Showing 147001 words to 150000 words out of 325849 words

Chapter 50 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

583

Middle Ads

d'aya ya figota ta fito kamar kaza, mannata yayi a jikin motar ya matseta sosai cikin b'acin rai da d'aga murya yace "Ke mahaukaciyar ina ce? Ni ne zaki raina? Ni tsaranki ne? Saboda kawai abinda ya faru zaki nemi ki raina ni? To baki isa ba kinji na fad'a miki."

Wurgata ya sakeyi cikin motar yana fad'in "Banza kawai."

Yanda ya hankad'ata cikin motar taji zafi sosai daga k'asanta wanda har yanzu ke mata zugi, wata k'aramar k'ara ta saki amma bai kulata ba sai Amna data juya tana kallonta, kafin ta mata magana taji ya figi motar da wani sabon gudu ya d'auki hanya, Hamna kam da ke jin azaba sosai dan ko adaidaita data shigo cikin dubara tayi zaman, kasa zaune tayi da kyau sai d'ogala k'ugunta da take, tana d'an cije leb'e tana dafe cikinta.

Babu wanda ya sake magana a motar har suka ga ya d'auki doguwar hanyar madarounfa, sabo kuma dogon titin nan ya samu yana ta raraka ba ji ba gani da kuma gudun tsiya, Amna dai na son tayi magana amma tana jin tsoro, Hamna da abun duniya ya dameta ne cikin zubo da k'walla ba tare data kalleshi ba tace "Dan Allah ni ka sauke ni anan na koma gida ko a k'afa ne, bana jin dad'in zaman nan fa gaba d'aya."

Amna ce ta juyo ta kalleta tace "Baki da lafiya ne?"

Cike da tausayin kanta tana zubo da k'wallan tace "Bana da lafiya, kuma shima ya sani."

Wani irin fad'uwa gabanshi yayi da sauri ya kalleta ta madubi, amma sam bata kalleshi ba sai cije baki da yaga tana yi, k'ala baice ba ya ci gaba da tuk'inshi, suna haka Hamna tace "Nifa bawali nake ji."

Da k'arfi ya juyo ya kalleta lokaci d'aya kuma ya kalli gabanshi, ba alamar wasa ta sake cewa "Wallahi fitsari nake ji."

Saida tayi tafiyar minti biyu kafin ya samu wuri ya paka motar, aje jakarta tayi ta fito ta duba da kyau ta samu wuri, matsawa tayi nesa dasu zata tsugunna taji ya bud'e murfin motar ya fito, da sauri ta mik'e tana kallonshi cike da raini, gurin yaje yana dube dube kamar yana neman wani abu mai daraja daya rasa, fuska a had'e ya kalleta yace "Ki hak'ura da fitsarin nan ki koma mota."

Shek'ek'e ta kalleshi tace "Ban gane ba? A matse nake fa."

Tsawa ya daka mata yace "Nace ki koma ko? Ba zakiyi fitsarin a nan ba, ke ba dan ma baki san ciwon kanki ba har nan kinga gurin da zaki iya tsugunawa da abinda yafi komai mahimmanci a tare dake, baki tunanin abinda zai faru dake?"

Saida ta harareshi sama da k'asa taja tsaki ta wuce tana fad'in "To meya rage min yanzun? Ko ka manta jiya ka fatatakashi."

Ba wai abinda ta fad'a bane ya tsaya mishi a rai kamar tsakin data masa da harara, sai yaji ya gamsu da mace na iya raina namiji inhar ta ganshi tsirara, wata zuciyar tace mishi "Amma ai kai bata ganka ba, wacce idonta ke rufe tana kokawa da kai tana kuka, amma kuma duk da haka lokacin da taji baka da niyyar barinta ai ta bud'a ido ta kalli k'wayar idonka tace " *Dan Allah yah Ammar ya isa haka, na tuba ba zan sake maka rashin kunya ba, dan Allah ka k'yale ni haka na gaji, wallahi kamar zan mutu.*"

A hankali ya lumshe idonshi saboda a daidai lokacin ita ma ido ta rufe ruf hawaye na mata zarya a fuska, wata irin shashek'a ce take saukewa mai barazanar tafiya da numfashinta, gaba d'aya jikinta ya saki kamar wacce babu lakka a tare da ita, bud'e ido yayi ya ga dukansu shi suke kallo, cikin mutuwar jiki ya zo ya shiga suka ci gaba da tafiya. Izuwa yanzu kam dukansu sun fahimci wajen mahaifiyarsu ne zai kaisu, sai dai me zasuje yi haka zuwan bazata shine basu sani ba, cikin mintin da bai gaza talatin ba suka isa garin har k'ofar gidan, Amna ce ta fara fitowa ta nufi cikin gidan, Hamna ma fitowa tayi cikin tako da k'yar ta nufi cikin gidan inda ya bita da kallo, saida ya ga shigarsu kad'ai ya tuk'a motar zuwa masallacin juma'a dake garin.

Da gudu Amna ta k'arasa shiga da kiran sunan "Mama, Maman mu."

Tana zaune kan kujerar k'arfe tana girki a k'aramin gas d'in ta taji muryarta, mik'ewa tayi da murna ita ma ta d'an fito daga cikin runfar zanar da tayi shamaki a wurin, suna ganin juna Amna ta rumgumeta sosai tana farin ciki, ita ma rumgumeta tayi tana fad'in "Auta ta, ke ce haka bazata? Ke da wa?"

D'agowa tayi ta juya bayanta da tsantsar farin ciki tace "Tare da Hamna da yah Ammar, shine ya kawo mu."

Murmushi tayi ta kama hancinta tace "Kice dake da angon naki ko? Ja'ira kawai ai nasan komai, Ummynku ta fad'a min a waya."

Sake fad'awa tayi jikinta tace "Kai Mama, da saura fa."

Da d'an mamaki tace "Amma ya akayi kika riga Hamna shigowa? Kullum ita ke fara shigowa da ihun murna, ko dai dan kuna tare da d'an albarka ne yasa ya daidaita mata zama?"

Tab'e baki Amna tayi tace "Tace bata da lafiya ne, tun jiya nima na kasa gane kanta."

K'arasowar Hamna yasa Hadiza kallonta, yanayin fuskarta ne ya canja lokaci d'aya saboda ganin wani sabon yanayi a tare da Hamnar, hatta tafiya ma da k'yar take yinta alamar tana mata wahala, Amna ce tayi bayan mahaifiyarta su tana bud'a fridge d'in dake kusa dasu ta d'auko ruwan sanyi, Hamna ma na zuwa fad'awa tayi jikin mamansu ta fashe da kuka, wannan abu shi ya d'aga hankalin Hadiza harda Amna dake shirin shan ruwa amma ta dakata tana kallonta da mamaki, cikin rud'u Hadiza ta d'agota tace "Hamna, lafiya? Meye na kuka kuma? Wani abu ne ya faru?"

Amna ce tayi saurin cewa "Mama kawai ki rabu da ita iskanci ne, na fad'a miki tun jiya fa take wani basarwa tana share mutane, ba wani abinda ke damunta."

Juyawa Hadiza tayi ta kalleta tace "Yi min shiru Amna, akan me zaki ce a rabu da ita? Kinsan me yale damunta ne? Ai kamata yayi ace ke kika fi kowa sanin abinda ke damunta duba da 'yan biyunki ce."

Mayar da hankalinta tayi kan Hamna da har yanzu take kuka ta jata suka zauna kan kujerun wurin ta ci gaba da tambayarta, amma sai Hamna ta share hawaye cikin shagwab'a tace "Mama kawai nayi kewarki ne sosai, munfi shekara bamu ganki ba fa, muna so mu zo amma Hajia ta hana mu, na fidda rai da zan ganki sai kawai boss ya kawo mu, dole nayi kukan farin ciki."

Dangware mata kai Hadiza tayi tace "Ke dai akwai sakarya wallahi, yanzu akan hakane kika d'aga min hankali."

Amna ce ta cire takalmi ta shiga d'akin tana fad'in "Ai dama na fad'a miki iskanci ne."

Da kallon jin haushi Hamna ta bita tace "Ke wallahi bana son iskanci kinji ko, ni sa'arki ce da zaki tsaya kina fad'a min abinda kika ga dama?"

Daga cikin d'akin tana cire kaya tace "Aje anyi d'in, inba raina mutane ba meye na duk wani canzawa lokaci d'aya? Tun jiya da kika je karatu d'akin Ummy kika zama wata iri dake."

Mik'ewa Hamna tayi ta shiga cikin d'akin tana fad'in "Wallahi kika min rashin kunya saina ci ubanki a wurin nan, ina ruwanki da canzawata to? Idan kinji haushi ki fita harkata mana, yar jaraba kai."

Daga waje Hadiza tace "Ya isa haka to, kar na sake ji bakin kowa a wurin nan."

Amna ce tace "Mama ki rabu da ita ta ci uban nawa mana idan zata iya."

Kallon Hamna tayi tace "Ke kinsan ko gawata wallahi tafi k'arfin ki, dan kin rigani fitowa duniya bafa tazara mai tsayi kika ban ba."

K'wafa Hamna tayi ita ma ta fara cire kayanta da nufin shiga wanka, kusan a tare suka jero kowace da d'aurin k'irji da zanin Hadiza na atamfa zasu fito hakan yasa suka matse junansu, ture juna sukayi inda Hamna ta bita da harara da tsaki, Hadiza dai na kallonsu tana jin dad'i dan ko ba komai yau tana jin hayaniya a gidanta na yara, Amna ce ta d'auki bokiti ta tara ruwa a bakin panpo inda Hamna ta d'auke kwandon sabulun wankan, Amna ce ta kalli mahaifiyar tasu tace "Mama ki fad'a mata ta ban kwandon nan."

Kallonta Maman tayi tace "Hamna ki bata kwandon idan ta fito kya shiga."

Cikin turo baki Hamna tace "Wallahi Mama ba zan bata ba saina fara yi, tun a hanya fa tasan ina cewa fitsari nake ji."

Hadiza ce tace "To ki shiga kiyi fitsarin ki fito saiki bata wurin."

Cikin yanayin sangarta tace "Mama kawai ki k'yalemu kiyi kallonmu, karki sa wannan sakaryar ta raina ni saboda kina d'aukar ta autarki."

Hadiza ce tace "To shikenan na saka muku ido, kafin nan ku fad'a min ina yaron kirkin yake ne? Kunce shi ya kawoku kuma banga ya shigo ba har yanzu."

Tab'e baki Hamna tayi tace "Waya sanin masa mugun kawai, Allah yasa ma ya tafi ya barmu nan mu kwana."

Girgiza kai kawai Hadiza tayi ta ci gaba da duba girkinta, tana kallo Hamna ta damk'i bokitin ruwan tana so ta raba Amna dashi, ita ma rik'ewa tayi sosai tace ba zata saki ba, hakan ne ya janyo musu kokawa da bokitin ruwan har suna ta zubewa a banza, wajen wannan tak'ak'abuwa bokitin ya fad'i k'asa ruwan suka watse a banza, da sauri Hadiza ta lek'o daga yar rumfar tana fad'in "La'ilaha illalahu, wai ku yanzu haka abun naku ya zama? Meye ha...?" Shiru tayi saboda ganin Ammar ya shigo cikin gidan.

Amna ce tayi k'asa da kanta yayin da Hamna kuma ta zabga mishi harara ta d'auke kanta, Ammar kam kawar da idonshi yayi daga kallonsu saboda ganinsu kamar 'ya'yan gwarawa, kowace da d'aurin k'irji hallitarsu ta fito fili, ta bayan Amna ya bi ya wuce yana kallon Hamna dake masa wani kallon iya shege, tun kafin ya k'arasa Hadiza ta aje masa kujera tana fad'in "Ammar ina ka shiga? Sun ce kai ka kawosu amma shiru baka shigo ba."

Sam babu fara'a a fuskarshi ya zauna akan labb'anshi ya amsa da "Masallaci na tafi Tanti."

Da fara'a sosai tace "Haba shiyasa, to anyi sallah lafiya?"

Ciki ciki ya amsa da "Lafiya lau." Kallonshi Tanti tayi tana murmushi a zuciyarta tana ayyanawa yau 'yan mulkin ne akan shi shiyasa ko gaisheta ya kasa yi, kallonsu Amna tayi da har yanzu suka kasa sulhunta kansu, girgiza kai tayi tace "Auta, ki barta tayi sai kiyi kinji, ki zo ki kawowa yayanku ruwa yasha kya samu lada ma."

Da sauri Hamna ta kalli Hadiza Amna ita kuma turo baki tayi ta sakar mata bokitin tana hararanta, cikin sand'a take takowa kamar wata marar gaskiya saboda ganin yanda Ammar ya had'e rai kamar hadarin gabas, cikin tsoron kar ya daketa ta samu ta shige d'akin ta d'auko hijab ta saka ta fito, ruwa ta d'auko mishi ta zuba ta bashi a lokacin da Hadiza ke tambayarshi meyasa bai tsaya d'aurin auren babban shi ba? Saida ya karb'i ruwan ya d'an kurb'a ya kalli Amna da jajayen ido yace "Wuce d'aki."

Kallonshi tayi kamar zatayi kuka cikin muryar tsoro tace "Yah Ammar..dama...alwala zanyi kafin ta fito."

Sake wurgo mata idonshi yayi wanda yasa gabanta fad'uwa, dan a yanda suka sani ko gaban mahaifiyarsu ta kama saiya kasheka da mari har ma ya d'auki madaki, ajiyar zuciya ta sauke mai sautin gaske saboda alamar daya mata da ido ta wuce, da sauri ta nufi wajen buta ta zuwa ruwa lokacin Hamna ta shiga wanka, bai sake tankawa ba har saida ya ga shigar Amna d'aki kafin ya kalli Hadiza dake kwashe abinci a kwanuka ya tab'e baki yace "Me yasa zanje d'aurin auren?"

Juyowa tayi ta kalleshi ita har ta manta ma data tambayeshi, tun yana k'aramin yaro take k'aunar shi har zuciyarta, ta sanshi tasan halinshi fiye da uwar data haifeshi, hakan yasa bata damu ba saima murmushi da tayi tace "Saboda mahaifinka ne mana, kuma zaiyi farin cikin ganinka a wurin a kusa da shi."

Murmushin rainin hankali yayi tare da kallon farfajiyar gidan yace "Ba zan iya wannan abun kunyar ba, tsofai-tsofai da kai kayi wani wai aure, auren ma ba da babbar mace ba ko wata bazawara, yarinya mai k'ananun shekaru, ko ni dake d'ansa wannan yarinyar ta min kad'an na aureta wallahi bare kuma shi."

Wani wawan tsaki yayi alamun dai abun ya dameshi sosai, banda dariya ba abinda Hadiza keyi kafin tace "Yaron kirki kenan, amma me yasa kake ganin ta maka kad'an?"

Sam babu alamar wasa ko kunya yace "Saboda ba zata iya d'aukata ba, zata iya mutuwa tun kafin aje ko ina, sannan ni banga albarkatun dake jikinta ba wanda zasu iya d'ebewa mutum kewa."

Murje ido Hadiza tayi ta nuna abun bai wani dameta ba dan tasan halin katob'aran yaronta tace "To dama wacece zata iya da kai yarona? Ai sai yar baiwa, amma fa duk da haka ita yarinyar ta dace da mahaifinku, tunda kaga kai sabon jini ne ka mata yawa, shi kuma an kwana biyu zai iya tafiya da ita yanda ya dace."

Cike da jin an fasa mishi kai yayi wani shak'iyin murmushi yace "Hmm; shi ma fa da sauranshi, dan yanzu haka zai iya samo mana cikakken k'ane."

Kafin tayi magana Hamna ta fito daga wanka, har tayi alwala bakin panpo ta basu sake magana ba, saida ta zo daf dashi zata wuce ta gabanshi dan hanyar da zata iya sadaka da d'akin ce kawai yace "Tanti ai duk wacce na kwanta da ita na tashi ita ma kuma ta mik'e da k'afafunta, to wannan ita ce daidai dani saboda ni jaruma nake so ba raguwa ba."

Da k'arfi Hamna ta kalleshi amma kash kamar ma baisan da tsayuwarta a wurin ba, cikin murmushi Hadiza tace "Zaka sameta mai jarumta yaro na, zanyi k'ok'arin ganin haka ta faru ko saboda jin dad'in ka."

Juyawa tayi ta kalli mahaifiyar tasu dake ta harkar gabanta, sake juyowa tayi ta kalle shi tayi k'wafa ta wuce, zata shiga ciki taji ya sake cewa"Kankana."

Cak ta tsaya ta juyo tana aika mishi wani mugun kallo, kallonta yayi ya gyara zama tare da shafar gemunshi yana dariyar iskanci ya kashe mata ido d'aya yace "...


*Alhamdulillah Allah*๐Ÿ‘
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_26_


Kallonta yayi ya gyara zama tare da shafar gemunshi yana dariyar iskanci ya kashe mata ido d'aya yace "Fita zanyi yanzu, zaki sha kankana ne na taho miki da ita?"

Sama da k'asa ta harareshi taja dogon tsaki ta wuce d'aki, ba tare daya daina murmushin ba ya bita da kallon *zaki gane kurenki*, Hadiza ce ta juyo ta bita da kallo tace "Ke Hamna lafiyarki kuwa? Meye na tsakin daga abun arzik'i? Bana son iskanci kinji na fad'a miki, wannan ba yayanki bane? Ko dan kinga yau ya sakar muku fuska ne."

Mik'ewa yayi tsaye yana gyara zaman doguwar rigarshi yana fad'in "Tanti ni zan fita na dawo."

Kallonshi tayi cike da kulawa tace "A'a, ka zauna mana ka ci abinci saika fita, nasan dai yanzu bakin ruwa zaka je ko?"

Murmushi kawai ya mata ya nufi k'ofar fita, da kallo ta bishi a ranta tana mamakin wani sauyi data gani a tare da shi tana fad'in "Yau Ammar babu saurin kai duka, har Hamna ta mishi tsaki amma ya nuna ko a jikinshi, lallai yau farar juma'a ce, ba dan haka ba ai da sai dai ta jiyo ihunta a d'akin."

Wata zuciyar ta fad'a mata "Dama ai yau da gobe sai Allah, mutum yana canzawa kamar yanda zamani ke canzawa."

Ba tare data daina kallonshi ba tace "Ko kuma dai dan za'a had'a shi da Amna ne, tabbas ma hakane, watak'ila kunyarta yake ji yanzu saboda sun zama surukai."

Bata gushe daga tunanin ba taji muryarshi cikin d'aga murya yana fad'in "Mutumin ya kake?"

Da kallo ta bisu ganin shi da mai gidan nata suna gaisuwa irinta yaran zamani marasa jin magana, murmushi kawai take saboda yanda suka birgeta kamar wani d'a da uba, dawowa sukayi ciki har cikin runfar inda Shu'aibu ya kama hancin Hadiza yaja sosai yana mik'a mata sallayar hannunshi yana fad'in "Matanmu ya aiki? Ashe bak'i kikayi bayan tafiyata?"

Hadiza data saba take kuma jin dad'in zama da mijin nata murmushi ta masa tace "Sannu da zuwa, bak'i kuma ba bak'i ba kam."

Ammar da soyayyar dattawan ke birgeshi sagala hannunshi yayi a kafad'ar Shu'aibu ya ja hancinshi yana fad'in "Duk ka jaye mana hanci uwa har yayi tsayi kamar karas, ka canza wani salo mana."

Shima kama wuyanshi yayi suna dariya yace "Uwar ka dai ce ka shammata bani ba ja'iri kawai, kuma ma wani salo zan canza bayan na saba da wannan."

Kashe mishi ido d'aya yayi yace "Muje waje zan fad'a maka irin wanda zaka sauya."

Hararan wasa Shu'aibu ya masa yace "Me yasa sai mun fita? A sani na dai baka jin kunyar fad'an komai ko a gaban wa."

D'ora kanshi yayi a kafad'ar Shu'aibu tare da jawo rigarshi yana rufe ido wai kunya๐Ÿ™„๐Ÿค” (bala'i, ban tab'a gani ba), cikin nuna jin kunya yace "Nima bansan ya akayi ba yau na ji na sauya, kawai dai muje waje na fad'a maka sabon yayi."

Ture shi Shu'aibu yayi daga jikinshi ya kalli Hadiza da banda dariya da girgiza kai babu abinda take yace "Wai ina yan biyuna ne ikon Allah? Amma dai banda Hamna aka zo ko?"

Hadiza ce tace "Har da ita ko, yau dai matsiyata ne bisa kanta shiyasa, dan da farko data shigo ma kuka ta saka mana, duk ta canza dai tayi wata iri."

Daga cikin d'akin cikin taushin murya Amna "Kawu ina wuni."

Cikin sakin fuska ya amsa da

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login