Showing 195001 words to 198000 words out of 325849 words
kayanta tayi saurin barin d'akin kafin ya fito, tana zuwa d'akinta ban d'aki ta shiga ta saka rigar wanka sannan ta fito, madafa ta shiga ta dafa ruwan zafi masu yawa kafin ta juye a bokiti ta shiga dasu d'aki, tana shirin shiga ban d'aki taji ya shigo d'akin, garin saurin shigewa ban d'akin yasa bokitin ya bugi k'ofar ban d'akin ruwan suka zuba a k'afarta, sakin bokitin tayi tare da sakin k'ara lokaci d'ayakuma take furta Inna lillahi wa'innailaihi raju'un, da gudu ya k'araso ya fitoda ita yana kallon fuskarta cikin fad'a yace "Meye haka? Kina haukane? Wa yace ki fito daga can?"
Hijabinta tasa tana goge hawaye, tausayinta ne yasa shi rumgumeta yana shafata yace "Yi hak'uri to, amma me yasa kika taso? Ba zaki iya kula da kanki ba, ko baki yarda dani bane?"
Girgiza kai tayi dan haka ya kama hannunta suka shiga ban d'akin, da kanshi ya had'a mata ruwan ya kalleta yace "Zaki iya ko na taimaka miki?"
Girgiza kai tayi alamar a'a, barinta yayi ta gyara kanta tsawon lokaci kafin ta kammala ta fito, kwantar da ita yayi yaja mata bargo, kallon fuskarta yayi yana murmushi mai tsadar gaske yace "...
*Comment*
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
โช{T . N}โช๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl
_Bismillahir rahamanir rahim_
_42_
"Nagode, aljannata."
Murmushi ta masa mai tafiya da imanin mutum kafin ta fara lumshe ido, sumbatar goshinta yayi tare da gyara mata bargon sannan ya kwanta gefenta, bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita, amma shi bai samu damar yin baccin ba sai durmiya da yayi tunanin rayuwa a sanda yake wanke zanin gadon da yaji matsa shi kanshi, yana wankin yana tunanin waccen ranar ma da halak d'inshi ce da shi zai wanke zanin nan, amma baisan waya wanke ba tsabar masifa. Yasan da babbar matsala a gaba idan asirin abinda ya aikata ya fito, amma a shirye yake da duk wanda zai tuhume shi, yana da hujjjojin kare kanshi ko da ba'a gamsu ba. Ko ya take? Ita ce tambayar daya ma kanshi, nan ma zurfafa tunani yayi sai yaga watak'ila tafiyartata zama alkairi a gare shi, tunda ya auri k'anwarta, hakan zaisa ya mayar da hankalinshi kan matarshi. Amma me yasa Ummy ta shiga firgici sosai daga yana son duba kankana? Me yasa daya anbaci ciki duk suka rud'e kamar dai cikin ne da ita? Akwai wani abu! Shine abinda zuciyarshi ta fad'a masa, da wannan tunanin bacci b'arawo yayi gaba dashi.
Tun *08:00* na safe colonel ya gama haramar tafiya shi da yaranshi masu tsaron lafiyarsa, yayi sallama da kowa sannan ya fito, a lokacin Ammar ya zo sukayi sallama, colonel zai shiga mota mai gadi ya taho da sauri ya gaishe shi, amsawa yayi kafin ya mik'e daga rusunawar da yayi ya bawa Ammar wata takarda yana fad'in "Wannan wani ne ya bayar yace a baka."
Karb'a yayi ya bud'e ya fara karantawa ba tare da yace mishi komai ba, wani shegen murmushi ya saki kamar an bashi katin shiga aljanna, ganin haka yasa colonel tsayawa yace "Yaro na ya dai? Lafiya ko?"
Ba tare daya daina wannan murmushin ba ya kalleshi yace "Lafiya lau tonton, wani k'aramin d'an daba ne zai min iskanci, amma zan nuna mishi na fishi iya buru'uba."
Yana fad'a ya tunkari hanyar komawa b'angaren shi yana fad'in "Za muyi waya tonton."
Cike da bala'i colonel yace "Da kyau yaro, karka ragamar duk uban da yace zai taka ka, a shirye muke muyi shari'a da uban ko waye, kaje Allah ya tsare."
*Da sannu halin kowa zai fito*
Yana shiga d'akinshi ya wuce ya d'auko makulin mota da wayarshi ya fito, ba dan ta fito daga d'akin ba a lokacin da ba zata san fitarshi ba, amma yana ganinta saiya jawota jikinshi yana kallon fuskarta yace "Matarmu zan fita, ki kula da kanki sannan ki ci abinci idan kin dafa, karki saka dani kuma karki jirani, ba zan dawo da wuri ba."
Tsoro ne ya fara bayyana a fuskarta tace "Lafiya yah Ammar? Ina zaka je?"
Shafa kumatunta yayi yace "Ba komai, zan dawo amma ba da wuri ba."
Yana fad'a ya saketa ya tunkari k'ofa kamar zai tashi sama, da kallo ta bishi sai gabanta da taji yana d'an fad'uwa, ba komai ta gani a idonshi ba sai bala'i, tana jin tsoron amsa gayyatar katin masifa ne yayi daga gurin wani, ita kam ina zata saka kanta da tashin hankalin bawan Allahn nan? K'arasawa tayi ta zauna kan kujera ta zuba tagumin zaman jiran tsammani. Jikinshi har rawa yake ya matsu ko ya isa ofishin, tunda ya cije leb'e ya kasa sakinshi sai k'yaci da yake yafi dubu, to wai shi Jano zaiyi k'ara? To ai ya ma raina masa hankali da baiyi k'ararshi wajen sojawa ba ko jendarme, sai wajen masu saka kakin police, jar uba! Da wannan bala'in ya isa wurin har gaban inspecteur d'in daya shirya sulhunta tsakaninsu da kanshi, dan baya so rikicin yayi girman da sunan gidan Gaga zai b'ace.
Daga zaman rashin mutumcin da yayi kamar zaiyi kwance a kujerar tare da d'ora k'afar dama a ta hagu yana kallon kowa da wutsiyar ido zaka san babu arzik'i, kuma k'irirs yake jira ya ta fara zazzage kwandon bala'in daya d'ebo, inspecteur d'in ne ya kalle shi yace "Malam Ammar, wannan ya shigar da k'ararka akan dukan daka mishi, sannan akwai tuhuma da ake maka ta cewa kana anfani da kakin soja alhalin kai ba soja bane, shin me zaka ce a game da hakan?"
Saida yayi murmushi yasa babbar yatsarshi a baki sannan yace "Idan shi wannan mahaukaci ne ai ku da hankalinku, a ina kayan suke? Wurin wa ya gani?"
Kallonshi Jano yayi yace "K'arya zan maka, kai kasan baka isa ba wallahi."
Da k'arfi ya taso daga kwanciyar da yayi kan kujera ya nuna inpecteur d'in yace "Yallab'ai da kai nake magana, ka fad'a mishi karya sake saka min bakinshi, inba haka zan zubar mishi da hak'ora kuma a gabanka wallahi."
Kallon Jano inspecteur d'in yayi da ido ya mishi alamar yayi shiru sannan ya kalli Ammar yace "Malam Ammar, ya fad'a mana ba kawai kakin ne jikinka ba har da bindiga, rik'e bindiga baga jami'in tsaro ko kuma wanda ke son kare kanshi ba shi ma saida lasisi babban barazana ce a cikin al'umma, taka doka ne da idan aka kama mutum za'a hukuntashi, amma idan kana da lasisi da takardar izinin rik'eta saika nuna mana hujja, idan babu zamu iya mik'a al'amarin gurin su sojawan sai suji da kai."
Saida ya d'an buga teburin gabansu yace "Da kyau, haka nake so ai dama, so nake muje wurin manyanku ta yanda za'a bi min hakk'ina na k'azafin daya min, yace wai ina saka kayan soja, to ni mahaukaci ne ko me? Dan ina son zama soja bashi ke nuna zan uya anfani da kayan ba na firgita mutane, dan haka idan har aka tabbatar k'arya ya min ni kuma zan shigar da k'ararshi na cewa da yayi na saka."
Kallonshi inspecteur d'in keyi da mamaki, bala'i da d'umu d'uminshi, Kai ba zan iya ba wannan har ni yasa cikin rigimar, dan haka yace "To shikenan munji, yanzu akan dukan daka mishi a baki har ya fito da jini, anci tararka ta 15 000."
Wata harara ya dalla ma Jano yace "Matsiyaci, ai da bara ka koma."
Kallon insp. d'in yayi yace "Yallab'ai, gaskiya bana da kud'i, kawai muje mataki na gaba."
๐ _Sis a haka kike son shi ko?_
Wani kallo Jano ya mishi ya d'an saci kallon wandonshi daya kama shi sosai har ana ganin shatin wayarshi da alamun kud'i, amma wai baya da kud'i. D'aure fuska insp. yayi yace "Malam Ammar, muna son sulhunta matsalar nan ne ta yanda ran kowa ba zai b'ace ba, ka biya wannan kud'in ku bawa juna hak'uri tare da alk'awarin kiyaye gaba, shikenan kowa ya tafiyarshi."
Zaman farko ya sake yi ba alamar wasa yace "Da gaske na ke fad'a maka banda kud'i, meya kamata nayi?"
"Sai mu rufe ka, idan aka zo belinka sai a biya tarar." Ya fad'a ba alamar wargi, murmushi ya masa yace "Bismillah to, ina so dama na shiga ciki na kwana ko d'aya ne, dan bana so har zamani na ya k'are a tarihi na ace ban shiga gidan maza ba."
Insp. d'in ne yace "To ai idan kana son shiga gidan mazan na k'warai sai kayi babban laifin da zaka shiga hannun mazan."
Kallonshi yayi yana murmushi yace "Indai nine ai zan aikata wata rana, zaka gani a jarida ma."
Wurga ido yayi irin kai ta shafa kafin ya kira wani cop yace ya shiga da shi ciki, saida aka karb'e komai na shi kafin ya iza k'eyarshi gaba, saida ya juyo ya kalli Jano yace "Tsinanne kawai, ai zan fito ne karka bari mu had'u da kai, sakarai mata-maza."
Juyawa yayi ya kalli insp. yace "Kar a kashe min waya ta saboda masoya na zasu iya kira na a kowane lokaci."
Har ya bud'e baki zai mishi magana sai kuma ya zura kai ya tafiyarshi dole ya k'yale shi, yau kam shi ya ga tijaja, shi in ba masu shan k'waya ba bai tab'a had'uwa da irin wannan mutanen ba, kallon Jano yayi ya bashi hak'uri tare da cewa idan anyi belinshi zasu nemeshi dan a musu tsakani, godiya ya mishi ya tafi shi kanshi zuciyarshi ta cika fal da tsoron sake had'uwa dashi d'in, dan yana da tabbacin Ammar da d'an ta'adda ne to ba zaiji wuyar yin k'unar bak'in wake ba, dan shi wani lokacin tsabar bala'i kawai a mutu ko ayi rai ne, ya kashe ko a kashe shi.
Ko da aka shigar dashi aka rufe akwai mutane a ciki, wani saurayin mashayi ne ya matso kusanshi yana mishi kallon raini da wani d'aukar kai, a hankali saiya zauna kusanshi irin yana neman masifar nan (kunsan dai a gidan yari kowa yana so yaga ya cuci na k'asa dashi, kuma kowa yana ma kowa kallon k'aramin d'an iska ne), har yanzu bai daina mishi wannan kallon kad'an nake jira ba, Ammar dake zaune kan bancin ya dafe hannayenshi a gwiwanshi yana ta bubbuga k'afa, Jano Jano Jano Jano, sunan da yake ta fad'a kenan ko tsagaitawa babu, jin wannan saurayin na matse mishi wuri yasa shi d'an kallonshi, ganin wannan kallon rashin mutumcin da yake masa irin shi wai shak'iyi ne yasa shi yin murmushin gefen labb'a ya jinjina kai, saida ya sake kallonshi da kyau yace "Meya shigo da kai nan?"
Cike da gadara yace "K'waya, ni mai siyar da k'waya ne."
Ba tare daya daina kallonshi ba yace "Wa ka tab'a kashewa a harkar taka?"
A d'an tsorace ya kalleshi yace "Kisa kuma? Ban tab'a ba."
Jinjina kai yayi yana d'auke idonshi daga kanshi yace "To karka shiga harkata, inba haka ba a filin wurin nan zan rataye ka."
K'wafa yayi tare da mayar da kallonshi gabanshi, matsawa nesa dashi yayi yana kallonshi yace "Kai ka tab'a kashe mutum ne?"
"Sosai ma." Ya fad'a ba tare daya kalleshi ba, da mamakinshi yace "Wa ka tab'a kashewa? Kuma meye sana'arka?"
A hassale ya kalleshi yace "Kai, kai zan fara kashewa yanzu idan ka sake min magana, shege kai jarababbe." Saida ya zabura saboda d'aga muryar da yayi, tashi yayi daga wurin gaba d'aya yana kallonshi.
A tare suka shiga yau dan gaishe da iyayensu, sai dai yau babu Hajia zaune a kujerar mulki, kai tsaye d'akin mahaifiyarshi suka nufa da sallama, daga ciki ta amsa tare da musu izinin shiga, suna danna kai cikin d'akin ko da ta gansu tare da Huda saita b'ata rai tana musu wani kallo, durk'usawa sukayi dukansu suna gaishe ta, a wani basarwa ta amsa kafin ta kalli Huda data sha shirinta tsaf tace "Yaushe kika zo? Da safen nan?"
Junaid ne yace "A'a Mama, tun jiya ta zo ai, yarinyar bata da hayaniya ne shiyasa baki san ta zo ba."
Cike da dakiya tace "Uhum! Ta zo ta kwana biyu ne kenan?"
Kallon kallo sukayi sai Maryama ce tace "A'a Mama, na sa a kawo min ita ne ta zauna tare dani."
"Ban gane ba? Kina so ki ce zata zauna a gidan nan din-din-din?"
Saida ta kalleta dan son gano yanayinta tace "Eh."
Fuska a d'aure tace "To naji, ki bamu wuri zanyi magana da d'ana."
Murmushi Maryama tayi ta mik'e rik'e da hannun Huda suka fita, suna bada baya ta balbale shi da masifa akan me zai yarda ta zo da yarta, ai ba haka akayi da ita ba, a k'arshe ma cewa tayi "Wai kai baka da zuciya ne? Matarka ta zo da 'yar da ba kai ka haifeta ba a gidanka, me zai hana ta kaita wajen dangin ubanta? Ko kuma a cikin karuwan nata bata san waya mata cikin 'yar ba?"
A d'an k'ufule yace "Mama, haba Mama, wannan wace irin magana ce? Ni na amince ta zauna damu, wacece Huda? Duk hidimar da zan mata ba zata kai wacce zan yi wa 'ya'yana ba idan na haifa, kawai ki bar maganar nan bana so."
Mik'ewa tayi tace "To kaji da kyau, wallahi ban yarda da zamanta a gidan nan ba, kuma kasan Hajia ma ba zata yarda ba, dan haka kafin ta muku wankin babban bargo ka gaggauta fitar da ita a gidan nan, idan ba haka ba babu ruwana duk sanda ta zo cin mutumcinka."
"Indai hakane to ni kawai zan koma gida na, dama ban so zama anan ba kawai Alhaji ne yasa na zauna."
Fita yayi daga d'akin ya barta tana bambami, yasan za ayi haka dama shiyasa ya shirya juya, a farfajiyar gidan ya sameta nan ya mata sallama ya fita, gidansu ta koma amma madadin ta shiga wurinta saita wuce b'angaren da bata da masaniya ko na waye, saida ta shiga da sallama a k'ofar d'akin suka ci karo da Amar zai fita, gaisawa sukayi a mutumce ya wuce, saida taga fitarshi saita wuce b'angare na gaba dan ba Umaimah take son gani ba, anan tayi sa'ar samun Jibril ko fita baiyi ba, ganinsu yasa Jamila saka hijabi akan k'ananan kayanta suka gaisa, suna zaune ya fito da alama tashinshi kenan, Huda na ganinshi ta ruga ta rumgume shi tana fad'in "Lahhh Abba, ina kwana."
Rintse ido yayi tare da gumtse baki yace "Shit!" A zahiri kuma bud'a ido yayi ya mata dariya ya rik'e hannunta yace "Yah beby Huda, ya kike? Yaushe kika zo gidanmu? Kin zo wajen mamanki?"
Da fari fad'uwa gabanta yayi jin yarinyar ta kirashi Abba daga ganinshi, amma yanzu tana son sanin dalilin da yasa ta kira shi da haka, kafesu tayi da ido tana kallo, har suka k'araso ya zauna nesa da ita Huda na mishi magana, a kaikaice ya kalleta yace "Madame ya kike?"
Wani shed'anin kallo ne take masa wanda bai dace ba, saida tayi murmushi tace "Lafiya lau Abban Huda, ka tashi lafiya?"
Saida ya d'an rarraba ido yace "Lafiya lau, ina mutumin ko har ya fita?"
"Ya fita." Ta fad'a tana kafeshi da ido, ganin ba zai juri wannan kallon ba yasa shi sakin Huda ya mik'e zai koma ciki, da sauri Maryama tace "Abban Huda nace ko zamu iya magana?"
Yawu ya had'e da k'arfi sannan ya juyo ya kalleta, Jamila ma da baki sake take kallonsu, cikin dai k'warewa ta bariki ta mishi alama da kai da ido cewa su fita waje mana, mik'ewa tayi tana rik'e da hannun Huda ta fita, bayansu ya bi jiki a sab'ule yana kallon yanayin yar matarshi wacce ke jin kamar ta shekara a soyayyar mijinta duk ta fara zufa, suna fita k'ofar d'akin ya tsaya ya rufe yace "Lafiya? Me kikeyi haka Maryama?"
Da yatsa ta nuna shi tace"Dakata malam, dama dan na fad'a maka Huda ta dawo nan da zama ne, ba wai dan mahaifiyarta na aure nan ba, a'a sai dan nan gidan ubanta ne, gidan da ko babu ni a raye nan ne yafi dacewa data rayu, dan haka ka fara shirya nuna mata gata ita ma tasan 'ya ce."
Juyawa tayi zasu wuce sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace "Anjima zan bata ta kawo maka takardar haihuwarta, ina buk'atar ka canza mata makaranta ita ma, ya rage naka ka samar mata dreba ko kuma ka kaita da kanka ko ma ta tafi a k'afa duk matsalarka ce."
Wucewa sukayi ta barshi tsaye kamar zai kashe kanshi, wane bala'in ne kuma wannan ke shirin danno mishi kai? A haka ya dawo d'akin Jamila na gyara teburin cin abinci, ta baya ya rumgumeta yana shinshinar wuyanta, ba alamar wasa a amon muryarta tace "Me yasa take kiranka Abban Huda?"
Dakewa yayi duk da fad'uwar da gabanshi yayi yace "Saboda ni da Junaid duk mun ce mata mun zama iyayenta, yarinyar kullum damuwarta ita ce mahaifi, amma yanzu kinga ta daina."
Ba tare daya saketa ba ta juyo ta shafa kumatunshi tace "Je kayi wanka ka fito ka ci abinci."
"To." Kawai yace ya shiga d'akinshi da tunanin k'ananan iskancin da Maryama ta taho mishi dashi kuma, shiryawa yayi ya fito ya sameta suka karya.
Amar na saman hanya lieutenant ya kira shi kan yana so ya tura ma Ammar kud'i ya bashi lambar account d'inshi, dan a ganinshi daya tambayeshi kud'i to baya da su ne shiyasa, ba dan haka ba zai tambaya ba dan rabon da sisin kwabo ta shiga tsakaninsu dashi har ya manta, tun bai fara aikin likita ba ya tsaya da k'afafun, matsala ko wacce ta shafi karatunshi ce shi ke tsaya ma kanshi. Amar dai cewa yayi wallahi baisan komai a game da abinda ya shafi Ammar ba, shi kuma lieutenant yana jin ba zai iya tambayar Ammar d'in ba dan haka yace Amar ya bud'e mishi sabon count a bankinsu, yana zuwa aiki ba b'ata lokaci yayi komai