Showing 87001 words to 90000 words out of 325849 words
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π _*MASOYA NA*_π
_Bismillahir rahamanir rahim_
π³πͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_7_
Da sauri Abbas ya rik'o ta dan yasan me zatayi, juyowa tayi ta kalleshi ganin ya had'e rai sosai yasa ta fincike daga rik'on daya mata ta fice a falon da sauri tana hawaye, girgiza kai yayi yana sake jadadda kai kukanshi ga ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta, cikin sanyin jiki ya zauna inda Abba ya kalli uwar d'aki data fara magana kamar haka "Amma yallab'ai sai naga kamar gaskiya matar waziri ta fad'a, dan ko ni dake uwar gidan takawa kuma uwa ga sarkin yanzu bansan da wannan magana ba, amma abun mamaki wai har kuna cewa ma burinshi kenan."
Kallonta Abba yayi, shin nesan da sukayi da juna na tsawon lokaci ne yasa *Hafsatu* mantawa da waye shi? Ko kuma sanyin da yayi ya rage tijara ne yasa har zata iya kallonshi ta fad'a masa wannan maganar? Wane irin raini ne wannan suka d'ora mishi haka harda matar da bai ma gama saninta ba ko a fuska? Me zaiyi musu ne ma wai? Ya jima yana mata wannan kallon mai tattare da nazarin abinda zan fad'a miki kafin ya nisa yana kallonta ido cikin ido yace "Hafsatu kinsan dai da nine a gaba da mijinki ko? Sannan kinsan da mijinki ma kallo na yake kamar mahaifi tun bayan rasuwar iyayenmu? Sannan nasan kinsan cewa kaf yaranshi ina da hakk'in da zan iya yanke hukunci a kansu ba tare da sanin shi kanshi margayi ba? Dan haka ki saurara min tare da d'aga min k'afa, kar kisa nayi abinda za'a buga sunana a mujalla shafi na farko da zata fito safiyar gobe."
K'wafa yayi tare da juyawa ya kalli liman yace "Liman, kana da wata matsala idan aka d'aura auren nan a yau?"
Girgiza kai yayi yace "Babu ko d'aya ranka shi dad'e."
Imran ya kalla yace "Kai fa Imran? Kana da matsala da hakan?"
Shi ma girgiza kai yayi cikin ladabi yace " Babu Abba."
Mik'ewa yayi tsaye tare da fad'in "Duk mai farin ciki da auren nan ya fara shiri yanzun nan, dan ana idar da sallah la'asar zan d'aura auren Imran da 'yar wajen liman Safiyya."
A wannan karan kam uwar d'aki ba wai tsananin son da take sai Imran ya auri 'yar waziri bane yasa ta shiga rud"u da firgici illa yanda take ganin za'a nuna mata iko da d'an data haifa, kuma wai ba ma uban daya haife shi ba, wannan ne yasa ta mik'ewa ita ma kamar zararra tace "Me? Aure? Zaka wa d'an nawa ba tare da amincewata ba? Wallahi baka isa ba, *Mus'ab*, karfa kaga muna d'aga maka k'afa, can ma kawaici ne a matsayinka na yayan mijinmu, amma ka sani shi kanshi yanzu baya raye, dan haka wallahi ba zan tab'a yarda ka had'a auren Imran da wannan yarinyar ba yar matsiyata, indai ni na haifi Imran kuma ta hanyar aure."
K'arama a cikin matan takawa ce ta kalleta a nutse tace "Haba uwar d'aki, sai naga kuma ko takawa baya raye ai akwai alak'ar data had'a ki zumunci da danginshi ko da kuwa ba kya so, wannan alak'ar kuma ita ce 'ya'ya, ki nutsu dan Allah sai a bi komai..."
Da hannu ta dakatar da ita da cewa "Dakata min malama, 'yan bak'in ciki kawai, ai dama nasan ba son yaya na kuke ba shiyasa hakan ba zai dameku ba, to ke ki bada d'an ki mana sai a had'a shi da wannan bak'in irin, amma ba ni ba."
Imran da tunda ta fara magana yake kallon yanayin Baffan nashi, sai jimk'e hannunshi na hagu yake yana ji kamar zai kai duka, inda yake d'an lumshe idon shi yana bud'ewa duk da haka saida sukayi ja, yasan zaman nan ba zai k'are musu da kyau ba, dan haka ya kalli uwar d'aki a sanyaye yace "Umma, dan Allah ki zauna muyi magana."
Cikin b'acin rai tace "Wane zama kuma zanyi, Imran a gabanka za'a tozarta mahaifata a nuna min ban isa da kai ba, aure? Ka manta aurenka na farko ma haka aka d'aura maka shi ba tare da ina so ba, shine yanzu ma zaka sake wani auren saboda mahaifinka, me kake so da ni? Kana so dole saika nuna min ka fi son mahaifinka a kaina? Imran uwa fa ba wasa bace, karka manta da haka, amma idan kace zakayi to ba zan hanaka ba, kaje kayi ga wurin nan."
Cikin tsananin rashin jin dad'i ya d'an girgiza kai, har zuciyarshi yana son auren yarinyar baisan me yasa ba, ga kuma abinda mahaifiyarshi take fad'a, d'agowa yayi ya kalleta a nutse cikin taushin murya yace "Umma, wallahi ba wai na fifita Abba a kanki bane, ba kuma zan bi umarninsa bane dan na b'ata miki rai, wallahi ni da kaina na shawarci takawa akan maganar auren da nake so na k'ara, kuma shi ya bani shawara ga 'yar liman nan, nasan ba zai min zab'in da zai cutar da ni ba shiyasa ma na amince da gaggawa, amma ina neman afuwarki idan ranki bai miki dad'i ba, kuma duk da haka ina rok'on alfarmarki da ki barni nayi auren nan Umma, shine cikar burin takawa, Umma idan kina so ma zaki iya bani wani umarni kema na miki alk'awarin zanyi duk abinda kika saka ni indai bai sab'awa shari'a ba."
Duk maganganunshi babu wanda ya shigeta bare har yayi tasiri a zuciyarta, amma kam maganarshi ta k'arshe tayi armashi, dan haka ma ta d'an saci kallon liman da shima ya kalleta a fakaice sukayi murmushi, saida ta gyara tsayuwa tace "Ka tabbatar zakayi duk abinda zan saka ka?"
Da ladabi yace "Eh Umma, insha Allahu zanyi indai baifi k'arfi na ba."
Kallon Abba tayi wanda ke tsaye yana kallon ikon Allah kafin ta kalli sauran kishiyoyinta, tab'e baki tayi sannan ta kalli Imran tace "Ina so ka auri 'yar waziri."
Da sauri Imran ya k'ura mata ido yana kallo, liman ya kalla ya kalli Abba dake tsaye har yanzu, kallon waziri yayi tare da matarshi da ya ga ita tuni harta washe hak'ora, a cikin ranshi kawai ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fi musibati, wak-lufli khairan minha."
Kallonta yayi yaga ta kafeshi da ido, babu yanda zaiyi haka yace "Na amince Umma, Allah yasa hakan ya zama alkairi a gare ni."
Sai lokacin ta nutsu ta zauna tana kallonshi tace "Kaga kenan sai a d'aura auren tare ko?"
A hankali ya kalli Abba da kamar ka k'yarta mishi ashana ya kama da wuta, d'auke kanshi yayi daga kallonshi saboda tsoro da kwarjini ya kalli liman, cikin girmamawa yace "Ku gafarce ni Liman, idan babu damuwa ko za'a iya d'aga auren nan har nan da sati d'aya, dan bana so daga rasuwar takawa ace nayi aure kuma har mata biyu a lokaci d'aya."
Da fara'a liman yace "Babu komai mai martaba, wannan ma shawara ce mai kyau, sannan sati kamar gobe ne idan da rai da lafiya, Allah dai ya nuna mana yasa alkairi."
Haushi ne yasa Abba barin falon rai b'ace inda Ammie ta bi bayanshi, harsu Imranatu da su Naseer ma bin bayansu sukayi, Abbas ma cikin kamala ya fita tare da Imran d'in inda suka k'ara tattaunawa akan lamarin, daga nan shima gidan kakannin na su ya nufo wanda suka rasu shekaru da suka wuce yanzu sai yan uwan mahaifiyarsu ne a gidan da iyalensu, tun a k'ofar gidan ya had'u da Abba da su Bashir cirko cirko suna kallon Abba daya jefa jakarshi a mota, da mamaki Abbas ya kalli Ammie da ita ma take kallonshi jiki a sanyaye yace "Ammie lafiya? Ba dai tafiyar ce ba?"
Cikin k'asa k'asa da murya tace "Nima tun d'azu abinda nake tambaya akai kenan ya min shiru."
Abba daya rufe boot d'in mota zai shiga mazaunin matuki ne yace "Duk mai tafiya ya zo mu tafi, wanda ba zashi ba kuma saiya zauna."
Aabbas ne yayi saurin cewa "Abba ka barshi to zan tuk'a mu zuwa airport d'in, bara na kira Sameera."
Da sauri ya shiga kai tsaye kuma d'akin da suke sauka ya wuce, kwance ya sameta akan gado, shi farko ma mamaki ta bashi daya ganta wai tana kuka, amma da yaji harda shashek'ar kuka take wai ita an mata magana sai ta ma bashi haushi, daga k'ofar d'akin yace "Malama ki taso mu tafi idan kin gama kukan to."
Shiru tayi kamar ba tasan ma dashi a wurin ba, cikin dakakkiyar murya yace "Nace ki taso mu tafi ko, Abba ne a waje ke jiranmu fa, kinsan kuwa a kan ki ba zan yarda na sake b'ata masa rai ba."
Ai kamar jira take sai ta d'ago cikin kuka ido sun mata jawur tace "Sai ka tafi mana, kasan ba zaka b'ata masa rai a kaina ba meyasa ma ka zo inda nake, ku tafi ku barni babu inda zanje ni."
Ko takalmi bai cire ba ya shigo d'akin ya d'auki gyalenta dake kan gadon ya rik'e d'aya hannun kuma ya kama damtse ya jata, tuburewa tayi tana fad'in "Wallahi ka sake ni, ka rabu dani na fad'a maka babu inda zanje fa."
Har sun fito fili gidan taga da gaske janta yake sai kawai ta kalli hannun nashi ta sunkuya ta gartsa masa cizo *(karo na biyu kenanπ)*, Abbas da saukar hak'oran kawai yaji baisan sanda ya saketa ba yace "Ashhhhh."
Kallon hannun yayi har jini ya kwanta abinka ga farar fata, a fusace ya kalleta da niyyar zabgeta da mari ma'ana tarihi ya sake maimaita kansa, sai kawai ta zabga da gudu ta koma d'akin ta mayar da k'ofa ta rufe, cikin k'arajin murya take fad'in "Na ce ba zanje ba, ka rabu dani mana ko ana dole ne?"
Dafe k'ugu yayi ya sauke ajiyar zuciya, a ranshi yake ayyana gaskiya badan suna cikin mutane ba, to fa daya b'alla k'ofar nan yau saiya tab'a lafiyar jikinta, dan har yanzu tana wasu abubuwan ne saboda tab'arar da ita da Ammie keyi, amma ba dan haka ba ai abinda tayi yanzu ko Raihan tayi shi saika mata tsinannen duka bare ita uwarta, wata uwar oda da Abba yayi daga waje yasa Abbas zabura ya juya ya kalli k'ofar, sake dawo da kallonshi yayi ya ga k'ofar a rufe, matsawa yayi jikin k'ofar yace "Zan tafi, idan kinga dama ki tabbata a nan, amma ki sani cizona da kikayi bashi kika d'auka kuma zan rama."
Daga cikin d'akin tace "Ka rama mana, ko kashe ni zakayi ba zanji ciwo ba indai har zaku tafi ku barni, dan wallahi saina ci uwar matar nan ko kuma na k'ona garin nan."
Wata zuciyar ta fad'a mishi hushi ba naka bane tunda kasan halin kayanka, a hankali ya saisaita nutsuwarshi ya d'an had'a kanshi da k'ofar d'akin yace "please Sam kar kiyi abinda bai dace ba, dan Allah na rok'e ki, kinji."
Cikin kukan daya tabbatar daga zuciyarta yake tace "Ba zan iya ba Abban Ameer, matar nan fa mahaifina ta kalla ta fad'a mishi mak'aryaci, kana ganin na zama 'yar halak idan har na rabu da ita?"
Wata odar ya sake ji wacce ta sashi sake fad'in "Meera ki bud'e k'ofar nan ki fito mu tafi, Abba yana jiranmu kuma kinsan shi ma ranshi a b'ace yake."
Ba tare data daina kukan ba tace " Ba zan biku ba Abban Ameer, kawai ku tafi ku barni anan."
Yasan tunda ta fara ba zata sauko da wuri ba, gashi kuma har ga Allah shi ma baida niyyar sake kwana anan saboda akwai muhimmin zaman da zaiyi a daren yau d'in, dan haka yace "Shikenan zan tafi na barki anan, amma ki min alk'awarin ba zakiyi fad'a da matar nan ba."
Shiru tayi sai kukan da take rerawa har yanzu, a hankali ya sake cewa "Please, do it for me, karki manta cewa ni mijinki ne, sannan kin min alk'awarin yin duk abinda zai faranta min raina."
Har yanzu shiru babu alamar zatayi magana, dan haka ya juya ya fita yana sake tattare gyalenta dake hannunshi, yana zuwa Abba bai bari ya amshi tuk'in ba, saida suka fara tafiya Ammie ta tambaya ina autarta? Yana fad'a mata tace ba zata taho ba ta kalli dake tuk'i kamar zaiyi ihu tace "Dan Allah ka aje ni na koma wajenta, gobe saimu dawo tare da ita."
Wani wawan birki ya taka daya sa su tsorata, sauke jajayen idonshi yayi a kanta wanda yasa gabanta dukan dubu uku uku, da sauri tayi k'asa da kanta hakan yasa Abba cewa "Ki zab'a to, idan har na ajeki anan sai dai kuyita zama ke da ita, tunda abun na ku iskanci ne."
Tun daga lokacin babu wanda ya sake magana a cikin su har suka isa airport suka shiga jirgi suka sake d'agawa, a haka suka kai gida tafiyar babu dad'i ko kad'an.
*Bayan tafiyarsu*
Tun bayan tafiyarsu da kwana biyu Ma'arufa da Ma'aruf suka zo Abuja a motar abokin Ma'aruf, shi da kanshi ya zo har k'ofar gidan wajen mai gadi yake tambayar ko yallab'ai yana nan? Kasancewar abubuwan da suka faru yasa Abbas d'aukar ma'aikata wanda suka san aikinsu yasa mai gadin cewa "Lafiya kake neman Alhaji?"
K'aryar da yayi cewa shi yaron yallab'ai ne yasa mai gadin cewa "To ka kira shi mana kaji inda yake."
Cikin son lauyewa yace "Eh kuma fa hakane." Daga haka ya juya ya bar k'ofar gidan, amma rashin sanin inda zai samu bayani akan Abbas na gari ko bayanan yasa ya fara sintiri a unguwar dan sanin ta yanda zasu fara, yana ganin lokacin da aka fita da yara idan zasu tafi school kuma yana ganin lokacin dawowarsu, haka kuma yana ganin shigar Saleem gidan wanda a wannan lokacin ke yawan sintiri gidan duk dan son samun kusanci da Raihan, idan zai zo haka yake kashe ma su Khalifa kud'i sosai sannan ya kawo musu da sunan tsaraba, faran faran yake nuna musu a fuska yayin da k'udirinshi kuma mummuna ne, kuma duk wani motsinshi Fadila ita ma a hankalce take da shi, sai dai har yanzu Raihan ta k'i yarda su keb'e daga ita sai shi bare harya fad'a mata wani abu da zai sa ta fahimta, a hakane washe gari kwana uku sai ga motar su Abbas sun dawo daga basraba wanda hakan ya wa Ma'aruf dad'i kuma ya hanzarta zuwa ya d'auko Ma'arufa a gidan da suka sauka.
Yaran sunyi farin cikin dawowar iyayensu da kakaninsu, amma basu ji dad'i ba da aka ce musu mahaifiyarsu bata taho ba, bayan sallah magriba Abbas ya shira tare da Abdul suka fita a motarshi, duk da yana sauri ya dawo dan akwai taron da zai shiga da compagninshi na motoci k'arfe *09:00* am saboda wasu manyan bak'in da suka zo bai hanasu tafiya a hankali ba suna hira, cikin minti ashirin suka isa asibitin kud'i wacce d'aya daga cikin yaran *ABBASIYA* ne mamallakinta, bayan sunyi parking ne Abbas ne ya kalli Abdul yace "Ka jirani ina zuwa."
Cikin mamaki da fargaban abinda ya kawosu asibiti Abdul yace "Dady lafiya ko? Waye ba lafiya? Kai ne?"
Murmushi ya masa yace "Bani bane, kuma kowa lafiyarsa k'alau, kawai dai na zo ganin wani ne a ciki."
Saida ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "Ok Dady, a fito lafiya."
Jinjina kai yayi ya fita daga motar ya shiga ciki Abdul na kallonshi harya b'ace mishi, bayan ya shiga ne yake fad'awa *Dr Kabir* sun zo tare da yaron da za mishi gwajin jini, kuma kamar yanda ya fad'a baya so yasan da an deb'i jininshi ne dan ayi wani abu da shi, saida ya sake tabbatar mishi da babu matsala, saida yayi kira a waya ba jimawa ya datse kiran kafin suka fito tare, Abdul na ganinsu ya fito daga mota cikin girmamawa ya gaishe da Dr Kabir, amsawa yayi cikin raha kafin Abbas ya kalli Dr Kabir yace "Muje na gani ko?"
Da girmamawa yace "Yes sir, zamu iya tafiya."
Wani b'angare na musamman suka nufa inda Abbas yace Abdul ya zo su tafi, suna cikin tafiya wani mutum ya fito daga cikin gurin da zasu shiga, saidai mutumin a matuk'ar firgice yake wanda zaka ita gani k'arara, suna kusa da juna shi da Abdul sai kawai yayi saurin dafe hannunshi tare da sakin 'yar k'ara, da sauri Abbas ya rik'e shi yana kallonshi yana fad'in "Son lafiya? Meya faru?"
Murmushin yak'e yayi yace "Nothing Dady, wani abu ne naji ya soke ni a hannu na." Ya fad'a yana d'aga hannunshi tare da kallon wurin, da sauri dr Kabir ya matso yana fad'in "Oh my goodness, yana zubar da jini fa."
Juyawa Abbas yayi ya kalli mutumin da yayi kamar baisan tsiyar da suke ba saboda tafiyarshi kawai yake, da nuna reaction d'in takaici yace "Kabir waye wannan? Ina kuka samu mahaukata irin haka?"
Cikin jimami dr Kabir yace "Sorry sir, maybe ko ya karb'i result d'in shi ne kuma sakamakon ciki ne ya d'aga mishi hankali, ko kuma dai wani ne babu lafiya ana neman jini ba'a samu a lab d'in mu ba."
Kama hannun Abdul yayi suka shiga ciki da niyyar ya duba shi, suna shiga ya zaunar dashi akan kujera, wata yar roba ya d'auko mai haske wacce tsayinta ba zai wuce d'an yatsa manuniya ba ya tara jinin, Abdul na kallo baiyi tunanin komai ba, saida ya gama ya shafa mishi magani a wurin tare da rufe mishi ciwon dan dama komai a tsare take ba wani babban ciwo bane, fitowa sukayi duk da haka saida ya bashi magani dan kawar da duk wani zargi yace yasha saboda kar yayi zazzab'i ko hannun yayi kumburi, a haka suka d'auko hanyar dawowa gida, wannan karan Abbas ne ya tuk'a motar har suka iso layinsu.
Kamar yanda Salma ta fad'a musu haka suka aiwatar da komai, Ma'arufa na ganin motar Abbas ta danno cikin layin ta taho a guje ta shiga gaban motar har saida ta bugeta kuma taji zafi, take ta fad'i