Showing 303001 words to 306000 words out of 325849 words

Chapter 102 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

588

Middle Ads

nutse yace "D'inki Ummy tayi miki?"

Da sauri ta shiga d'aga masa kai alamar eh, a hankali ya jawo yatsarshi ya cire, kwance yayi kusanta ya rumgumeta kamar zai fashe da kuka yace "Kiyi hak'uri kinji, ban sani ba ai, Ummy bata fad'a min ba ke ma haka."

Hamna da a lokacin take wa kanta hud'ubar zaunawa dashi lafiya saita k'ara ruk'umk'ume shi da hannunta da ba kanshi take kwance, tusa kanta ta shiga yi cikin k'irjinshi tana ta damuk'ar damtsenshi tana kuka, rirrik'eta yake yi sosai yana bata hak'uri, a haka bacci ya d'auketa tana ajiyar zuciya.

Ko da ya tashe ta da asuba ta bud'a ido ta kalle shi, doguwar riga ce jikinshi da sallaya hannunshi, yar ajiyar zuciyar data sauke ta tuna mata da kukan data kwana tana yi da kuma dalilin kukan, ai da sauri ta tashi zaune tace " *Ina kwana*...boss."

Wani kallo ya mata mai d'auke da yanayin mamaki a cikinshi, ba tare daya nema ba Hamna ke gaishe shi, amma sai ya d'an basar yace "Me ye kuma boss? Hamna ba zaki daina min wannan sunan ba?"

Langab'e kai tayi tace "Kayi hak'uri ka bani dama na ci gaba da kiranka haka, kai ma ai har yanzu kana ce min kankana."

Murmushi kawai ya saki ya nufi hanyar fita yana fad'in "Ki tashi kiyi sallah."

Da kallo ta bishi har ya fita, data shiga ban d'aki saida ta had'a ruwan d'umi ta jima zaune a ciki, wanka tayi tayo alwala ta fito ta kabbara sallah.

Har rana ta take ta hantse bai shigo, ta tashi da niyyar shica madafa ya shigo da kular abinci a hannu, mik'a mata yayi yace "Inji uwarki."

Kallonshi tayi a ranta tace "Kaji wai inji uwarki? Ina ma laifin ka ce Ummy ko mamanki, hmmm Allah ya sawake."

Ajewa tayi kan tebur ta juya zata shiga d'aki yace "Ina zaki je?"

Juyowa tayi tace "Wankan zanyi."

Saida yaje gabanta ya kama hannunta suka shiga d'akin tare, ita dai gabanta na fad'uwa haka ta daure ta bishi, har ban d'aki suka shiga cikin kwanciyar hankali ya rabata da komai shi ma haka ya fara wanke tsaf.

Wani hegen siket ne da rigarshi na kanti ya matseta ya saka mata, saida suka fito falo ya zauna kan kujera yana kallon tv yace ta kawo abincin nan, juyawa tayi ta fara bada step (inji malam ba), a hankali ya shiga lumshe idonshi yana bud'ewa yana sauke su kan k'ugunta, kutumar bala'i sai yau ya k'ara tabbatarwa ba k'arama bace, haka ta d'auko ta dawo ya shiga kallon gaban da komai da komai.

Har k'arfe *09:00* yana gida ta zubawa sarautar Allah ido, ta gaji ta k'agu ta k'ufula ta jigata da matsar da yake mata, duk jikinta ji take kamar wacce tayi nak'uda, labb'anta banda zafi da zut zut babu abinda suke, sai yanzu kad'ai ya shirya fita ya kama hannunta har k'ofar d'akin, bud'e hannayenshi yayi yace "To rumgume ni ki min addu'a zan fita."

Wani kallo ta masa da shi dai ya fassara shi kallon baka da hankali ne, a hankali ta bud'e hannayenta ta fad'a k'irjinshi kamar mai k'yank'yaminshiπŸ˜‚ kafin tace "...


*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:39 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_73_

"A dawo lafiya."

Tallabo fuskarta yayi yana murmushi yace " *Je t'aime* (ina sonki)."

K'wayar idonshi ta kalla, ganin shima ya kalli idonta sai tayi k'asa da nata tana murmushin da bata san damilinshi ba, sake d'ago kanta yayi yace "Ke ma ki ce wani abu mana."

Da sauri ta kubce daga rik'on daya mata ta juya zata shige ciki, hannunta ya rik'o ya sake had'ata da jikinshi yace "Idan baki ce komai ba zan dawo ne mu zauna tare, kuma ke dai kinsan me zai faru."

Juyowa tayi tace "Kunya nake ji mana."

Sakin hannunta yayi yana murmushi yace "Su kunya manya, ita ma yau ranarta ta zo."

Juyawa yayi ya fita yana fad'in "To Allah ya bamu irin ta ku."

Juyawa tayi ta bishi da kallo har ya fita, dawowa tayi ta ma kanta mazauni kan kujera, a hankali take sauke numfashi had'e da murmushi a fuskarta, ta ji dad'in kalmar sosai data fito daga bakinshi, wani nauyi taji ya ragu a kanta data jima tana dakonshi a zuciyarta. Tana cikin tunanin nan ta shiga d'aki ta shirya ta fito dan shiga wajensu Ummy ta ga lafiyar yaranta, tasan Ummy ce ta rik'esu dan a bata damar morar ranarta ita ma, shiyasa ko mitsinsu bata ji ba daga randa aka kawota zuwa yau.

Da sallama ta shiga falon ta samu Ummy tare da Hajia zaune da Husseina, k'arasawa tayi ta gaishe su suka amsa da tambayarta ya take ita ma? Ummy ta kalla tace "Ummy ina yarana suke?"

Kallonta tayi tace "Kin manta suna islamiyya?"

D'an turo baki tayi tace "Ummy me yasa basu tafi gani na ba?"

Ba tare data kalleta ba tace "Zasu tafi, amma ba yanau ba."

Shirun da tayi yasa Ummy kallonta tace "Ya jikin naki?"

Saida ta sunkuyar da kanta tace "Da sauk'i Ummy."

Jinjina kai tayi kafin su ci gaba da hira, ita ma nan tayi zamanta har Zeinab da su Jamila suka shigo sukayi ta hirarsu.

*Bayan sati uku*

Ya shigo kenan ya had'u da Zeituna zata fita, sauke gilashi yayi yace "Uwa ina zuwa da rana haka?"

Saida ta gyara goyon *Shakur* tace "Wallahi kasan Jumare ta haihu, zan tafi can ne yau ake sunan."

Da dariya a fuskarshi yace "Iyee! Su Jumare manya, to uwa ina motar naga zaki fita k'asa?"

Cikin damuwa tace "Saida na gama shiri zan fita kuma sai Ayuba yake fad'a min motar na wurin gyara, kawai zan hau taxi ne."

Girgiza kai yayi yace "Haba uwata, idan ma baki kira Abbanmu ya zo ya kaiki ba, to mu miye anfaninmu? Muje na sauke ki kawai dama bacci na zo yi."

Murmushi tayi tace "Nagode." Zagayawa tayi ta sauke goyon ta bud'a ta shiga, suna tafe suna d'an tab'a hira tana nuna mishi gidan har ya sauke ta, juyawa yayi ya koma ita ta shige ciki. Hanyarshi ta dawowa ne ya hangi Amie kan moto, duniyanci sai abinda ya ci gaba bawai ya rage ba, tsayar da ita yayi suka tsallaka titi suka tsaya, kallon juna sukayi sosai har yau yana tuna Ummy ta fad'a mishi wai Amie ce ta fad'awa marigayiya Shureim d'ansa ne, saida ya fito daga motar ya tsaya gabanta tana fad'in "Mai kyau ya kake? Kwana biyu?"

Kallon fuskarta yake da tasha kujera kamar an watsa takin gona yace "Da dama? Ya harkokin?"

"Da dama." Ita ma ta fad'a tana d'an sakin kan moton, ba tare daya daina kallonta ba yace "Me ya had'aki da k'awarki?"

Kallonshi tayi ita ma tace "Wace k'awar tawa?"

"Matata mana, kankana."

Wani kallon rashin mutumci ta masa tace "Ba komai, me ka gani?"

Murmushi yayi yace "Ko yaron yasan da komai, yaushe rabon dana ganku tare? Sannan har akayi bikinta aka gama ban ganki ba."

Cikin rashin damuwa tace "Hakane, kasan duniya juyi juyi ce, k'awance ma yana da tsuntsun soyayya, yau ya hau kanka gobe ya tashi ya koma kan wata."

Murmushi ya sake yi yace "Hakane, amma haka yafi faruwa kan k'awancen da ba'a gina dan Allah ba."

Tab'e baki tayi tace "Ok, ni zan tafi dan ina da abunyi sosai a gabana."

Wani kallo ya mata yace "Ba damuwa, amma idan kin samu dama kije ki ci abincin amaryata."

Saida ta kashe masa ido tace "Zan zo, amma ka fara saka min lambarka ta yanda zan sanar da kai zuwan nawa idan na tashi zuwa."

Ta k'arashe da mik'o masa wayarta, saida ya kalleta kallo na fahimta sannan ya karb'i wayar, saka mata lambar yayi ya mik'a mata, karb'a tayi tana tana kallon lambar tace "Kai babba ne, lambarka sauk'in hardacewa gareta kamar shan ruwa."

Murmushi ya mata yace "Amma ai kinsan ruwa kala kala ne ko, sannan idan ka shanye ruwanka a duniya ko a cikin tekun maliya kake ba zaka iya had'a ko d'igo d'aya ba."

Ko da ya fad'a ya wuce abinshi ya barta nan, kai tsaye gidan ya koma ya nufi b'angaren amaryarshi, amma daya shiga k'ofar rufe bai same ta ba, kuma gashi ba zai iya baccin ba idan bata kusa dashi, a hankali ya fito ya nufi b'angarensu Ummy.

*Da* sallama a bakinshi ya shiga wanda yayi daidai da fitowar Hamna daga madafa da plate a hannunta da Ummy da Soueiba bayanta da alama aiki suka gama, tana ganinshi ita tasan meya kawoshi gida wannan lokacin, da sauri ta ratsa tsakanin Ummy da Soueiba zata koma madafa ta b'uya, da sauri yace "Algunguma na ganki, maza zo wuce mu tafi to."

Juyowa tayi tana turo baki tace "Ba zan je ba ka tafiyarka."

Nuna kanshi yayi da yatsa yace "Ni ne kike fad'a ma ba zaki zo ba? Ni kankana?"

Lab'ewa tayi bayan Ummy ta rik'eta da hannun d'ayan tana lek'enshi, tunkarowa ya fara yi yana fad'in "Zaki san wa kika fad'awa ba zaki zo ba kankana, ba dai ni ne kika ce ma ba zaki zo ba? Ni ga sakarai ko?"

Sake rirrik'e Ummy tayi tana ihu tana fad'in "Ummy ki ce masa ya tafiyarsa, dukana zaiyi."

A hankali Ummy tace "Hamna, ke dai kinsan halin kayanki, dan Allah rufa masa asiri ki jashi ku tafi, ke kinsan yanda zaki bashi hak'uri."

Kamar zatayi kuka tace "Ummy ni ba zan je gaskiya na gaji."

Rik'e baki Soueiba tayi tana kallonta Ummy ma kallonta tayi, takowa yayi da sauri hakan yasa ta dakawa da gudu madafar ta shige, kafin ta mayar da k'ofar ta rufe ya shige ciki, kallon juna sukayi inda Ummy ta girgiza kai tace "Muje Soueiba, ta fito da kuka yanzun, anjima kuma sun shigo nan suna dariya."

Dariya Soueiba tayi ta juya zata wuce d'akinta, ihunta sukaji yasa duk suka juya dan ganin me ye? Abun mamaki ganinshi sukayi ya mata dokin wuya ya d'aukota, wutsil wutsil ta shiga yi da k'afafu tana ihu da kwaroroton kiran Ummy tasa ya sauke ta, Ummy ita dariya ma ta shiga yi har da rik'e ciki, ita kam da take ganin kamar zata fad'o ihun ta ci gaba da yi iya k'arfinta, mai gadi da yaji kuwar saida ya d'an lek'o, ko da ya ga soyayya ce saiya koma yayi gum, daya shiga b'angarensu ma saida su Jamila da Farisa suka lek'o, Umaimah ko ko a jikinta dan ba sabon abu bane, tunda akayi aurensu abinda ke faruwa kenan, wani abun ya baka takaici wani ya baka haushi, wani kuma saiya baka dariya har cikinka ya k'ulle, wani kuma in sukayi shi sai su matuk'ar birgeka ka gane cewa akwai fahimta sosai a tsakaninsu, kowa yasan kowa babu mai bawa wani wahala.

Sai kan gado ya direta yana b'alle mab'allan rigarshi yana fad'in "Hamna ba ni ne na ce ki zo kika ce k'in ki ba? Zaki ga ikon Allah yau wallahi sai kin haifi yan uku ko na barki."

Cikin kuka tace "Kayi na ce to ba zan sake ba, Allah na maka alk'awari."

Dungurar mata kai yayi yace "Ke tafi can alk'awarinki na banza, kullum ba haka kike ba."

Kallonshi tayi idonshi sunyi launin ja alamar fitina, gashi ta jawa kanta zai murk'esheta da rana patsal patsal, in tayi wasa yau ma sai an mata sabon d'inki, dan yanzu indai ta mishi iskanci to tana nan yake horonta, dan ta samu lafiyarshi sai kawai ta tashi zaune ta shiga cire d'amararshi, yana kallonta ya ga me zatayi sai gani yayi ta fito da...bata tsaya komai ta ba mata masauki a bakinta.

Da sauri ya rintse ido ya k'amk'ameta tare da danna kanta yana sauke wani wahalallen numfashi...😎

*Bayan awa biyu* kanshi na kwance tsakanin mamanta biyu, shafa kanshi take a hankali idonta rufe tana ji kamar ita ma tayi k'undubala tace tana son shi, yanda hannunshi ke mammatsa mazaunanta yasa take ta sauke numfashi, dukansu babu mai magana sunyi shiru suna jin dad'in yanayin, wayarshi ce tayi k'ara dake kusa da Hamna kan gadon a cikin aljihunshi, ba tare daya d'ago ba yace "Duba kiga."

Hannu tasa ta fito da ita ta duba tace "Babu suna."

Hannu ya zura ya karb'a ya danna ya sata a speaker ya d'ora wayar kan cikinta yana saurare, cikin wata irin muryar bariki ta d'aukar hankali aka ce "Hello mai kyau."

Ba tare da damuwa ko tunanin komai ba a kasalance ya amsa da "Ya kike? Har kin shirya zuwa ne?"

A hankali ta amsa da "Eh, zan zo anjima, me zaka tanadar min?"

"Me kike?" Ya fad'a idonshi rufe, cikin kashe murya tace "Kai, kai kad'ai ma ka ishe ni."

Ido rufe yace "Na miki yawa, ki dai canza wani abun."

Saida ta sake kashe murya tace "Ni kai d'in kawai nake so, in kuma ba zan samu ba nayi zamana."

Yana shirin cewa eh tayi zamanta kawai yaji Hamna ta mishi wata hankad'ar tsiya wacce baisan da zatayi hakan ba ya fad'i k'asa kwance, tashi tayi da k'arfi tare da rik'e wayar a hannunta, saida ta sauka daga kan gadon ta d'aga wayar iya k'arfinta ta b'arsata k'asa, fashewa tayi inda ta kalleshi rai a b'ace cikin fitar hayyaci tace "Ni zaka raina Ammar? Me ka d'auke ni nima? Karuwar kamar ta? To baka isa ba wallahi, banyi wannan lalacewar ba."

Da sauri ta bud'a kayanta ta zago doguwar riga ta zura ta d'auki hijabi ta saka, ta juyo zata fita ta ganshi yana mayar da kayanshi shima, saida ta harare shi sama da k'asa taja tsaki tace "Na bar maka gidanka ka d'auko duk wacce kake so ku zauna tare."

Da sauri ta fita inda ya bita da gudu yana kiran "Hamna, Hamna tsaya ki saurare ni, Hamna dake nake magana."

Juyowa tayi a hassale tace "Je veux te tuΓ©."

Wucewa tayi ta bar d'akin sai b'angarensu Ummy, kai tsaye d'akin Ummy ta shige ta same ta zaune ta idar da sallah la'asar, fad'awa tayi kan k'afafunta ta fashe da kuka, Ummy da gabanta ya shiga fad'uwa da sauri ta aje carbin hannunta tace "Hamna lafiya? Me ya faru kike kuka? Dukanki yayi?"

D'agowa tayi abun tausayi tace "Ummy ba gwara ma ace dukana ne yayi ba da abinda ya min, da dukana Ummy ko ji ba zakiyi bare har na zo na d'aga miki hankali."

"To meya faru?" Ummy ta fad'a hankalinta a tashe, cikin kukan tace "Ummy yah Ammar baya k'aunata baya so na ko kad'an, Ummy a gabana yake hira da K'awata yar iskan nan Amie, wallahi Ummy ita ce na gane muryarta kuma ita kad'ai ke kiranshi da mai kyau, Ummy yah Ammar ya gama dani a rayuwa."

Ajiyar zuciya Ummy ta sauke, sai yanzu ta fahimci al'amarin wato na kishi ne, d'an jinjina kai tayi ta juyo da fuskarta suna kallon juna cikin nutsuwa tace "Me ye tsakaninshi da Amien?"

Cikin hushi tace "To ni ina na sani, kawai suna son tozartani ne, Ummy yarinyar fa yar iska ce wallahi ta sawa a gaba, baki ga nima na daina kulata ba saboda ba mutuniyar kirki bace."

Kallon fahimta ta mata tace "To yanzu yana ina shi?"

Saida ta turo baki tace "Yana can na baro mishi gidanshi."

Zaro ido Ummy tayi tace "Kin baro masa gidansa? Hamna me kike nufi?"

Saida tayi k'asa da kanta tace "Ni ba zan koma ba."

Lallai ta yarda tana son Hamna fiye da yanda take son 'ya'yan data haifa a cikinta, musamman da yar uwarta ma ta mutu saita k'ara ninka soyayyar, amma a yanzu da ake magana kan gidan aurenta, dokenta ta nusar da ita ta kuma nuna mata ita uwa ce, wannan karan ba zata goyi bayanta ba kamar yanda take yi kullum, dan haka ta kalleta tace "Kenan ki ce yaji ne kikayi?"

Cikin zumud'i tace "Eh Ummy."

Wata tsawa Ummy ta mata da bata tab'a mata ko kamar ta ba tace "Dallah malama tashi anan."

Saida ta zabura ta kalli Ummy da mamaki, mik'ewa tayi jiki na rawa tana kallon Ummyn da ita ma take tashi tsaye, kallonta tayi ita ma tace "Kina nufin yaji ne kika min nan? Hamna mahaukaciyar ina ce ke? Auren naki duka yau kwana ashirin da uku ki ce min wai yaji kikayi? To maza wuce koma gidanki."

Hannu tasa ta shiga murza ido tana kuka tace "Ummy yanzu ko kiranshi ba zakayi ki tambaye shi me ye tsakaninshi da ita ba? Ni wallahi ba zan iya zama dashi ba indai yana tare da wannan tsinanniyar, haka kawai yaje ya jawo min jarfa."

Ita kam dariya ma ta so bata amma saita gimtse fuska, inta fahimta ita ma kamar ta fara son shi kenan, sai dai kuma tana da gaskiya tunda tafi kowa sanin wacece k'awarta ta, dan haka tace "Zo nan."

Saida ta tsaya gabanta tana ta share ido ko hawayen babu Ummy tace "Zan kira shi naji me ya faru, amma idan ya fiki gaskiya Hamna dole zaki koma d'akinki, ba zan yarda kullum ana cewa ni ke d'aure miki gindi kina abinda kika ga dama ba, kin yarda?"

Turo baki tayi tace "Na yarda."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan to, mik'o min wayata."

Kan gadon ta nufa inda ta nuna mata ta d'auko wayar ta bata, ban d'aki ta shiga dan tsarkake kanta ta samu tayi sallah. Bata kai ga danna kiran ba ya shigo d'akin kamar wani ne ya turo shi daga baya, d'aga kai tayi tana kallonshi kallo na fahimta, duk a hargitse yake hatta kayan jikinshi ma.

Shi kanshi tunda tace wai na bar maka gidanka tasa yaji kamar ta soka mishi mashi, kai shi fa wallahi tallahi idan ta sake maganar zata rabu dashi saiya zaro harshenta ya datsashi biyu, ta yanda gobe ba zata sake fad'in haka ba, yo inba ta raina shi ba kan wata yar iska da bata san ma akan me ake magana ba zata fad'a masa hakanen, da marinshi tayi duk

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login