Showing 63001 words to 66000 words out of 325849 words

Chapter 22 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

540

Middle Ads

da haihuwa ba."

Jibril da shi dai tun shigowarsu yaji gabanshi sai fad'uwa yake, yana kallon tsohon kuma sai yake ganin wani yanayin mahaifinshi a tare da mutumin, baisan dalili ba amma yaji tsohon ya shiga zuciyarshi daga *kallo d'aya*, tunda suka fara musayar yawun nan yake jin baya jin dad'in abinda Ammar d'in keyi, yanzun ma mik'ewa yayiya kama hannun Ammar ya matse sosai ya kalli tsohon yace " Dan Allah kaka kayi hak'uri, yana da zuciya ne."

Malam rabi'u shima sai yanzu ne ya kalli Jibril d'in kallo na tsanake, shi kanshi gabanshi ne ya fad'i, Jibril dake rik'e da hannun Ammar fita yayi da shi waje inda malam ya bi Jibril da kallo, wata zufa ce yaji tana tsatsafo mishi ba gaira babu dalili, take ya fara tuna abubuwan da yayi zamanin k'uruciya wanda har yanzu wannan banzar d'abi'ar bai wani barta ba sai dai in bai samu dama ba, sai dai ya kasa tuna wace uwar ce ta haifa mishi wannan yaron? (Ko kuma ta haifa maka wannan jikan ba, wato shi aiki ko na alkairi ko na sharri dama kana iya mantawa idan kayi, amma wanda kayi wa baya mantawa), Amar da Junaid da kaka ne suka dinga bawa malam hak'uri suna tausarshi, da k'yarsuka shawo kanshi bayan Junaid ya nuna mishi yana so su taimaki rayuwar Mari wacce ke tallar kanta ga kowane namiji yana biyanta, sosai ya jima yana mishi nasiha cikin girmamawa, gamsuwa malam yayi hakan yasa yace ya amince da buk'atarsu, amma indai da gaske yake to dole ya turo iyayenshi dan suyi magana ta manya, alk'awari suka mishi kan zata turo manyansu kafin daga bisani suka mishi sallama suka taso suma.

Jibril dake rik'e da hannun Ammar suna fitowa ya fizge hannunshi, bud'e mota yayi ya fito da gorar (bidon) ruwa ya bud'e ya sunkuya yana dararawa a kanshi, saida suka k'are yayi cilli dashi yasa hannu aljihu da niyyar fito da abinda zai goge fuskarshi, lalitarshi ce ta fara fitowa dan haka ya rik'e a d'aya hannun ya sake mayar da hannun aljihu zai fito da shi, kai mai tsautsayi da Allah ya aiko ka kana ganin bak'i ne a garin sai kuwa wani matashin saurayi yayi wup da lalitar ya sura a guje, da sauri da kuma mamaki suka kalli juna shi da Jibril, haba ai saiya mik'awa Jibril mouchoir d'in ya fito da wayarshi a gaban aljihu ya damk'a mishi, da mamaki Jibril ya ke kallonshi yace "Me zakayi Ammar?"

"K'ure mishi gudu zanyi." Cewar Ammar dake hangen yaron nata gudu.

*Kai jama'a*๐Ÿ˜‚

*Sai A shafi na gaba muji wai da gaske artawa zaiyi ko kuwa zai rabu da wannan daya tari aradu da kai.*

_Rashin comment, hummm, saura kad'an ku daina jina._
05/06/2020 ร  20:21 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_9_


Kamar a almara Jibril ya hangi Ammar ya zage k'arfi ya palla a guje ya bi bayan yaron, tuni hankalin jama'a ya koma kansu ana kallo, yanda yake gudun kamar wanda aka ce idan ya fad'i ya rasa gasar shiga soja kenan, shi kanshi gudun da akeyi saiya birgeka, dama kuma haka Allah yake hallitarsa, idan ya maka kyau sai kaga komai kayi saiya maka kyau ko kuma wani yaga kyanka, duk gudun yaron nan saiga Ammar ya cimmasa har yana neman take shi, k'afa yasa ta baya ya harbi nashi k'afafun hakan yayi sanadiyar fad'uwar yaron warwas a k'asa, kafin ya ankara yasan fad'uwa yayi Ammar ya shak'o wuyan rigarshi tare da bank'are hannunshi ta bayan wuyanshi ya murd'e ya amshi lalitar, ba tare daya sakeshi ba kuma ya izo k'eyar shi gaba izuwa inda suka bari, mutane dake kallon k'aramin kafce wasu na tunanin su bayar da hak'uri su raba, sai dai tunanin su yafi basu cewa soja ne duk da cikin wani yadi yake kalar ruwan madara shara-shara, dan haka meya kaisu shi ma yaron tsautsayi ne da kuma k'arar kwana, yaron da yaga Ammar na dawowa dashi fashewa yayi da kuka yana so ya durk'ushe ya bashi hak'uri amma ya k'i barinshi ma ya kai k'asan, cikin kuka dake nuna tashin hankali yake fad'in "Dan Allah baba na kayi hak'uri, wallahi yunwa ce tasa nayi maka k'wace, ka rufa min asiri kayi min rai."

Ko saurarenshi baiyi ba har suka zo inda Jibril ke tsaye mamaki ya gama kashe shi, suna zuwa Amma ya jingina ga koma ya saki yaron ya kalli Jibril yace "Ban hankici (handkiciep) na."

Mik'a masa yayi yana kallon yaron da tsoro ya gama bayyana a tare da shi kamar ya ga mala'ikan d'aukan rai, yana cikin goge zufar dake tararowa kanshi zuwa fuska da wuyanshi ya kalli yaron yace "Durk'usa."

Kamar marar k'ashi a jiki haka ya lauye ya durk'ushe yana sake fad'in "Dan Allah kayi hak'uri baba na, wallahi ni ba b'arawo bane tsautsayi ne da yunwa, dan Allah magajina ka bashi hak'uri kar ya kaini prison (magark'ama)."

Ya k'arashe maganar da duban Jibril, idon nan sun kad'a sunyi jawur ya kalli yaron da kyau yace "Kai, kasan ko wanene ni?"

Da sauri ya girgiza kai yace "A'a."

"To meyasa duk garin nan ka rasa wa zaka figi kayanshi sai ni?"

K'uri ya masa da ido yana kallo jikinshi banda rawa babu abinda yake, hannu ya d'aga kamar zai mareshi yace "Da kai nake kana jina ka min shiru."

Cikin kukan firgici yace "Wallahi yunwa ce tasa, kwana biyu ban ci komai ba, kuma nayi bara ban samu abinda zan ci ba shiyasa, dan Allah kayi hak'uri ka gafarce ni."

Fuska a had'e yace "Ina iyayenka suke?"

Ba tare daya tsagaita kukan ba yace "Ba yan garin nan bane, suna zinder ne, almajiranci suka kawo ni."

A lokacin ne su Junaid suka fito sun gama tattaunawa, Amar ne yayi saurin ciro wayarshi ya duba mai kira, saida gabanshi ya fad'i ganin Hajia ce, Junaid daya fahimta yace "Karka d'auka tunda yanzu zamu koma, gwara musha giyar ta dubu sai ayi kankat."

Wayar ya kashe tare da jefata aljihu a lokacin ji sukayi kawai Ammar yace "Shiga mota zan mayar da kai gidanku."

Pik'i-pik'i yayi dan shi dai bai bai yarda gidansu zai kaishi ba, amma tsoro yasa ya mik'e yana d'an rakub'ewa da d'ar-d'ar har ya shiga inda su Junaid suke, saida suka d'auki hanya Amar ya tambayi Jibril meya faru? Jibril da yake tunanin wai Ammar wane irin mutum ne? Anya wannan ba Allah ne ya dubesu ba ya k'i bashi aikin sojan da yake so, girgiza kai yayi yace "Kai dai abar kaza cikin gashinta kawai."

Junaid ne yayi dariya a harshen fransanci yace "Dan Allah ka bamu musha mu ma, meya faru?"

Nan Jibril ya canza harshe shima ya fad'a musu, ba jimawa kuma sun iso gidansu kaka, ko cikin gidan basu shiga ba sukayi alwala suka shiga masallacin dake kusa da su sukayi sallah, nan kaka tace su shigo su ci abinci, basu mata musu ba suka shiga ciki suka zauna kan tabarma, shinkafa ce da miyar taushe (tauhe ๐Ÿ˜‚) aka kawo musu, sai ruwan sanyi a gafe suna korawa, duk da Ammar sai wani had'e fuska yake amma har ranshi miyar ta birge shi, tare da almajirin nan suka ci har suka ida sukayi hamdala, nan suka musu sallama suka tafi tare da cewa sai sun dawo, daga nan suka sake d'aukar hanyar komawa gida.

*Gidan roumji*

Suna sauka suka fahimci babu motar yaransu samari wanda suke jinsu kamar wasu garkuwarsu ne idan suna tare da su, mamaki suke ko lafiya, amma sai Labaran yace watak'ila ko motarsu ta samu matsala dan k'arfen nasara babu tabbas, a haka aka bar maganar aka shiga abinda ya tara kowa, har akayi addu'a aka gama aka kwashe awa d'aya babu su babu labari, nan aka fara kiran wayoyinsu amma a lokacin suna hanya akwai matsalar hanyar sadarwar yasa kiran ma baya shiga, wannan abu ya basu mamaki hankali kuma ya fara tashi, lieutenant da ranshi ya b'ace ne yace kar wanda ya sake kiransu, ai babu yaro a cikinsu, kuma da idonshi ya ga motarsu biye dasu har cikin garin nan, dan haka ba musakai ne ba zasu iya k'arasowa k'asa ai, idan kuma hakan ya gagara ai zasu iya kiransu su fad'a musu, dan haka yace su k'yalesu kawai su zuba musu ido, amma basu bari Hajia taji me ake ciki ba, duk da kowa ya bar maganar a zahirance amma haihuwa ta shiga tsakaninsu da b'acin ransu, kowa da abinda yake tunani a ranshi a game da nashi yaron da sauran yaran, a hakane fa har lokacin sallah azahar yayi, lokacin ne Hajia tace ayi haramar tafiya gida dan ita ta gaji da zaman k'auyen nan, a lokacin taji abinda ke wakana, kafin tace komai ne ta kira lambar shalele amma bai d'aga ba, tana sake aika wani kiran kuma sai aka ce wayar kashe, lokacin ne ta rufe ido ta dinga surfa masifa a cikin gidan har akayi sallah hankali ba kwance ba, kuma abinda yafi damun lieutenant da Sa'ada shine cewa da take wannan d'an banzan Ammar d'in ne ya d'auke mata shalele, ita bata ma san ina ya kaishi ba, inda Zeinabu ta tabbatar lallai Hajia bata k'aunar nasu yayan saina Sa'ada suma kuma d'a d'aya take so, Soueiba kuma ta k'ara yarda bata son duk wani jini daya fito daga jikin sarakuwarta Husseina, Alhaji kuma yana ji ya zuba mata ido dan in yace yayi magana zata mishi rashin mutumci ne cikin mutane, dan haka kawai yake kallonta har tayi ta gama, a haka dai tasa suka sake dawowa gida dan ganin meke faruwa.

Tashin hankali, labarin da suka samu a gida ma shine ai tare kuka fita dasu, cikin masifa Hajia tace "Kuma basu dawo ba?"

"Basu dawo ba Hajia." Cewar Nana mai aiki, cire gyalenta tayi da jakarta ta aje ta zauna kujerar falo tana rau da kanta, duk wani motsin Sa'ada saita kalleta, hakan yasa ta kasa motsawa daga inda take saboda gudun karta zargeta, sallah la'asar kad'ai tasa kowa ya gusa daga falon dan gabatar da sallah, haka gidan ya ci gaba da zama shiru Hajia kuma na zaune a falo ta kasa ta tsare sai taga shigowarsu, inda Alhaji ke zaune a bayan gidan iskan 'ya'yan itatuwa na kad'a mishi.

*Saida* wannan yaron ya nuna mishi har k'ofar gidansu saidai kamar suna k'uryar gari ne, yaron na fitowa Ammar ya ciro lalitarshi ya fito da kud'i, jaka goma goma guda uku ya bashi yace "Wannan kayi sana'a dashi, idan kuma na sake ganinka a irin wannan banzar rayuwar wallahi saina lahira yafi ka jin dad'i, kasan dai da aljanuna zasu iya nuna min duk inda kake ko?"

Da sauri yaron ya dinga girgiza kai alamar eh kamar k'adangare, jinjina kai shima yayi alamar ah to ka ma shiga hankalinka kafin ya sake had'e fuska yace "Idan kuma ka shiga gidanku ka ce da iyayenka shugaban *sojojin niger* (general) ne ya dawo da kai yace ka zauna gida, idan har suka sake mayar da kai..."

Saida ya kalli gabanshi ya d'an cije leb'e ya kalli yaron yace "Ka fad'awa mahaifinka da kaina zan sauke mishi kafad'a ta hannun hagu."

Da sauri yaron yace "Babana ya rasu, nan daga mamata ne sai k'annan Baba na."

Zaro mishi ido yayi cikin d'aga murya yace "To su k'annan baban na ka basu da kafad'a ne?"

"Suna da." Ya fad'a a muryar kuka, wani jinjina kai yayi alamar jin dad'i yace "To ka fad'a musu haka."

Yana fad'a ya d'aga gilashin motar ya fizgeta da k'arfi ya tayar da k'ura suka koma baya dan su hau titi, yaron da baki sake saida ya ga b'acewar motar ya juya gida, tunaninshi wannan ba wai aljanu ne dashi ba, shi da kanshi ne aljanin, amma inba haka ba taya kawai zai d'auko ni ya dawo dani? Yanzu karatun nawa fa da nake duk da yunwa bata vari na ma fahimta? Ya malaminmu zaiyi? Ya k'annan babana da kakata zasuyi idan suka ga na dawo? Zasu d'auka tserewata nayi ai tunda dama banso nayi nisa da uwata ba, da wannan tunani barkatai ya shiga cikin gidan, duk abinda aka fad'a mishi ya fad'a sai dai bai fad'i gaskiyar dalilin rabuwarsu ba, gidan tunda suka ji yace shugaban sojoji ma suka sha jinin jikinsu, kakar yaron wacce ta haifi babansu ce tace ma autan ta ai a kwaso duk yaran dake sauran garuruwa su zo nan suyi karatun, dama can yawan gidan ne yasa suka rage ta hanyar turasu almajiranci.

Su Amar banda dariya babu abinda suke, amma Ammar kamar baisan sunayi ba sai tuk'i da yake, a *Ague* sukayi sallah magriba suka sake wucewa, wannan karan ba jimawa suka shigo cikin gari sai dai anata sallah isha'i saboda tsakanin lokacin dama ba wata tazara ake samu ba, sannan gashi Ammar ba wani gudu sosai yake ba da zai kawosu gida cikin k'ank'anin lokaci, suna kaiwa *immeuble Gago* ya taka birki ya juya yana kallonsu, Junaid dake gaba ne ya washe baki saboda hango mai gasa kaza da yayi ya kalli su Amar yace "Kai 'yan uwa, babban yaya fa kaji zai siya mana mu ci, kai Allah dai ya k'ara girma yayanmu."

Wani jan kallo Ammar ya mishi yace "To jikan kura, kazar uwar wa zan siya muku? Sai kace na d'auko karuwa a mota zan tsaya siyen nama a hanya?"

Jibril ne ya kece da dariya yace "Wato ita karuwa idan aka d'auko ta sai an siye nama?"

Ko kallonshi baiyi ba sai gani da sukayi ya bud'e ya fita ya zagaya mazaunin Junaid, da sauri Junaid ya fito ya dawo mazauninshi ya tayar da motar suka fara tafiya, cikin masifa Ammar ke fad'in "Shegu 'yan banza, ai dama zura muku ido nayi naga mai hankalin da zai iya karb'ar tuk'in nan a hanuna, ashe duk k'ananan marasa mutumci ne ku."

K'wafa yayi sai Amar da yace "Yi hak'uri yaya, ni wallahi in so na karb'a amma a raina kuma nace watak'ila dan kana babba ne shiyasa ka hutashe da yan uwanka ababen soyuwarka."

Wata ashar ce ya malmalo irin ta yan zamani yace "Na soya mata..."

Gyara zama yayi ya jingina tare da lumshe ido yace "Ku tanadi abinda zaku fad'awa tsofaffin can, dan ni nan banga abinda zai sani magana ba."

Kallon kallo suka fara, ai kuwa sai suka fara shiga k'irk'iro labarin da zasu fad'a a gida wanda zai dace da hankali, suna tsaka da haka Ammar da idonshi ke rufe yace "Ya kamata kusan cewa da Allah yana so ku zama sakarkaru to fa daya halliceku babu baki, akan me zaku musu k'arya? Duk cikinku akwai wanda zai tsireku ya rataye? Ko kuma akwai mai wutar da zai saka ku a ciki? Kunga, ban yarda na biku ba saida na tabbatar aikin alkairi muka je yi, amma kuna so ku mayar da kanku lusarai kamar ba maza ba, a hakane yanzu kuke so kuyi aure, to ya zakuyi da matan?"

Cikin turo baki irin na shagwab'a Junaid yace "Yanda kowa yake yi da su mana."

Tsaki Ammar yayi ya bud'e ido ya kalleshi yace "Shin ko kasan a cikin maza akwai mata-maza? Sannan akwai muna-maza, kamar yanda ke akwai mun rako maza duniya, to zaku kasance d'aya daga cikin ukun nan ne in kuka ci gaba da haka."

Amar ne yace "Ammar zafa mu baka mamaki wallahi, ai namiji zai amsa sunanshi ne a lokacin da yake iya ciyar da matarshi, yake mata sutura iya iyawarshi, yake kula da lafiyarta da addininta, sannan yake gamsar da ita a shinfid'a."

Murmushi yayi wanda Junaid dake gaba ne kad'ai ya gani kafin yace "To ko ita gamsarwar da kake magana a kai tana buk'atar zarra, sai ka zama namijin gaske kafin ka gamsar da yan matan yanzu, idan kuma ba haka ba wallahi kaine zaka wahala har ka zubar da hawaye, dan irin kayan da suke anfani dasu wajen gyara jikinsu sunfi k'arfin tunaninka."

Jibril ne ya d'an lek'o kai ya dafa kafad'ar Ammar yace "Babban yaya ince dai in zamuyi aure kai zaka zama malamin mu?"

Bige hannunshi yayi ya juyo a harzuk'e yace "Saboda d'an iska ne ni?"

Kwashewa sukayi da dariya, suna tsaka da dariya yace musu "Billahil-azeem duk wanda ya fad'a musu k'arya saina tona asiri, dan ni ba zan yarda ayi k'arya dani ba."

Da haka dai suka iso gida suka danna ham (๐Ÿ˜‚) mai gadi ya bud'e musu suka shiga, a wajen ajiye motoci suka paka ta su kafin suka fito cike da gajiya, cikin wani takon izza da k'asaita Ammar ya nufi b'angaren su, Junaid ne yace "Ammar ka zo mu fara shiga ciki dan Allah, ni nafi son ayita ta k'are."

Tsaye yayi ya juyo ya kalleshi yace "Kai ne uban tafiyar ai, ka fara shiga ciki ka fara d'aukar naka rabon, ni daga baya na shigo bayan nayi wanka."

Jibril ne yace "Amma dai da mun fara shiga a mana bala'in, in ya so daga baya ma huta gajiyar."

Rai had'e yace "Na ce wanka zanyi ko."

Amar daya d'an lek'a kusa da falon Hajia ne yace "Ka zo muje dan Allah, wallahi nasan mu suke jira dan ayi magana."

Juyawa yayi ya fara tafiya yana fad'in "To duk wanda ba zai iya hak'ura na fito daga wanka ba kuce su sameni a ban d'akin sai muyi maganar."

"Kana wankan?" Cewar Jibril yana zaro ido, ba tare daya juyo ba yace "To meye a ciki, su d'in iyayena, ku kuma yan uwana ne maza, hallitar iri d'aya ce, ko kun kalla babu abinda zaku ji a ranku, wannan tsohuwar ce ma kawai bana so ta ganni babu kaya, kallon data min ina yaro ma ya isa haka, taje ta kalli mijinta."

*Ma Sajida sai kin taimaka min

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login