Showing 219001 words to 222000 words out of 325849 words
ganin ta daina kukan yasa shi zagayawa ya kalli abokanshi dake rik'e da bebyn, fita sukayi inda Zeinabu da Soueiba sukayi ta bata baki kan karta yarda damuwar ta kusa illata ta.
*Safiya* na yi ta gama shiryawa dan zuwa ganin Jamila, dama tare suka shirya tafiya dan haka suka fito duk a tare, Hamna na tare da Ummy wacce yau zata fara zuwa aiki, tayi fes da ita kamar tayi bik'i fa haka ma Shureim yasha shiri tsaf da shi, saida Ummy ta bud'a mota ta zauna cikin mota suka k'araso wurin, da girmamawa dukansu suka ce "Ina kwana Ummy."
Kallon Amna tayi tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"
"Lafiya lau." Amna ta amsa, matsowa Ammar yayi kusan Hamna dake rik'e da Shureim ya tara hannayenshi zai karb'eshi, kallonshi tayi da fararen idonta haka kawai ta tsinci kanta cikin jin dad'i yanayi, mahaifin d'anta zai karb'eshi a hannunta, murmushi tayi da ita kanta bata san ya zo mata ba, zata bashi shi cikin had'e fuska Ummy tace "Kawoshi na kusa makara."
Take murmushin fuskarta ya b'ace ta sake kallonshi, wallahi bata san wane irin yanayi ne take ji ba a game dashi, amma dai har k'asan zuciyarta tausayi taji ya bata da Ummy ta k'i yarda ya amshe shi, mik'a mata shi tayi suna kallo ta rufe motar ta tayar ta bar gidan. Amna ya kalla ya kama hannunta yace "Muje."
Suna gaba Hamna na bayansu har suka shiga gaba ita baya, saida suka daidaita ya juyo ya kalleta yace "Dan ubanki ni kike jira na fara gaishe ki kome? Wai ke me yasa baki da wayo ne?"
Saida ta rumgume hannaye ba tare data kalleshi ba tace "Bana da wayon ne, kuma idan kai ka fara gaishe ni miye a ciki indai har kasan darajar mutum."
Da k'arfi ya juyo cikin nasara ya finciko wuyanta had'e da hijabinta ya matse sosai yace "Ni kike fad'awa duk abinda ya zo bakinki, sa'anki ne ni? Tambayarki nake?"
Yanda ya k'arashe da d'aga murya yasa ta rintse ido tace "Kayi hak'uri to, ina kwana."
Turata yayi da k'arfi kanta ya kaiwa kujerar karo, hararanshi tayi shi kuma ya tayar da mota yana baya baya yana fad'in "Shashanci, ita ta raba kanta dani, k'anan nawa ma rabani zatayi dashi, zanyi k'ok'ari na dakatar dashi daga nan, ba zan bari ya ci gaba da faruwa ba, ba zan bari soyayyarshi ta ci gaba da wanzuwa a cikin zuciyata ba, Allah kaine shaida ina ganinshi naji nafi son shi fiye da sauran 'yan uwana, miye laifina a ci? Wane irin virus ne a jikina da har zata nemi nesanta ni dashi? Matsala."
Daga Hamna har Amna sun fahimci abinda ke zuciyarshi ne ya fito, Amna kuma dake kallonshi tuni ta ga idonshi sun fara rikid'a alamar kad'an ya rage ya zubo da hawaye, Hamna ma tasan dalilin Ummy kenan tana so ta nesanta shi da d'anshi ne, sai dai kash gashi daga abinda ya fad'a yanzu ta gane soyayyar yaron ta riga data shiga zuciyarshi, haka suka d'auki hanya tana danna wayarta har suka isa. Tare suka shiga wajen Jamila suka dubata, taji dad'in ganinta ita ma dan haka ta saki jiki suka fara hira, ganinsu ne yasa Zeituna da Soueiba suka ce su zauna anan suje gida su dawo, ita Soueiba tana son yin wanka a tsanake saita dawo, Amna ma shiga tayi wajen awo abinka ga masu abun tuni aka gama mata ta dawo, jiransu sukayi dan dama basu zo da niyyar tafiya da wuri ba.
*Samun* labarin rashin kunyar da tayi a gidan yasa malam Rabi'u tahowa da ita har gidan, yace dole ta basu hak'uri kuma ba zai ba mijinta hak'uri danya maidata ba, duk da babu yara kuma ita kanta Zeinabu likita take kwana wajen Jamila, amma anyi katarin ta zo saboda zuwan colonel da zai kwana d'aya ya wuce *Mali*, gaban Hajia ya zaunar da ita tace "Dan Allah kuyi hak'uri da rashin kunyar dana muku."
Jin wani murmushi da Hajia tayi yasa Maryama d'agowa cikin jin haushi, murmushi ta mata tace "Haba."
Cike da iyayi Hajia tace "Ke ni fa abinda kikayi ko a jikina wallahi, kin tona mana asirin da bamu sani bane, dan haka ni banga abun damuwa ba, ban sani ba dai ko ga ita wacce abun ya shafa."
Ta fad'a tana kallon Husseina, murmushi Maryama tayi ta kalli Hajia tace "Hajia ke babba ce a gidan nan, babu kyau fariya ga d'an adam bare ke musulma, bai kamata ki dinga tsarkake kanki da ahalinki ba, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, ko matan baki isa kiyi shaida akansu ba bare mazan, to wai ma akan me kike cika baki? Tare dasu kike fita? Ko kuma kina bibiyar duk abinda sukeyi ne a wajen? ko kuma a cikin gidan kina saka ido akan lamuransu? Ko d'aya fa ba kyayi Hajia, kuma a hakane kike ganin ya zama wajibi akansu su kare kawunansu? To ubangijin daya hallicemu ma ai muna sab'a masa bare kuma ke 'yar adam."
Mik'ewa Maryama tayi sai malam Rabi'u cikin barbarci da yace "Mari rashin kunyar ce har a gabana? Lallai kin rik'a."
Nuna Hajia tayi tace "Malam ba rashin kunya bane, ita tana ganin kamar iyalinta sunfi k'arfin aikata laifi laifin ma kuma na zina, alhalin bata san tana tare dasu ba kuma suna kewaye da ita."
A hankali Hajia ta sauke k'afa d'aya kan d'aya tana kallonta tace "Ban gane ba? Kinsan me kike fad'a kuwa? K'arya kike wallahi."
Murmushi tayi tace "Babu maganar k'arya sai gaskiya, ya kamata ki farka daga baccin da kike Hajia ki tabbatar kin gano asalin kowane yaro daya fito daga tsatsonki, dan zai iya yiwuwa akwai yara dayawa wanda aka samu kafin aure kamar irinsu *Junaid*."
Zunbur ta mik'e tana kallonta ido a tsaitsaye, da sauri Zeinabu ta dafe bakinta da hannun dama ta daskare a wurin, Husseina Soueiba malam Rabi'u duka sororo sukayi, Junaid kam bai d'auki abin babba ba ganinshi kawai sharri ne, matsowa yayi kusanta yace "Kisan me zaki fad'a Maryama, dan na rabu dake bashi zaisa ki min wannan sharrin ba, ba k'aramin abu bane wannan fa."
Tab'e baki tayi tace "Dan ka rabu dani? To autan maza ne kai da zanyi bak'in cikin rabuwa da kai, kaga malam ka tambayi mahaifiyarka ta fad'a maka yanda komai ya faru, karka tsaya kana zare min ido."
Malam ta kalla tace "Malam mu tafi, zasuji da matsalarsu."
Tashi yayi yana waiwayen Husseina da shi dai yake son neman yafiyarta, suna fita colonel da lieutenant suka shigo tare da Alhaji cikin farin ciki, suna ganin yanayin mutanen wurin kowa yayi sororo ga Junaid yasa Zeinabu gaba yana magana k'asa k'asa yasa lieutenant k'arasawa da sauri wurin Hajia yace "Hajia lafiya? Meya faru duk na ganku haka?"
Colonel ma matsawa yayi kusanta yana karantar tsantsan tashin hankali daka fuskarta yace "Hajia lafiya?"
Dab'as ta zauna kan kujerar da kullum take jin dad'in zama kanta cikin isa da izza, duk yanda numfashinta ya fara barin gangar jikinta saida tayi k'arfin halin kallonshi cikin fitar da numfashi sama sama tace "Husseini..da gaske...ne.Ju...Junaid baaaa..."
Kasa k'arasawa tayi wanda hakan yasa colonel sunkuyar da kai, *wal'iyazu billah* shine abinda ya fad'a ร ransa, kamar an jonata da kuran sai kawai ta tashi tsaye da k'arfinta, hannu ta d'aga sama da niyyar palla masa mari, sai kawai jikinta ya d'auki b'ari hannunta ya fara rawa da k'arfi kamar ta kama wayar lantarki, lieutenant da colonel d'in ne sukayi azamar rumgumata a jikinsu cikin tashin hankali lieutenant "Mu kaita mota."
Da gudu Zeituna ta k'araso tana k'ok'arin rik'eta tace "Ku saketa zamu kamata."
Soueiba ce ta taso da sauri suka kamata su kuma suka nufi mota, ana fita da ita sai asibiti wajen su Ammar, ganinsu ya d'aga musu hankali suma ba kad'an ba, Ammar da Ummy da kuma wata malamar asibiti ne suka rufa kan Hajia aka fara k'ok'arin ceto ranta.
*Awa biyu* suka d'auka kafin su fito fad'a musu halin da take ciki, Hajia kam dai...
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_49_
Ammar ne yace "Cikin sarautar Allah komai ya daidaita, jininta ne ya hau sosai, amma yanzu mun samu mun shawo kan lamarin, ba wata bazarana a yanzu zaku iya komawa da ita gida, akwai magunan da za'a bata ta samu bacci."
Alhaji ne yace "Ammar kana ganin zamu iya tafiya da ita gida tun yanzu? Me zai hana ba zaku barta nan ba ta samu ta huta."
Dafa shi yayi yace "Ba komai Alhaji zaku iya tafiya da ita, kuma ko da wani abu ya faru ma ba gani ba duk da bama fatan haka."
Sallamarta sukayi tare da Jamila ita ma amma sun rigasu tafiya, ko da aka je gida d'akinta suka kaita aka bata magani tasha, ba jimawa bacci ya d'auketa idonta na kan colonel da take matuk'ar son marin fuskarshi, suna ganin bacci ya d'auketa kowa ya sauke ajiyar zuciya, a tsanake Alhaji ya kalleshi yace "Husseini shin gaskiya ne abinda aka fad'a d'in?"
A hankali ya sulale ya durk'usa gabanshi duk da babu hawaye a idonshi amma muryarshi na rawa yace "Alhaji kuyi hak'uri ku gafarceni, kuskure na wallahi, hakan ya faru tun kafin a d'aura aurenmu, ta so na fad'a asan halin da ake ciki amma, Alhaji ina jin tsoron Hajia sosai, tsoron abinda zatayi yasa muke b'oye wannan sirrin har wannan lokacin, amma wallahi kullum da fargaban hakan muke kwana kuma muke tashi."
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya kamo shi ya tashi, kallon idonshi yayi yace "Husseini, ba'a gyara kuskure da kuskure, shiru ba shine mafita ba illa ma ya k'ara haifar da wata matsala, na so ace a lokacin ko ni ka tuntub'a da lamarin dan asan abunyi, abinda kukayi kuskure ne, kuskurenku ma akan kuskure kukayi shi, yanzu kaga me hakan ya haifar? Shi yaron da wane ido zai kalleku?"
A hankali ya d'aga kai ya kalli Junaid dake gefenshi, Zeinabu dama bata tafi asibiti ba saboda tafi Hajia ma shiga tashin hankali, kawai ita nata ya fito fili ne aka gani, k'yar kam idonshi cikin na shi, kallon babu wanda yasan na miye ma kawai suna kallon juna ne, cike da dattako Alhaji ya kallesu dukansu yace "Yanzu dai tunda haka ta faru kawai komai ya wuce, Junaid hak'uri zakayi wannan ita ce jarabawarka, kai kuma kai da ita sai kuyita istigfari wajen ubangiji, abun kuma a bud'e yake cewa yanzu shi ma magajinka bane."
Saida ya sunkuyar da kai yace "Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba."
Saida ya goya hannayenshi baya ya fara tafiya ya fita daga d'akin, da sauri Junaid ya bi bayanshi da alama kuka ya fashe dashi, ajiyar zuciya lieutenant ya sake saukewa mai k'arfi, shima fita yayi tare da Ummy data baro asibitin suka taho tare.
Ko da aka dawo Jamila tace a mata shinfid'a a d'akinsu na yan mata, a lokacin babu wanda ya kula saboda duk jikin kowa yayi sanyi *gwamnatin* gidan babu lafiya, ga kuma zulumin abinda ya faru da mamakin al'amarin, can aka gyara mata ta zauna ita da jinjirinta, basu kula ba saida Jibril ya zo yana tambayar inda take kad'ai aka gano, Soueiba da Husseina ne sukayi ta bata baki amma ta rufe ido ta botsare tace ita fa ta gama zaman gidan shi, k'yaleta sukayi da tunanin idan ta huce sai a mata magana ta koma. Tunda Zeinabu ta shiga d'aki ta kasa fitowa sai dai colonel ya shiga kawai ya fito, sai kuma Zeituna dake kai mata abinci ta aje ta fito. Haka kuma ita ke kula da Hajia tunda ta farka da la'asar, da taimakonta tayi alwala tayi sallah, da hannunta ta bata abinci tasha magani.
Bayan sallah magriba lieutenant ya shirya cikin kakin shi ya fita, oda ya bayar tare da rahoto akan motar cewa a dakatar da ita, kafin a sanar dashi ganin motar wasu abubuwan ya shiga yi, sai misalin *11:40* aka kirashi aka fad'a mishi ga motara hannu d'auke da kaya, nan yayi umarni aka taho da ita har ofishinsu inda ya fito da kanshi bayan anshiga da ita ciki, saida ya gama kallonta ya ga sak kwatancen da Ammar ne ya masa, nan yasa yaransa suka bud'e motar aka fara fito da kayan ciki, dreban na gani ya fara fad'in "Ba fa komai bane yallab'ai, indomie indomie ce sai madara."
Wani kallo lieutenant ya masa yace "Ka bari to mu gani da kanmu."
Pilla pilla lieutenant yasa aka ma kayan nan, sai gashi karton d'in da ake tunanin indomie ce ciki da kwalayan madara an samu tramol a ciki, haba ai sai hankalin dreba ya tashi dan baisan abinda ya d'auko ba, mai kayan aka sa shi ya kira sai ga Jano ya zo ya d'auka kamar yanda aka saba ne, idan aka rik'e kayan ko kuma aka musu awo a caji kud'i masu yawa, sam basu sarara masa ba hannun jami'an tsaro suka mik'ashi tare da dreban, sai dai shi daya rantse baisan menene ba kuma ya fad'i yanda akayi ma har ya d'auko kayan sai suka gamsu, musamman da shi kanshi Jano d'in ya tabbatar musu da babu ruwan dreban, shi ma kuma cewa yayi ba kayan sa bane, abu dai yaja daga an sake dreba Jano kuma yau gashi da kwanan magark'ama.
Da dare tana zaune ita kad'ai a d'akin ta had'e fuska, tunani take irin matakin ma da zata d'auka na wannan cin zarafi da Husseini ya mata, ita zai kunyarta ya wulak'anta a idon duniya, tana kalkad'a k'afa alamar masifa Zeituna ta bud'a k'ofar ta shigo da sallama, saida ta zo har ta aje kwanukan abincin zata fara zuba mata tace "Dakata malama bana so, fice min a d'aki."
Da ladabi ta kalleta tace "Hajia lokacin shan maganinki yayi fa."
"Nace bana so ki fitar min a d'aki." Sake k'asa tayi da muryarta tace "Dan Allah Hajia ki daure..."
Tsaye ta mik'e ta nuna mata k'ofa tana fad'in "Nace ki fita ko, ko saina sa an fitar min dake ne?"
Juyawa tayi cikin sauri sauri ta fita, da harara ta bita duk sai take jin haushin matan ma, kawai ita bata yarda dasu ba, dan haka sai kowace ta fito mata da d'an da ba jininta ba, inba haka ba duk saita kaisu asibiti an gwada uban kowa dan tasan yaran da suka ciyar a banza. Tana cikin safa da marwa Ammar ya shigo da siririyar sallama, tana juyowa ta ganshi ranta ya sake b'acewa tace "Fitar min a d'aki kaji, bana son kowa ya sake shigo min d'aki ina buk'atar zama ni kad'ai."
Rufe k'ofar yayi ya tako da sauri yana fad'in "Hajia ta nayi kewarki fa."
Cakumota yayi ya rumgume da k'arfi yace "Kin tsoratani fa sosai, ban tab'a yarda cewa ana jin k'amshin lahira ba sai yau dana kusa rasaki."
Tureshi tayi daga jikinta cikin tsawa tace "Kana hauka ne? Ammar fice min a d'aki kafin ranka ya b'ace."
Hannunta ya kamo ya zaunar da ita bakin gadon ya fara zuba abincin yana fad'in "Ba zan yarda ki sake min wasa da lafiyarki ba, Hajia dole sai kinci abinci kafin kisha magani, inba haka ba zansa Alhaji ya rik'e min ke mu miki d'ure."
Zaune yayi bayan ya gama zubawa ya d'ebo a cokali ya kai bakinta, k'ank'ance idonta tayi tace "Baka da hankali ne Ammar?"
Kai ya d'aga mata yace "Eh Hajia ta, akan ki mahaukaci ne ni."
"Shin baka fahimtar abinda nake fad'a maka ne?"
Saida ya turo baki yace "Ai ba zan fahimta ba har abada."
Cike da k'aguwa tace "Akan me to zaka nuna ka damu dani bayan nasan ba so na kake ba kamar yanda bana sonka?"
Murmushi ya mata yace "Saboda bana so na rasaki."
Kallon idonshi tayi tace "K'arya kake Ammar, nasan zaka fi kowa murna idan na mutu."
"A'a Hajia, zanfi kowa bak'in ciki." Ya fad'a shima yana kallon k'wayar idonta, cikin taushin murya tace "Me yasa?"
Ba tare daya d'auke idonshi ba yace "Saboda zanyi kewar masifarki, zanfi kowa damuwa na rasa babbar mai yi min fad'a da zagina da kuma yanke hukunci akaina ba tare da shakku ko shawartata ba."
Me Hajia zatayi ba dariya ba, ita kanta ji tayi ta taho mata, bata san me yaron nan yake ji dashi ba da har yake iya tunkararta ya fad'a mata abinda ke ranshi ba tare da shakku ba, ita yake kallon idonta yake fad'a mata wai zaiyi kewar *masifarta*, ba tare data tsagaita da dariyar ba tace "Ammar kai mahaukaci ne."
Yana kallonta yace "Na sani Hajia, haka kuke fad'a kullum."
Lomar ya mik'o mata sai kawai ta harareshi tace "Ban ci nace ko."
Langab'e kai yayi yace "Hajia jan ajin ya isa haka mana."
Wata dariyar ta sakeyi ta kamo hannunshi ta zura lomar bakinta, kallon bakinta yake yanda take tauna abincin yasa yake hango k'uruciyarta, abun mamaki shine karb'an abincin da Hajia ta dinga yi daga hannun Ammar kai kace dama can haka suke, shi kanshi sai yake jin abun na daban bai saba ba, duk da bata ci sosai ba haka ya aje ya bata magani tasha, tana sauke kofin daga bakinta ta kalleshi, haka kawai taji kamar kunyarshi na son lullub'eta ba gaira a dalili, aje kofin tayi a hankali ta d'ora goshinta kan gwiwarshi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ammar kaga abinda kawunka ya min ko? Kaga irin k'ask'ancin daya ja min? Kana ganin irin tozarci da zubar da mutumcin daya min? Wane irin mataki ne zai d'auka akan shi? Akan me zasuyi min haka saboda kawai ina son kare iyalina."
Cikin murmushi ya k'ara jawo kanta saman cinyarshi yana wasa da yatsun hannunta yace "Hajia na fahimci duk k'ok'arinki na son karemu ne daga aikata abinda bai dace ba, amma kuma tsananin da kikayi ne