Showing 150001 words to 153000 words out of 325849 words
"Lafiya lau yan biyu ikon Allah, amma wace tayi magana? Kinsan ban cika gane ku ba har yanzu."
Amna ce tayi dariya zatayi magana Ammar yace mishi "Ba kankanar bace, d'ayar ce."
Kallonshi Shu'aibu yayi yace "Kai kam dama ai ko mahaifiyarsu ba zata nuna maka saninsu ba, Allah ya maka wannan baiwar tun haihuwarsu."
Murmushin jin dad'i yayi ya shafo gemunshi yace "Da wayona fa akayi auren Tanti da Tonton, sannan tare da ni tanti ta ci amarcinta, tare dani tayi laulayin cikinsu, hasalima ni nake shafa cikinta ina fad'a mata zata haifi yan biyu kamar ni da d'an uwa na, sannan a idona ta fara nak'udarsu ni ne ma na kira mutanen gida aka kaita asibi, tare dani akayi jegonsu, sannan tare da ni Ummy ta rainesu har sukayi wayo, to ni kam meye zai shige min duhu a tare dasu?"
Duk da Shu'aibu ya ji kishi a zuciyarshi lokacin da Ammar yace sun ci amarci, amma kuma bai nuna ba ko a fuska sai darewa da yayi yace "Gaskiyar kam, amma yanzu dai bari na gano kankanar ta bakinka."
Zai shiga d'akin Ammar ya rik'o hannunshi yace "Muje waje haba muyi hira, rabu da kankana nasan matsalarta."
Daga d'aki Amna tace "Kawu sallah ma take."
"Shiyasa dai banji muryarta ba ashe." Cewar Shu'aibu kafin ya kalli Hadiza yace "Idan kin gama abincin ki aiko mana shi k'ofar gida, wannan sarkin zancen ba zai barni na gama kallonki ba."
Dariyar shak'iyanci yasa suka nufi waje yana fad'in "Ai mutumina shiyasa nake so muje waje na k'ara baka wasu shawarwarin yanda zaka ci gaba da kula mana da tantinmu, dan naga ba tsufa kuke ba ku, shiyasa nake so naga kullum kana nan a jaruminka kana bada wuta a ciki."
Shu'aibu dariya yayi yace "Cikin me?"
Sunkuyar da kai yayi yace "Kai ma dai har saina fad'a? Ka sani mana."
Shu'aibu ne ya d'auki tabarma suka fita, suna zuwa ya shinfid'a a k'ark'ashin bishiyar dake k'ofar gidan tare da wata k'atuwar darduma suka zauna, a cikin gida kuma Hadiza k'walla kiran Amna tayi tana fitowa tace ta d'auki abinci ta kai musu, cikin ladabi ta d'auka har da ruwa ta kai musu.
*Gaga's House*😍
Hankalin Ummy ne ya fara tashi ganin babu Hamna kuma babu Amna, wayarta ta fara kira amma abun mamaki saita samu wayar a d'akinta, alama dai wahalar da tasha tasa ta manta da wayar ma a d'akinta, Amna ta koma kira ita kuma kashe wayar dan tunda zasu shiga aji ta kashe oga boss kuma yasa ta manta bata kunna ba, saida rana tayi sosai lokacin su Hamna na cin abinci ta d'auki wayar ta kunna, ganin kiran da Ummy tayi bata samu ba yasa ta mayar da kira, da sauri Ummy ta d'auka tana fad'in "Amna, lafiyarku k'alau kuwa? Ina kuka tsaya ne haka?"
Da murmushi a fuskarta tace "Ummy kiyi hak'uri banga kiranki ba sai yanzu na kunna wayar, wallahi muna lafiya lau babu komai."
"To kuna ina har yanzu baku zo gida ba?" Ta fad'a cike da k'aguwa, kallon Hamna tayi da ita ma ke kallonta tace "Ummy gamu nan gida wajen Mama."
Da k'arfi Ummy ta zaro ido tace "Me? Mamanku? Ke da wa?"
Jin yanda Ummy ta rud'e yasa tayi dariya tace "Ummy kwantar da hankalinki, yah Ammar ne ya kawo mu tare da Hamna muke."
Da sauri cike da tsoron abinda Hamna zata fad'awa mahaifiyarta Ummy tace "Ina Hamnar take? Bani ita."
Mik'awa Hamna wayar tayi ta ci gaba da cin abincinta Hamna kuma ta amsa da "Ummy lafiya lau muke fa."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Hamna ina cikin damuwa sosai, kar Hadiza ta fahimci wani abu ya faru dake, dan Allah ku dawo yanzu Hamna kafin Hajia ta ankare da rashin dawowarku, kinsan a kaina k'urar zata sauka tace da sani na kuka tafi babu izininta."
Cikin rashin karsashi Hamna tace "Ummy wallahi ba laifinmu bane, kawai muna fitowa daga makaranta ya zo ya d'auke mu da k'arfi."
Cikin rashin kulawa Ummy tace "Ni ban damu da lamarinshi ba, ko da kun dawo ma yasan yanda zaiyi ya fitar da kanshi wajen Hajia ko kuma ya sake tsula mata wata tsiyar, ku kawai nake ji Hamna, dan Allah ku k'ok'arta ku dawo kafin sallah la'asar, kunga gida anata hidima kuma ana tambayar ina kuke."
Cikin sanyin murya tace "Ummy yanzu ba zamu iya kwana a nan ba? Mun jima fa rabonmu da nan."
Da sauri tace "A'a Hamna rufa min asiri dan Allah, ni dai na rok'eku ku dawo yanzu kinji, inba haka ba ni zan zo garin na taho da ku, Hamna ko kin manta kina buk'atar kulawa ne?"
Turo baki tayi kamar tana gabanta tace "Shikenan Ummy zamu dawo."
Murmushi tayi mai sauti tana fad'in "Yawwa yar albarka, sai kun zo kinji, ina maman taku ne?"
"Tana waje." Cewar Hamna a dak'ile kafin Ummy tace "Bani ita mu gaisa."
"To." Ta fad'a tare da mik'awa Amna wayar tace "Kaiwa Mama."
Figar wayar tayi tana dalla mata harara da fad'in "Ke musaka ce da ba zaki iya tashi ba ko me?"
K'ala ba tace mata ba har ta fice ta kaiwa Mamansu wayar, sosai suka gaisa inda Hadiza take sake godewa Ummy kan kula mata da yaranta da take, sannan ta d'ora da "Munji kuma abun alkairi had'in da Hajia tayi, Allah ubangiji yasa alkairi yasa ayi muna raye."
Ummy ce ta amsa da "Ameen, insha Allahu ma ai zan zo ko dan muyi magana da shirye shiryen abinda ya kamata na bikin, ina jira ne a gama wannan sabgar lokacin an kawo komai da komai sai na zo."
Ita ma Hadiza murmushi tayi tace "Sa'ada kenan, ai ke ce uwar yaran nan, duk abinda kikayi wallahi d'aya ne, babu abinda zan ce muku ke da lieutenant ai sai godiya."
"Ba komai wallahi yiwa kaine ai." Da haka sukayi sallama ta mayarwa da Amna wayar d'aki wanda ta same su suna rigima Hamna ta dage sai Amna taje waje ta fad'awa Ammar Ummy tace su tafi, ita kuma tace ba zata ba salon ya mata rashin mutumci, dariya Hadiza tayi tace "To ke da zai aureki kina shakkar yi masa magana tun yanzu, ya kenan idan anyi auren?"
Hamna ce tace "Sai ya raina ta mana ya juyata yanda ya ga dama."
Hararanta tayi tace "To ina ruwanki idan ya juya nin? Ai ba ke ya juya ba ko? Kuma dama haka ake so mace ta zama k'asan mijinta."
Wata dariyar shak'iyanci ta mata tace "Lallai ma yarinya, to ki zama k'asan wannan mahaukacin, wallahi wata rana saiya saki kin lashe tafin k'afar shi."
Cikin jin haushi tace "To sai me idan na lashe? Ai k'afar mijina ce."
Hadiza ce tace "Kinga ku bar rigimar nan tashi kije ki fad'a masa."
Mik'ewa tayi ta fito ta wanke hannunta ta d'auki hijabinta ta saka ta fita rai a b'ace, data same shi ta fad'a mishi cewa yayi sai bayan sallah la'asar zasu tafi dan haka su jira, ba tace komai ba face to ta dawo ciki.
*A can gida* kuma ba laifi ana ta bikin lieutenant da Zeituna, anci an sha sosai ana gwangwajewa, kuma daga Ummy har lieutenant babu wanda ya damu da rashin kasancewar Ammar a wurin hidimar, a wurinsu ma hakan ya fi musu kwanciyar hankali a madadin yana nan d'in, rana tsaka babbar mota ta paka k'ofar gidan aka fara shiga da kaya ciki, saida aka shiga dasu tsaf farfajiyar gidan sannan suka nemi inda za'a zuba, Zeinabu ce ta tambaya daga ina suke suka ce Alhajin gidan ne ya aiko su, Hajia suka fad'awa inda ta kira Alhaji ta tambaye shi kayan meye? A cewarshi na amarya ne a ware d'aki na musamman a zuba mata a ciki, nan aka ware mata d'aki ita ma a falon k'asa aka shiga da kayan ciki, Alhaji ne ya umarci Zeinabu da Soueiba su jagoranci al'amarin a gyara d'akin, ba b'ata lokaci suka shiga gyara tare da taimakawar mutane dayawa, cikin k'ank'anin lokacin saiga d'aki ya d'auki saiti sai zuba k'amshi, Hajia data shigo ganin gyaran ranta ya b'ace sosai, dan kayan daya zuba mata ba kad'an bane ba kuma masu arha ba, tana al'ajabin yanda yar aikin gidanta k'azama zata shigo gidan nan a matsayin matar baban d'anta, haka dai aka rufe d'akin ana jiran lokacin da mai shi zata shigo.
Sai bayan sallah la'asar ne Hajia ta fahimci rashin ganinsu Hamna da batayi ba, ta so tambayar Ummy ina yan rainonta suke, amma kuma daga ita har Ummy d'in suna tare da bak'i, hakan yasa tana cin karo da Jamila a falonta ta kalleta tace "Ke ina su Hamna suke?"
Da d'ard'ar tace "Eh to Hajia wallahi nima ban sani ba, tunda safe rabona da su."
Kallon tuhuma ta mata tace "Amma ai jarabawarsu sauka d'aya ne ake ko?"
"Eh Hajia." Ta fad'a kanta k'asa, a kaikaice tace mata "Ki kira min shalele a k'ofar gida."
"To." Ta fad'a tana fita daga falon, a k'ofar gida ta samu Amar tare da abokanansu da duk samarin gidan suna ta hira da raha, sallama tayi suka amsa kafin ta d'ora da "Ina wuni."
Jibril daya kafeta da ido duk yaji haushinta ya cika mishi zuciya saboda masha Allah d'inkin dake jikinta ya bi k'irarta sosai tare da fito mata da komai, kuma wani gyale ne ta sab'a a kafad'a wanda dashi gwara babu, amsawa sukayi inda shi kuma ya bita da harara, suna had'a ido ta k'ura mishi ido tana mishi kallon mamakin meye na harara kuma? Bata d'auke idonta ba taji yace "Me kike nema anan kuma?"
Saisaita kallonta tayi tace "Dama Hajia ce tace na kira mata yah Amar."
Amar ne yayi saurin kallonta yace "Ni kuma? Lafiya?"
Girgiza kai tayi tace "Ni ma ban sani ba." Juyawa tayi zata tafi Jibril ya bita da kallo, abokinshi ya kalla zaiyi mishi magana sai kuma yaga shima ita yake bi da kallo, wani wurga ido yayi alamar jin haushi tare da zabura daga kan kujerar ya mik'e ya bi bayanta, rufe ta yayi ta yanda ba'a ganinta yana binta har suka shiga cikin gidan, sam a tunaninta Amar ne ke biye da ita ashe ko tahowa ma baiyi ba, k'eyar ta taji an zungura ta baya da fad'in "Ke miye haka?"
Juyowa tayi tana dafe wurin ta kalleshi, ganin shine yasa tace "Yah Jibril."
Saida ya matsa daf da ita kamar zai had'e ta ya kalli idonta yace "Baki san da maza a wurin bane zaki fito haka babu hijabi?"
Cikin rashin fahimtar kalamanshi tace "Ban gane ba yah Jibril? Naga biki akeyi a gidanmu ai..."
"Ai me?" Ya katseta da k'arfi har saida ta d'an zabura, nunata da hannu yayi yace "Allah kika sake fitowa waje babu hijabi saina karyaki a wurin nan, maza wuce ciki malama."
Turo baki tayi irin na ranta ya b'ace ta juya a fusace zata shige, hannunta taji ya fizgo ya dawo da ita gabanshi ba tare daya saki hannun ba yace "Wa kike turowa bakin?"
Kawar da kanta tayi gefe bata daina zunto bakin ba, yatsunshi biyu yasa ya jawo leb'en ya murd'e sosai yana fad'in "Ni kike turowa bakin Jamila, saboda na miki magana kisa hijab shine zaki zage ni."
Bud'a idonta tayi da sukayi jawur dasu hawaye suka zubo mata ta kalleshi tace "Wallahi yah ni ban zage ka ba."
Sakin leb'en nata yayi yace "To me kikayi kenan? Meye marabar wannan da kika min da zagi?"
Jin ya saki bakin nata yasa taja baya tace "Kayi hak'uri to."
Juyawa ta sakeyi ta shige har saida ya daina ganinta kad'ai ya koma waje, Amar kuma na zuwa Hajia tace "Ka kira min yaran nan kaji ina suke?"
Da kallo ya bita yace "Wane yara kuma?"
Fuskarta a sake tace "Su Amna mana, har yanzu fa basu dawo daga makaranta ba, kira min su kaji uban me ya tsayar dasu, naga alama yaran nan suna nema su zamar min yan iska."
Cikin rashin jin dad'i ya soma danna wayarshi, da sauri tace "Ka kira lambar Hamna, dan ita ce fitsararriyar cikinsu, duk yanda akayi ita ce zata ja yer uwar koma ina suka tafi."
Danna kiran lambar Hamna yayi amma tana ta k'ara ba'a d'aga ba, dan Ummy data ga wayar ma b'oye mata tayi har ta dawo, dole ya kira Amna amma Hamna na ganin kiran tace mata "Kinga idan kin d'aga kice gamu nan kan hanyar zuwa gida, dan na tabbata Hajia ce zata saka shi ya kira mu, kuma nasan ni zata d'orawa laifin ta min tijara, gwara idan mun koma ayi duk wacce za ayi."
Hadiza dai dariya tayi inda Amna ta d'aga ta kuma fad'a mishi duk abinda ta fad'a mata, kasancewarshi ba mai son jan magana ba yasa ya kashe wayar ya kalli Hajia yace " Suna zuwa yanzu, sun tsaya bitar jarabawarsu ne ta gobe kasancewar lissafi zasuyi."
Yana fad'a ya juya zai fita tace "Shalele ka jira yanzu za'a kawo muku abinci."
Uhum bai ce mata ba ya fice, Hadiza data saka su Hamna gaba suna tattaunawa irin na mahaifiya da 'ya'ya, umartarsu tayi da su shirya tunda anyi sallah, haka kuwa akayi suna gama shiryawa Ammar ya shigo tare da Shu'aibu, sallama sukayi cike da kewar juna suka d'auki hanyar komawa gida, yanzun ma Amna ce gaba sai Hamna a baya, yanzu ma cikin mintin da bai gaza ashirin da wani abu ba suka iso saboda yana gudu sosai.
D'akinsu suka wuce ba tare da kowa ya lura da su ba suka shiga shiryawa suma, yamma tayi sosai suka gama suka fito, lokacin ne akasan da zuwansu gidan, Ummy har d'aki ta shiga da Hamna ta k'ara duba lafiyar jikinta, ana sallah magrib Hajia ta hangesu farfajiyar gida suna d'aukar hotuna tare dasu Umaimah da Jamila, k'anwar Jamila mai bi mata *Nazeefa* ta turo ta kira su inda ta e su sameta a d'akin ta, dukansu babu wanda jikinshi baiyi sanyi ba tare da tsoron abinda zai faru suka nufi d'akin nata.
A tak'aice dai fad'a da masifa da bala'i babu wanda basu gani ba, saida tayi ikrarin idan haka ta sake faruwa to su kuka da kansu, suna fitowa suka ci gaba da harkokinsu kamar kowa tunda dama sun saba da irin wannan tijarar, anyi sallah isha'i ana ta shirin tarban amarya Ammar ya shigo falon Hajia, duk da kowa na hada hadar gabanshi amma ganin Ammar da wasu manyan kwalaye har biyu yasa kowa ya tsaya dan kashe k'wark'watar idonshi, gaban Hajia wacce ke zaune cikin manyan tsofaffin mata k'awayenta ya diresu, juyawa yayi ya fita bayan wani lokaci kuma sai gashi da manyan salkar goro ha guda biyu ita ma, ajewa yayi gabanta kafin ya kalli idonta yasa hannu aljihun wando ya fito da babbar enveloppe, mik'a mata yayi tare da fad'in "Hajiar mu ga lefena na kawo, ga kud'i na tambaya da gaishe da iyaye da duk wata bidi'a, sadakin kuma sai ranar d'aurin aure Alhaji Hassan zai biya."
Hajia data saki baki tana kallonshi d'ora k'afad'aya kan d'aya tayi ta kalli Sa'ada dake zaune gefe ko kallonshi ba tayi tace "D'an ki ya rasa yan uwan da zasu kawo mishi kayan ne? Ko kuma dai rashin kunyar tashi ce ta motsa? Shiyasa ya kawo kayan da kanshi saboda ya nuna mana shi kangararre ne."
Kallonta Sa'ada tayi cikin taushin murya tace "Hajia kema kinsan halinshi ai, yana so ya nuna rashin kunyarshi a fili ne, sannan ya nuna babu wanda ya isa dashi."
Shi ma bai juya ya kalli Ummy ba yace "Banga abun rashin kunya ba anan, k'anwata ce zan aura da muke gida d'aya, saboda kawai na ragewa mutane wahala sai ya zama fitsara?"
Enveloppe d'in daya mik'a mata ta karb'a ta jinjinata tana kallonshi tace "Da alama kud'in dayawa, ai banyi tsammanin zakayi k'ok'ari haka ba."
Murmushin nan dai ya mata wanda yake mata idan zai b'arkota yace "Hajiata kenan, Amna fa kika bani, tunda kika ga nayi wannan k'ok'arin kisan da cewa ni kad'ai naga abinda na gani."
Ita kanta Hajiar wani wawan murmushi ta masa tace "Allah ko marar kunya? Kenan dai jikar tawa tayi ko?"
Wannan karan har saida sautin murmushin ya fito kafin yace "Sosai ma, ai ko baki bita da gyara ba nasan zan huta da kayana."
Wata dattijuwa ce gefe Hajia tace "Kai fice mana a wurin nan bama son surutun nan na kwankwatsar kwalabe."
Dariya suka saka mata inda shi kuma yace "Tsohe ikon Allah, to ku da kun riga kunci naku zamanin, kuma fa kinsan ance kamar *kumbo* kamar *katanta*."
Tshohuwar a zuciyarta ta amsa masa da "Tabbas, yanda kayi gadonta wajen kyau da zubin hallita, haka kayi gadon rashin kunyarta da sako zance."
Kallonshi Hajia tayi tace "Ina fatan dai uwarka ta fad'a muku irin hidimar dake gabanku? Dan kamar yanda na fad'a ne dole za ayi aure irin auren buzuwa."
Hannayenshi ya zuba aljihu yana mamakin yanda ko gaban idon mahaifiyarshi ko bayan idonta ba zata iya cewa mahaifiyarka ko mamanka ba sai dai uwaka, juyawa yayi zai fita yana fad'in "Zanyi komai akan zab'inki ai a shirye nake."
Cikin d'an d'aga murya tace "Kace ubanka ne zai biya sadakin? A wane dalili ne kai ba zaka biya ba?"
Ba tare daya tsaya ba bare ya juyo yace "Saboda shi za'a haifawa jikan."
Ummy ce ta d'aga kai ta bi k'eyar shi da kallo tana jinjina wannan al'amari na d'an nata, kamar ba shine jiya yayi wa yarinya fyad'e a cikin gidan nan ba, kai dole ma su b'oye wannan sirri ita da Hamna, dan ko sun fito dashi shi dai babu ruwa a idonshi bare yaji kunya ko nadama, zai ma iya fassarawa mutane yanda al'amarin ya kasance kad'an ne daga cikin aikinshi, Hajia kuma ko a jikinta sai jawo akwatinan da tayi aka bud'e, sam babu wanda yayi tsammanin da kaya a cikinsu duba da yanda shi kanshi ya d'auko su ya shigo da su, amma abun al'ajabi dukansu guda goma sha hud'u cike suke da kaya masu yawa da kyau, ga kuma goro da kud'i har million biyu rigis, Hajia kam ya birgeta a karon farko na rayuwarta, nan aka manta da jiran amarya ake anata duba kayan nan wasu na d'auka hoto, isowar motocin da suka tafi d'aukar amarya ne yasa Hajia kallon Sa'ada tace "Ki shiga da kayan d'akinki ki ajiye."
"To." Ta fad'a tana mik'ewa ta d'auki kayan tare da taimakon k'awayen ta ita ma da suka zo tausar k'irji.
*Alhamdulillah*
09/09/2020 à 17:58 - Ummulkhairi: