Showing 30001 words to 33000 words out of 325849 words

Chapter 11 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

508

Middle Ads

yace "Kenan kana so ka ce sam baka jin zafin cin amanar da Zeenat ta maka? Kenan ko ka tuna cewa aminin yayanta ne ya lalata ta sannan ya mata ciki wanda ta zo da shi gidanka baka jin komai?"

Tapi ya dinga yi yana dariya yana fad'in "Amma gaskiya kayi k'ok'ari yaya, kaga kuwa idan da ni ne haka ta faru dani da tuni zuciyata ta buga, dan ni ba zan iya zaunawa a duniyar nan ba ina tunanin matar da ta shigo da cikin wani k'ato gida na ba, to taya ma haka zata faru? Matata ta sunna na haskota a ido na tare..."

" Stop it Saleem, ya isa."

A hankali Saleem ya kalli yayanshi da tuni hawayen nan dake mak'alewa suka fito, rufr idonshi yayi zuciyarshi na bugawa da k'arfi yana ji kamar ya mangare Saleem d'in, a hankali ya bud'e ido ya sauke a kanshi ba tare da yace komai ba ya mik'e daga kujerar, kasancewar har yanzu yana da yar matsala wajen tafiya saboda tun lokacin da yayi paralysé yasa bai iya tafiya da kyau, cikin jan k'afa d'aya ya shiga cikin falo ya bar Saleem nan, da kallo ya bishi harya b'ace kafin ya rik'e k'ugu, har k'asan zuciyarshi yana jin zafin ganin d'an uwanshi a wannan halin, halin da ba kowa yayi sanadiyar shigarshi ba sai mace, tabbas Zeenat ta cutar da su sosai, domin kuwa a dalilinta ne har yanzu yayanshi baya iya tafiya daidai, a sanadin abinda ya faru dashi ne yasa mahaifiyarsu data rage musu kwantawa jinya wacce dama take tare da hawan jini, suna ji suna gani ta mutu da bak'in cikin abinda Zeenat d'in ta musu, yanzu gashi shi kanshi Abbacar d'in baya da aiki sai tunanin ta da zubar da hawaye, shi kad'ai ne yake gani yaji dad'i tunda babban magajin nasu yana Gombe acan yake harkokinshi tare da iyalinshi, sai in ya zo duba su kawai ko kuma su sunje.

D'auke hannayenshi yayi d'aga k'ugu yana d'an cije leb'e da wani irin yanayi a tare da shi mai wuyar fassarawa, ko cikin gidan bai shiga ba ya sake shiga motar shi ya bar gidan, duk da dai yasan Abbas shima kuma ya sanshi, amma hakan ba shine zaisa ya fasa abinda yayi niyya ba, domin kuwa duk da abinda ya faru sam su Abbas basu raba alak'arsu da Zeenat ba, ko ba komai dai yar kawunshi ce wacce ita ma ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar shi.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Da dare suna zaune dukansu kamar yanda suka saba kullum bayan sun gama cin abinci, hira suke sosai ana dariya sai dai yaran tsakaninsu suke hira haka ma manyan, ana haka Sameta ta kalli Abbas da suka fi kusa tace "Sir, ina da magana fa da kai."

Ameer dake ta mak'ale mishi a wuya yana ci gaba da wasa da shi yace "Ina jinki, amma kafin nan sau dubu nawa na fad'a mi ki bana son sunan nan?"

Turo baki tayi tace "To ai idan na fad'i sunan ne saina dinga tunawa da baya, lokacin da bana iya kallon idonka kullum kaina k'asa ina fad'a, good morning sir, good evening sir, sir your food is ready, sorry..."

Bata k'arasa ba ya dakatar da ita yace "Heee, ya isa to naji, fad'a min abinda zaki fad'a min, idan ba haka ba zaki sa Ammie ta ji kina tuna baya yanzu zata fara mita akan bautar da ke da akayi a baya."

Dariya tayi tace "Kai kuma shine baka so ko a tuna baya? Saboda kasan baka da gaskiya."

Saida ya sumbaci bakin Ameer yace "Indai ba fad'a kike so muyi ba a daren nan to ki fad'i abinda zaki fad'a."

Tab'e baki tayi tace "Tunda na tuna baya kuma ai kaima kasan dole muyi fad'a, dan kasani dai ba tsoro nake ji ba."

Sai lokacin ya kalli k'wayar idonta cikin k'ara k'asa da murya yace "Na gano ki munafuka kawai, wato neman hanyar fad'a kike dan na biye miki muyi bala'i a daren nan, dan kinsan a k'arshe kowa zai kwana d'akin shi ne ko kuma ki kawo mana Ameer a tsakiyarmu ko, to ba zanyi hushi ba kuma ba zanyi masifar ba can kiji da abarki."

Tashin su Naseer da iyalensu ne yasa suka kallesu Abbas na fad'in "Ya dai malamai naga kun mik'e?"

Bashir ne yace "Yaya wallahi bacci muke ji, zamu je mu kwanta ne saida safenku."

Hararanshi yayi yace "Ku d'in ne zaku kwanta tunun yanzu?"

Wani kallo Sameera ta masa tace "Yallab'ai, miji da matarshi yace bacci yake ji, meye na ka a ciki dan Allah?"

Bilkisu ce tace "Yafi so muyi ta zama anan ke kuma saboda gobe da ace ya makara bai tashi ba yace surutun mu ne ya hanashi bacci."

Kallonta yayi yace "To ba surutun naku ke hanani baccin ba? Musamman ke da wannan mai..."

Ya fad'a yana nuna Sameera wacce ta tilasta mishi yin shiru saboda kallon data masa, fuska a had'e tace "Ka k'arasa mana kai nake sauraro."

"Shikenan kawai abar maganar." Ya fad'a yana sunkuyar da kai, mayar da kallonta tayi garesu sukayi ban kwana kusan duka yaran saida suka zo suka bata hannu suna fad'in saida safe, su Abba ma tashi sukayi suka musu saida safe, Abbas ne cikin shafar kai ya mik'e ya tari gaban Ammie da Ameer yace "Ammie na ce ko zaku tafi da Ameer wajenku ne yau dai kam ya tayaki hira har kiyi bacci."

Wani kallo ta masa tace "Ban gane ba? Ni na fad'a maka ina son ya tayani baccin? Me zaisa ba zai kwana tare da yan uwanshi ba kamar kullum?"

"Eh to Ammie, da yake wai naga kamar baku tashi bacci bane yanzu." Yana fad'in hakane dan yasan Ameer da rigima zai iya cewa a wajensu zai kwana, ko kuma idan suka samu sab'ani da uwarshi tace anan zai kwana tare da su, shi kuma yau kam yanda yake jinshi babu abinda zai hanashi sukuwa idan har ya samu filin nan.

Kallon Ameer tayi wanda keta latsar wayar Abbas bai ko san sunayi ba tace " Wannan sarkin had'iyar ne zan tafi dashi ya kwana wuri na, ai kafin gari ya waye duk ya cinye min katakon dake d'aki na."

Su Raudat da suma suke shirin tashi ne suka bushe da dariya, sai Raihan da murmushi kawai tayi wanda ya bayyanar da hak'oranta, Abba ne ya kamo hannu Ameer d'in yana fad'in "Yanzu takwaran nawa ne kike fad'a ma wannan maganar? Lallai ma matar nan kin samu wuri dayawa, aboki muje d'aki na ka kwana kaji ko."

Abbas ne yace "Kuma fa Abba madarar ma da yake tashi yasha cikin dare yanzu ya daina, tunda yayi yawu kunga ai baya zauna wuri d'aya ba."

Ammie ce ta tab'e baki tace "Ai ina d'aga mishi k'afa ne ma saboda yana da sunan na ka, amma badan haka ba ai daya gane kurenshi."

Kamar daga sama Khalifa yace "Wai ke da duka mazanki sai kinyi fad'a ne? To idan kika b'ata mana dukanmu ya zakiyi kenan?"

Da yatsa Ammie ta nuna shi tace "Kai rufe min baki a wurin nan, ina shirin bacci ne zaka sani cacar baki, kai idan za'a kwana a hantse ba gajiya zakayi ba, parrot kawai."

Hararan ta Khalifa yayi yace "Zan kama ki ne tsohuwa."

Nuna Abbas tayi tace "Kaga tsohon nan bani ba."

Kallonta Abbas yayi yace "Ammie maganar mata ce fa, ai da Ammienshi kika kira tsohuwar ko."

Wani kallo ta masa tace "Kai yanzu waccen ta maka kama da tsohuwa a ganinka? Ko dai ba kya duban madubi ne?"

Abba ne yace "Kai kuwa ina zata kira 'yar gwal da tsohuwa, ai sai kai data raina kuma da bata haifa ba, amma ai abin a fili yake kowa yasan waye tsoho a cikinku."

Sun jima tsaye wuri d'aya suna wannan gardamar da cacar bakin kafin kowa ya nufi makwancinshi, da k'yar Abbas ya karb'i wayarshi a hannun Ameer wanda yace da ita zai tafi ya kwana, saida Sameera ta shirya cikin kayan bacci ta nufi fita dan zuwa d'akin Abbas, a k'ofa suka had'u wanda ya kasa jira yake ganin kamar ba zata zo ba, yana shigowa ya rufe d'akin ya rage hasken wutar d'akin, rumgume juna sukayi a cikin kunne ya rad'a mata "Kinsan da nayi kewarki?"

"Uhmmm." Ta fad'a cikin mak'oshi, cikin salo ta fara tsotsar bakinshi har tayi nasarar kama harshenshi, salon da take masa yasa ya fara jin kamar bashi ba, ana cikin haka ta raba bakinsu ta zura harshenta a kunnenshi ta fara wasa da shi a ciki, wata sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da k'ara k'amk'ameta, daga nan komai ya canza abun ya girmama zuwa kan gado.

*Bayan awa biyu* dukansu bacci ne ke son d'aukar su, cikin taushin murya Abbas yace "My Meera ina son haihuwa dayawa har cikin zuciyata, shin kina ganin nan gaba zaki iya haifo min yara shida? Kinga idan aka had'a da wanda muke da sai su zama goma sha biyu cif."

Zunbur ta tashi zaune tana kallonshi tace "Da gaske kake yallab'ai? Amma fa ni na d'auka zamu barsu ne daga guda shidan, kaga nima na huta ai."

Lumshe ido yayi ba tare daya tashi zaune ba yace "Wallahi iya gaskiyata nake fad'a miki, ina so naga kin haifa min yara dayawa, amma idan ba zaki iya ba saina..."

Kafeshi tayi da ido tace "Sai kayi me? Ka k'ara aure kake nufi?"

Bud'e ido yayi a kanta yace "Eh mana, tunda ke ba zaki iya ba."

Gyara zama tayi ta d'auki pillow ta soma dukanshi dashi tana fad'in "Je kayi auren dan Allah ga wurin nan, wallahi kana aure zan koma basraba da zama, ba zan k'ara saka kaina a had'ari ba saboda kai tunda kuskurenka ne."

Da k'yar yayi sa'ar rik'o ta ya had'a da jikinshi sosai ya sake lumshe ido yana murmushi, ita kam k'ok'arin raba jikinta da nashi take amma ya matseta sosai, masifa take tana fad'in "Rabu dani malam ka tashi ka koma d'akin ka, 'ya'yan ne ba zan haifa ba kaje kayi auren, naga ma ko Salma ai zaka iya dawowa da ita ta haifa maka yaran tunda har yanzu baka saketa ba, humm, wallahi kana bani mamaki mutumin nan, na ce ka saketa ka ce kayi tun tuni, na tambayeka saki nawa ka mata amma ka gagara fad'a min, nasan ma baka saketa ba saboda kana sonta har yanzu, watak'ila ma kana zagayawa wajenta ban sa..."

Da k'arfi ya matseta sosai ya danna bakinta a nashi yana mata wata mahaukaciyar tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi saida ya saketa da kanshi kafin ya kalleta da idonshi kamar zaiyi bacci yace "Mai sunan mamana surutunki ya fiki yawa, idan kika fara bala'i ba kya tsayawa ko numfashi ki sauke."

Zata yunk'ura ta tashi ya sake matseta yana shafa gashinta yana fad'in "Shiiiii, yi bacci kinji ko, yi baccin abinka."

Kamar zatayi kuka tace "Amma fa na fad'a maka tun tuni cewa zamuyi magana."

Cikin magagin baccin dake fizgarshi yace "Ki bari da safe zamuyi maganar kinji."

"Maganar fa na da mahimmanci."

Shiru ya mata baice komai ba hakan kuma yasa ta tashi zaune tace "Uhum wato ba ma ka da lokacina ko, to gaskiya ban yarda ba tashi muyi maganar, dan idan nace sai gobe to wuri ya k'ure."

Yanda take jijjigashi ne yasa ya bud'e ido ya sauka daga kan gadon ya nunata da yatsa yace " Allah badan ina tsoron hushin Ammie ba dana tsula miki d'an karan duka a daren nan, wai Sameta yaushe ne zakiyi hankali ke? Har abada ace ba zaki bar mijinki ya huta ba kamar wata..."

Bai k'arasa ba ya juya ya bar d'akin, dan dama maganganun daya fad'a mata ya fad'a ne dan karta bishi d'akin shi saboda ya santa da zuciya, shiyasa ya tak'aita daga nan, yana shiga d'akin shi ya kwanta amma saiya kasa bacci, dan basa raba shinfid'a inba rigima sukayi ba ko sunyi fad'a, tunanin halin da take yanzu yakeyi kafin daga bisani ya fara tunanin Salma, tabbas ya saki Salma tun ma ranar daya gane da sihiri ya aureta, sai dai bai fad'a ma kowa ba inba Abba ba, amma da ana saki billion daya ma salma, da wannan tunanin bacci ya d'auke shi.

Sameera ma haushin maganganun daya fad'a mata ne suka sakata yin kwanciyarta tana huci, ta kuma san safiya nayi zai fara bata hak'uri yana cewa dan ta barshi yayi bacci ne ya fad'a mata hakanan, da haka ita ma bacci ya d'auke ta.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Tunda Harira ta koma gida ta samu Baaba mai wake ta fad'a mata ta samu aiki a gidan tsohon mai gidanta, bud'ar bakin Baaba cewa tayi "Karki raina min hankali mana Harira, wane irin aiki ne mutanen nan zasu baki bayan abinda ya faru? Kawai ki fad'i gaskiya idan karuwanci zaki fara, koda yake ma ba wannan ne karo na farko da zaki fara ba, amma ki sani wallahi ni babu ruwana duk abinda kika je kikayi can ke kika jiyo da matsalarki."

Bata damu da abinda ta fad'a ba haka ta ci gaba da shirye shiryen tafiya, da dare kuma ta tara k'annan ta a d'akin su ta fad'a musu zatayi tafiya, Karime ce mai wayon cikinsu dan haka tafisu shiga damuwa, sosai Harira ta rarrasheta tare da nuna mata zata je yin aiki ne dan su dinga samun abinci suna ci suna k'oshi, sannan ta dinga biya musu kud'in makaranta akan lokaci, sannan ta cire dubu uku ta basu a kud'in da Sameera ta bata tace ta b'oye karta yarda Baaba ta gani, haka kuwa akayi haka suka kwana da tunanin wayewar garin gobe.


*Mu had'e a shafi na gaba insha Allah.*
29/05/2020 à 11:10 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


*Wannan kyautar taku ce*

_My Heenat_
_My BK_
_Aunty Aishan Umma_
_Mamienmu_
_Maman Annur (ma chérie)_
_Momyn Dady_
_My Hawwa_
_Sweet Hawwer_
_Sis Chappa_
_Mamar Hassan_
_Yar Baba (yar tsohuwa😜)_
_Rahila_
_Voisine Ruky_


_Auntynmu *Madame Dakoro*, jinjinar ban girma tare da fatan alkairi zuwa gareki, hak'ik'a samun masoyiya kamarki abun alfahari ne ga kowane mutum mai zuciya, alkairi yana da dad'i komai k'ank'antarshi, farin cikin da kika saka *habibiyata* yasa naga ya dace nima na mik'o godiyata zuwa gareki , domin kuwa duk wanda zai farantawa wani na kusa da kai, to hak'ik'a kai ya farantawa, da wannan nake miki addu'a Allah ya sama rayuwarki albarka, Allah ya jik'an mahaifa, Allah ya albarkaci rayuwar 'ya'yanki, Allah ya k'ara yalwata miki, Allah ya k'ara dank'on soyayya tsakaninki da mijinki, Allah ya saka miki da gidan aljanna, wannan k'ok'ari da kike Allah ne kad'ai zai iya biyanki, fatan farin ciki *mdm Dakoro*._👍


🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_4_



*Tunda safe* Abbas ya shirya saboda tafiyar data kama shi dolenshi zuwa k'asar *Belgium*, a wannan lokacin yasan Sameera na kitchen dan in har yana gari da kanta take had'a mishi abin break, dan haka ya kira da téléphone d'in dake kitchen d'in, tafi kusa da wayar dan haka Razeena na matsowa zata d'auka ta kalleta tace "Bari na duba."

Tana d'orawa a kunne tace "Hello."

Murmushi ya saki kamar tana gabanshi yace "Uwar gida sarautar mata, daga kanki an gama mulki na kowane fanni, matar Abbas kuma k'anwar Abbas sannan garkuwar Abbas, uwar 'ya'yan Abbas kuma wacce ke mulki a zuciyar Abbas, farin cikin gidana, na ce ko zan iya ganinki a part d'ina yanzun nan?"

Duk da kalamanshi sun bala'in fasa kanta kuma taji dad'i sosai har zuciyarta, amma dayake daren jiya ya b'ata mata rai sai ta dake tace " Why not? I'm coming."

Saida ya sake kashe murya yace "Takawarki lafiya 'yar sarki jikar sarki k'anwa ga sarki mai mulkin garin *Basraba*."

Aje wayar kawai tayi kafin ta kalli Razeena tace "Ki kula da sauran aikin, ina zuwa yanzun."

K'ofar falon tasa makullinta ta bud'e ta shiga, wani katafaren falo ne daya gaji da kyau da tsaruwa, duk da tayi mamakin ganinshi zaune akan kujera yana d'aura takalminshi k'afa ciki bak'ak'e sai shek'i suke da d'aukar ido amma saita sake had'e rai ta rumgume hannaye tana kallonshi, d'ago kai yayi ya kalleta har dariya na kusan kubce mishi, amma dariyar da zaiyi itama rigima ce zai b'allowa kanshi dan haka yayi shiru, har ya gama d'aure takalmin ya mik'e tsaye yana ci gaba da kallonta ya kuma d'auki jakarshi bak'a ya d'ora a kafad'a, tabbas yayi kyau ya kuma birgeta, dan gaba d'aya bak'ak'en suit d'in daya saka sun zabge mishi shekarunshi, gabanta ya tako ya tsaya yana kallonta yace "Are you stil angry with me?"

Kai ta d'aga mishi alamar Eh, dan haka ya kamo hannunta ya marairaice yace "Sorry mai sunan mama na, tafiya zanyi yanzu bana so na tafi kina hushi dani, please kiyi hak'uri ki manta kinji."

Wani kallo ta masa ta zage hannayenta tace "Abban Raihan wai me ya sa yanzu kake min haka? Sam yanzu baka da lokaci na, jiya fa magana na ce zanyi da kai amma ka k'i ban dama, amma yanzu ka tsaya gabana kana fad'a min wai zakayi tafiya."

K'asa yayi da kanshi yayi shiru saboda baida hujjar kare kanshi, ya sani shi kanshi yanzu ya zama buzy sosai, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai gabatowar zab'e, duk da baya siyasa amma yana da ruwa da tsaki a harkar sosai ta yanda ya kan zama haka, kallonta yayi yace "Amma ai nace kiyi hak'uri ko."

Cikin hassala tace "Amma ai hak'urin jiya ne ka bani, kuma ban hak'ura ba har sai ka fad'a min me ka so fad'a a k'arshen zancen ka."

"Na fa riga da na sha maganin zama dake Meera, kin daina wahalar dani yanzu." Shine abinda ya fad'a cikin ranshi, amma a fili saiya shagwab'e yace "Dan Allah ki yafe min, tafiya zanyi fa na fad'a miki, kinsan kuma ance tafiyar hali, ba lallai na dawo garekkkk..." Bata bari ya k'arasa ba ta rufe

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login