed dake zaune akasa kusada Abba, ga upan atampopi da lace sunkai kusan 50, each da shaddodi anan tsakiyan dakin, ahankali yakarasa cikin falon har zuwan gaban Abba anatse yace “ina kwana Abba” kanshi Abba yashafa yace “yaya karfin jikin?” Kanshi akasa yace “dasauki” tashi yayi yabama Ya Faisal hannu cikeda girmamawa yace “ina kwana” murmushi yamai cikeda so yace “ya jikin” gyadamai kai yayi yabama Ya Abdullahi shima yacemai “ya karfin jiki” hannu yabama Ya Mustapha kanshi akasa yace “good morning Ya Mustapha” anatse yana kallonshi yace “how are you? Wat time katashi?” Ahankali yace “3” yajuya zai wuce Abba yace “dawo kazauna cikin yan uwanka” ba musu yadawo ahankali yazauna kusada Ya Mustapa, Ya Abdallah yayi murmushi kawai daidai Mamie na shigowa falon duk suka gaidata Abba yace “Maman Dr zoki zauna kicirema kowa nasa inaso da safen nan Faisal ya aika da komi Bauchi” Gyadamai kai tayi tace “toh Masha Allah” Abba yace “Doctor tashi kadauki naka danasu Areef” gyadama Abba kai yayi yatashi yadauki shaddan su yadi goma ya isheshi shida yaran yace “Allah amfana Abba”.
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn
EPISODE 5️⃣
Abba yace “Abdallah saikai” tashi yayi yadauki 5yard yace “Allah amfana Abba Allah kara budi” Abba yace “Faisal” tasowa Faisal yayi yadauki 5yrd shima yace “Abba Allah saka da allhairi” Abba yace “Hassan sai kai” tashi yayi ahankali yadauki 5yard” Abba yace “zabi another one ku baku da iyali so kala bibbiyu zan muku” murmushi Hameed yayi yakara another color daya yace “nagode Abba” Abba yajuya yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa yace “saikai Hussaini” tashi yayi ahankali yadaura hannunshi yadauki the first two shadda dake in line Mamie tace “iri dayane duka change color” cikin calm voice nashi yace “Mami zaban mini” Hameed yace “toh yaron Mamie” Abba yace “ina ruwanka” hararansa Mamie tayi tasa hannu ta zaba masa irin na Hameed ya karba kanshi akasa yace “Jazakallah Abba” murmushi kawai Abba yayi yace “to cire mata naku Hajjaju ina Gwaggo”? Mamie tace “taje makota anyi haihuwa wai an mata takwara” Abba yadanyi murmushi kawai tadauki atampa daya lace daya tace “gana Ramla” tasake ciro wasu biyu tace “gana Asma’u” “Yusra da Amina” Abba yace “to kwasan ma mazan ma Shadan su su Munir” haka Mamie tacirema duk wani yara na danginsu kayan salla sai mai aikinsu Lami da yaranta Faisal yahada kayan a babban gana masgo yafita yakai mota yadawo Abba yakalli Mustapa yace “yau salla saura sati biyu ko” Abdalla yace “saura 13days Abba” Abba yace “okay ina ganin ana gobe salla zamu wuce Bauchin akwai abinda zanyi” yakalli Abdallah yace “next week sai akai duka motoci ayi musu service ko” Abdallah yace “toh Abba” Abba yace “Masha Allah” yataba aljihunshi yaciro 50k guda biyu yabama Hameed daya yace “gashi kudin dinki da kudin takalmin salla” dasauri Mustapha yace “Abba don’t worry about that zan basu please dawainiyan yayi yawa” dasauri Hameed ya karbi nashi 50k yace “Ya Mustapha kudi baya yawa” Abba ya girgiza kai yakalli Hamad yace “Hamad zo ga naka” kin motsi yayi tausayin Abba yakeji sosai baida arziki kaman da kuma sai kashe kudi yake anatse yace “Abba kabarshi inada takalmin salla” atare dukansu sukace wanne?” Dan kallon Abba yayi kadan yace “Ya Mustapa bought sabon takalmi last week for me dashi zanyi amfani” Abba yace “dudda haka amsa wannan nina baku nace kusaya take it” kasa tashi yayi yadan kalli Ya Mustapa dayamai alamu da idanu ya amsa hakan yasa yatashi yasa hannu biyu ya amshi kudin ahankali yace “nagode Abba” Abdallah yace “zansa mai dinki na yazo ya amshi kayan ya aunaku I will pay for the 2 of you” Mamie tawuce aka kawo breakfast kunu ne lafiyayye da kosai Abba kuma aka dumamai tuwo cus he can’t do without tuwo, ko half cup na kunnun bai iya sha ba yawuce yatafi sama kowa ya kalleshi but aka barshi gamaci Ya Mustapa yayi yawuce sama Hamad na zauna kan gadonshi yana taba laptop dinshi Ya Mustapa yashigo gently ya ijiye laptop din, Ya Mustapa yakarasa wajen yace “too much sitting is not good for you allow system dinka to rest okay, da lafiya ake komi”zama yayi yaduba ciwon is looking very good magani kawai yabashi da allura sannan ahankali yace “do you need anything?” Girgizamai kai yayi
Ya Mustapha yace “zamuyi tafiya next week going to family house for salla you know how you get so tell me idan kana bukatan anything for traveling din” ahankali yace “bakomi” gyadamai kai yayi yace “okay zanje hospital yanzu anjima i will call you sai muje tare na siya maka desktop dinka tunda na da ya lalace” Dasauri ya kalli Ya Mustapha hancins a Mustapha yaja yace “dudda you will never say it out loud I know how much all this su system and desktop dinka daya lalace means to you, my tech little bro so we will get it today anyone kakeso” baki yabude zaiyi magana Ya Mustapha ya harareshi yace “yimin shiru just complete project din daka fara and send it to Microsoft muga abinda Allah zaiyi, in sha Allah you will win, I also speak to wani friend dina za’a nema maka aiki idan an samu any slot, idan kuma babu I think I will just enroll you kafara phd muga abinda Allah zaiyi kafin aiki yazo saikai aure” dawani irin sauri Hamad ya sunnar da kanshi kasa abin saida yasa Mustapa yayi dan dariya sannan yawuce zai fita, harya taba handle gently Hamad yace “Yaya” juyowa Mustapha yayi yakalleshi batare daya amsaba, sauke kanshi kasa yayi ahankali yace “thank you Yaya” murmushi Mustapa yayi yajuya yabude kofan yafice, daukan laptop din yayi yasa ajikinshi yashiga site dinshi yana duba message da mutane sukamai he’s into creating website, building application, prototype, software development and maintenance and so much more anything tech he just knows it, banda haka yana program daban daban a online yana karban certificate, kwanan nan nema baya iya aiki sosai sabida operation din nan, aiki kadan yayi ya ijiye laptop din akan gadon Hameed yana lumshe idanu bacci na neman kwashesa.
Shigowa dakin Hameed yayi ganin yana bacci yasa yafada bayi yayi wanka yashiga shiryawa cus one of his colleague na aure yau zasuje daurin auren tsaf ya shirya cikin wani lafiyayyen shadda ya kafa hula aka tareda fesa turare saikuma yajuyo ya kalli Hamad kafin yasa hannu yadauki turarukanshi wajen kayanshi dake nan a gyare, yarasa yaya Hamad ke selecting oil perfumes dinshi cus turarenshi smells out of this world shafawa yayi ya maida ya ijiyesu hargitse sannan yarufe wardrobe din nasu yasaka takalminshi Hermes yadauki key motarshi ya wayanshi yawuce yafito Mami ne kadai a falo tana magana da Lami dazata kasuwa tana ganinshi tace “sai ina yan samari” kai ya sosa yace “colleague dina a bank ke aure yau Mamie shine zamuje mai daurin aure” Mamie tace “mesa bakaje da dan Uwanka ba”? Kallon Mami yayi yace “Mamie are you seriously asking this question kema kinsan ko sama da kasa zata hade bazaije ba besides ma he’s sleeping I think magungunan shi na sashi bacci” Mamie tace “to adawo lafiya drive safe” wucewa yayi yafice yashiga motarshi Camry ta 2010 yabar gidan.
Around zuhur ya farka yatashi zaune ahankali yana kallon dakin he hates dirt, Hameed ya bata ko’ina, sauka yayi ya shiga gyara dakin ya gyara gadajen su ya kwashe kayan Hameed daya cire yasaka a laundry basket yadauki broom ya share dakin ya kwashe a Parker yazuba a leda yabari awajen yashiga bayi yadauro alwala yafito yadauki leda yawuce yasauka kasa bakowa falo yatafi mosque yayı salla yadawo afalo yaga Mamie tana zaune tace “zokaci abinci” ahankali yace “anjima”.
Around 4 yadawo daga masallaci wayanshi yafara ringing, screen din yakalla ganin Ya Mustapa ne yasa yadauka Ya Mustapha yace “start coming ina hospital” gyadamai kai yayi tareda katse wayan yafada bayi wanka yasakeyi batare daya bari ruwa yashiga ciwon ba sannin babu kowa yasa yafito yazo wajen kofansu yasa key sannan ya tsaya gaban wardobe nasu yana budewa yaga aikin Hameed kawai yazaro wani dark blue jean da t-shirt fari ya shirya tsaf kayan sunmai bala’in kyau turare ya fesa yadauki p-cap dark blue yasa akanshi, he loves wearing p-cap sabida iska sannan yadauki wani black shade, he always put on shade idan zai fita cus idanunshi somehow makes people to be looking at him both men and women kuma he hates that, wayanshi yadauka yasa a aljihu yadauki wani key dake saman side drawer shi yasa wani easy pam yafito yana tafiya ahankali looking expensive and classy kaman wasu designers yasaka, Mamie na zaune tana sauraron wani wa’azi a Sunna tv taji kamshinsa hakan yasa tadago sai kawai ta tsareshi da ido Masha Allah! Hamad is simply handsome kawai karasowa falon yayi tace “zaka fita?” Gyadamata kai yayi tace “ina zaka?” “wajen Doctor a asibiti” gyadamai kai tayi tace “jekadauki key mota na kaje dashi” girgiza mata kai yayi yace “da machine dina zani” shiru Mamie tayi tace “Tom saika dawo ayi gudu ahankali” gyadamata kai yayi yafice wajen lipan dake tsakar gidan fari yaje yadaga katsa yadauki tsuma ya goggoge yadade bai fita ba he hardly go out baida wajen zuwa idan yafita kawai da dalili, tass ya goge machine din dayayi kura sannan ya warware glass din yasaka ya kara gyara p-cap dinshi yahaukan machine din yayi wani irin kyau ya kunna machine din mai gadinsu yabudemai gate yafice.
Kusan 30min yabata cus saida ya tsaya yashamai sannan yakai hospital din yayi parking yaki shiga yaciro wayanshi yakira yayanshi, Mustapa na zaune yaga kiranshi kawai ya girgiza kai yatashi batare daya daga ba yadauki key yafito yaganshi yace “let’s go to my car” ya wurgamai key yace “drive nagaji” karba yayi suka wuce shiya jasu har zuwa computer village wani shago na slot Mustapa yace “you know wat u want pick up” shiru yadanyi Ya Mustapa yace “muje” wucewa sukayi direct wajen wani desktop yafara zuwa na dell yana duba spec din, HP EliteOne 800, 200 G45420 All-inOne G3Touchscreen... AiO - 6th Gen....CORE 13 11. This is the perfect desktop dayake bukata for his kind of work but ganin kudin #1,600,500.00 kawai saiya wuce da sauri yana duba wasu saiya juyo yakalli yayanshi yanunamai na wani 700k yace “this” Mustapa yakalla sai kawai yawuce yakalli mai shagon yanunamai na farkon yace “wannan mukeso” dasauri Hamad yazo kusada shi murya chan kasa yace “Yaya the money is too much” anatse Ya Mustapa yace “but this is the spec your kind of job needs, don’t think about the money think about abubuwan dazakayi dasu kasan how worried I was da desktop dinka ya lalace, you are stuck a software da kake developing sabida rashin desktop, I know Abba baida karfi sosai zamu karamai burden ne bayan responsibility na kanshi da yan uwansa, look at kudin daya kashe na kayan salla dudda baida shi kaman da but bazai taba dena abun nan ba cus it’s something daya saba yi batun yauba, even if it’s all my salary I will use it to get this for you, kai kadaine cikinmu da har yanzu baka kama wani takamaiman aiki ba and ka kama hanya desktop ya lalace just let me do my duty” daidai yaciro katinshi Hamad ya kalli katin na UBA dinshi ne which is salary account nashi maybe ma all his savings ne zaiyi using cus duka duka salary Doctor nawane, he has family ga dawainiyan su Abba, gashi ba’a dade damai operation ba duk sun kashe kudi” duk sai jikinshi yayi wani iri, zare kudin akayi aka bashi ATM dinshi back mai shagon ya dauko kwalin brand new desktop din yaba sales boy nashi yace “take it to their car” suka bishi suka fita ana kokari sawa a both kaman ance Musty yajuyo yaga wata yar matashiya tana kokarin bude motanta tashiga amman sai kallon Hamad da hankali shi ke kan abinda ake sawa a booth yake, dan murmushi yayi da gangan yadan taba Hamad yace “Hamadi ana magana dakai look over there” juyowa Hamad yayi yakalli yayanshi ya kalli inda yake nunamai cus yadauka wani abune ganin wata ke kallonshi dawani irin sauri yadauke kai yarufe booth yawuce yakoma driver seat ya zauna yajawo kofa yarufe itakuma yarinyar ta taho harda dan gudunta sai kawai tai knocking gaban motan Hamad yadago kai yakalleta dan glass din motar tinted ne bata iya ganoshi yaki bude kofan yajuya yana jiran Ya Mustapa yashigo subar wajen, ganin Hamad yaki bude kofan yasa Ya Mustapa yazagayo yabude kofan dasauri Hamad ya kalleshi, Ya Mustapa yace “ana magana dakai sauke glass” kaman zai mutu dan haushi ya sauke glass din, da sauri yarinyar cikin turenci tace “you are Mr Hamad ko? The Tech genius” Hamad ya dauke kanshi yaki magana yaki kallonta, yarinyar tai murmushi takalli Ya Mustapa tace “it’s him I know him, he developed wani EHR software for my Dad’s hospital ranan dayazo yamusu installing nataba ganinshi can I have your digit please” wlh kazo wajen zaka dauka da Ya Mustapa ake magana cus Hamad doesn’t even look like wanda akema magana ko kallon yarinyar bayayi Ya Mustapa ke kallonta, dan sanyi jikin yarinyar yayi saitai murmushi takalli Ya Mustapa tace “sorry for approaching you guys” tawuce da sauri jikinta yayi sanyi tayi motanta shikuma Hamad yatada motan yaja dasauri abinsa sundanyi nisa a hanya yasake kallonsa saikuma yayi shiru, Hospital suka wuce saida yayi parking motan a parking space zai bude yafita calmly Ya Mustapa yace “Hamadi!” Sauke hannunsa Hamad yayi kawai saiya kasa dago kanshi cus somehow and deep down yasan maganan da Ya Mustapa zaimai. Anatse yace “bawai sabida this incident na this girl that happened a while ago ne nake maka maganan nan ba, I’m just talking to you sabida yakamata” yayi shiru saikuma murya chan kasa yace “Hamadi bakaso kai aure ne?” Rasa inda Hamad zaisa kanshi yayi gashi he can’t walk out on Ya Mustapa kaman yanda yakema Hameed sai kawai yakai hannunshi yataba p-cap dinshi yawani janyo shi yama rasa yanda zaiyi duk Doctor na kallonshi, ahankali yace “I’ve seen and heard Hameed spoke to budurwanshi countless time infact rannan he gave her phone ta gaidani i guess Zainab sunanta idan ban manta ba” yayi shiru yana kallonshi yace “there’s no one in your life Hamadi, all of us munyi aure saura ku twins” yasake shiru yace “the whole point na this conversation is Hamad i know how u are and how you get but try and give a lady chance a rayuwanka dole kai aure one day, eventually, kaima ka haifi naka yaran at least maybe matarka will be official first ever friend naka tunda bakada su kaima kadinga samin natsuwa ajikin iyalinka” dawani irin sauri Hamad ya juyar da kanshi yana facing glass na kofa har pcap nashi nataba glass din, Ya Mustapa duk yana kallonshi wlh baitaba sanin maza can be this shy ba sai akan kanninsa this particular Hamad, dan ijiyan zuciya yasauke yace “fita kadauki bike naka lemme follow u abaya nakawoma desktop din u can’t carry it a bike” dasauri yabude mota yafita Ya Mustapa na zaune yabishi da kallo har zuwa wajen bike nasu kusan Hamad yafi dukansu kyau dudda shida Hameed are look alike but still yafi Hameed kyau far far he has lots of features naban mamaki, ga jiki mai kyau, jikinshi kaman dan gym and baya gym kawai he run daily saida akamai aikin nan yadena, he’s tall and he’s huge though ba sosai ba ga dimple ga idanunshi da zaka rantse yanasa kwalli and kwayan idanunshi are squeaky clean farare tass dasu kwaiduwan idon baki sidik girls are crushing